5
by @hafnancy
SHIN SO DAYA NE?
Hafnancy...
Zazzafar soyayya, Cin amana, mugunta da kuma Sadaukarwa
#Free Book#
5
Tun sanda Suhaima ta furta mun cewar wai Mubeen zai k'ira yau, na kasa Samun sukuni, bini bini nake duba wayata ko zanga missed calls d'insa, text message ko kuma message ah watsap, amma ko daya ban gani ba har zuwa yanzu da muke k'arfe goma sha daya na dare shiru kake ji, cire rai nayi kawai dashi.
kwance nake saman gado amma na kasa bacci sai tunaninsa nake gashi naki sauke girman kai na k'ira kamar yadda 'yar'uwata ta shawarceni. Duba nakai gefena jin motsin gyara kwanciya, Yesmin ce kwance take bacci cikin kwanciyar hankali amma da k'yar na sami tayi baccin sabida ta dameni da rigimar son ganin Umma, da lallashi da kuma 'yan dabaru na sami tayi baccin.Na gyara mata lullub'i da bargo kasancewar babu laifi ana d'an tab'a sanyi dayake muna cikin lokaci na hunturu ne.
Ahankali na sauka kan gadon gudun kada na tasheta, nayi dakin su Suhaima wanda yake akusa da Nawa... Ita da Lubna ke Kwana daki daya ayayin da Faruk ke Kwana tare da Abba, idan kuma Umma nanan to anashi dakin yake kwana.
Tura k'ofar dakin nayi ahankali dan duka gidan bama rufe kofofin dakunanmu, abin mamaki Suhaima ce na gani zaune saman gadonta ta zuba wani uban tagumi alamun tayi nisa cikin tunani, Cike da sanyi na furta"Ashe itama batayi baccin ba.." k'arisawa har inda take nayi na zauna a gefenta amma still bata sani ba.
Dafa kafadanta nayi tare da k'iran sunanta ahankali"Suhaima.. wai ni tunanin mai kike ne haka wanda har yasa kika kasa bacci da kananun shekarun nan naki ? "
Firgigit! Ta dawo daga duniyar tunanin data lula tace"Sis yaushe kika shigo ban sani ba ?" Nace"Taya za'a ki sani kuwa bayan kin lula duniyar tunani... Tell me meke damunki? Idan kuma akan accusing naki dana yi dazun ne to dalilin dayasa nashigo kenan dan na baki hakuri, Nasan nayi kuskure babba hadda marinki... Wallahi ki yarda nayi ban san menene ya shiga k'wak'walwata ba da har yasa nayi tunanin hakan, Sis pls ki yafewa Yaya Fadimarki wacce baki da kamarta arayuwarki...dan Allah ki gafartamun hadda marin dana miki dazu"
Hararar wasa naga ta jefeni dashi, na gane hakan ne sabida Dim light daya haska dakin, tace"Ai ni am not like you.. Babu wanda ya isa ya shiga tsakanina dake musamman ma d'a namiji, amma meyasa kikayi tunanin na fad'a tarkon soyayyar Saurayinki ?"
Ni kaina sai dana ji kunyar tambayar data min, ahankali nace"Banyi hakan da wata manufa ba.. kawai subutar baki ne amma bari in gaya miki gaskiya, hak'ik'a ina jin haushi sosai idan kina fad'in cewa kin tsani Aliyu alhalin bai tab'a miki laifin komai ba, yanzu dai kiyi hak'uri mu manta da komai kinji ?" Murmushin takaici naga tayi tace"Hmm Subutar baki ? To shikenan naji komai ya wuce amma next time kiyi k'ok'arin tauna magana kafin ki amayar " Azuciyata nace" Suhaima kenan, bazan tab'a daina fad'a miki cewar alallai kin kamu da soyayyar Leedar bane, sai dai zanyi shiru inga iya gudun ruwanki " tace"Uncle Mubeen ya kiraki din kuwa? "
Girgiza mata kai nayi alamar ah'ah,Cike da tashin hankali tace"Sis gaskiya yakamata ki k'irashi yanzun nan dan wallahi dad nashi aka fitar zuwa k'asar waje (India) aka masa dashen kod'a, jiyan jiyan nan dana k'irasa ne suka dawo, dalilin dayasa kika ga bai k'iraki ba kenan harna tsawon kwanak'in nan, ba wai akan maganar Leedar ne kadai ba "Mik'ewa nayi jiki na rawa nace"what?? Dan girman Allah da gaske kike ?" Tace" Sis mezai sa in miki irin wannan wasa ?"
