BLOOD CROWN (THE HEIRS APPARENT)
PAGE _______7 & 8
by @swrites22
Zaune suke gabaɗayan su a dinning suna breakfast dad, Mumu, Nayrah da kuma kannen ta uku Nashwa, da majeed sai kuma Nashmi. "Nashwa ya jikin naki?".......Dad ya tambaya yana kai Mug bakin sa.
"Naji sauƙi dad Alhamdulillah".........." Masha ALLAH, ALLAH ya ƙara sauƙi, amma in kinji zazzaɓin ya dawo kuje asibiti".
"In sha ALLAH dad"..........kallon Mumu yayi da faɗin, "to Hajiya Latifa ni zan fita ba wata Matsala ko?"......... tissue ta ɗauka ta goge bakin ta sannan ta ce, " Akwai abu ɗaya, batun Farshad gata nan ka faɗa mata da bakin ka saboda ni ta raina ni, ban isa nayi magana ɗaya ba saita maida min goma".
Rufe Nayrah da faɗa dad yayi kamar zai haɗiye ta ɗanya har abin yaso ban mamaki, cikin zafin rai ya ce, " kin san dai abinda ya faru dangane da wancan baragurbin da kika kawo mana dalilin jajiɓe jajiɓan ku na tsiya, sannan na riga na muku iyaka ke da shi kuma batun baikon ma yanzu babu shi na warware. Akwai yaron Aboki na Farshad, kuma na riga nayi magana da mahaifin sa na kuma bashi auranki saboda bana ma so aja Lokaci, zaizo ku gaisa sauran naji wani abu marar daɗi sai na mugun saɓa Miki whl".
Cikin rawar murya ta ce, "Haba dad, haba dad dan ALLAH karku yiwa Amjad haka, shi ɗin bai cancanci hakan daga gare ku ba, dad nasan kai ɗin babban mutum ne kuma ka riqe muqamai da yawa, amma ka tuna halaccin Amjad a gareka ba wai ina ma gori bane, kawai ina ma tuni da baya ne, a lokacin da dukkanin abokan naka suka gujeka suka daina yi da kai saboda kawai ka samu raunin arziki ba tare da sun duba kai ɗin waye bane ada, amma shi fa ? Yana tare da mu . Dad zuciya me halacci bata manta alheri dan ALLAH dad karka rufe idanun ka ".
Mumu ce ta amshe da, "A lokacin ai bamu san ainahin ɗayar fuskar tasa ba, waya sani ma ko dan ya gan mu da yara ne yayi cinikin su ya bamu kuɗin idan ya samu sarari ya yi gaba dasu, ko kuma ke da shegen rawar kanki in ya samu dama ya ɓata Miki rayuwa ya cucemu. Kin shiga zuciyar sa kinga niyyar sa ne a lokacin da ya taimake mu? ba'a isa ayi magana ba sai kice a dinga tuna alherin sa".
"Ko ɗaya Mumu Amjad zuciya ɗaya ya taimake mu, kuma nayi mamakin yadda zantukan mutane suka samu wurin zama a zuciyar ku, whl Mumu! dad!, in kuka tsananta akan Amjad zakuji kunya, Ni nasan waye shi kuma nasan bazai taɓa aikata wa'annan abubuwan ba, kawai dai mutane ne suke son masa ƙazafi saboda shi ɗin sananne ne, ko kuma masu son yin amfani dashi su ɓatawa mahaifin sa suna, amma Gsky zatayi halinta nan bada jimawa ba".
"Ke Nayrah saurara duk wannan maganganun naki bashi zai wanke shi daga zargin laifu......."
"Kaji ko dad kai ma zargi kace".......... Ta katse shi, tashi yayi bata ankara ba ya wanke ta da mari sannan a dake ya ce. "Keee dakata min haka kinji ko, dan mun baki damar magana ba shi yake nufin zaki dinga ja in ja damu ba, har kina ikirarin zamuji kunya, akan wani banza can da baki haɗa dangi dashi ba kike fatan iyayanki suji kunya tsabar baqar zuciya, to bari kiji ko ya aikata ko bai aikata a yanzu bamu iya bashi auran ki saboda sunan sa ya riga ya ɓace a idon duniya, in kuma ɗan taimakon da ya mana ne ada a yanzu zan iya linka masa na maida masa, kuɗin ma da bamu san na halal ne ko haram ba, wawiyar banza wawiyar wofi".
