KUNCIN ZUCI

Kuncin zuci

by @bintuuu

Mami tace "Aikine yadan riqe Yayan naku, amma Abban ku zai taho gobe daga Toronto" sai Nafisa ta ciro wayanta daga jaka tace "Let me call him, ya mana alkawarin zuwa fa" Na'ima tace "Eh fa" Al'ameen ya kalli Mami yace "Mami nidai zan koma, ba ta mu suke ba" sai Na'ima tayi saurin qarasawa garesa tace "Haba dai, munyi murna sosai mana, kawo jakan naka in riqe maka" Mami tayi murmushi tana kallon Na'ima, aranta tanajin dadin ganin yanzu tafara zama lively ba kaman da ba, Al'ameen na murmushi yace "Wasa fa nakeyi Anty, ki bari zan riqe" da haka Mami ta riqo hannun su jafar tace su tafi mota, har sannan Nafisa tanata trying line din Faruk baya tafiya, suna isa gurin motan Al'ameen yace "Ya Ahmad yana qasarnan ne, wannan kamar irin rides dinsa" Mami dake kallon motan tace "Nafisa motan waye wannan, ina naku?" Nafisa da ta zagaya dayan side din motan tace "Na Yaya Ahmad ne Mami, tamu tana can Oxford" sai Mami ta gyada kai tace "Toh muje" sai ta juya gurin boys din tace "Al'ameen yi sauri ku saka kayannan da Allah, inason mu qarasa in huta, tsk zaman jirgi ko cin rai" su Na'ima na dan dariya suka shiga, sai da Al'ameen da Abu suka gama saka kayan a boot sannan suka shiga gaban motan suma, dan this time Al'ameen ne ya karbi driving din, suna kan hanyar tafiya Mami tace su kaita masauqi tukunna sai ta huta zasuje gidan Anty Amnahn, wani babban Hotel suka kama dan Abba bashida gida a England sai Canada, har 'yan'uwansa su Baba da Daddy ma haka kasancewan familyn sun rayu a Canada sosai sai ya zamto kowannensu yanada gidan kansa acan, babban daki su Mami suka kama harda falo aciki amma su Al'ameen sun kama nasu daban kusada na Mamin dan washegari zasu wuce Oxford kasancewan a kwana na biyun ne ceremony din, Mami ta sa sun taho da wurin ne dan taga kintsawan yaran nata tukunna, anan falon suka zauna dama tun shigowansu Nafisa tayi ordern abinci, madadin su ci a dining area dake falon sai suka zauna nan qasa kan babban carpet dukansu sunacin abincin, sai da suka gama suka tattare wajen , Nafisa na kurban Apple juice tace "Mami kun taho mana da gyadan da Lantana tace zata mana?" Al'ameen yace "Har nima tamin na tafiya" Nafisa ta hararesa tace "Ba dai acikin namu ka diba ba ko?" Abu yana dan dariya yace "Kema kinsan sai mun debi rabonm ai" ai nan suka hau musun da suka saba Mami na jinsu ko ta kulasu sai ta kalli Na'ima dake zaune gefenta dan twins sun samu su Al'ameen kuma, hannu ta kai taja dankwalin Na'iman tace "Habibiti ya baki gyara gashin naki ba, bakuje salon bane?" Na'ima tace "Dama mukace sai gobe zamuyi in munje Oxford" sai Mami ta gyada kai tace "Ga kayan naku da zaku saka din can a jaka, in kun huta sai ku duba" Na'ima tace "Mungode Mami" murmushi Mami tayi sannan tace "Ya rayuwan makarantan, babu wani matsala dai ko?" ta amsa da "Babu komai Mami" sai Nafisa ta kalli Mami tace "Mami wai su Mamma zasuzo yau suma?" tace "In sha Allah, can gidan Ahmad zasu sauqa tace min, zuwa anjima kuje ku gaisheta, saboda ku tazo itama"...
