SHIN SO DAYA NE?

15

by @hafnancy

SHIN SO DAYA NE?

    

 Hafnancy...

Zazzafar soyayya, Cin amana, mugunta da kuma Sadaukarwa.

   15.

Wasa-wasa zazzabi ya rufe Hanan.Jikinta duk ya d'au zafi, da alamun hannun nan ne ya saukar mata da zazzabin.Sai da Mubeen yai mata allurai har uku tare da sanya mata drip bayan ta samu ta danci abinci.Sai aikin bacci take ta Zubawa bana wasa bah.Duk hankalin Mubeen ba'a kwance yake bah sabida duk Hanan ta bi ta rud'ashi, gashi yana son ya k'ira Fad'ima amma bai samu damar hakan ba, sannan kuma fushin da Mummy tayi akansa bah karamin damunsa yake ba.

Kanwarsa Labeebah ce tayi masa waya take fad'a masa cewar gata akofar gidansu, don haka yazo ya bud'e mata.Cikin sanda ya fice daga d'akin gudun kada ya tashi Hanan.

Yana gama bud'e gate d'in, Labeebah tace"Wai ni Yaya sai yaushe zaku soma barin kofar gidanku abud'e ne? Wai ace kullum gida baka taba samunsa abud'e sai dai koh wani lokaci akulle... sai kace wani gidan kurkuku? "

"Yo! don sarkin garinku so kike ko wani gardi ya shigo gidan unexpected ya gane mini mata anyhow right? "

Murmushi tayi tare da rik'e hab'a, tace"Hmm! Ina ruwansu brother kakannin kishi kenan..."

"Tukunna dai..... Meya fito dake da goshin magrib d'in nan wanda kamata yayi ace warhaka kina d'akin mijinki? " yayi mata wannan tambayar, wannan karon babu alamun wasa tattare dashi. (watanta shidda kenan da aure).

Tace"Daga Na'ibawa muke.... Shine Mummy tace mu taimaka mu kawo Jasmine tunda duk kusan unguwa d'aya muke daku...... " Ta fad'i hakan tare da nuna Mus'ab mijinta wanda rike yake da hannun Jasmine suna kokarin karasowa inda suke.

Musabaha sukai da Mus'ab d'in, suka gaisa amutunce with due respect.

Jasmine ce ta saki hannun Mus'ab, da gudunta ta rugo ta rungume Mubeen, ayayin da shi kuma ya dagata sama.

Tace"Daddy I really missed you.... amma ina fushi dakai hadda mummy tunda kukai tahowarku jiya kuka banni acan gidansu granny inata kuka.... "

"Sorry babyna bazan k'ara bah kinji... " ya fad'i hakan tare da marairaicewa kamar zai saki kuka.

Juyowa yayi ga su Labeebah wanda suka shagala ga kallon soyayya irinta d'a da mahaifi, yace"Mus'ab bismillah mana ku shigo... "

Duk Jasmine tabi ta dameshi da surutu.

"Daddy kaga Uncle ya siyamin tsirei da youghourt akan hanyarmu ta zuwa nan...ga bag d'in kayanmu ni da mummy can ahannun Anty wanda ta manta dashi acan jiya.... "

"Laah! Lallai wannan uncle d'in yana son 'yar babyn nan tasa... Hope dai kince masa thank you? "

Da sauri tace"sosai mah... Lodi lodi mah Kuwa... "

Aka fashe da dariyar maganarta wanda adaidai lokacin suka shigo cikin falon.Jasmine sai tambayarsa inda Mummynta take.

Yace"Baby mummynki bata da lafiya... she's in the bedroom sleeping, so don't wake her up okay? "

Ahankali ta daga kanta alamar taji maganarsa.

Labeebah tace"Ayyah! brother ya jikin Anty Hanan d'in? Mummy ta fad'a mana cewar bata jin dadi and again taji rauni ahannunta..... "

Da sauri yace"Eh!! tsautsayice ta afka mata... ta yanke ne da wani glass amma da sauki yanzu.... "

Mus'ab yayi masa jaje tare da tambayarsa mai jikin.

Labeebah tace"Bari na d'an dubota.Ta mike zatayi d'akin Hanan d'in, da sauri yace"No, tana dakina.... "

Jin hakan ya sanyata Juyawa ta nufi direction d'in d'akin nasa.

Tana zuwa kuwa taga Hanan d'in har lokacin baccinta take abinta.

Ahankali Labeebah tace"idan banda abin namiji... Mai mace kamar Hanan ta nema ta rasa, yarinya gata dai k'yakkyawa, mai hakuri da kuma godiyar Allah... She has everything da duk wanda yake jin shi d'in classic man ne zai so atare da Ita... Toh mai zaisa yaya yayi tunanin karo wani aure? "

Girgiza kanta tayi, ta juya ta fice daga dakin zuwa falo.