Bataji zafin Marin da dad ya mata ba sai zafin maganganun da yake jifan Amjad dasu. Cikin dacin rai ta ce, "Dad sai dai kuyi hakuri ban taba qin wani abu da kuke so ba Amma in dai kuka hanani auran Amjad to whl bazan auri kowa ba, saidai ku kai gawata"......... Tana kaiwa nan ta miqe ta bar dinning ɗin da gudu tana fashewa da kuka.
"Sai dai kuwa ki mutu shashashar banza shashashar wofi, dan kin mutu zan damu ne". Dad ya faɗa cikin tsananin fushin da ya sake ɗauremin kai.
"Ka gani ko Alhaji, kana dai gani, yarinyar nan nema take tafi ƙarfin mu anya yaron nan ba asiri ya mata ba, yarinya lokaci daya ta birkice ".........….. Mumu ta faɗa tana tana nuna hanyar da Nayrah tabi da hannu. A hankali Nashwa ta ture plate ɗin abincin dake gabanta ta miqe tabi bayan Nayrah ɗin. Majeed ma miqewa yayi tare da faɗin, "Nashmi tashi mu wuce school kar muyi late, dad mu zamu wuce".
"Ku sauka lpy".........Ya faɗa har lokacin sauke numfashi yake da zafi zafi alamun akwai abinda ke cin ransa. Ba tare da Mumu ta lura da yanayin sa ba ta ce, "Alhaji yaran nan duk sun zama munafukai fa, ka duba duk sun tashi sun bar abincin saboda kawai an yiwa wannan me shegen taurin kan faɗa"..........."To laifin waye?"........ Ya tambaya a kausashe.
"ban gane laifin waye ba?"............itama ta maida masa tambayar tana zuba masa ido, kallon ta yayi na tsawon seconds kafin ya sauke ajiyar zuciya da faɗin, "laifi na ne. Bari naje sai na dawo".........kwafa taja ta bishi da kallo har ya fice sannan ta tashi ta bar dinning ɗin itama.
____________Nayrah na shiga ɗaki gaban mirror ta wuce ta tsaya tana kallon kanta yayin da hawaye ke zarya akan kumatun ta, ta dau tsawon 3 minutes kafin ta share hawayenta ta nufi inda wayar ta take ta ɗauka tare da dannawa Amjad kira, har tayi ringing ta katse bai ɗaga ba , sake kira tayi a karo na biyu saida ta kusan katsewa ya ɗaga, a lokacin fitowar sa kenan daga wanka yaga wayarsa na ta haske alamar shiga da fitar kira, dauka yayi tare da picking call ɗin yasa a handsfree sannan ya matsa gaban mirror ya ɗaura wayar. "Ya Niniyous ɗi na ta tashi?"........ Ya faɗa yana goge gashin kansa da ƙaramin farin towel ɗin dake rataye a wuyansa.
"Amour kana ina?"........... Ta tambaya in a serious tone. Tsayawa yayi da abinda yake saboda yanayin yadda yaji Muryar ta, sa hannu yayi ya ɗauki wayar da faɗin, "Meke faruwa?"........ Ajiyar zuciya ta sauke kana ta ce, "Da matsala Amour, Dad yace wai ya warware baikon mu sannan ya bada ni ga ɗan abokin sa wai Farshad".
A maimakon ta ji alamun damuwa a tattare dashi kamar yadda ita take ciki tunda wanna abun ya faru, sai taji saɓanin hakan dariya taji ya kwashe da ita, dariya yake cike da jan hankali wanda in kana sauraron sa baza ka so ya daina ba, haka in kana gabansa ne baza ka gaji da kallon sa ba, saboda yadda dariyar ta masa kyau da kuma salon da yake yin ta. Shiru tayi tana sauraron sa har ya tsagaita sannan ya ce, "To yanzu miye abun tashin hankali Ninie, ke fa Matsala ta dake kina da saurin rikicewa abu kaɗan ke firgita ki, ina kika taɓa ganin an warware baiko haka, in kin manta in tuna Miki harta sadakin ki fa na bayar kawai fatiha ce ba'a shafa ba, sannan daga sama ace Miki an warware baiko kuma ki tashi hankalin ki".
" Ka fahimceni Amour kar ka dauki abun nan wasa, whl su mumu sun watsar da duk wannan"...........ajje wayar yayi yana daukan Gris dior body creme ya ce, "Ki kwantar min da hankalin nan naki Niniyous, zanyi wani Abu a Kai Karki damu kinji "...........Shuru tayi dan hankalin ta ya rabu ne gida biyu kuma. "Baki yarda dani bane tawan?"......... Ya faɗa cikin wata irin murya me saukar da kasala.