Da dan gudu guduna na fita adakin na koma nawa don dauko wayata inbi shawarar da Suhaima taban, Cin karo nayi da Yesmin da wayar ahannu alamar zata kawo min, tace"Anty tun dazu nake ta nemanki na baki waya anata k'iranki kuma na duba bathroom bakya ciki shine ada zanje nemanki afalo ko dakin su Yaya Suhaima " Shafa kanta nayi nace "Nagode baby sis, oya koma ki kwanta abunki" Na karbi wayar daga hannunta ayayin da ita kuma ta koma baccinta. Na duba naga 5missed calls din my Mubeen, atake anan wani murmushi ya lullub'e min fuska, Ji nayi ance"Shi ya k'ira ko ?" Waigawa nayi naga Suhaima tsaye abakin kofa ashe ta biyoni ban sani ba, kai kawai na daga mata kana na latso lambar tasa.
Bugun farko naji wayar switched off.. Nayi ta gwadawa har kusan sau goma amma still switched off shegiyar baturiyar nan keta cewa. Ji nayi kamar zanyi hauka don bak'in ciki, Suhaima ce tace min"Lovly sis please ki kwantar da hankalinki watakila wayar ta mutu babu chargy ne, amma muna fatar Allah dai yasa lafiya, Kiyi hakuri zuwa gobe sai mu sake gwadawa kinji ?"..Ahankali nace"Ba damuwa Allah ya kaimun"Daga hakan mukayi sallama kowa ya koma baccinsa amma zan iya cewa yadda naga rana haka naga dare, kuma bayan minti biyar biyar nake k'ara gwadawa inga ko za'a dace ya shiga amma shiru kake ji.
****
Misalin shidda da mintina hamsin ta safiyar laraba 'yan makaranta suka kammala shirinsu cikin shiga ta uniform d'insu. Muna zaune kan dinning ana breakfast hadda Abbanmu Wanda shima sauri yake ya tafi gun aikinsa. Abba ne ya kada baki yace"Antynsu wai yaushe umman taku zata dawo ne ? naga kamar ke kin fimu samun information daga gareta" Murmushi Kawai nayi nace"Tace mun ata idanu kan hanya cikin kwanak'in nan tana tafe insha Allah " Su Yesmin kowa ya hau ihu ana murna. Abba kuma Gyad'a kai Kawai yayi sannan yadan yanki tissue ya goge bakinsa, ya mik'e hadi da daukar briefcase nashi yana fad'in"Antyn yara nadan ganki mana" Yayi hanyar fita falon kannena na"Abba adawo lfy"
Daidai barandar sashinmu muka tsaya, nace"Abba gani " Shiru ya danyi harna tsawon dak'ik'u goma, kana ya soma magana"Fadima don Allah ku cigaba da hak'uri da rashin zaman mahaifiyarku akusa daku, Nasan abin na damunku amma ayau na daukar muku alk'awari Wannan itace karon k'arshe da Kareema zata sa kafa tabar k'asar nan da nufin kasuwanci... Lokaci, kulawa da kuma soyayyar nan dole ne ta baku, ni ina Uba kenan Wanda aka sanmu da cewar bama cika zama sabida yanayin aiki amma duk da hakan ina iyakacin bakin k'ok'arina fiye da ita da take mace ? Ai ni bance mata na gaza ba da har zata dage da kasuwancin nan, Ki duba fa kusan wata daya take nema ak'asar mutane, abunda bata tab'a yi ba, tana can tana cudanya da iri irin kazaman Mutane... No I can't take that any longer ya zama dole na dau mataki.... "
Da sauri na tsugunna ina kuka nace"Abba please don Allah kada ka kawo k'arshen dogon burinta akanmu, Abba in tamu ne wallahi mun Riga mun saba da irin wannan rayuwar don haka kada ka damu da batunmu ka batta ta cigaba da kasuwancin nata " Yace"Look Fadima karki hanani daukar mataki akanta wannan karon, nayi hak'uri kuma kanku kunyi, dan haka ya isa hakanan, i will take action, idan ta dawo kema akwai maganar da zamu tattauna akanki "Damn! Naji k'irjina ya buga, atake anan naji hankalina kuma ya tashi. Murmushi naga Abba yayi yace"karki tada hankalinki ba wani k'wakk'waran abu bane amma trust me tattaunawace mai matuk'ar muhimmanci wanda ya shafi rayuwarki ta nan gaba, Nina tafi saina dawo"
Mukayi sallama ya tafi, driver mah ya kai yan makaranta ayayin da ni kuma aka Banni ni kadai agida sai kuma house girl Indo. Allah Allah nake monday yayi na koma school because I rilly missed many tinx especially my Leedar.