Kafin Mami suje gidan Anty Amnah sai ga ta bayan magrib ta faka motanta a bakin hotel din kuwa, da fara'anta suka yi hug da Mami da ta shigo falon, nan suka fara gaisuwan yaushe gamo, saida suka gama gaisuwan tace "Su Mamma ma sun iso munyi waya" Mami tace "Yanzu nagama waya da ita fa" sai Anty Amnah tace "In Allah ya kaimu goben zanje suma mu gaisa yanzu asibiti zan wuce" Nafisa tace "Anty ki bar twins su kwana anan toh" tace "Gaku gasu ai ina zan kaisu" aikuwa jafar ya hau tsallen murna Na'ima na dariya, bayan tafiyanta sai Mami tace su shirya sai su kira su Al'ameen suje can gidan Ahmad din tare itama tanason tayi bacci tukunna, ahanya Nafisa tace su tsaya su sayi donuts da ice cream, aikuwa da ciye ciyen nan suka isa gidan Ahmad din, bayan sunyi parking a gefen motocinsa na gidan sai suka fito Al'ameen da Nafisa na gaba da twins while Na'ima da Abu na biye dasu, shigansu falon suka samu Mamma da Anty Fatima zaune a kujera, Husna da fitowanta daga kitchen kenan hannunta riqe da tea flask tayi tsallen murna ta nufi Nafisa dake tahowa da murnan itama, Anty Fatima tace "Husna in kika zubar da tea dinnan zaki gamu da Yaya kinsani" Mamma na murmushi tace "Lale lale yan makaranta" da Nafisa ta sake Husna sai ta nufi Mamma da ta bude mata hannu, Husna ta qarasa gurin Na'ima tana fadin "Sis inata cigiyanki, kwana dayawa" Na'ima na murmushin sukayi side hug sannan suka qarasa cikin falon dukansu, Mamma ta kalli Na'ima dake duqar da kai tana murmushi tace "Na'ima ko?" sai ta gyada kai ta amsa da "Eh" ahankali, Mamma tace "Qaraso mu gaisa daughter, ya makaranta, kun gama lafiya?" sai ta miqe ta nufi dayan gefen Mamman tana sunkui da kai Anty Fatima na kallonta tana murmushi, nan aka hau gaisuwan yaushe gamo, Anty Fatima na kallon Na'iman tace "A qasar nan kike kema" kafin Na'ima ta amsa Mamma tace "Yarinyar Mami ce itama, yar nijar ce" Husna ma tace "Baki hadu da ita a bikin salma bane sis?" Anty Fatima ta dan girgiza kai sai kuma tace "Laa ko kece wadda kika riqe min hamra lokacin" sai Na'ima ta gyada kai tana murmushin, Anty Fatima tace "Ayya kiyi hakuri ban ganeki bane" ta amsa da "Bakomai" tana ganin yanda duk suke kama da Ahmad a fuska, sunanan zaune Ahmad ya fara sauqowa daga stairs cikin shirin white Tshirt da black jean trouser, mutan falon suka daga kai suna kallonsa banda Na'ima, dan turarensa ta jiyo tasan shine, a sannu ya iso falon ya nemi guri a kujera ya zauna sai duk qannen nashi suka hau gaishesa dan yana dawowa daga office ya gaisa da Mamma ya wuce dakinsa a sama sai yanzu ya sauqo, acikin chorus din gaisuwan Na'ima ta gaishesa itama amma bata kallesa, bayan ya amsa sai ya miqo hannu asu Al'ameen sukayi musabaha, nan Husna tayi serving dinsa tea ta miqo masa yana magana sama sama da Mamma ya karba, dan kishingida yayi jikin kujeran tareda crossing kafa yana kurban shayin suna dan hira sama sama, duk wannan abun yana lura da yanda Na'iman taqi kallon gefensa, har sannan tana gefen Mamma a zaune duk jin ta take a taqure, acikin hiran Husna tace da Nafisa "Nafee kuma a Oxford din kuke zama ko nan gidan Anty Amnah?" Nafisa tace "Bamufi two months da dawowa nan din ba fa" sai Husna ta gyada kai tana kallon Ahmad ta nuna masa Na'ima tace "Yaya ka ganeta kuwa, kawar Nafisa da sukaje gidan mu kwanaki nace maka sunanta Na'ima" sai lokacin Na'ima ta dago