"I tr..ust you "............Ta amsa tana sauke wasu tagwayen ajiyar zuciya.
"Sai da dai kikayi kuka ko? To na dai na cewa karkiyi kuka duk lokacin ma da kikaji kina sha'awar yin sa ki kirani nazo da bucket na tari kayana".
"Dama ai Baka damu ba, tunda abar tsokana nake zama a wurin a a maimakon ka lallashe ni".........dariya ya kyalkyale da ita kafin ya ce, "Kina da katoton aiki a gabanki kuwa, ni dake wa zai lallashi wani?".
Murmushi kawai tayi da faɗin, "ALLAH ya yafe ma amour".........." Ameen tare da Niniyous". Haka suka cigaba da hira yana shiryawa har ya gama sannan suka sallama ya dauki abubuwan da zai buqata ya fita . Dinning ya fara zuwa yayi breakfast sannan ya wuce sama, a falon farko ya same su ita da Adla, ƙarasawa yayi ciki ya zauna tare da gaishe da Anah , shi kuma Adla ta gaishe shi.
Amsawa yayi tare faɗin, " ke yau baza ki makaranta bane?"..........."bani da lectures yau yaya"........ Jinjina kansa yayi sannan ya ce, "Anah ni zan fita, dama nace barin hawo naga ko kin fito".
"To yanzu da sassafen nan ina zaka Babban mutum"....... ɗan shafa fuskar sa yayi kana ya ce, " Anah na riga na saba da fitar, in na zauna gidan takura zanyi, amma ba nisa zanyi ba".
"Ba wai bana son ka fita bane, hankalina ne baya kwanciya in Ka fita har sai naga ka dawo".
"Karki damu Anah zan biya na ɗauki su Aram ai, ba abinda zai faru in sha ALLAH".
"Shikenan amma ka kula da kanka, ALLAH kuma ya kare min kai ya maka Albarka ya kuma baka Sa'a"..........."Anah Ni fa ?"....... Adla ta faɗa tana bata fuska. Miqewa yayi tare da dungure mata kai, "Uwar gasa, Anah ni na wuce".......Ya faɗa yana daukan hanyar barin falon. "To ALLAH ya dawo da kai lpy "........ Anah ta sake faɗa.
Saida ya biya ya duba Dada sannan ya fita in da ya tarar da kamal yana jiransa. "Ina kwana boss"......... "Ka tashi lpy?". Ya tambaya yana shiga motar da kamal ɗin ya bude masa. "Alhamdulillah". Kamal ya amsa yana rufe masa ƙofar sannan ya zagaya mazaunin driver ya shiga ya tada motar yaja suka fice. Gidan sa suka nufa, suna shiga su Aram suka zagaye motar tasa fitowa yayi yana amsa gaisuwar kowanne su sannan ya wuce ciki ɗaya daga cikin su ne yabi bayan sa sai da suka shiga falon can ciki sannan ya tsaya ba tare daya juyo ba ya ce, "Philip da wani abu ne?".
Da sauri Philip da dama jira yake a bashi umarnin magana ya ce, "Yes boss, wata gagarumar nasara ce domin mun samu request daga SHADOW yana so mu masa aiki ne, duk wasu sauran details na tura ma "..........Amjad da tun lokacin da aka ambaci SHADOW ya juyo cikin wani irin slow move, murmushi yayi yana tafa hannu kana ya ce, " Weldon Weldon Philip, lalle wannan ɗin nasara ce a gare mu, yanzu zan duba komai, kaje zan neme ka in na gama"..........."Okay Boss". Philip ya faɗa yana dan rusunawa alamar girmamawa sannan ya juya ya fita.