Now left alone with My Mubeen's thought Wanda har zuwa wannan lokacin wayarsa taki shiga.
* * *
Misalin karfe tara na safiyar ranar kamar amafarki call din my mubeen ya tada ni daga bacci.kamar na zuba ruwa akasa nasha don murna.. Infact rasa inda zansa kaina nayi tsabar farin ciki. Hehehe relax, amma sai dana dan ja ajin nan kafin nayi receiving call din don har ya kusan tsinkewa.
Koda na dauka shiru nayi ko sallama ban masa ba.
Ahankali naji yace"My baby Zahra"
Ban san lokacin dana ce"My mubeen”ba
Dan murmushi naji ya saki yace"babyna wato idan ban nemeki ba kema bazaki nemeni ba,is dat so?.. Gaskia Alhamdulillahi for our little sis dana lura ta fiki kaifin hankali,imagine she was d one dat call tana ta bani hakuri and I told her dalilin daya sanya bana kiranki dix days... Infact bata wayata mah nake ba ... I guess Suhaima ta fada miki cewar mun fita da Abba kasar waje an masa transplantig kidney Right?"
Ahankali nace"Yeah she told me.. "
Yayi murmushin takaici, yace"And u didnt even bother to call... "
Nace"wallahi I hav bin trying ur line since yesterday nyt Buh it couldnt get through har zuwa safen nan kafin ka kira... "
Yace"Buh ai sai da kika gan missed call dina ne kika kira if not wayata na kunne throughout yesterday kafin na kiraki... Anyway tun jiya na kira don nayi sharing bad news din nan dake Buh u didnt pick... An yiwa Abba aiki har mun dawo, sai dai kash! Ba'ayi nasara ba... Jiya da misalin karfe tara na dare ya rasu, da safen nan akayi jana'izarsa... Fadima Abbana is late today... Ya tafi ya barni, yanzu banda Uwa da Uba... Na rasa kowa nawa including you tunda naga kamar wani ya dauke min hankalinki" ya fashe da kuka.
Jikina ne ya hau rawa nima ban san lokacin dana fashe da kukan ba, na hau rarrashinsa"Mubeen dina please take it easy... Baka rasa kowa ba kana dani... I promise to stay wit u forever and love you the more... Mubeen dina please karka Banni because I so much love you wit all ma heart... Allah yaji kan Abba... "
Ahankali naji ya furta"Ameen... Yaushe zaki kawo ta'aziya? "
Gabana ne ya fadi amma sai na daure nace"Insha Allah ranar sadakar uku dats on Friday. "
Yace"Allah ya kaimu... Babyna later ana nemana. "
Mukayi sallama ayayin da ni kuma na dunga tausayawa Mubeen dina na rashin da yayi...yanzu ba Uwa ba Uba, sai naga ai gara mu muna dashi amma basu dai Bamu time nasu ne. Sanda Suhaima ta dawo na fada mata rasuwar Abban Mubeen dina Itama tayi kuka sosai har ta kirasa ta masa ta'aziyya tare da jaddada masa lallai muna tafe ran Friday.
Dabara muka Fara nema yadda zamu samu har abarmu muje kanon.
Suhaima ce tace"Sis I hav come up wit an idea... Why not ki fadawa umma gaskia kin san Itama macece and tasan ya kamata... Idan yaso sai ita tasan dabarar da zatawa Abba... "
Bude baki nayi alamun mamaki nace"ke kina hauka ne? So kike tace dama am cheating on Leedar barin ma yadda naga tana masifar sonmu dinnan tare? "
Tace"Sis juz trust me wallahi it will work I promise... "
Ahankali nace"Sure? "
Tace"yeah"
Na bata beautiful smile nace"Dats ma lil sis, who always ghat ma back.. Tanxx durlin."