kai aikuwa idonta ya fada cikin na Ahmad dake kallonta shima, gyada kai yayiwa Husna sai ya kai cup din tea bakinsa yana sipping, Na'ima tasan murmushi yake qoqarin karewa shiyasa yakai cup din bakinsa, sai itama ta maida kanta qasa murmushin na zuwa mata, Nafisa dake jin dariya na taho mata tayi saurin zuba ruwa a cup takai baki itama, har aka gama hiran kan Na'ima a duqe tana wasa da yatsunta, Mamma sai kallonta take jefi jefi nutsuwar yarinyar na kwanta mata arai, kira ne ya shigo wayan Ahmad ya miqe ya fita, bayan ya gama yana can wajen Na'ima taga shigowan message dinsa a wayanta dake gefenta, hannu takai sai ta kife wayan ta cigaba da sauraron hiran da su Al'ameen keyi da Anty Fatima, daga gefensu kuma Nafisa na qus qus da Husna suna dariya, Mamma na kallonsu itama tace "Aifah, kun hadu ko" sai Husna tace "Mamma binsu zanyi" tace "Dama duk gurinsu mukazo ai, bisu abinki" ..Da suka tashi tafiya bayan sunyi sallama da Mamma sai Anty Fatima ta rakasu wajen motan suka samu Ahmad waya kare a kunnensa yana wani wayan kuma, kashe wayan yayi ya qaraso gurinsu yayin da suke shiga motan, Husna tace "Yaya tare zan koma dasu" ya gyada kai tareda cewa "Adawo lafiya" yana kallon Na'ima da ke cikin motan, sai sannan ta dago kai ta kallesa cikin ido, shima yana kallonta yaga ta masa murmushin ta me sanyi, samun kansa yayi da maida mata murmushin bai dena kallonta ba har suka tada motan....
Washegari suna cikin shiryawa zasu je gidan Anty Amnah daganan su wuce oxford sai ga kiran Faruk ya shigo wayan Nafisa, bayan sun gaisa yace mata ya iso yana Airport, sai Mami tace suje su daukosa in yaso zata tafi gidan Anty Amnah tareda su Al'ameen sai su samesu acan, hakan kuwa akayi su ukun suka tafi dauko sa suna isa arrivals suka gansa tsaye rataye da qaramar jaka a bayansa, yana hangosu ya maida wayansa aljihun jacket ya nufosu yana murmushi, Nafisa ce ta fara qarasawa garesa sai Husna suka masa side hug cikin fara'a, Na'ima da ta qaraso tana murmushi takai hannu zata karbi jakan nashi sai yace "Ki barshi Habibti" bata bari ba saida ta karba suka nufi motan nasu Nafisa na cewa "Ya Faruk da baka zo ba ko, in muka koma gida sai nayi sati ban kula ba" Husna na dariya tace "Har nima" bai dena murmushin ba yana kallon Na'ima yace "Habibti zata kulani ai ko" murmushi tayi tace "Suma wasa sukeyi ai" da suka qarasa shima Faruk sai da ya bi motan da kallo sai ya kalli Nafisa yace "Bai koma bane har yanzu?" sanin wa yake nufi yasata cewa "Eh Yaya"...
Da sukaje gidan Anty Amnah ma basu dau lokaci ba su Na'ima suka debo kayayyakinsu da suka hada already, su Al'ameen suka loda a motan sannan suka dau hanyar Oxford cikin mota biyu, daya wanda ke Hannun su Nafisa Al'ameen na driving while dayan na Anty Amnah Faruk yana driving, dan ita zata taho tareda dasu Ahmad dazai taho da su Mamma goben, cikin awa biyu da wasu mintuna suka isa apartment din su Na'iman, Mami na bin living room din da kallo ta kai hannu tana bude kofan dakunan nasu, anan falon sukayi sallah su Na'ima suka shiga kitchen suka dafa musu light food sannan 'yan mazan suka tafi kama nasu masauqin, sai da yamma su Na'iman suka tafi salon din suka bar Maman tasu a gidan, aikuwa da suka dawo suka samu duk wani abubuwan su da basu hada ba ta hade musu shi tsaf guri daya har ta musu girki tareda su Faruk da zasu dawo anjima suci..

