MAKAUNIYAR ZUCIYA

SHIMFIƊA

by @alhunqawee

Sanyin damina yanayi ne da yake taka muhimmiyar rawa wajen sanya nishaɗi a zuƙatan dukkanin al'umma, hakan baya rasa nasaba da yadda iska mai haɗe da ƙamshin ruwa ke busawa. Bugu da ƙari ga furanni da bishiyoyi da ke rangaji suna ƙoƙarin samar da lafiyayyar iska. Sai dai akan samu saɓanin wannan nishaɗin wajen wasu daga cikin jinsin mutane masu fama da wata lalura.

Yammacin ranar Asabar; yammaci ne da ya zo ɗauke iska mai daɗi da ke busawa sakamakon hadarin da bai gama washewa ba, mutane ta ko ina suna ta zirga-zirgarsu ba tare da fargabar dawowar ruwan saman da ba a jima da ɗaukewa ba.

Sai dai duk da sanyin garin a jiƙe na ke sharkaf da gumin da ke faman keto mini ta kowane lungu da saƙo na jikina kamar wanda ya haɗiyi kunama. Kiyayewar Allah ita ta zama linzamin ƙarasowata harabar asibitin ba iyawata ba, duk da jami'an kan titin da su ka yi ƙoƙarin tsayar da ni tare da jama'ar gari da ke bi na da zagi da tofin ala tsine sakamakon tuƙin gangancin da na ke yi, hakan bai sa na saurara ba sai da na kai ga inda na ke hanƙoron zuwa. Ban saurari kiran da yaran ke yi min ba balle in rufe ƙofar motar na nufi cikin asibitin, cikin wani irin mawuyacin yanayin da ni kaɗai na ke iya tantance abinda na ke ji a zuciyata.

A bakin ƙofa na ci karo da Salmanu yana biye da Shirgegen likitan da yake juya tumbinsa kamar na mai tsohon ciki, Salmanu na nufa da a kallo ɗaya na karanto damuwar da ke shimfiɗe a saman fuskarsa.

"Muna buƙatar jini da gaggawa domin ceto rayuwar baiwar Allahr nan, amma, kafin nan a je a fara zuwa da waɗannan magungunan da na rubuta."

Abin da na iya tsinta ke nan daga maganganun da likitan ke shaidawa Salmanu wanda daga haka ya fara juya tumbinsa yayi gaba bayan ya umarci Salmanu da ya biyoshi ofishinsa domin ƙarasa maganar.

"Salmanu ya jikin na ta? Me ya sameta ne haka?"

"Kamar dai yadda ka sani ciwonta ne ya tashi sakamakon canjin yanayi da aka samu sai dai wannan karon ciwon ya zo da wani yanayi da har ƙafarta ta gagara taka ƙasa."

Hannu na sa na dafe kaina da ya fara yi min dakan lugude, tsananin nadama ta sake yi min ɗaurin huhun goro a karo na barkatai. Ba zan gushe ina mai kallon kaina a matsayin mutum mai son kai ba, mutumin da ya zaɓi son zuciyarsa ya wofintar da iyalinsa.

Tamkar raƙumi da akala haka na ke bin bayan Salmanu zuwa ofishin

likitan.

"Salmanu gaskiya kuna sakaci da lafiyar baiwar Allahr nan. Da ace kun san haɗarin da take ciki ba za ku bari ciwonta ya dinga ta shi a kai a kai ba"

"Likita, wallahi ban san komai ba game da tashin ciwon a yau ba, na dawo ne dai na sameta a sume bayan ta gama shan murƙususun da na fahimci hakan ta yadda shimfiɗar da aka sirranta gadonmu ta yaye."

"Likita don Allah faɗa min kai tsaye, me ya samu ɗiyata?"

Na katsesu daga musayan zancen da su ke yi ne domin na zaƙu in san halin da ɗiyata ke ciki.

"Duk da ƙoƙarin da mu ke yi don ganin ta tsallake wannan matakin abun yana neman ya fi ƙarfinmu domin ƙafarta ta taɓu."

"Ban fahimceka ba likita ka yi mana bayani yadda za mu fahimta."

"Kamar yadda na yi maku bayani a baya, masu lalura irin nata akwai lokacin da ƙashin kan cinyarsu ke fara zaizayewa sakamakon katsewar gudanuwar jini. Sakacinku bai wuce yadda ku ke bari ciwon na motsa mata irin haka ba har a samu rashin wadatuwar jini a jikinta. Wannan katsewar gudanuwar jinin babban ƙalubale ne ga masu ɗauke da lalura irin nata. Domin shi amosanin jini lalura ce da ke janyo cikas ga gudanuwar jini a sassan jiki, hakan kuma na shafar ayyukan sassan jikin har da ƙashi. A yayin da ƙashi ya rasa isasshen jini zai fara yin rauni sannan ya fara zaizayewa har kuma daga ƙarshe ya lalace. Ƙarin jini a yanzu shi ne matakin farko da za mu fara ɗauka domin rage ma ta raɗaɗi da azabar da ta ke fuskanta."

Salmanu ne ya ke ƙara jaddada min maganar Likita ta nemo jinin da za a ɗaurawa Ummulkhairi, sai dai kafin nan na buƙaci ganinta hakan yasa yayi min jagora zuwa ɗakin da aka kwantar da gudan jinina, ɗiyar da na zama silar gadar mata da abinda zai iya zama sanadin bankwanarta da duniya a ko wani loƙaci.