Murmushin nima ta mayar mun tace"U welcm my Yaya Fadima"
* * *
Zazzaune muke saman gadon Umma mun sanyata atsakiya, kowa sai murnar dawowarta ake musammam Yesmin wacce ta hanata sukuni.Akalla an sami kusan awa biyu kenan da dawowarta.Fira muke sosai irin ta da da mahaifi.can Umma ta rarrabawa kowa tsarabarsa anata ihu da tsalle tsallen murna.
Umma tace"Oya auta, soja aje ayi wasa abarni na huta kadan.. Ko dayake nasan daga nan Sojana dakin karatu yayi babu ruwansa da wasa koh? "
Ina ruwansu Faruk cikin feeling proud yace"Umma aini kullum bana wasa karatu nake, koh ah school mah malamin mu na cewa nafi kowa kokari ah class dinmu. "
Dukkanmu muka fashe da dariya, nace"C'mon wuce ka bamu wuri sai shegen feeling proud. "
Umma tace"ku kyale min shi yayi because yasan mey yake yi and am proud of u my boy.. "
Daga hakan shida Yesmin suka fice, umma tace"Oya Lubna kema bisu..."
Ahankali ta mike tabi bayansu, yanzu na lura Umma so take dakin ya rage daga ni sai ita da kuma Suhaima.
Ta juyo ta kalle mu,tace"Fadima... Suhaima.."
Da sauri muka dago kai muka kalleta har muna rige rigen cewa"Naam Umma"
Dada gyara zamanta tayi saman gadon ayayin da ni nake gefen damanta, Suhaima kuma tana gefen hagunta.
Tace"Abunda yasa kuka gan ku na tsai daku, its becuz kune manyan and am very sure dat everything am going to say now zaku bashi kyakkyawar fahimta especially u Fadima dake babba..Fadima I want to talk about the issue we started discussing on phone a day before yesterday which was Tuesday... And guess Wat?"
Da sauri muka ce"What ma'am?"
"Fadima kamar yadda kika fadi cewar u guys really nid ma love, time care and nid me beside u all, wallahi na zauna nayi tunanin lallai ban taba kyauta maku ba, kuma nayi tunanin yau idan har na koma ga Allah mai zan fada masa kan amanarku daya bani? Dats why ayau din nan nake farin cikin shaida muku cewa na daina kasuwancin abroad... Zan dunga yinsa acikin gidana, Duk mai son wani abu sai dai yazo ya siya anan bawai na kuma fita siye da siyarwa bah... So now mummy wil always b staying by ur side starting from today... Hope I made maself clear?"
Suhaima ce ta saki ihun murna ta rungumeta tana fadin"Woww Umma can't juz believe dix.... Ar u serious dat now we ar going to get much of ur time, love and care?"
Murmushi Umma tayi sannan tace"Yeah ni na fadi hakan so ki rubuta ki Ajje my pretty angel. "
Umma ce ta juyo gareni ganin ni bance uffan ba,ta kamani ina goge dan gutun hawayen daya digo saman kumatuna and at the sametime ina murmushi,janyo ni tayi kusa da ita tana fadin"Haba 'yar Kareematu ya naga kina murna and at the same time kina hawaye?tell me Wats wrong? Kodai baki ji dadin hukuncin dana yanke bane?"
Murmushina na cigaba dayi ayayin da hawaye sai dada kwaranyowa yake saman kumatuna, nace"Ummu Fadima the best moment in life is 'Smile' and 'cry', they won't meet each other at a time.. if they do, then believe me its the best moment in ur life... Mother I can say dat today is the best moment of my life becuz I can't juz express how Happy I am hearing dat u wil always b staying by our side from now on... Umma thank you so much we all love you"
Na rungumeta, wannan karon kuka nake sosai, umma Duk tabi ta rude tace"Haba my baby kiyi shiru ko so kike nima nayi kukan? "
Da sauri na tsaida kukan, na shiga share hawayena ina fadin"Ummu Fadima ki banni nayi kukan it indicates my Happiness towards hukuncin da kika yanke."
