2
by @asmybaliyu
HAWAYEN MARAICI
By
Asmy b Aliyu
2
Alh. Yusuf mai keke haifaffen dan garin Bauchi ne haka kuma dan siyasa dan kasuwa ya rika mukamai da dama ya rika mukamin senate, Dan majalisa hka aka gangaro kan governor ya xauna a kujerar governor.
Bayan ya sauka ya fada harka kasuwan ci inda ya buda wani babban company na motoci da sunan sa ( mai keke motors)
(Mai keke petroleum) da sauran companies waya'ndda ake ji dasu a kasar nan Alh Yusuf mai keke yyi fice a kasar nan Nigeria da wajen ta haka mutunen mai tausayin gaske ,Sam Sam baya kyankyamin tallakka A kullum gidan sa cike yake dam da mutanen Arziki.
Haka yana da manya-manyan gonakki wandda a duk shekara yake nome amfanin gona mai yawan gaske ,anan take ake lodasu a fita dasu kasuwan ci garuruwa daban-daban
Masu karatu zakuyi mamaki idan nace maku duk wannan dukia dake da Yusuf mai keke ,shi daya ne dal A gurin mahaifinsa Wandda yake a matsayin da namiji ,sai mata kwaya biyu da suke bimasa sadiya itake bima Yusuf akwae shekara 5 a tsakanin su sannan Salma wadda take bima sadiya ita kuma shekara 2 ne a tsakanin su . xo kuga yarda dan uwansu ke nuna masu so tun suna yara Dan maifin su ya rasu tun yana da shekera goma sha takwas a dunia.
Babu laifi maihaifinsu yabar masu dukia shima shahararren Dan kasuwa ne ,haka ya mallaki gonakki tun kaka da kakan ni bayan rasuwar mahaifin su ,mahaifiyar su Hajia Asma'u macce mai sanin ya kamata mai kokarin hada kan ya'yanta ta cigaba da basu tarbiya inda Yusuf ya tafi UK. Yyi karatunsa a fannin kasuwanci...
A gurguje Yusuf mai keke yana da matar aure kwaya daya Hajia laila ,asalinta balarabiya CE ya'r kasar misra A saudiya suka hadu da Yusuf mai keke a nan suka fara soyayya bayan dawowarsa gida Nigeria ya tuntubi hajiar sa da xancen Duk da yana fargabar hajjah dinsa baxata amince masa ba .
Amma ga mamakinsa sai yaga tayi masa fatan Alkhairi haka ma su sadiya da salma lokacin ita sadiya tana aji shidda na secondary school Yayinda salma take aji ukku na secondary ..
Bayan Auren Yusuf da lailah ,ya daukota cikin ya'n uwan ta ya kawo ta garin Bauchi inda ya Gina wani babban Estate ,dake unguwar (g r a)dake nan cikin garin bauchi.
Wanda shine suke a ciki.bayan aurensa arxikinsa ya Dada habaka ,yana rayuwa ne acikin gidan shida matarsa mahaifitarsa kanninsa ,shekara daya da auren sa aka samu cikin Abdulhakeem xo kuga tsananin son da Hajia Asma'u ke nuna ma Lailah bayan wata Tara ,ta haifi Dan ta namiji mai kama da mahaifiyar sa sak!!
Dan a zahirin gaskiyya Yusuf mai keke bakin mutum ne sai dai yana da kyau ,Anyi shagalin suna anyi bidiri tamkar ba'a san xafin naira ba.
Shekarar Abdulhakeem biyar A dunia lokaci daya aka yiwa Sadiya aure da wani ma'akacin banki abokin Yusuf ne ,lokacin hidimar kula da Abdulhakeem ya dawo gurin salma wankan sa Abincinsa shirin makarantar sa gabadaya salma keyinsa wani irin so suke nunawa yaron Dan uwan nasu.
Shekarar Abdulhakeem goma cif a dunia lokacin laila na da tsohon ciki a jikinta cikin bakaramin wahala yake bata ba ,bayan haihuwar ta da kwana biyu rai yayi halinsa dan ko kafin ta haihu ta zubar da jini dayawa.mutuwar ta girgixa Yusuf .ta haifi kyakkyawar ya'rta mai kama da Abdulhakeem haka aka radawa ya'r sunan lailah Abdulhakeem shima mutuwar ta girgixa sa inda ya dauki son dunia ya dorawa Ya'r kanwar tasa ...
