SHIN SO DAYA NE?

11

by @hafnancy

SHIN SO DAYA NE?

    

Hafnancy...

Zazzafar soyayya, Cin amana, mugunta da kuma Sadaukarwa

#Free Book#

    11.

*…Bari Mu Waiwayi Mubeen..*

Tunda motarsu Fadima ta tashi, ya bi motar da idanuwa,bai daina kallonsa ba har sai daya ga motar ta bar layin.

Tambayar kansa yake, ‘anya na kyautawa Zahrata kuwa?’

‘Meyasa zan boye mata cewar ina da mata har da 'ya?’

‘Meyasa zan b'oyewa dangina zancen soyayyata da ita akan dalili mara tushe Wanda na lura abinda ma yafi bak'anta ranta kenan?’

Tambayoyin daya shiga jerowa kansa kenan wanda bashi da amsar ko daya. Gunjin kukar Hanan ne ya dawo dashi daga duniyar tunanin daya lula.

Sannu ahankali ya juya ya soma takawa har yakai inda take tsaye take kukarta mai tab'a zuciya.

Ganin ya iso dab da ita ne ya sanyata saurin d'aga masa hannu,tace"Meh kuma zaka ce min? Koh ba'a fad'a ba kowa ya shaida ka fi sonta akaina.... Na maka abinda kakeso don farin cikinka mijina ya fiye min komai... Zan iya jure ko wani irin kuncin rayuwar da zan shiga in har akanka ne, Inaso ka bani izini ni da kaina zanje na nuna wa Mummy cewar nice na baka goyon bayan ka k'aro wani auran..... Abu Jasmine bana k'aunar wani abin ya sameka sabida ba karamin so kake yiwa wannan baiwar Allahn ba, ka bari kawai inje in fahimtar da Mummy "

"And do you think this is a minor problem da har kike tunanin tunkararta da wannan maganar? "

Murmushin takaici yayi, sannan yace"Hanan ke kanki kin kwana da sanin cewar yadda mummy ke masifar kaunarki ba zata taba yadda na karo wani auren bah.... Ke dai kawai ki bari zanyi handling wannan issue din da kaina, zanyi k'ok'ari in sameta da batun zuwa gobe "

Kokarin magana take ya katseta ta hanyar rungumota"Shhhhh! Its okay Hanan dita karki sake cewa komai.... Kuma bana son kina fadin cewar nafi sonta akanki... No, kowacce da matsayinta azuciyata,  zan mah iya cewar matsayinki yafi nata aguna because ke din 'MATATACE' kuma 'UWAR YA'YANA'........ Don gashi muna expecting wani babyn very soon.... "

Ya fadi hakan tare da shafo 3months old pregnancy dinta wanda babu wanda zaiyi tunanin tana da ciki sai su d'in da suka san da abinsu.

Yace"Hanan d'ita I love you so much.. Hakika ke macece ta gari... Allah ya miki albarka matata"

Maganganunsa ba k'aramin dad'i sukai mata bah, don haka tace"Ameen mijina.....Mubarak d'ina nima ina mutuwar sonka... Pls kada ka juya min baya idan har Allah ya kaddara aurenku da sister Zahra..... "

Da sauri yace"Haba Hanan stop saying dat.... Taya za'ai na soma tunanin rabuwa dake? Idan har mah nayi hakan toh wallahi na cika babban butulu kuma na rasa mace ta gari wacce kowa zai so ace matarsa ce ke....Don Allah kisa aranki cewar ni dake mutu ka raba ne takalmin kaza insha Allah..... "

Murmushi tayi tare da furta"Thank you hubbyna...."

Yace"U most welcome wifey.... Gaskiya ni dai bazan iya shiga cikin gidan nan yanzu ba don ban shirya fuskantar rikicin Mummy ba .... Nasan tana cikin b'acin rai ahalin yanzu, dan haka zan bari ta huce idan yaso gobe zanzo na sameta sai muyi wacce zamuyi.......yanzu akwai abinda zaki dauka ne acikin gidan?"

Tace"Kayan sawanmu nida Jasmine kala bibbiyu ke ciki amma ga wayata nan ahannuna.... Sai kuma ita Jasmine d'in "Yace"Rabu da Jasmine ta kwana anan tunda dama gobe zamu zo..... Kinga taho mu hanzarta mu tafi gida kada hajiyar ta lek'o waje ta ganni.... "

Da sauri sauri suka shige cikin motar, ya jasu suka bar layin. 'Hotoro Dan marke' suka nufa inda anan gidansu yake.Shi da kansa ya fito ya bude gate d'in gidan sabida bashi da mai gadi (Mubeen kenan akwai shegen Kishi because, sabida Hanan ne yaki ajje mai gadi).

Yana gama parking, ya fito yaje ya kulle gidan, sannan ya dawo ya ciccib'i matarsa wanda sai faman zuba masa shagwab'a take.