Umma ta gyada kai cikin gamsuwa, ta mike ta shige bathroom don watsa ruwa. Dadi ne ya lullubeni ganin yanzu Mahaifiyarmu zata dunga bamu time dinta as she juz said... Don bana mantawa tun Suhaima nada shekaru uku kacal aduniya Umma ta soma harkan kasuwancinta, Wanda tun alokacin muka daina samun time dinta har izuwa wannan lokacin, don ko su Lubna ba wani jin dadinta sukayi ba.Again, ina matukar murna da Umma ta yankewa kanta hukunci kafin Abba yama yi mata magana akansa sabida I hate to see parents fighting or arguing,zan iya cewa tunda na mallaki hankalin kaina ban taba ganin iyayena na fada atsakaninsu bah, shiyasa nayi matukar murna da ita tayi saurin ganewa harta sauko kafin shi ya hau Wanda nasan sam abin da bazai yi dadi ba idan har aka sami banbancin ra'ayi.
Ahankali na furta"Alhamdulillahi kaseeran"
Ji nayi Suhaima tace"Toh crying beauty its over.. Can we now set the drama to start idan Umma ta fito wanka? "
Hararar wasa na wurgeta dashi don na gane abinda take nufi, nace"Toh sannu drama queen ai kya bari ta huta ko?"
Da sauri tace"No, Mrs Mubeen ance da zazzafin nama akan bugi karfe... Its beta for us to knw tun wuri idan har plan dinmu zaiyi aiki or not... Balle ni bana jin za'a samu matsala daga Ummu Suhaima, Abu Fadima kawai nake ji... "
Dariya nadan tsaki nace"No, Abu Suhaima dai... Kuje can ku karata ku barmu nida Ummu Fadimata"
Adaidai nan Umma ta fito daga wanka tana fadin"My angels inata jin dariyarku tun dazu... Wats the secret behind the happiness? "
Na kalli Suhaima wacce Itama ni din take kallo, na mata signal alamar ta baiwa umma labari because da kunya ni na bata labarin my Mubeen da kaina.
Na mike ina fadin"Umma I hav prepared ur favourite danbun shinkafa, lemme get it for you right away.. "
Tace"Woww thanks 'yar Kareematu, u the best"
Na fakaici idon Umma wacce take gaban wadrope ta bamu baya, sai dana tabbatar hankalinta baya kanmu sannan na juyo na dubi Suhaima,cikin kwantar da murya nace"Ke drama queen try and make ur Drama lively... Make it real yadda heart dinta zaiyi touching har muyi winning okay? "
Ahankali ta murmusa tace"Trust ur lil sis mana Yaya Fadima"
Ai idan Suhaima ce bani da fargaba akanta don haka na mata thumbs up hadi da fadin"Goodluck Mrs Leedar. " sai dai ban bari taji Sanda na ambaci 'Mrs Leedar' din ba becuz na fade shine in my lowest tune yadda ni kadai nasan mai na fada.
Akalla sai dana share kusan mintuna talatin zaune ababban falo don Suhaima ta samu ta warwarewa Umma komai ba tare da taga idanuwana ba balle taji nauyin fada mata wani abun ko kuma ni naji nauyin Ummar.
Can na mike nayi kitchen don daukowa Umma danbun shinkafarta da kuma kunun aya wacce taji kayan hadi. Na hada komai akan tray sannan nayi dakinta, kirjina na dukan uku-uku because ban san wani irin sakamako zan tarar ba. Kowacce addu'a tazo bakina yinta nake,, wayyo wallahi tension is very dangerous.. It can kill.
Ahankali na tura kofar dakin hadi da sallama, suka amsa min tare da zubomin idanuwa. Abin mamaki daga Suhaimar har Ummar sakon murmushi suke ta aiko min wacce ta sanya nayi sensing lallai akwai hope kenan.
Azuciyata nace"Weldon Suhaima the drama queen.... Kinyi kokari don ko ba'a fada min ba daga ganin annurin dake shimfide saman fuskar umma ya bani tabbacin lallai munyi nasarar touching heart dinta da labarin Mubeen dina"
Ba zato ba tsammani sai kawai naji umma tace min"My lovely daughter com to mum and gist her properly about her new in-law Mubarak. "
Wani dadi ne naji ya tsikareni daga saman kaina har zuwa tafin kafafuwana, wayyo ina zansa kaina don murna don Kana gani kasan Umma tayi na'am da zancen my Mubeen,yanzu sauran mana Abba.
