KUNCIN ZUCI

Kuncin zuci

by @bintuuu

Da qarfi Na'ima ta turasa baya hawaye na kawowa idonta sai ta sauke hannunta daga fuskanta, cikin daga murya tace "Don't touch me, get out Bilal" ya marairaice yace "Please listen to me Na'ima i just.. i just want you back" rufe idonta tayi a tsayen ranta na suya, aranta tana ayyana tayaya Bilal ya samu courage din magana irin haka a gabanta, sai kawai ta bi gefensa zata fita ya dawo da ita ta tsaya bakin sink din yace "Na'ima akan wa'encan baren zaki gujemu 'yan'uwan ki, haka kikeda butulci a rayuwa?" muryanta na rawa tace "Dama kai dan'uwana ne Bilal? dama ka taba sanin hakan? indai sai na koma qangin da na baro a gidan ka sannan zaisa 'yan'uwana su dawo gareni to na yafesu" sai kuka yaci karfinta ta sake cewa "Ko ni kadai zan yi rayuwa na gwammace in yafeku duka da in koma gidanka" Bilal ji yayi jikinsa kamar an kwara masa ruwan qanqara a lokacin, ya tsaya kallonta ya kasa cewa komai dan bai da wani hujjan magana kuma, yananan tsaye aka turo kofan restroom din sai Na'ima tayi saurin duqawa tana wanke fuskanta acikin sink, Husna ce ta shigo tana fadin "Na'ima har yanzu ba.." sai tayi stiff bata qarasa maganan ba tana kallon Bilal dake tsaye nesa kadan da Na'iman, tace "Hey, haven't you read the sign outside? It's says females only" sai sannan Na'ima ta dago kanta tana kallon Bilal din, cikin sanyin jiki ya juya ya nufi qofan fita daga restroom din, qarasowa gurin ta Husna tayi tace "kinsan sa ne sis? ko baki lura yashigo bama" Na'ima na wanke fuskan ta tace "Ban ma lura yana baya na ba" Husna tayi tsuka tace "Yan iska, sai kace makafi ne su basa iya banbanta signs na gender awajen" Na'ima bata ce komai ta dago tana kallon fuskanta a madubin, adan kwanakin baya zuciyarta ya fara sauqa akan abunda Bilal din ya mata amma aduk lokacin da taci karo dashi yake qara tada mata duk wani ciwon dake kwance a zuciyar ta, sai da ta jira Husna tayi nata uzurin dan Mami ce ta aikota ta duba mata Na'iman saboda ta dauki lokaci sosai, da suka fita sai Husna ta fada mata su Nafisan sun fita lokacin grand entrance dinsu yayi, sai ta gyada kai ta nufi fita ta kofan bayan Hall din ta zagaya, acan entrance ta samesu amma ba entrance dinda suka shiga ta nan ba dazun, Dean dinsu ne a gaba riqe da ceremonial mace zai jagorance su, nan cikin line din Na'iman ta kusa tareda excusing kanta har ta idda Nafisa dake fadin "Haba Na'ima kin dade fa, da munshiga babu ke fa" tace "I'm sorry" da haka suka shiga Hall din a jere ana tafa musu, Ahmad da Lamin ne suka fara miqewa suna tafi tareda su Abu a row din da familyn ke zaune, sai su Mami da Abba har su Mamman suka bi baya, tafi suka rinqa yi su Abu har da kai hannu baki yayi fito na murna, fuskan Na'ima cike da murmushi suka qarasa gaban shugabannin makarantar, Bilal dake zaune cikin mutanen Hall din yayi ta kallon Na'iman har zuwa lokacin da sukayi bowing kansu kadan agaban professors din nasu, sai ya juya yana ganin yanda iyalin WADZANI suke ta tafin murna da farin ciki, ya sake juyawa ya kalli Na'ima data juyo kadan ta kalli familyn nata tana murmushi me fadi sannan ta juya aka nuna musu hanyan da zasu fita, in akwai abunda yafi mutuwar jiki toh Bilal ya jita a wannan lokacin, this is not the Na'ima he knew before, wannan ba Na'iman da aka taba kawo ta gidansu daga qauye bace, wannan ba Na'iman da tayi rashin gata abaya bace, sake juyawa yayi yana kallon su Abu da suka nufi fita daga Hall din zasu bi bayan su Na'iman, sai ya tsinci kansa da dan duqar da kai ganin Ahmad ya dan juyo da kansa ta side dinda yake zaune.
