𝒀𝒂𝒓 𝑵𝒐𝒍𝒍𝒚𝒘𝒐𝒐𝒅

E.P1️⃣1️⃣⏩1️⃣2️⃣

by @prettys01

CHANNEL 👇🏾
***

AREWAPEN
https://arewapen.com/u/prettys01




💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️

🕊️ *May Allah keep us united, uplift us, and make our pens a means of positive change.*

Much love and respect to each and every one of you. ❤️🔥  
*Keep shining, JAW family!* 🌺
  
  *JARUMAI WRITER'S TEAM📚✍️*


𝒀𝒂𝒓 𝑵𝒐𝒍𝒍𝒚𝒘𝒐𝒐𝒅

Story and writing✍️
      ```PRETTY SK```
           ~SAKINA ABDULLAHI~
> *PRETTYN JAJIRTATTU 💪✍️

       
 ✽‌»‌≿━༺🌹﷽🌹༻━≾»‌✽
 

E.P1️⃣1️⃣⏩1️⃣2️⃣




    *BAYAN WATA BIYU*
    
    A'isha ta ƙara shiga tafkin soyayyar Yaya Ayan, ba shi kulawa take kamar me, wasa-wasa shima yake kulata sosai, amma har zuwa lokacin ba ya jinta a zuciyarsa, sai dai yana so ya aureta ɗan abu biyu, na farko da soyayyar da take mai, na biyu ko dan ya kauce ma auren Ruma.

  *GIƊAƊO MANSION*

____________Gaba ɗaya sun yi shuru suna sauraran Baba Musa dake tsaida lokacin auren su, su 8, an sanya nan da wata biyar ne kacal. Ayan dake kallon iyayen nasa rai a haɗe ya ce.

“Baba ina da magana.” 

“Ayan ina jikin ka, yarona.” Sai da ya sosa kansa sannan ya saci kallon kowa ganin yarda suke binshi da ido, dakewa ya yi sannan ya ce.

“Kunfi kowa sani cewa banson Ruma...........wallahi banson ta da aure, sai dai ina sonta a matsayin ƙanwa, Ni ina da wacce na yi ma alƙawarin aure.” ya kai nan yana shirin miƙewa da sauri Baba Yusuf ya mai da shi ya zauna.

Idan ransu ya yi dubu ya ɓaci, balle ma Ruma da Mahaifiyarta.

“Me ka ce?.” baba Yusuf ya tambaya ransa a haɗe.

“Akwai wacce na yi ma.......” wani sanyayyar mari ya ji Abba ya sauke mai a kuncinsa.

“Kar ka mai da mu mutanen banza, wallahi idan na kuma jin irin wannan furucin a bakinka sai na saɓa maka. So kake mu yi watsi da wasiyyar mahaifin mu ko ya ya?.” ya kai nan yana ɗan huci. 

Ayan dake dafe da wajen, ya ɗan yi murmushi sannan ya miƙe tsaye.

“Shike nan, amma idan har wani abu ya bayya wa ƴan jaridu, kune sila, ina so na kare mutuncin gidan nan ne, amma tunda haka kuka ce shike nan.” da haka ya miƙe, yana musu kwarjini sosai, babu wanda ya dakatar da shi har ya fita, kowa cikin maimaita maganarsa suke yi dan kuwa babu abin da suka fahimta. 

Sun dai riƙe. “Ƴan Jaridu, mutumci."

Babu dai wanda ya yi magana a cikinsu. Ruma kuwa tuni hawaye sun fara gangaro mata masu zafi.....




Cikin wannan takun nasa wanda kai ka ce sarki ne ko shugaban ƙasa, haka yake taku ƙasa na amsawa.

Direct motarsa ya nufa sannan ya bar gidan, yau Sunday Babu school dan haka ya nufa gidansu Aisha wacce ta yi mai kwantan ce. 

A bakin get ɗin gidan su ya yi parking, sannan ya kira wayarta.

“Ina ƙofar gida."

“Okay ganin zuwa.” ta furta, da haka ya aje wayar yana ji kamar an yi mata abu dan yarda ta yi maganar kaman ranta na ɓa ce.

 Ilai sai ga ta fito fuskarta babu annuri duk da suprice ɗin da ya yi mata na zuwa babu notice.

Ta yi ƙyau cikin dogon Blue Black na hijab har ƙasa, fuskarta babu komai dan be ta ɓa ganin ta yi makeup ba.