Ɗakin ya wuce gaban wani ƙayataccen curtain da ya ƙarasa dakin kyau ya tsaya, zaro wayarsa yayi tare da yin wani danne danne sannan ya ɗago ya yaye curtain ɗin, wata computer ce ta fara magana a jikin bangon ga wata danger dake kawowa da ɗaukewa, hannunsa ya ɗaura akan danger take computerta gabaɗaya ta kawo wata greenlight tare da shatin yatsun hannunsa saida ta gama scanning din tafin hannun nasa da fingers print sannan wata kofar sirri ta buɗe ta jikin bangon, wani madaidaicin ɗaki ne ya bayyana baza ka taba cewa rana bace dan dim light ne kawai a ciki, yana shiga kofar ta rufe kamar ba a tsaga ƙofa a wurin ba, gaban wani tsararren table ya nufa da kafa yaja kujerar ya zauna, tare da danna wani abu a wayarsa wuta ya kawo a socket socket ɗin, wayan ya sake latsawa take Ac ɗin dake ɗakin suka Kunnu su ma, wayar system ɗin dake kan table ɗin ya jona jikin socket, still hankalinsa akan wayarsa har system ɗin ya gama budewa sannan ya ɗaura wayar gefen system ɗin a kan table, ya gyara zama tare da maida hankalin sa akai gabaɗaya ya fara wani aiki, sai da ya ɗau good two hours sannan ya kashe komai ya tashi yana miqe hannuwansa da suka tara jini. Wayarsa ya ɗauka ya kashe AC da wutar ɗakin sannan ya buɗe ƙofar ya fita. Gaban gadonsa ya nufa yana zuwa ya faɗa akan gadon tare da janyo pillow ya ɗaura kansa akai ya lumshe idanunsa amma ba bacci yake ba saboda ƙafarsa da yake dan jujjuyawa kaɗan kaɗan, ya ɗau tsawon lokaci a hakan dan har sai da akayi kiran sallar azahar sannan ya tashi yayi sallah.
Fitowa yayi ya wuce dinning, ɗinbin mamaki ne ya kamani ganin yadda dinning ɗin ke shaqe da manyan warmers, komai cikin tsari. Plate ya dauka da spoon ya ɗaibi abinda zai iya ci sannan ya tsiyayi juice ya koma ya zauna.
Yana kai spoon bakinsa wayar sa ta fara haske ba tare da ya daina cin abincin da yake ba ya yi picking call ɗin daga ɗaya bangaren akace, " Whl kai ba ƙaramin Kwaro bane Amjad, ka iya ƙera mota me tafiya da kanta sannan ka bar mutum da faman wahalar tuqi".
Murmushi yayi me sauti sannan ya ce, "To ai shi ne wahalalle shi wanda yake ganin shi ne matuƙin".
"Baka da kyau Sam Sam Whl, Mu kan mu tsoro kake bamu"..........lemo ya kurɓa da faɗin, "Habaaa ranka ya dade ai banda ku".
"Kai dai a bar zancen, na gama karanta saqon ka har na ma reply amma nace sai na kiraka, dan haka kaga sai anjima mayi magana".......bai ce komai ba har ya kashe wayar. Ajje wayar yayi sannan ya cigaba da cin abincin sa har wani kaɗa ƙafa yake . Yana gamawa ya koma parlour tare da kiran Philip.
"Have a seat "......... ya faɗa a lokacin da Philip ya karaso. Zama yayi kamar yadda ya bashi umarni yayin da shi kuma hankalin sa na ga wayar dake hannun sa can kuma ya ce, "Philip who do you think you can take with you to former deputy governor house Alhaji nu'uman?".........Shuru Philip yayi kafin ya ce, " I think Nazbeer".
Dan girgiza kansa yayi da faɗin, "No you are not going with Nazbeer I have got something else for him"........."But boss, what's the issue?"
Shiru yayi kamar ba zai yi magana ba yana cigaba da latsa wayar sa ya ce, "check your phone, I sent everything to you, Jan kunne ne kawai. Ina da Abubuwa da yawa a gaba na zan shiga ciki, fatan ba wata matsala ?".........."Then Danny will go with me, if that's the case".
Dan matsa yatsan hannun sa yayi har sai da yayi ƙara sannan ya ce, "Be careful, Ku San takun ku, karku bani matsala".
"Yes boss!"
"Alryt you can go".......... Ya faɗa yana kallon wani wuri kamar me tunani, har Philip ya tashi zai fice ya kira shi, "Philip!"
"Yes boss"...........Philip ya faɗa yana tsayawa tare da juyowa yana fuskantar sa.
" Call Baba Sufi and ask him to call Awaais and the rest. Tell him to tell them dada's seriously sick, he's looking for me but he couldn't reach me, and send doctor kinal. Then make sure you cut our resident's network after they arrive, and take care of the rest of the matters. karka bani matsala ka san dai komai, I've repeated myself"..........Yana gama faɗin haka ya tashi ya wuce ciki.