Bai sake ganin ikon Allah ba sai da ya fita haraban Hall din ganin yanda duk familyn suka zageya Na'iman da Nafisa kowa yanason yin hoto dasu, in Na'ima ta dauka da wannan sai wannan ya jawo hannunta adauka again, Hugs kuwa ta shashi ta ko ina, da tazo kan Faruk sai ya miqa mata hannu da nufin suyi handshake, dan kallon Ahmad tayi ganin yana tsaye a varenda din Hall din hannunsa cikin aljihu yana kallonsu ga Lamin da kuma Abba agefensa yana magana da wani babban mutum, sai ta juya ta miqa hannunta sukayi shake din yace "Congratulations sis, i pray this will be the beginning of your new beautiful chapter in life" hannunta na cikin nasa tana murmushi ta amsa da "Thank you yaya Faruk, thank you for everything" yana kallon idonta yace "You're welcome anytime Habibitin Mami" sai ya juya yana kallon Ahmad yace "Kije kuyi hoto dasu Abba da Yaya mana" ta gyada kai sannan ta zare hannunta daga cikin nashi duk akan idon Bilal dake tsaye can nesa dasu, da taja Nafisa sukayi hoton dasu Abba din wanda itada Nafisan na tsakiya while Abba da Ahmad na gefe, nan ma su Abu dasu Al'ameen suka shiga harda Faruk din sukayi nasu na maza, Nafisa na murmushi aka dauka musu tareda Lamin wanda har sannan kowa dauka yake kara ya musu a matsayinsa na abokin Ahmad yazo gurin taron, bayan an gama sai Ahmad yaqi barin gefen Na'ima yana tsaye sai yayi qasa da murya cikin rada yace "My beautiful Na'eemah" sai ta fara juyawa tana duban ko ana kallonsu amma sai taga anata hotuna ne hankali baya kansu, data juya ta sake hada ido dashi sai yayi murmushi ko a jikinsa yace "In kama hannunki sai su san what is going on here?" ayanda tayi saurin barin gurinsa sai da abun ya basa dariya amma beyi ba, sai yayi murmushi yana bin bayanta da kallo, aikuwa juyawan da zeyi idonsa ya fada kan Bilal dake tsaye can nesa, duk wani annuri bacewa yayi daga fuskan Ahmad ya gyara tsayuwa yana kallonsa.
Naima komawa tayi gurinsu Mami suka yi hoton tareda dasu Mamma da Anty Fatima, shima in group sukayi na iya matan, sai sannan Mami ta samu sararin Hugging yaran nata, bayan tayi hugging Nafisa tazo kan Na'ima ta rungumota tana fadin "Ma Sha Allah Habibiti na, Allah ya qara kawo tarin nasarori cikin rayuwanki" sai sannan idon Na'ima ya fada cikin na Bilal dake kallonta shima cikin ido, bata dauke idonta ba ta rinqa kallonsa Mami na shafa bayanta, sai da Anty Amnah taja hannun ta tana cewa "Daughter zo ku gaisa da sistern Abban twins" sannan ta dauke idonta suka tafi, sai shima Bilal din ya juya yana tafiya a sannu zai fita daga premises din yanajin jikinsa na sanyi, at that moment..that moment da ya kalli mutanen dake zagaye da Na'ima ya gane wani abu da bai taba sani ba, He was never for once, 'Her Family'...talkless of a Brother to her. Ahmad dake tsaye a gefe har sannan hannuwansa cikin Aljihu yabi Bilal din da wani irin kallo sannan ya juya ya kalli Na'ima dake gaisawa da qanwar Abban twins cikin fara'a, sai dariya take suna maganan, sai ya sake juyawa yana kallon Bilal har ya fice daga premises din...

Sai da aka gama duk hidiman sannan gabaki dayansu suka tafi gidansu Na'iman banda Lamin, dan Abba cewa yayi zai je ya ga inda yaran nasa sukayi rayuwa tukunna, Mamma da duk sun gaji aka tafi tare dasu can, cika falon sukayi matasan na zaune a dining area sukuma matan na zazzaune a falon, Abba ma na zaune bisa kujera twins suna jikinsa, saida duk akayi salla sannan aka bude kayan ciye ciyen da suka siyo kala kala ahanya, su Na'ima da Nafisa sannan Husna suka hau serving kowa a plates suna miqawa, hira sukeyi sosai afalon, da Na'ima sukaje serving din su Ahmad kanta a qasa take zuba masa abincin, sai kallon hannunta da yasha henna yakeyi sai ya dago kai suka hada ido tayi saurin nufan su Abu tana taya Nafisa zuba musu mixed salad din, sai da suka gama sannan suka zauna nan gefen su Anty Amnah suka fara cin nasu, da aka gama suka tattare komai, sai mazan duk suka dawo cikin falon suka zauna sannan aka fara bawa su Na'ima da Nafisan gifts, Abba ne yafara musu albishir yace "Saura Umrah yaran Abba, that's my gift to you" idon Na'ima sai da ya kawo hawaye tana godiya Ahmad na ta kallonta, Nafisa ma ta hau tafin mura zata koma wani umrahn, Mami tace "Nidai zuwana shine gift dinku" akayi dariya sai Mamma tace "A'a, yarana basu yarda da hakan ba" ta qarasa fadin hakan tana miqo musu babban box guda biyu mai dauke da dadduma, Qur'an da kuma tasbaha acikin kowanne, kowa na falon sai da ya bada nasa kyauta, Faruk daman sabbin waya ya ba kowannensu, Al'ameen kuma Ps, Abu kuma sai ya nuna musu hoton Art frame dinda yayi musu installing a saman gadon su na can gida cikin dakin kowannensu, Husna ta basu sarqan gold me dauke da harafin sunansu, Anty Amnah da Fatima ma da nasu wrapped gift din.
