1
by @asmybaliyu
By
Asmy b Aliyu
#January2026
#Hausa novel
#Family /crises
#Love/sacrifice
#Love /Grade
Manya -manyan motoci ne na alfarma kirar ( bugatti Mistral )guda biyar suka jero cikin unguwar (g r a) dake jahar bauchi.
tsadaddiyar unguwa ce cikin jeren gidajen masu kudi kosasshin ya'n siyasa manya-manyan ya'n kasuwa na Nigeria da wajen ta waya'ndda ake damawa dasu.
Kai tsaye wani katon gida naga sunyi parking tsayawa ,tsara gaban gidan zai daukeni tsayin mintuna biyar ban gama ba.yana da bakin rufi na zamani kalan rufin gidan da get din gidan duka baki ne. Haka a gaban gidan anyi wani irin Rubutu da farin fenti Mai dauke da sunan ( Yusuf mai keke Estate) horn aka danna,
Da sauri maigadi ya wangale katotuwar kofar gidan Kai tsaye motocin suka soma shigowa cikin harabar gidan wani bangare daban suka dosa inda aka kafa manya-manyan Rumfuna dan adana motoci kawai.
Wanda a kalla mota Zata Kai kwara goma a gurin ,tsawon mintuna biyu da tsayuwar motar ,da sauri wasu irin mutane suka fito daya daga cikin motocin da aka parker.wasu irin mutane masu wata irin kira ,wandda bature ke kira da( body guard).
A kalla zasu kai mutum biyar cikin sassarfa suka nufi wata motar .gefen barin dama dayan yasa hannu ya bude marfin motar .
Wani hadadden guy ne naga ya fito daga cikin motar yana cikin fararen kaya sol da kuma babbar Riga ya kafa hula akan sa haka kuma ya manna bakin glass a idonsa mai duhun gaske wandda ba'a hango kwayar idanun sa rufaffun talkami ne a kafan sa .sau a gogon hannunsa wandda kudin sa yakai kimanin dubu Dari biyu da hamsin .
Kyakkyawa ne na karshe haka fari ne tas kamar balarabe yana da kirar maxa dogone mai ingirma jiki wato yana da fadeden kirji sai dan karamin gemunsa da ya aza wandda yyi matukar kayata fuskarsa , hannunsa yasa a hankali ya cire babbar Riga gamida mikawa daya daga cikin masu kula da lafiyarsa ,batareda yayi magana ba da sassarfa cikin takunsa na kasaita ya nufi entrance din shiga gidan.wanda kofarsa ke kallon gabas ..
Abdulhakeem Yusuf maikeke kenan matashin saurayi wandda bai wuce shekara talatin da biyar ba a dunia ,wandda ya'mmata da yawa ke haukan so...
Body guard din dake biye dashi yayi saurin bude kofar falon ,ya shige manya -manyan mata na hango dam acikin falon da alamar akwai wani gagarumin taron da akeyi kowace tana cikin kaya na Alfarma ...
Daya daga manyyan matan dake zaune a falon ta nufo wurinsa da fara'arta itama tana cikin shiga na alfarma ,haka gwala gwalai ne dam a ajikin ta tun daga kan Sarka ya'n kunne xuwa a warwaro.
Sannu da zuwa my son!
Ta fada cike da Tsantsan farin ciki haka ta amshi babbar Rigarsa dake hannun body guard din ya russuna ya bata cike da girmamawa , daya daga cikin kujorun dake babban falon na Alfarma mum ta samu ta xaunar da dan nata.
Gaba daya falon ya hau ihu ana masa kirari yehhhhhhh! Ango ! Ango! Ango kasha Mai. Ahankali ya xare gilashin idonsa subhanalillahi ! Nan na kara tabbatar da kyawun Abdulhakeem wasu irin idanu garesa masu ban Sha'awa wandda bako wace hallitta keda irin suba. Wandda bature ke kira da (blue eyes) yana da Zara -zaran gashin ido haka yana da yalwar gira sosai wacce ta kusa hadewa ,Amma tayi masa masifar kyau.
A tsakkiyar goshinsa yana da tabon sallah wandda ya kara kayata fuskarsa haka tun daga saman bakinsa zuwa kasan sa gashine kwance baki wuluk sai kasan habar bakinsa Inda ya aza karamin gashi haka ya masa kyau sosai saboda dan tsayin da yayi ,hancinsa mikakke har baka haka kanshi akwai tarin suma.
Mum ta kalli dan nata a karo na biyu ,ta sassauta murya haba Adulhakeem meye haka??"
Dan saki fuskar mana ranar farin ciki kowa na murna kai kuma ka hade fuska kamar an aiko maka da sakon mutuwa."
Murmushi kadan yayi wandda ya bayyana fararen hakoransa farare tas ,mum nagaji ne shiyasa yanxu ma haka ina son naje na huta.
Abincika fa?.."
Tukuna mum sai xuwa anjima su sagir fa?".. Suna tareda friends din jawaheer ko suna magana akan yadda xasu tsara dinner da xasuyi."
Ya dan tabe baki nidai na fadamasu baxan jeba mum ya karasa xance gamida mikewa tsaye ,cikin fushi mum din ta Mike tsaye me kake nufi Abdulhakeem."
Meye abun fushi mum?? Ya fada cikin sanyi muryarsa nifa tun farko na fada masu baxan jeba ! So please mum karki tilasta ni akan abunda xa'a xo a samu matsala."Ya fada sounding so very cool ,
"Auren da kike so an daura so pls excuse me...anan yabar mum bude da baki tana ganin yadda mutane ke binta da kallo,
Tana jin wani abu mai nauyi na danne mata zuciya.