Da sauri na karasa wurinta na ijje tray din hannuna akasa ina dan sussunar da kaina kasa Wai ni kunya. Kamo hannaye na tayi tare da zaunar dani akusa da ita tana fadin"Suhaima ta bani labarin Dr. Mubarak...Ke kuma ta waya Allah ya hada jininki da wani? Because acikin maganganun kanwar taki babu abinda na tsinta illa kuna masifar son junanku ke dashi Wanda nake ganin kila mah kinfi sonsa akan Haidar...ikon Allah!! Kenan... Toh yanzu ya kuke son ayi da Haidar don kuma kun san nidai shine Nawa."
Da sauri na dubi Suhaima wacce take kokarin magana amma data ga na kalleta komai ta tuna kuma sai naga ta fasa tayi shiru.
Ganin shirun yayi yawa ne yasa Umma tace"Ya naga kowa yayi shiru? Daga gani wannan Mubarak din ya gama kwanta muku arai.. Anyway mafi alheri dai Allah ya zabar and my advice shine Fadima ki daiyi taka tsam-tsam dashi don da namiji bah abin goyo bane, ba fata nake ba juz be very careful kada ya kaiki ya Baro... Hope u understand wat am trying to figure out? "
Cikin sanyin jiki na amsa da"Yeah i understand ummu Fadima tankx alot"
Ta cigaba"Good... Allah ya jikan mahaifansa da Gafara... "
Ni da Suhaima muka amsa da"Ameen thumma ameen".
Umma ta cigaba"Kanwarki ta nemi alfarman dana sanya baki ayi wa abbanku magana daya barku kukai ta'aziya gobe... Idan kukai haka kun kyauta amma nidai tsoro nake sabida wannan bawan Allahn awaya fa kawai kuka hadu, baki sansa ba, haka zalika kuma baki san halinsa ba, kuma baki san wani irin mutum bane... My dear dix world is full of wonders, mutanen duniyar nan da abin mamaki suke da kuma tsoro dat is why am damn scared,idan tani ne kawai ku fasa tafiyar nan.... "
Da sauri na dago kai na dubeta,ban san lokacin dana furta"Ummu Fadima please don't do dix to me... Don Allah ki min rai ki banni naje ta'aziyyar nan wallahi believe me Mubarak will never be a bad person kamar yadda kike tunani... Ummata ki tuna addu'a itace takobin mumini, kuma Allah yana tare damu... Ummu Fadima please juz say yes ko zanji sanyi araina.. Wallahi idan banje ba Mubeen bazai ji dadi ba kuma it really kills me to see him sad becuz I so much love him.. "
Na kife kaina akan cinyarta, sannu ahankali na soma rera kuka mai taba zuciyar mai sauraro,Umma ta dago kaina tana goge min hawaye, kallona take cike da mamakin yadda nake ta zuba zance babu ko dan alkunya.
Girgiza kai tayi sannan tace"Lallai soyayya gaskiya ce... Fadima ko baki fada ba nasan Kinyi nisa kan soyayyar bawan Allahn nan... Ni dai addu'ata shine, yadda kike sonsa din nan Allah yasa shi yana yi miki mafi yinsa... Anyway naji zan ari bakunanku naci muku albasa wurin yima Abban naku magana, sai dai zan masa karyar mahaifin wata course mate and your tight friend ne ya rasu shine zaku kai ta'aziyya akano Wanda can ne asalinta,kuma tare da Wasu course mates dinku za'a... I know ur dad wil believe dix story becuz he trust you guys kuma bazai yi bincike ba... And don't use dix opportunity to break d trust he has for you all nan gaba... Is dat taken? "
Gaba daya muka amsa da"Insha Allah Umma.. "
Ta cigaba"Good... Sai ki sanar da kawarki Aysha ta shirya gobe ta muku rakiya, Malam Iro driver zai kaiku ya kuma dawo daku... "
Cike da murna Wanda bakina har kasa rufuwa yayi na rungumeta ina mata godiya, nace"But Umma u hav to talk to Aysha's mum on phone becuz her parents are somehow strict too.. "
Tayi dan jim can tace"Alright, juz let me know idan kikai waya da ita so dat I wil talk to the mum"
Ahankali nace"Alright... Amma mum kina ganin Abba zai bari kuwa? "
Tace"Ya salam! 'Yar Kareematu kedai je kuta shiri ki bar komai ahannuna I will handle everything okay? "
Murmushi nayi nace"Shikenan Ummu Fadimata love you"
Na janyo tray din danbun Shinkafar ina fadin"Umma here is ur favourite."