Tana isa falon tace"Brother please I want to have a talk with u... "

Gabansa ne ya fad'i, ba tare da tunanin komai bah ya mike yana cewa "ok".

Wani karamin falo suka je.Zama sukai akan kujeru daban-daban.

Yace"ina sauraronki.... Kuma kiyi sauri kada Mus'ab ya gaji da jiranki... "

"Yaya Mubarak why? Mai ya shiga cikin ne yau da har ka iya tsayawa ka fuskanci mummy ka fad'a mata maganganu son ranka abin da ko amafarki idan akace kayi shi, am very sure bazaka tab’a iyawa ba? Matar data nuna mana so na tsakani da Allah tamkar ita ta haifemu., Wai itace ayau kake mata tuni da cewar ba ita ta haifeka ba?"

Ta ci gaba da magana tana ciccije leb’e.

"The most suprising part shine da aka fad’a min cewar ka had'a k'ashi da wanka. Kuma wai duk akan wannan shegiyar kake neman b'atawa da family dinka?"

An zo inda ba zai iya hakuri ba sbd an tab’o rabin ran nasa, cikin zafin nama ya mik'e ya isa gareta, babu wani b'ata lokaci ya d’auketa da wani zazzafar Mari.

Nan da nan ta fashe da kuka don azaba, ta ce

"Yaya ni zaka mara don na fada maka gaskiya?”

Sake d’auketa da mari yayi, yana huci yace"An mareki d’in, ke kin isa ki taso kizo har cikin gidana kina min nasiha, har nawa kike Labeebah da har zaki sanyani agaba kina min fad’a? Iyyeh?.... Okay I understand.... Mantuwa kikai da ko waye babba tsakanin ni dake.... to bari in tunasar dake, Ni Mubarak nine 'wa' ayayin da kuma ke Labeebah kece 'kanwa'."

A fusace ta mike tana fad'in"Yaya Mubarak godiya nake kwarai da gaske.... Amma ina son ka sani cewar ita wacce ka zabeta akanmu, insha Allahu asannu zata gwada maka halinmu na mata..."

"Fitar min agida before I loose my temper na tattataki anan wurin.... "

Ya fad’i hakan da karfi.

A yanayin da take ganinsa tasan tabbas zai iya aikata abin da ya fa’da sbd mahaukacin son da yake wa Zahransa.

Hakan yasa tayi ta kanta ta fice da daga falon da gudu tana fad’in

"Shegiya, mayya... Waya sani ma ko wankewa tayi ta baka kasha.... "

Biyota yayi har falon ya sake d’auketa da wani gigitacciyar mari a gaban mijinta Mus'ab.

Sakin wani k'ara tayi don hakika wannan Marin yafi shigarta Akan sauran.

Yace"Ina ruwanki idan mah wankewar tayi ta bani nasha?... Kinga Labeebah kiyi sauri ki bace mun daga gani idan ba haka ba wallahi jikinki ne zai gaya miki gaskiya"

Mus'ab ne ya taso zuwa inda suke, don tun suna dayar falon yake tajin hayaniyarsu da kuma karar Marin da matarsa take tasha, amma kunya ya hanashi zuwa inda suke.

Da alamun wannan karon Mubeen yakai shi bango, yace"Haba Yaya ina ganin girmanka, don haka kada ka sake girman nan ya zube ah idanuwana..... ai wannan yawa ne ka daki 'ya mace kuma matar wani akan idonsa mah, babu koh kunya..."

Azuciye Mubeen ya juyo yana kallonsa, yace"Hey! Man shut the hell up!.... kai kuma asuwa ? Kare da gudun layya ? Who are u to interfere into a family matter?.... look, wannan abu tsakanina da 'yaruwata ne dan haka ka cire bakinka aciki "

"Idan kai KANWARKA ce, toh ni kuma MATATACE..... Don haka nasan darajar 'ya mace, so karka sake ka kuma taba mun mata...... " Mus'ab ne ya fadi hakan cikin tsananin b'acin rai.

Murmushi Mubeen yayi tare da fad'in"Kasan mey? Ku tafi kawai... Amma kasan meyasa zan kyaleka?... sabida kai d'in sirikina ne kuma bazan so ace na had'a kashi da siriki na bah... ai kaga da kunya ko? Dan haka maza ku gaggauta barin mun gida kafin nayi loosing temper d'ina "

Mus'ab yace"Ko baka fada ba dama Muna da niyyar wucewar"

Juyawa sukai suka fice, Labeebah sai kuka take ayayin da Mijin ke aikin lallashinta.