Anan ya wuceta ,ya nufi wani bangare mutane sai tsokanar sa suke yi
bai kulasu ba burinsa Kawai a wannan lokacin yaje yaga kakarsa ya shiga ajikinta ko xaiji sauqin abunda yakeji a xuciyarsa..
wani hadadden part naga AY mai keke ya nufa katon gaske haka xakayi mamaki idan akace duk fadin wannan part din macce daya ke rayuwa acikinsa ,wato Hajia Asma'u mai kimanin shekara 70 a dunia tsohuwa mai ran karfe mai halin dattako ,duk da kasan cewar ita kadai ke rayuwa acikin part din haka yasa aka zuba mata ya'n aiki mata zalla kwara biyar masu hidima a gareta .
Da sallamarsa ya shiga kayatattacen falon Wanda aka kawata da kayan zamani ,ba kajin komai sautin komai a katafaren falon sai karar Ac.ga masu aiki nan birjik
Sai kai da kawo sukeyi .yayi mamakin da bai samu hajja a wannan falon ba dan yasan anan ne gurin xaman ta
kai tsaye dayan falon ya nufa gabansa sai da ya buga hada ido da yayi da hajja a wannan lokacin sai ya'yanta da suke xaune a gefenta ganinsa yasa sukayi shiru da tattaunawar da sukeyi ,haka suka xuba masa ido sabanin kakar tasa da bata kalli ko inda yake ba balan tana tasan akwai halittar sa...
Kanwar mahaifinsa kurum CE tayi karfin halin fadin karaso daga ciki abdul wato aunty salma.
Har an daura auren kenan?" Ta tambayesa gamida tsaresa da ido kuttttt! Ya hade wasu yawu masu dacin gaske.
Karka kuskura ka karaso min cikin falo ,cewar hajja ka koma gurin matar da tafimu daraja matar da ka fifitata akanmu
cikin bada umurni hajja ke maganar fuskarta babu alamr fara'a wani irin tashin hankali ya shiga tunda yake da hajja bata taba fushi dashi irin haka ba ,tun kuwa tasowar sa har girman sa rau rau yayi da ido ya kara kallonta idanunsa cike da kwallah .
Da sassarfa ya isa gareta ya kankameta ajikinsa tamkar zai shige ciki ya Dora Kansa a bayanta haka hajja ta dinga jin bugun xuciyar jikan nata.
Na tuba hajja
Nabi Allah ki yafemun Dan Allah fushin ki na azabtar dani ,nikaina bansan meyasa bana iya yiwa mum musuba " Aure anriga an daura addu'arki nake bukata."
Kinfi kowa sanin bana kaunar jawaheer !!.
Hasali ma ban taba sonta ba! Na yiwa mum biyayya kurum ne kasancewar ta uwa a gareni matar Uba" haka hajja ta dinga jin saukar hawayen sa a bayanta.
Da kyar aunty salma ta samu ta janye Abdulhakeem daga jikin hajja ta xaunar dashi daya daga cikin kujorun dage xagaye a falon saukar hannun hajja yaji akan fuskarsa nasa hawayen idonsa ta shiga goge masa .
Granny!
Saurin dakatar dashi tayi karka ce komai a hankali hajja ta kalli aunty salma ."salma a hada masa lunch da alamar babu komai acikinsa .
Haka aka cika gabansa da cima kala-kala tareda axa masa katuwar darduma tsakiyar falon sauko na ciyar dakai Abdul cewar hajja ta fada tana kallon AY cike da so .
Babu musu ya rarrafo gurin hajja ya xauna tamkar yaro karami ,takun tafiya sukaji cikin falon kwas !!kwas!!
Cikin wani irin sauti gaba dayansu suka maida hankalinsu inda su kejin sautin.
Ido biyu yayi daita cikin wani tattausan lace mai tsada fuskarta tasha make up
Kallo daya zakayi mata kaga amarya ..babu laifi tana da kyau na ban mamaki..
Kai tsaye ta tunkaresu da sauri hajja ta dauke kanta itakam Allah ya gani bata son jawaheer da jikanta . nan ina tarbiya take??"
Wannan rashin tarbiya har ina ace amarya ta biyo ango har gidan su."
Barka da gida hajja
jawaheer tayi saurin katse ma hajja tunani tareda yin masauki daya daga cikin kujorun dake xagaye da falon kannen mahaifinsa kuwa ko kallonsu batayi ba Aunty salma da Aunty sadiya sai sakon harara suke aika mata Allah ya gani basa son jawaheer da Abdulhakeem
Baby I want to speak with you in Private."ta fada da wata irin murya mai dauke da tsantsar kissa ,
Not now jawaheer!!"
Muyi magana xuwa anjima,
maganar yana da muhimmanci daman stop it !
Bana son ji please ki fita
Ya fada Yana kallon cikin fuskarta,kallon da AY yake mata a wannan lokacin irin kallon raini ne irin kallon da tayi kadan ta juya sa ,Sai taji duk ta mu zanta a gaban small mum's dinsa Wanda ko gaishesu batayi ba.
A fusa ce jawaheer tabar part din na hajja cikin wani irin fushi...
#ASMY B ALIYU
#LOVESTORY2026
#AY MAI KEKE
#JAWAHEER
#HAWAYEN MARAICI