Bashi ya fito ba saida akayi sallar laasar, sanye yake da wani crazy blue jean da ash shirt, kafarsa sanye da sneakers na kamfanin Louis Vuitton, haka fuskarsa ya sanya wani makeken sunshades tare da noes mask sannan ya kawo wata arniyar P cap ya sanya tare da juya gaban ya koma ta bayan . Tafiya yake cikin nutsuwa har ya fito compound ɗin gidan, nan su Aram dake zazzaune suka taso suna masa Barka da fitowa, hannu kawai ya ɗaga musu ya nufi mota, da sauri suka bude masa ƙofar ya shige, kamal ya shiga mazaunin driver. Janye wa sukayi gefe dan sun san tunda bai neme su ba baya buqatar su a fitar tasa. A hankali Kamal yayi reverse tare da juya kan motar ya harba ta kan titi ba tare da yasan in da zasu ba, saida sukaje kan roundabout sannan ya ce , "Airport muka nufa"............"okay boss"......... Kamal ya Amsa.
--------------------√
Ba tare da wani tsoro ko fargaba ba a tare da ita ta dumfari majalisar su karafiya inda ta hango su suna ta yan zuqe zuqen su. Tana zuwa ta fisge wiwin dake maqale a gefen kunnen jagwa tana ci da wuta, wurgarwa tayi a kasa tare da tula mata ƙasa da kafa ta mirtsiketa sannan ta ɗago tana huci a fusace ta ce, " Wani ƙaramin tataccen ɗan iska ne a cikin ku ya daki Sahnish?"............ Ta ƙarashe tana wani mutsitsike ido. Kana kallon ta kasan bata san wani abu wai shi tsoro ba.
"Hahaha". Suka kwashe da wata irin dariya irin ta basawa kafin ɗaya daga cikin su wanda ke sake naɗa musu rizla ya ce, "Dukkan mu ne amma ni na jagoranci tawagar, ya akwai Magana ne?".
"Maganganu ma, ashe ƙaryar iskanci kuke, ina cewa ni kuke bi kuɗi, to ku tare ni mana tunda dani ta haɗoku bada shi ba, meysa zaku sanya shi cikin faɗan da ba nasa ba, to whl zaku san kunyi da yar halak sai na baku mamaki".
"Keeee bar nan kafin na Miki ɓalli ɓalli anan wurin billahillazi ".......... Karafiya ya faɗa yana miqewa riqe da wuqa a hannun sa sai langi yake shi kaɗai kamar igiyar shanya. "In naki fa ko zaka matsar Dani ne".........Ta faɗa tana juya masa manyan idanuwan nan nata masu rikitarwa. Yunkorowa yayi da faɗin, "kwarankwatsa zan bazar dake a wurin nan in bi ta Kan ruwan cikin ki in wuce".
Gyara tsayuwa tayi da faɗin, " In Ka fasa Ka raina iyayen da suka haifeka banza wawa ragowar hayaki, kuma na rantse sai kunsan dani kuke wasan, kun sanni sarai ai kunsan hali na"......... Wata zaftareriyar wuqa jagwa ya ɗauko a can gefen su tare da sara ta akan ƙasa ya ce, "ware!".......... girgiza kanta tayi da faɗin, "ALLAH ya ragewa Aya zaqin ta ba'a shirye na fito ba, amma da kai kaii dai whl baka isa ɗaga min wuqa ba, amma ku jira juyowa ta"..........Ta ƙarashe tana nuna su da yatsa sannan ta juya ta bar wurin .
"Yihuuu wa yace damu bamu ba muma muce dashi bashi ba, har akwai mai ɗaga mana yatsa a garin nan bamu gille hannun ba gabaɗaya"..........Ya ƙarashe cike da kuri. Ɗaya abokin nasu ne ya taso shi ma kamar zai kifa ya dafa kirjin jagwa ɗin da faɗin, "kwanta kwanta naman kaji, a huce haka"......... ƙoƙarin wucewa ya fara yana faɗin, "ka barni in je in qaddamar Mata zandam, mu da mukeyin gaba da gaba da maza a dawa ma bare wannan ƙaramar kwaron".
"Huce haka, barta zamuyi maganin ta kai kasan ko yanzu mun zabure ta, dan ba ƙaramar illa mukayiwa wancan yaron ba, dan haka rabu da ita in kere na yawo zabo na yawo........" Ya ƙarashe yana jan fito. Ƙwafa jagwa kana ya ce, "Amma ba dan ka hanani binta ba ko, da sai an kasa gane kamannin ta"......... Ya ƙarashe yana komawa gefen karafiya ya zauna tare da zarar kara ɗaya ya bata wuta.