Murmushi tayi tace"'Yar Kareematu so kuke ku fasa min tunbi yau ko? Kowa sai kawo min girkinsa yake... Toh bari na dan taba naki kema..
Na kalli Suhaima, cikin tsokana nace"Ai so nake ki gama cin concoction nasu wannan yarinyar kafin kici hadaddan"
Dariya muka fashe da ayayin da Suhaima ta kalleni, ahankali ta furta"I will spoil everything right now.."
Na fakaici idon Umma wacce tayi busy tana kwasar danbun Shinkafarta tana santi, na soma rokon Suhaima, ina cewa ahankali"Please dear don't do dix to me. "
Murmushi tayi min. Daga haka muka mike don baiwa umma wuri ta samu tadan huta.
•∆∆∆∆∆∆∆∆•
Agogo ya nuna karfe 9:35pm na daren alhamis. Kwance nake saman gadona nayi ruf da ciki, waya nake da My Leedar Wanda sai faman sanyani dariya yake abinsa.
Yace"My dear ke daga hutun kwana uku kacal ke kin kara wa kanki har kwana biyu agida... Yanzu if not because nasan kofar gidanku and again na zama dan gida da haka zanta missing dinki har sai Monday kafin na ganki?"
Dariya nayi sosai nace"Toh ai koh shekaranjiya kana gidan nan, kuma koh yanzu kace zaka zo ba mai hanaka ko ya takuraka.... "
Da sauri ya tari numfashina yace"Akwai mai takurani da kuma hanani sukuni... Koh kin manta da 'yar sarauta Suhaima ne? "
Damn!! naji gabana ya fadi, nace"No, ban manta ba ina sane"
Cikin yanayin damuwa yace"Buh Fadima anya kina ganin akwai alamun nasara atare da ita kuwa? "
Shiru na danyi kamar bazan yi magana ba, can nace"No hope for now... Leedar you hav made ur hatred to develop so much in my sister's heart...you and her made a big mistake... Anyway I wil kip on trying har ta sauko... I assure you everything will gonna b fine... "
Ji nayi yace"Shit!!! am dead.... Fadima please ki taimaki rayuwata ki daidaita tsakanina da Suhaima... Idan kika min haka wallahi kin gama min komai arayuwa."
Murmusawa nayi tare da fadin"I promise you Leedar za'ayi nasara buh its not as easy as u think... "
Adaidai nan Suhaima ta banko kofa ta shigo tare da sallama nima daidai lokacin mukayi sallama da Leedar.
Kallona take cike da tuhuma kamar na mata wani laifi Wanda hakan yasa na tsargu nace"Ke why the strange look? "
Tabe baki tayi tace"Nasan da Leedar kika gama waya... Hmmm sis am sorry buh I juz hav to say it, wallahi I cant stop hating him... "
Azuciye nace"Good and fine, wannan matsalarki ce ba tawa ba... "
Kokarin magana take na daga mata hannu"please its okay don't try to spoil dix nyt for both of us.. "
Ji nayi tace"Naji... Abba sent me to call you... Ki sameshi afalonsa right now". Tana gama fadin hakan tasa kai ta fice daga dakin ba tare da ta jira taji amsar da zan bata ba.
Hijab dina na zura na fice daga dakin ina fadin"Suhaima wallahi I pity ur life... Yarinya sai shegen zurfin ciki da kuma ruko... Allah dai yasa ki gane kafin lokaci ya kure miki. "
Ina tunkaro falon Abba sai kuma gabana ya shiga faduwa, fargaba nake kan sakamakon da za'a samu daga bangaransa. Ahankali na tura kofar falon tare da sallama,Abba ne zaune ya kishingida saman cushion, ayayin da Umma ke zaune agefensa suna fira.
Sallamar da nayi ne ya janyo hankalinsu gareni, Duk suka amsa min. Na karasa wurinsu na durkusa agabansu, nace"Abu Fadima, Ummu Fadima barka da dare. "
Duk suka amsa min.
Abba yayi gyaran murya yace"Fadima naji sakonki daga gun Mahaifiyarki... Allah yaji kan musulmi"
Ahankali na amsa da"Ameen Abba. "
Ya cigaba"Karfe nawa za'a tafi goben?"
Ban san sanda nace"Kamar zuwa tara na safe, sannan kafin karfe biyu an dawo..