Koke-koke kunnuwansa suka jiyo masa daga bayansa, juyawarsa keda wuya, idanuwansa suka kai ga Hanan wacce take rungume da Jasmine, sai aikin kuka suke.Hannun Hanan wanda aka sanya mata drip dashi sai d'igar jini yake, sabida cire drip d'in tayi ta fito jin hayaniyarsu.

Da gudu Jasmine ta ruga ta rungume Daddyn nata tana kuka"Daddy mai yasa ka mari Anty Labee kuma kayi wa Uncle Mus'ab fada.... Gashi yana da kirki sosai ya siyo mun tsirei da youghourt....mey suka maka? gashi Anty Labee sai kuka take"

"Yanzu dai kaji dadi tunda 'yarka taga abin kunyar daka aikata akan idanuwanta.... Don mah bata ga na dazun kenan bah wanda yafi wannan tashin hankali.... Haba mijina akan 'ya mace kake neman b'atawa da family dinka? Ni naga mah wannan yarinyar ba wani damuwa tayi akanka bah sai idan mah kai ka nemeta.... Wannan yarinyar Sam bah alheri bace ga rayuwarka Abu Jasmine.... Pls ka gaggauta rabuwa da ita tunda yan'uwanka basa so."

"Hauwa'u!!!!!! " kiran sunanta yayi da k’arfinsa wanda tunda yake bai taba ambaton ainihin sunanta bah sai ayau.

Gabanta ne ya hau bugawa da sauri da sauri,ignoring d'in Jasmine yayi, ya nufi inda Hanan din take zaune.

Tsugunnawa yayi daidai saitinta, yace"Daga yau sai yau... Karki sake interfering acikin relationship d'ina da 'FADIMA ZAHRA' ..... Nagode kwarai da gaske da dukkan taimakon da kika min... Amma daga yau, karki kara sanya baki acikin maganarta tunda naga kin soma gajiyawa da taimakon nawa, tunda har zaki iya cewa in rabu da ita, Hauwa'u Ina sonki amma ki sani bazan iya hakura da Zahra ba...... "

Mik'ewa yayi ya nufi daki, yana jin sanda ta rushe da wani sabuwar kuka mai ban tausayi wanda sai daya ji kukan na dukar zuciyarsa.

Dawowa falon yayi da auduga ahannunsa, ya goge mata inda jinin ke fita.Ya rungumo 'yarsa wacce har yanzu kuka take. Lallashinta ya soma yi tare da mata wasu 'yan dabaru da wasannin.. Kun san yara ai,nan da nan ta ware, ta dauko tsirenta da youghourt ta hau ci.

Komawa yayi inda Hanan take,zama yayi agefenta tare da ruko hannayenta, yace"Hauwanah!! Pls am so sorry... Forgive me... Wallahi na rasa ko wani irin soyayya ne haka nake wa Fadima wanda hakan yake sanyani fada da family d'ina akanta... amma na dau miki alk'awari daga yau na canza, No more fighting da yan'uwana akanta.... "

Hanan bata san lokacin da wani murmushi ya subuce mata bah,rungumeshi tayi tana murna.

Yace"Buh hakan ba wai yana nufin na hakura da ita bane........................."

Kallonsa take cike da mamaki........

*******

Har zuwa wannan lokacin Mubeen bai nemeni ba, haka zalika nima d'in ban nemeshi ba. Tunanin Suhaima ne ya fado min arai.Atlast, ayau ta gane cewar da gaske son Leedar take wanda ada take musa min.Hmmmm!  That means game d'ina da Leedar will soon be over wanda bah hakan naso ba dan game d'in ya soma mun dad’i. Lallai Suhaima da sauranki, amma saina tabbatar da cewa kin azabtu yadda nakeso kafin mu kawo k'arshen wannan wasar.

Wanka nayi na tafi makaranta kasancewar yau litinin. Ash na kira don zuwa makarantar nan da zanyi ayau kacokam domin ita da Leedar ne, don bamu cika yin much lectures ran litinin ba.Ayau nake son na bayyanawa Ash komai dake tsakanina da ALI HAIDAR Leedar ...........................

           

HAFNAN'S POV

Tofa jama'a akwai bidiri kenan.

Shin wani game kuma Fadima da Leedar suke playing?

Wannan kuma wani irin mahaukacin so ne Mubeen kewa Fadima da har ya sanya yake fada da yan'uwansa akanta?.... Ku dai ku biyo Hafnan.

To be continued..

#’Yar Mutan Naija#

***.