Washegarin ranan tun da sassafe Husna ta fara tashinsu daga bacci wai su tashi su fara shiri, Na'ima dake jin kaman baccin kar ya qare har sannan taqi tashi dan gajiya, wayanta dake kan bedside drawer taji yayi qara alamun shigowan kira takai hannu tayi receiving tana kaiwa kunne idonta cike da bacci, Ahmad dake dayan bangaren anutse yace "Ranan gama karatu ba'a bacci Babe" sai tayi murmushi har sannan idonta a rufe cikin muryan bacci tace "Ina kwana" sai yayi shiru be amsa ba, jin shirun yasata dago wayan ta bude idanunta tana kallo ko kiran ne ya katse, ganin har sannan is on yasata maidawa kunne, ahankali ta sake cewa "Are you there?" sai taji muryansa kamar me rada yace "Your voice is doing everything to me right now" gyaran murya tafara cike da jin nauyin maganan nasa tayi murmushi, sai ya sake kwantar da murya yace "Ranan da kika zo dubani dakyar na riqe kaina.. muryanki yana samin abunda bai kamata ba a zuciya Na'eemah" batasan lokacin da tace masa "Nima haka" ba, sai ta kai hannunta baki da wuri tana dana sanin maganan kuma, daga dayan bangaren Ahmad ya gyara zama ajikin gadon nasa, cikin rada yace "Did i turn you on Na'eemah?" jin tayi shiru ya sake cewa "You always turn me on Na'eemah, Allah ya gani na kusa kaiwa geji, muna komawa gida zan sako su Baba cikin maganar mu" zuciyarta ne taji yana mata wani irin bugu tuna cewa watarana zata iya zama matar Ahmad su rayu tare, and he'll get to do things to her, meyasa take jin shauqin tuna hakan ba kamar yanda ta tsani touches din Bilal ba, meyasa zuciyarta ta fara rage kunya akan Ahmad ne?...Jin shirun ta har sannan yasa Ahmad cewa "Babe" sai sannan tace "Uhm" yace "Anjima in munzo ki kulani kinji? dan in bakiyi ba bansan me zan iyayi agaban Mamma ba" tana murmushi tace "Me zance toh" kafin yayi magana sukaji Husna da ta fito daga toilet tana cewa "Wai bazaku tashi bane" ta qaraso tana jan eye mask din Nafisa dake kwance gefen Na'ima tana bacci hani'an, dan dariya Na'ima ta fara ganin Nafisa ta tashi a birkice cikin baccin, Ahmad yace "Da me hayaniyan nan kuka kwana?" Na'ima na dan dariya tace "Batada hayaniya fa" sai yayi murmushi yace "Call me to save you duk lokacin da kika gane halinta" wani dariyan ta sake yi sukayi sallama, Nafisa na gyara zama akan gadon tace "Gaskiya yau in muka dawo gurin Mami zaki kwana Husna, dan kina daukan al'hakin mu da safen nan" Husna na dariya tace "Kece dai baki tashi ba amma Na'ima har da boyfriend dinta tayi waya" sai Nafisa ta juya suka hada ido da Na'ima, gyara zama tayi tana facing Na'iman cikin murmushi tace "Inye, shi boyfriend din har ya kira da safiyar nan" sai Na'ima ta harareta tanajin dariya na zuwa mata, Husna na kallon Na'iman tace "Ni kuwa zan so inga boyfriend dinki Na'ima, amma shima baya magana sosai kamar ki" sai Nafisa ta kwashe da dariya tana kallon Husna dake kallonta cikin confusion, sai ta sake juyawa tana kallon Na'iman tace "Bobo ki bata amsa mana" sai kawai Na'ima tafara qoqarin miqewa daga gadon, Nafisa na murmushi ta kalli Husna tace "Banza toh da Yaya Ahmad take wayan, You dummy...jiya har da reintroducing dinta a gurinsa" hangame baki Husna tayi tana bin Na'iman da kallon mamaki, Na'ima bata yarda sun hada ido ba ta nufi toilet dan tayi wanka, saida ta rufe door din Husna ta kalli Nafisa tace "Amma Nafisa ke munafukace" kwantawa a gadon Nafee tayi tana babbaka dariya tace "Ba nace sai kinzo zan fada miki ba, toh Yayan mu dai ya rigaki haduwa da Na'ima ma" Husna ta ware ido tace "Goodness, Bobo wai dan Allah da gaske kike?" Nafisa ta gyada kai har sannan bata bar murmushi, sai Husna takai mata duka a cinya tace "Amma ke muguwa ce Nafee, maimakon tun farko ki tareni" sai Nafisa tace "Toh in banga kinyi kwafsin ba ta ya zansha dariyan" aikuwa sai Husna ta hau kai mata dukan wasa tana tarewa da hannu suna dariya dukansu...Da Na'ima ta fito daga wankan tana gyara gashinta sai Husna ta rinqa kallonta admiringly, aranta tana ayyana "Toh ya sukeyin wannan soyayya" dan a iya saninta Yayan nasu maganan bakinsa aiki ce balle kuma ya hadu da mace me shiru irin Na'ima, amma har ranta taji dadin wannan lamarin, abu ne wanda dama take son faruwansa sai Allah ya riga ya hada abunsa.....