Tun tana karama yake kiranta da Mimi, Saboda sunan hajia Laila taci tun a waccan lokacin ..haka sunan ya cigaba da binta shekarar ta biyu a dunia ,ana shayar da ita madarar yara lokacin kuma Alh.yusuf mai keke ya dauke Abdulhakeem ya kaisa UK. Karatu..
Bayan shekara goma sha biyar
haka Abdulhakeem ya cigaba da karatun sa a UK ...acan ya gama secondary school inda ya fada jamia ,yana da shekara Ashirin A dunia yaxo Nigeria ya samu mahaifinsa ya auri wata banufa amma a Bauchi take rayuwar ta Hajia jummai Haka kuma lokacin mahaifinsa ya tsunduma cikin siyasa ,yadda yaga jummai na tsananin kulawa da Mimi yasa ya saki jiki daita wandda a zahirin gaskiyya a xuciyar Hajia jummai ba haka bane ,tana son duka ta saye xuciyar ya'n gidan ne kafin ta fito masu da ainahin kalan ta na gaskiyya .Yusuf mai keke yana matukar son Hajia jummai musamman irin kyautatawar da take yiwa mima ,dan a lokacin Aunty salma tariga tayi aure inda take auren Wani farfesa dan jahar kano ne haka yana aiki a nan jami'ar Ahmad bello .
Jinin dangin mijin nata ko kadan bai hadu ba Basa kaunarta, haka ma mahaifiyar su Hajia Asma'u kawai dai kullum Tana ma Dan ta Addu'a Allah ya karesa da sharrin mutum.
haka kuma a lokacin yana cikin tsaKkiyar siyasa , wannan xuwan da yayi Abdulhakeem yaga gata sosai gurin matar uban nasa . da yake shi ba mutunen ne mai son hayaniya ba da kuma son magana komai nasa cikin sanyi yake yinsa haka yake tun yana karamin sa.
Da hajja tamasa complain din matar ubansa murmusawa yayi inda yake cemata hajja mum bata da matsala bakiga yadda takeson mimi bane ,kawai dai keda su Aunty ne Baku fahimce taba,
Baki so mum ta kawo maki jikoki ??
A wasance xata jefesa da filo tace Allah ya raba Yusuf dinta ,bata ma so mum ta haihu da Yusuf Sai dai Abdulhakeem
ya kanyi daria yace hajja rigimar ki yawa garesa.
Cikin haka Mimi ta shiga Aji daya na secondary school, da haka shikuma Abdulhakeem ya koma UK.
Abdulhakeem yana shekarar karshe A jami'r wanda shima yayi karatu a fannin kasuwan ci ne kwatsam yaji rasuwar mahaifinsa mutuwar da ta girgixa tunanin sa ta haifar masa da ciwon zuciya wandda sai da ya kwanta gadon Asibiti shekara biyu ya kamu da tsananin ciwon zuciya.
Da kyar da Addu'a da sadaka Hajja tasamu jikanta ya dawo lfia wandda a shekarar da ya tashi ,sai da hajja tasa sukaje umra duka har mima lokacin tana aji 6 na secondary.
Da yake shima Abdulhakeem ba banxa bane gurin Addinin Islam ya samesa sosai ,haka yyi ma mahaifinsa Addu'a da mahaifiyarsa.
Shekara ukku da mutuwar mahaifinsa ,ya koma UK Ya cigaba da karatunsa Dan da yanxu ya gama shekarar sa hudu acan ya samu ya hada masters dinsa ,ya tattaro ya dawo Nigeria.
A haka ya cigaba da jagorantar dukiar mahaifinsa ,haka kuma abun mamaki dukiar sai kara habaka takeyi dan Abdulhakeem kaman yafi mahaifinsa kwarewa akan harkar kasuwanci.
Mum ganin bata aje ko kwai a gidan ba takara samun gurin xama ta cigaba da kula dasu Abdulhakeem ba wai dan tana son suba hanya take nema ta samu ta kashe Abdulhakeem kamar yadda ta Kashe mahaifinsa a sirrance Dan ta cigaba da jagorancin dukiyar tunda taga su Aunty sadiya da salma basu damu da dukiyar ba uwa uba hajja suna gida daya amma sai tayi sati bata sa hajja a ido ba.
A yanxu haka shekarar AY 34 A dunia duk wannan tsawon shekarun nasa baita ba kula wata macce ba da sunan so duk da kuwa ya'mmata sun sha kawo masa hari ,hajja tayi fadan rashin Auren sa har ta gaji haka ma su Aunty sadiya .