Yace"babyna meye? "

Ashagwabance tace"Naga baka k'ira Sister Zahra ka tambayesu ya hanya ba.... "

Yana sane da Zahransa,baya iya daukar minti d'aya ba tare da yayi tunaninta ba, but baya cika son yana kawo zancenta agaban Hanan don yin hakan agunsa cin fuska ne.Yasan ita karan kanta Hanan d'in ba wai bata jin kishin Zahran bane, kawai tana dai daurewa ne.

"Baby wayarta ta mutu babu chargy.... So kinga koda na kira bazai shiga bah... Fatanmu dai Allah ya saukesu lafiya koh matata?  " Ya fadi hakan sanda ya direta ya hau kiciniyar bud'e entrance door d'in.

Rungumo bayansa tayi tare da fadin"Ameen mijin Hanan.... " adaidai lokacin ya k'arashe bude kofar, ya juya ya sake ciccibarta suka shige ciki, wannan karon ita ta taimaka masa ta hanyar rufe kofar still dai tana hannunsa.

Bai direta ako'ina bah sai kan matrimonial bed d'insu.

"Yace"Matar yanzu mai zamu ci? "

Tace"Nifa ban jin yunwa"

Lak'atar k'aramin hancina yayi, yace"Are you sure becuz ni dai banji..."

Daga masa kai tayi alamar bata ji din. Wanka suka yo,  sannan shi kuma ya d'auro alwala don biyan sallolin da ake binsa.

Sai data jira shi ya idar sannan suka kwanta, don sam bata iya bacci ba tare da ta jishi akusa da ita bah.Wannan shine abu na farko da take tunanin zata sha matuk'ar wahala da idan har ya auro Fadima sabida ya riga ya sabar mata da kwanciya akusa dashi.

Tunanin Zahransa ne ya fad'o masa arai... Koh yanzu awani halin suke ciki? Sannan kuma wani irin bala'in zasu je su tarar agida?

Rungumosa da Hanan tayi shine ya yanke masa wannan tunane-tunanen nasa.

Tace"Hubby oya addu'ar bacci.... "

Atare sukayi addu'ar tare da baiwa juna simple peck ah lips suna fad'in"Good night" to each other. Daga hakan wani nannauyar bacci yayi awon gaba dasu sabida dukkansu sunyi bala'in gajiya.

BANGAREN  LEEDAR

Leedar ne zaune saman sallaya ya idar da sallar asubahi. Ya hau rera karatun Qur'ani cikin zazzak'ar muryarsa mai dadin sauraro. Bashi ya dakata daga karatun bah har sai daya ga gari ya soma haske sannan ya ijje Qur'anin yaje ya kwanta.

So yake ya koma bacci amman baccin yaki zuwa. Idan ya rufe idanuwansa yayi kamar zaiyi baccin sai kuma kaga yayi saurin bude idanuwan.

Kana ganinsa kasan yana tattare da damuwa, don hankalinsa mah ah tashe  yake.Dauko wayarsa dake saman gadon yayi, ya sanya k'iran Fadima akaro na barkatai, don tun yammacin jiya yake ta trying line dinta amman yaki shiga, sai faman ce masa 'switched off' ake.

Wannan karon mah 'switched off' d'in aka sake ce masa wanda haushin hakan ya sanyashi yin cilli da wayar saman gado har takai karshen gadon, kiris! ya rage ta fado k'asa amman koh ajikinsa.

Rasa inda zai sanya kansa yayi.

"Anya pretty tana lafiya kuwa?" Hakan ya fadi afilli cikin tsananin tashin hankali don shi dai sanin da yayi wa Fadima bata taba barin wayarta babu chargy,koda babu wuta toh za tayi charging d'insa da wutar Generator.

Ya tabbatar da cewar amsar tambayarsa yana ah gidansu Fadimar. Don haka ya yanke shawarar zuwa gidansu d'in idan gari ya gama wayewa.

Daga hakan bacci barawo yayi awon gaba dashi mai nauyi kuwa don bai sami wani wadataccen bacci bah adaren jiya,all thinking abouh Fadima Sa'ad.(Hahaha ke dai 'yar fillo kin shiga uku)

FADIMA SA'AD

Tunda na idar da sallar subhi na sami wani daddad'ar bacci yayi awon gaba dani tare da samin wata irin nutsuwa acikin zuciyata sabida na kwana ina ibada tare da karance-karancen al'Qur'ani mai girma.

Suhaima wacce tafi kowa morar bacci, ita d'in kuma ta riga kowa tashi. Tana kicin tana taya Umma had'a breakfast, wanda plaintain da potatoe chips suke ta aikin soyawa har suka kammala.Agefe d'aya kuma suka dafa ruwan zafin da za'a sha shayi dashi.

Umma ce tace"Suhaima pls ki gyara nan wurin zan shiga gidansu Madam Iyabo (makobciyarsu) 'yarta Rose ta haihu kuma tazo wanka gida.... So bazan dad'e ba sabida kada Abbanku ya tashi....." (Da yake Abban nasu da sassafe ya dawo).