Hushaima kuwa daga wurin su karafiya ba gida ta koma ba wani wuri ta nufa, sai da tayi tafiya ta tsawon minti talatin da kafarta dukda uban ranar da akeyi amma sam bataji Saboda murɗaddiyar zuciya irinta ta. Tana zuwa ta faɗa wani uncompleted building kamar wadda aka jefo, mamaki ne ya kume ni ganin wasu irin riƙaƙƙun yan daba na gaske masu ji da tashen tsageranci da tashanci, tana zuwa ta wuce ta tsakiyar su ta ɗale kan wani bulo ta zauna tana goge gumin fuskarta da bakin gyalenta.
Sai da ta ɗau tsawon minti goma a ciki sannan ta fito ta wuce gida. Tana shiga Sahnish dake kwance yana dakon jiranta, ya fara kokarin miqewa, da sauri ta ƙarasa ta taimaka masa ya zauna, cikin damuwa da kuma takaici ta ce, " Tashi Ka daure muje asibiti ".
Wani yawu me zafi ya haɗiye saboda ciwon da maqogoron sa ke masa kafin ya ce, "Baza muje asibiti ba chemist ma yayi".
"Sahnish raunin dake jikin Ka yafi ƙarfin chemist, Ka daure Ka tashi mu tafi kaji".........ta sake faɗa tana kallon sa cike da tausayawa.
"Asibiti yanzu in munje ma zaman jiran layi zamuyi, zaifi kyautuwa muje chemist ɗin dai ".
"Kai daina min musu Sahnish muna Ƙara ɓata lokaci ne ni inada abunyi, Ka tashi muje mu dawo kuma ai ba asibitin gomnati zamuje ba".
Waro idanunsa yayi kana ya buɗe baki zaiyi magana ta ce, "kar fa ka ƙara ce min komai, a tafashe nake bana so na sauke haushi na a kanka".........Bai sake yunqurin cewa komai ba ya fara ƙoƙarin miqewa ta taimaka masa ya miqe, a haka suka fito, a soron ƙofar gidan ta barshi taje ta ɗauko abun hawa, sannan suka taimaka masa ita da me tuk tuk ɗin ya shiga suka tafi.
Kamar yadda ta fada private hospital suka nufa, da taimakon me tuk tuk suka shigar dashi ciki sannan ta sallameshi ya tafi, file taje ta Buɗe masa sannan aka musu iso zuwa ɗakin likitan, bayan ya duba shi ya rubuta masa magunguna da allurar tetanus, sannan akayi dressing raunikan, aka ɗaura kashin hannun nasa da ya goce. Kallon ta likitan yayi bayan an gama ya ce, "Hatsari ya samu ne ?".
"Yan iskan unguwa ne kawai"........Ta bashi amsa dukkan hankalin ta na Kan duk wani motsi na Sahnish ɗin.
"Ashsha haka suke whl duk sunbi sun addabi mutane, ka yi magana su bi dare su datsaka kamar rake, ALLAH dai ya kare gaba. Amma saisa ake so mutum ya guji abinda zai haɗashi dasu dan in suka bugun nan cinnaku ne basu san na gida ba, kallo wannan laifi yake zama a wurin su.
"An gama ne Dr zamu iya tafiya?"........Ta tambaya dan yanda takeji zuciyarta na Ƙara hauhawa a duk kallon da zatayiwa Sahnish ɗin, shi kansa Dr ɗin maganganunsa ƙara ɓata mata rai suke, kamar ta rufe shi da duka.
"Eh zaku iya tafiya, Amma zaki dinga kawo Shi ana dressing raunikan, ga wanna in kin fita pharmacy saiki biya kuɗin ki karbi magungunan".
Karɓar takardar tayi sannan ta ƙarasa ta taimaka masa ya tashi suka fito. A reception ta zaunar dashi sannan ta wuce pharmacy tayi payment, ta fita ta Nemo tuk tuk ta dawo ta taimaka masa suka fita, tsayawa sukayi suka dauki Shazeen daga makaranta sannan suka wuce gida gabaɗaya.
Ko da suka isa gida ɗaki ta kaishi ya kwanta domin ya samu yayi bacci ya huta.
Kitchen ta shiga ta ƙarasa abincin data fara kafin shigowar Sahnish sannan ta zubawa Shazeen ta gyara gidan, dan ita ko yunwar ma bataji abinda ya dame ta ma ya ishe ta, ga yan kuɗaɗen da suka rage musu ba yawa, ga kuma jinyar Sahnish, aikin data samu kuma ba wai daga zuwa za'a fara biyanta ba dole sai tayi aiki zuwa ƙarshen wata. Wunin ranar sukuku tayi Shi har dare saida Sahnish ya tashi ne ma ta ga jikin nasa sannan ta samu ta sawa cikin ta wani abu shi ma dan Sahnish ɗin ya dame ta ne.