Akwai wata rana da aunty sadiya ke fada masa idan bai fitar da mata ba zata hadasa da ya'rta ta biyu wadda sa'annin juna suke da Mimi ,Rukaiyya haka kuma kawaye ne Mimi tana yawan xuwa gidan tayi kwana biyu.
AY. Yakan yi daria haba Aunty sadiya daina hadani da Rak Mana haka yake kiran Rukaiyya karamar yarinya CE fa ni har yau ban ga matar aure ba ne shiyasa."
Haka suka xuba masa ido dan likitansa ya tabbatar masu da cewa ciwon sa baison yawan damuwa .
A haka Abdulhakeem ,ya buda wani babban Asibiti da sunan mahaifinsa [YUSUF MAI KEKE HOSPITAL ] haka ma makarantan islamiyya da na boko
Wanda ya saka sunan maiahifaiyarsa.
Kwatsama wata rana wata kawar Hajia jummai ta kawo mata ziyara dake xaune a garin Legos ita da ya'rta jawaheer ,Dora idonta akan Abdulhakeem shikenan ta rude da kyawunsa.
Suna a xaune take tambayar mum wannan fa?"
Wai Abdulhakeem
dan maigida nane margayi mum ya xa'ayi ki shigar dani a gurinsa wallahi ya riga ya lashe xuciyata ina sonsa !!!"ta fada sounding so very free ,
Ido waje mum ke kallon jawaheer,nan take mahaifiyar jawaheer
tayi kicin -kicin da rai meye haka Jummai?" Naga kin wani fiddo da ido.
Ajiar zuciya mum ta sauke ,ba haka bane Hajia azumi yaron nan baya son Aure rayuwarsa haka ba'a so a takurama Rayuwarsa Dan yana da ciwon zuciya ko wane lokaci yana iya tashi uwar ubansa ma tayi fada ta gaji barantana ni ..
Maman jawaheer taja tsaki bansan yaushe kikayi sanyi har haka ba jummai."
Tunda jawaheer ta tabbatar da tana son Abdulhakeem ai mu da talauci har Abada ke kanki xakiyi mamakin dukiar da xaki Tara anan gaba kawo kunnen ki kiji kawata.
Anan Hajia jummai taba kawar tata kunne murmushi hajia jummai tayi tana kallon kawartata kai Azumi baki da dama to yanxu yaushe xa'a kawo mun??
jibi insha allahu."
Zakiga yadda Abdul xai xamar maki bawa sai abunda kikace nasan aurensa da jawaheer cikin wata daya an gama komai,
Gaba dayansu suka kwashe da daria har jawaheer,
OMG!
Mamy na!
Dan haka nake tsananin sonki I love you so much mamina."
Allah ya bar min ke"
2 days letter .
Aka aikowa da Hajia jummai kulin magani a daren ranar tasaka ma AY Shi a abinci ,washegari ta tunkaresa da maganar jawaheer,
Ga mamakin ta sai taga ya amince babu musu haka ta gargadesa akan kar ya fadawa su hajja ya'n uwanta maxa tasaka aka je nemarwa Abdul auren jawaheer a garin Lego's da yake ubanta bayerrabe ne yaga kudi nan take ya amince.
Anan aka biya sadaki da komai ,haka mum taje Dubai itada jawaheer suka hado kayan lefe na gani na fada
Har wannan lokacin Abdulhakeem baita ba tsayawa da jawaheer ba Dan shi har ga Allah baya jin son jawaheer ko kadan a ransa dan dai baya iya yiwa mum dinsa musu ne kawai.
Jawaheer irin yaran nan ne sangartattu gogaggun ya'n bariki haka idonta ya bude sosae akan abun duniya jawaheer babu kayan mayen da bakinta baisan dandanon su.
Sai dai muce Allah ya kyauta kawai.
Anan mum ta shiga gayyatar manyan kawayenta da kuma ya'n uwanta ana gobe daurin Aure hajja taji labari itada ya'yanta ko shi mijin Aunty sadiya yaxo mata da labarin.
Hajja tayi mamaki sosai ,shiyasa ta kullaci Abdul aran ta.
Ita kuma Mimi dama bata kasar tana kasar india tana karantar medicine dan shine burinta tun tana karama Wannan kenan..
Cigaban labari.....
#HAWAYEN MARAICI
#AY MAI KEKE
#LOVE/ROMAINE
#HAUSA NOVEL 2026
#ASMY B ALIYU
#***