Suhaima tace "ok" kawai, ayayin da Umma ta fice.

Suhaima tayi abinda aka sanyata sannan taje tayi wankanta taci kwalliya cikin doguwar riga 'yar kanti. No makeup juz natural tabar face d'inta amma still tayi k'yau sosai, dama can gata mai k'yau d'in ce.

Koh mintuna ashirin bai gama cika bah da fitar Umma, Suhaima taji ana bubbuga kofar falo.

Afilli tace"Kar dai ace har Umma ta dawo ? koda yake tace mun ba zata dad'e bah.... "

Ta mike don zuwa bude mata kofar because su basa barin entrance door d'insu unlocked.

Tana bud'ewa taga bah wacce take expecting d'in bace, ganin wanda ke tsaye abakin kofar ya sanya ta sakin wani malalaciyar tsaki tace"Wallahi da ace nasan kaine babu abinda zai sanya nazo na bude maka kofar nan.... Sai dai ka k'araci knocking d'inka, idan kaci sa'a wani yazo ya bud'e maka toh Alhamdulillah..... Idan kuma baka sami hakan bah,inka gaji ka wuce.... amma kam dai nayi nadamar b'atar da energy d'in wajen bud'e maka wannan k'ofar, Yanzun ma haka kullewa zanyi....."

Ta fad'i hakan ayayin da take kokarin maida kofar ta rufe, da sauri wanda ke tsaye abakin kofar ya tare kofar, da alamun dai yafi k'arfinta don turo kofar yayi da hannu d'aya ya shigo.

Murmushi ya sak'ar mata tare da furta"Ruhee kullum sai k'ara k'yau kike.... Tell me meye sirrin? "

Cike da jin haushinsa ta watsa masa miyau kan fuskarsa tace"Karka sake bakinka ya sake furta wannan sunar agareni because baka cancanci ka kirani dashi ba, Leedar na tsaneka sosai kuma bazan tab'a daina tsanar naka ba "

Da sauri yakai d'an yatsarsa saman lips d'inta yana fad'in"Haba Ruheena ki tsaya ki saurari abinda zan fad'a..... "

Da sauri takai hannu ta wanke masa fuska da Mari"Maci amana mai zan tsaya na saurara?.... Salon yaudararka koh kuwa meye?.... Wallahi tun wuri ka fita hanyar 'yar'uwata kafin nayi taking actions akanka....... "

Da alamun koh kadan baiji haushin Marin da ta masa bah, don Murmushi yayi tare da fad'in"Meyasa zan rabu da Fadima? Sabida kina mutuwar sona right? Tell me mana my dear u are now making sense..... Fad'a min ina jinki......? " Ya fad'i hakan tare da kashe mata ido d'aya................

Hayaniyar dana ji sama-sama shine yayi nasarar tashina daga daddad'ar baccina. Jin hayaniyar kamar daga falone kuma muryar Suhaima kadai ake ji ya sanya ni saurin d'aukar zumbuleliyar hijabina na sanya tare da saurin barin dak'in.

Ahankali na furta"Suhaima ita kuma da waye da safiyar Allahn nan? "

Na k'arasa falon adaidai lok'acin da naji Suhaima na fad'in"Haidar kaje na barka da Allah amma fah ka rubuta ka ajje cewar mak'iyarka ta farko anan duniyar itace SUHAIMA SA'AD..... I hate u so much...... "

"Anji kin tsanesa kuma ayau kinyi nasarar fad'a masa hakan gaba da gabanta duk da cewar kin sha nuna masa by ur actions, amma yau kadai kin fad'a masa agabansa..... sai dai ki sani cewar Yadda kika nuna kin tsani Haidar, hakan na nufin nima kin tsaneni kenan, Suhaima ki jira ki gani nan bada jimawa ba ni dashi zamu zama abu gud'a insha Allah.... ma'ana zamu zamo ma'aurata..."

Arazane ta d'ago kanta ta kalleni jin kalaman da suka fito daga bakina. Cikin tsananin tashin hankali ta furta"Sister Zahra Mubeen d'in faah? Shi kuma ya zakiyi dashi ? Karki gayamun har kin soma tunanin rabuwa dashi dan kawai yana da mata da 'ya................. Huh? "

HAFNAN'S POV

Tabdi jam!!! anfa zo gun....... Nasan kowannenku na Cike da mamaki kan abubuwan chapter din nan da dama.... So also I am!!

Shin meke faruwa ne tsakanin SUHAIMA DA KUMA LEEDAR? Becuz as we can see here ana nuna mana kamar bah tun yau suka san juna ba, sannan kuma kamar shi Leedar d'in ya tab'a gogawa Suhaiman bak'in fenti da har yasa tsanarsa yayi matukar tasiri a zuciyarta

Masu son double update kullum to su nemeni. Da 500naira d’inki kacal zaki mori karatunki, ta wannan asusun bankin 7065481260, Hafsat Mustapha, palmpay, sannan a turo da shaidar biya ta ***

To be continued..

#’Yar Mutan Naija#

***