Tsaye suke bakin Convocation Hall din makarantar, mutane sai shiga suke amma su Na'ima sun gagara shiga suna jiran isowan Abbansu, Mami dake tsaye takai hannun tana gyarawa Nafisa hulan graduation gown dinta da ya karkace, tace "Baby inaga traffic ne ya riqesa, but i'm sure he's on his way" sai Nafisa ta kalli Mami a shagwabe tace "He promised fa Mami" Husna na shafa bayanta tace "Zaizo dai Bobo" Na'ima ma sai raba idanu take tana jiran taga ta inda zai bullo, su Faruk ma suna dan nesa dasu waya akare kunnansa da alamun waya yake da Abban, aikuwa ko minti biyar basuyi ba suka hangosa yana tahowa da saurinsa cikin manyan kaya, Nafisa har hulanta na faduwa gurin tarosa tana fadin "Abba naa" Na'ima dasu Abu sukabi bayanta da gudu gudunsu, hugging Abban nasu sukayi kamar zasu kadashi yana dan dariya, Na'ima da ke tsaye gabansa yakai hannu ya shafa kanta yace "Congratulations daughter" ta amsa da "Thank you Abba" su Ahmad da Mamma ma sai lokacin suka shigo premises din, wannan karon har da Mami duk aka qarasa wajensu tana musu maraba sannan suka dunguma Hall din gabadayansu, dan matsowa Ahmad yayi suka jera da Na'ima ya dan rada mata "Congratulations Babe" tana murmushi tace "Thank you" sai ta koma gefen Mami dake tafiya tare da Mamma suna magana, hada ido tayi da Faruk dake kallonsu tun dazun sai tayi sauri kauda kai bata bar murmushin ba....
Hall din danqam ya cika da jama'a kowa da familynsa wasu suna upstairs a zazzaune wasu kuma a nan downstairs, set din graduands din suma suna zazzaune a kujeru a nasu fannin da ake ware musu na musamman, Na'ima da Nafisa suna zaune kusa da juna cikin gown din su da hula, kafin afara qaddamar da taron Na'ima ta radawa Nafisa "Bari naje restroom yanzu zan dawo" sai Nafee ta gyada kai tana bata gurin da zata wuce, hango su Mami Na'iman tayi suna zaune cikin jama'an suma, sai Mami ta daga mata hannu alaman ina zataje, tayi nuni da hanyan fita sannan ta fice da sauri Ahmad na bin ta kallo, da saurinta ta tafi female restroom din, tana shiga ta wuce toilet yin uzurin da ya dameta, sai da ta gama komai ta bude kofan fitan kenan ta kusa cin karo da Bilal dake tsaye bakin kofan yana kallonta, yanda zuciyanta ya buga sai da tayi baya kadan, yana kallonta yace "So..wani makarantan kika gudo yi qasar nan kenan" duk yanda Na'ima kejin zuciyarta sai ta dake ta wuce ta gefensa yabita da kallon mamaki, bakin tap na sink din restroom din ta qarasa ta fara wanke fuskanta bata ce masa qala ba, da ta gama sai ta juya da dauki gown din ta datayi hanging kafin tashiga toilet din tasaka, tana kokarin fita ya tsaya a gabanta yana kallonta har sannan yana mamakin sabon halin nata, daga kai tayi tana kallonsa, coldly tace "Ka bani hanya zan wuce" sai yayi murmushi gefen baki bai dena kallontan ba, shi sai yanzu yake ganin gogewar da komai nata yayi ma, sai yace "Na'ima ni kike fadawa haka kina kallon idona?" sai ta dunqule hannunta dayake shaking ta boyeshi cikin gown dinta, sannan ta sake cewa "Bilal kabani hanya in wuce ko in maka ihu" Mari yakai mata fuska tayi baya tana dafe gurin sai kuma ya nufeta da sauri yace "Shit....I'm sorry Na'ima, i'm sorry, wallahi ke kike sa wa nake kai hannu jikinki, i didn't mean to".....