Yana zaune shi da shazeen a ɗakin sa Hushaima ta shigo, wuri ta nema ta zauna tare da faɗin , "Shazeen zo ki cikemin takardar nan".........Ta ƙarashe tana miqa mata Form ɗin data taho dashi tare da pen.
"Takardar miye wannan ɗin ?".......... Sahnish ya tambaya yana binta da kallo.
"Form ne na aikin da na samu a wani wurin saloon starlight beauty co., To da sukace gobe ma nazo na fara amma kuma tunda naga baka da lpy zan bari ka ɗan ji sauqi tukunna ".
Cikin farin ciki ya ce, "Kai alhamdulillah ALLAH abun godia. Kina ji baza ki fasa zuwa gobe ba, kije aikin ki dan bana so azo a samu matsala daga farawa kuma suzo su canza shawara. Kinsan a yanzu aikin yana da matukar muhimmanci a yanayin da muke ciki".
Bata bashi amsa ba har sai da ta gama faɗawa Shazeen abubuwan da zata cike dasu sannan ta ce, "to wai taya ma zan tafi na Barka kai kaɗai a gida alhalin baka jin daɗi. Zan je ɗai na kai musu Form ɗin sai na faɗa musu uzuri na yaso ko jibi in jikin naka ya sake yin kwari sai na fara zuwa".
"Wai jikina yayi kwari sai kace wani jariri, dan ALLAH ki bar wanna zancen kawai da safe ki shirya ki tafi".
"ALLAH ya kai mu, Shazeen miqo min ledar magungunan sa da pure water can na bashi mu tashi muje mu kwanta dare yayi kema Karki kasa tashi makaranta ".........tashi Shazeen tayi ta ɗauko ruwan da magungunan ta bata. Sai da Hushaima ta tabbatar ya sha magungunan sa sannan suka masa saida safe suka fita.
Washe gari da sassafe ta tashi kamar yadda ta saba ta gama duk abinda zatayi ta shirya Shazeen, suka yi kalaci a tare sannan suka fita gabaɗayansu suka kullo gidan. Sai da suka fara sauke Shazeen a makaranta sannan suka wuce asibiti aka masa dressing ciwukan, bayan sun fito Sahnish ya ce, "Mu biya a saukeki sai a wuce dani gida"........."Ah ah muje dai naga ka shiga gidan sai ni a juyo dani".
"Ke fa kullum kike maidani kamar wani Yaro, sannan kuma kizo kina faɗan cewa in zama jajirtacce"..........."To ai baka nunamin kai ɗin jajirtaccen bane ballantana na sake ma ragamar komai".
"To ai ke kika hanani zama jajirtaccen"........ Shiru ta masa shi kuma ya cewa mai tuk tuk ɗin ya kaisu starlight beauty co.
Basu ƙara magana ba har mai tuktuk ya faka ƙofar wurin Sahnish ya ce, "To sauka kije ALLAH ya bada Sa'a, amma tsaya wa zai ɗauko Shazeen a makaranta"........ Dan jim tayi kafin ta ce, "zan cigaba da daukota zuwa lokacin da zakaji sauki sai Ka karba".
"To islamiyyar fa?"............"Eh to wannan dai gsky saidai ka kira malamin nasu ka sanar masa uzurinka saboda kaga bazai yiwu na bar wurin aikin har so biyu ba".
"Shikenan to ba damuwa zan kirashi. Sai kin dawo"........ɗaga masa hannu tayi tana faɗin, "ka kula da kanka ". Sannan ta juya ta shige, shi kuma ya bawa mai tuktuk ɗin umarnin tafiya.
Yau ma Jumayma ta tarar sai cleaners dake ta aikin tsaftace wurin, "barkan ki"........Hushaima ta faɗa tana zaro Form ɗin a jaka ta tura mata gabanta. Kallon tara saura kwata jumayma tai Mata sannan ta ɗauke Kai, taɓe baki Hushaima tayi sannan ta wuce ta nemi wuri ta zauna. Shuru shuru har 10 sai sauran ma'aikatan dake ta shigowa, tashi tayi ta koma wurinta tare da faɗin, "sannu"........."Yauwa"........ ta amsa tana yatsina kamar taga kashi. "Hajiya fa?"........."Bata zo ba"..........."Jiya bata Miki bayani bane ".........."Wani irin bayani?" ........."Na ɓangaren da zan dinga aikin mana".