Ba yarda ta iya ko dan rana ma sai ta shiga motar tana sallama, murmushi ya saki kafin ya amsa.

“Aisha bazata na miki amma naga kina cikin damuwa meya faru?.” ya tambaya yana jin babu daɗi da ganinta a haka.

 Kai ta girgiza mai.

“No faɗa min dai kin ji.” sai ta saki ranta dan dai komai ya wuce.

“Yaya Ayan ba komai walla...........” da sauri ta tsaida da maganar sakamakon ya sanya hannunsa ya kulle mata baki.

“Shhhhhh. Magana na zo mu yi mai muhimmanci amma idan ba ki faɗa min abin da aka miki ba, wallahi ba zan faɗa ba, kuma sai na.....”

“Shike nan zan faɗa maka.” ta faɗa tana gyara zamanta, shi kuma ya zuba mata fararen idanunsa akanta.

“Shalele ce.” sai ya yi murmushi, be ta ɓa ganin Shalele ba amma yasan akwaita da rashin ji, babu rana da za ta wuce ba tare da ta ɓata ma A'isha rai ba.

“Nikam wannan Shalelen duk randa na ganta sai na sa an rataye min ita, tana takura miki da yawa, me ma ta yi miki?.” murmushi ta ɗan yi sannan ta ce.

“Yau Sunday tana gida, wallahi tun asuba ta fara damuna, yanzu ta mun abu jima haka ta yi wani, kuma ban da ikon mata magana yanzu sai Mom ta ce *ina takura mata* kalla yarda ta fasamin yawa, wallahi da ganganga ta yarda shi, da na yi mata magana sai ta hau kuka wai natseta, shine ta faɗa ma Mom, sai Mom.................”

“Yi shuru na fahimta.” ya katseta dan kuwa gab take da yin kuka, a zamansu abu abu ya sani dangane da A'isha shine saurin Fushi ga ɗaukan abu da zafi.

“Zan siya miki waya shike nan.”

“A'a na gode, ai tsaga ne kawai.” ta faɗa tana kallon wayar da ya fashe sosai, har ya taɓa screen ya yi baƙi gefe ɗaya.

“Gobe insha Allah zan tawo miki da waya. Yanzu dai babban magana ne ya kawo ni.” sai ta mai da hankalinta a kansa.

“Aisha.” ya faɗa cike da rauni mai haɗe da taushi.

“Na'am.”

“Nasan kina sona sosai, balle a yanzu da nake baki lokaci na, sai dai aure tsakanin mu abu ne mai wahala saboda wata *WASIYYA* ” 

Take ya ba ta taƙaitaccen labarin *Giɗaɗo Family* tare da abin da aka yanke a gidansu yanzu.

Wani abu ta ji ya doki zuciyarta, ta sauri ta rintse idanunta tana maimaita duk abin da yace.

“Yanzu......a...a...aure za ka yi?." Sai ya yi murmushi.

“Nasan za ki ce me yasa na miki haka. Me yasa na fara kulaki ko?.” sai ta ɗaga mai kai.

“Ni kaina banson auren.........uhmmmmmm ina da shawara amma yana da wahala sosai, in ɗai za ki iya to aure tsakanina da ke kamar an yi.” buɗe dara-daran idanunta ta yi tana kallonsa kamar yarda yake kallonta.

“Akwai wahala.” ya sake faɗa kamar mai raɗa.

“Koma menene shi zan yi muddin zamu yi aure.” ta faɗa tana jin zafi a ranta har lokacin. 

“Gidan mu suna da abu guda ɗaya, idan har akan mutumcin gida ne to za su iya komai dan ganin be zuba ba, nasan kunsan familyn sosai ko da a labarai, to akwai son riƙe mutuminci.............yanzu mu mafita ɗaya ne tak mutumcin Familyn zamu yi ƙoƙarin mu ta ɓa, idan muka musu bayani to za su yarda.”

“Bangane ba Yaya Ayan.” sai ya ja dogon numfashi sannan ya ce.

“Uhmmmmm........Mu'aluma matar da miji kafin aure.” zaro idanuwanta ta yi dan jin furucinsa, dan kuwa ba ta yi tsammanin jin haka daga bakin sa ba, kai ta fara girgiza mai hawaye na gangarowa daga idanunta sannan zuciyarta ta tsananta bugu cikin sauri-sauri........................✍️
END.



> Duk wasan yara muke, har yanzu ba mu shiga labarin ba.

Kar a manta Like 👍 and Comment. Ngd SOSAI.