Yace"Good... Na baki izinin zuwa... Sai dai zanso Wasu course mates dinki su biki ataki motar sabida ban yadda da tafiyar nan taki ke daya ba, ba tare da wani naki ba... Don haka kanwarki Suhaima zata miki rakiya, zansa kuma Malam Iro driver ya kaiku. "
Wani dadi ne ya lullubeni, azuciyata nace"Abba kamar kasan mun riga munyi planning hakan already. "
Afilli kuma nace"Masha Allah Abba hakan yayi Thank you so much. "
Kudi naga ya miko min yana fadin"Ga dubu biyar ba yawa kya bada sadaka...I trust u, na yadda da tarbiyar dana baiwa 'ya'yana dats why bana wani bincike ko dogon tunani idan kuka zo min da magana makamancin wannan.. Don haka please don't disappoint me,dnt break the trust I hav for you... inda mutum yace zaije ya tabbatar wurin zashi banda karya don bazan yafe ba. "
Jikina ne yayi sanyi na dago na kalli umma tayi min Signal alamun kada na sami damuwa tunda ai da gasken ta'aziyyar zani.
Na karbi kudin ina masa godiya. Abba yayi min albishir da hunkuncin da Umma ta yanke na game da kasuwancinta, Na nuna masa ai mun rigashi celebrating ai.Kana ganin Abba kasan yana cikin tsananin farin ciki maybe dats the reason daya sanya ya amince with my request of travelling to Kano, if not Abba is very strict.
Dakin Suhaima nayi, Na fada mata cewar munyi winning,zan Iya cewa kusan kamar tama fini murna. Na kira Ash queen na fada mata zancen rasuwar dayake ta sanni da Dr. Mubeen, ta'aziyya ta min, sannan nayi mata zancen tafiyar, tace basai an yiwa mum nata magana bah sabida dama tana da niyyar zuwa gidanmu washegarin ta yini.
Nayi matukar murna sosai da komai yazo min da sauki kuma atsare as planned.Mubeen dina ya sake kira nayi assuring dinsa cewar lallai gobe muna tafe da safe, yayi murna sosai wanda hakan ya sanyani farin ciki because I always want to see him happy.
•∆∆∆∆∆∆∆∆•
Washegari Jumma'a wanda ya kama ranar tafiyarmu,da misalin karfe hudu na asuba Umma ta tashemu with full of surprises... Surprises din shine, wai zamu soya panke, sannan da kunun aya da zamu kai gun sadaka.Ashe Umma ta kwaba fulawa tun jiya da daddare ba tare da sanina bah, suya kawai ya rage. After that,ajiyan kuma tasa aka kawo mata su casbaha da kuma su kananan bagadadiya, da kuma hisnul Muslim da zamu bayar na sadakar ukun.
Kukan murna na soma yiwa umma ina mata godiya, tace"'Yar Kareematu idan ban miki ba wazai miki? "
Nace"Umma babu kam"
Kafin takwas mun kammala shirinmu tsaf tsaf, Ash queen ta iso misalin 8:30am. Umma ta dada ja mana kunne tare da nasiha,Tace"Fadima Kuje lafiya ku dawo lfy.. Allah ya tsareku, kuma ku rike addu'a abaki... And again ku tabbatar kun dawo kafin biyu kamar yadda kika fadiwa abbanku... Is dat taken?"
Ahankali nace"Insha Allah Umma bazamu watsa miki kasa ah idanuwa bah..."
Tace"Good ku tashi Kuje lokaci na kurewa... Allah yai muku albarka... Aysha, Suhaiman Abbanta Allah ya tsare. "
Duk muka amsa da "Ameen. "
Har waje ta rakomu, Abba tun bakwai ya wuce aikinsa. Sai da Umma taga tashiwar motarmu sannan ta koma ciki.
Na kira my mubeen na shaida masa tashinmu tare da tambayarsa address, yace idan mun iso Na'ibawa kawai na kirasa.
Ahankali na furta"Kanon Dabo...... see you soon!!!!
Wai what’s really going on between Leedar, Fadima and Suhaima? Ku dai Ku biyoni🏃
For Now... Let's watch out @ Fadima Sa'ad's visit to Kano which will be seen in chapter six (babi na shidda)... Thank you and don't forget to vote.
To be continued
#’Yar Mutan Naija#
***