Sake ƙyabe fuska tayi sannan ta ce, " ki koma ki zauna sai ta shigo".........Bata sake cewa komai ba dan bata so a ja zancen da zai Kai matsayin da matar nan zata Kai ta bango dan tsab zata iya kwaɓe musu tun ba'a yi nisa ba. Kusan minti talatin ta ƙara sannan ta kirata. Kamar baza taje ba saboda a wulaƙance tayi kiran amma ta taushi zuciyarta ta tashi ta ƙarasa wurin nata. "Muje a nuna Miki aikin da zaki dingayi"..........Binta tayi a baya suka shige ciki, suna shiga ta ce, "Bunayna ga sabuwar ma'aikaciya nan ku nuna mata yadda aikin yake".........Da " to". Bunayna ta amsa sannan Jumayma ta juya ta fita. "Bismillah ƙaraso".......Bunaynan ta faɗa tana Murmushi, dan ita sam bata da matsala haka ma sauran abokan aikin nata, hakan yasa Hushaima bata samu wata matsala ba wurin koyon abubuwan da suke nuna mata.
Zuwa rana suka fara attending customers, sosai wurin ke cika da manyan hajiyoyi da ya'yansu, hakan yasa ta zage suke ta jibgar aiki kamar jakai, har zuwa lokacin da hajiya ta iso nan tasa aka kirata bayan sun gaisa ta ce, "Ina fatan dai ka gane komai ai?"........" Eh hajiya ai ba wahala ma aikin".
"To yayi kyau , akwai kayan aiki in ka tashi yau zasu baka, shi Ake sawa, sannan albashin ka dubu Arba'in monthly, cox ni kaga ma bani da buqatar Ƙarin maaikata kawai dai dan na tausaya Maka ne".
"Ba damuwa hajiya a hakan ma nagode, saidai ina da ɗan uzuri anjima zanje ɗauko yarinya a makaranta, dama qanina ne zai dinga ɗauko ta to kuma baijin dadi yanzun"........."Ba damuwa, amma Karta shiga lokacin aiki da yawa".
"In sha allah ".......... Ta faɗa tana tashi ta koma wurin aikin su, wurin jakarta ta nufa ta sanya wayar ta a ciki sannan ta koma ta cigaba da aikin da takeyi kafin hajiya ta kirata ta bari ta fita.
"Kam burauban can, Ni za'a yashe, to whl ko sama da ƙasa zata haɗu bazan yadda ba sai an fito min da dukiya ta".
Da mamaki duk ma'aikatan dake wurin suka kalli juna da faɗin , " Ai kuwa hajiya wurin nan wani abu bai taɓa ɓata ba bare kuma sata ki dai duba ko kin barshi a mota, amma tabbas ba wanda zai dauka Miki wani abu a nan".
Wata budurwa ce ta ce," To wai me aka sace Mata ne ma?"
"Kudaɗe na gabaɗaya babu sannan akwai zobe da bangles ɗina na gold da na cire nasa a jaka yanzu saboda zaa yanke min farce, amma yanzu na duba babu su ba alamar su, ƙafa ne dasu da zasu fita da kansu in ba ɗauka akayi ba".
ɗaya daga cikin ma'aikatan ce taje ta sanar da hajiya abinda ke faruwa tana zuwa matar ta ce, " Gwara da ALLAH ya kawoki, sata suka min kuma whl tun muna shaida juna kisa yaranki su fitomin da abubuwana".
"Ya hakuri Hajiya mu bi a sannu, kaya basa ɓata anan wurin amma bincike bai bar komai ba"....... Ta ƙarashe tana kallon su tare da tambayar, "iya Ku kenan ko akwai Wadda ta fita kafin nazo?".
"Iya mu kenan sai wanna yarinyar data fita ta dawo, sai kuma ma'aikaciyar dataje ta sanar Miki yanzu"......... Ta karashe tana nuna Hushaima da kuma Elijah .
"Ita wannan ba wani wuri taje ba sabuwar ma'aikaciya ce ma ni nasa aka kirata Amma tunda abun yazo da haka bari ayi caje kawai, barin kira Jumayma "......... Ta faɗa tana dialing contact din Jumayma, sunkuyar da Kai Hushaima tayi tana cigaba da abinda take.
Jumayma ce tazo ta caje kowa, saida ta gama ta ce...............