Saida kowa ya gama basu kyautan sai duk aka juya ana kallon Ahmad dake danna wayansa hankali kwance, Jin kamar falon yayi shiru yasashi dago kai yana ganin yanda suke kallonsa, Anty Amnah ta daga masa gira daya alamun shi ake jira, sai ya kai hannu aljihun jamfan dake jikinsa ya ciro wasu papers guda biyu ya miqawa Nafisa yace "The car is yours, I'll shift it back home to you" wani tsalle Nafisa tayi tana murna, Mami na murmushi tace "Ji shirme" Nafisa tace "Yaya nagode Allah ya baka abunda kakeso" ta qarasa maganan tana kallon Na'ima da ke wasa da bakin gyalenta, sai kuma duk aka sake zuba masa ido alamun ina na Na'ima, Faruk ma wannan karon shi ya daga masa gira daya, shi Ahmad abun nasu dariya ma yake bashi sai ya kalli Abba yadan sunkuyar da kai yace "Abba ina neman amincewan ka na barin Na'eemah tayi amfani da App dinda na bata, nayi mata transferring all ownership regarding my App Bizgo, sannan na baiwa Nafisa wani crypto App dina itama" dan stiff mutan falon sukayi, Mamma na mamakin dogon maganan dan nata, Al'ameen yace "Theee Bizgo?" Ahmad ya gyada kai sai Abba yace "Shi menene?" Mamma tace "Ahtoh duk yakai motan ne, adai bawa daughter babban abu itama" Abu ne ya fara dariya sai Al'ameen ya dafashi suka rinqa dariyan tare Husna na tayasu da Anty fatima, Mami na murmushi tace "Wa'ennan, Allah ya shirya" Faruk ma yana danne dariya yace "Mamma App din babban ne sosai, sannan yasamu global ne kuma, ataqaice zai iya bata 500 thousand US dollars duk wata" Mami ta kalli Ahmad din sai Mamma tayi murmushi tace "Ma Sha Allah, ka kyauta sosai, duk da haka muna maulan motan muma" sai Faruk yace "Zan siya mata ai Mamma" tace "Yauwa dai" Anty Amnah na kallon Ahmad tana ta murmushi itada Anty fatima ganin har sannan bai kalli kowa a falon ba, Husna na murmushi ta zauna gefen Na'ima da har sannan kanta na qasa tanajin wani iri itama, Abba yace "Muna godiya son Allah ya biyaka" kan Ahmad na duqe yace "Nagode Abba" ahankali Na'ima ta furta nata godiyan bata dago ba sai Nafisa ma tace "Mungode Yaya Allah ya biyaka" ta sake dago takardan motan nata ranta tasss, dan ita bata App din take ba ma, saboda kaf cikin yaran falon babu wanda net worth dinsa baya bashi fin abunda Na'iman zata rinqa samu a watan, that's why babu wanda yayi mata qyashi cikinsu, sai suka cigaba da lamuransu kamar babu abunda ya faru, da su Mamma suka tashi tafiya sai Ahmad ya rigasu fita, Na'ima na zaune taga text dinsa sai ga kira ya biyo baya, miqewa tayi a sannu ta nufi balcony kamar wadda zatayi waya sai ta leqa qasa ta hangosa jikin motansu kare da waya a kunne, tsayawa sukayi suna kallon juna babu wanda yayi magana a wayan Na'ima najin bugun zuciyarta na sauyawa har sannan batace komai ba tana kallonsa, ahankali yace "Sai a Nigeria zan sake ganinki Babe?" ta gyada kai tana sauqe kanta qasa sai ya sake cewa "Look at me Na'eemah" kasa dago kanta tayi, Jin yayi shiru sai ta dago din taga kallonta yakeyi yana murmushi, ahankali ya sake cewa "Gobe zan wuce Lagos, nima na gama zamana a qasarnan" sai ta samu kanta da cewa "Yaushe zaka koma Abuja?" yace "Next week Babe, Next week kinji" ta gyada kai tana murmushi ahankali tace "I'll be waiting" yana murmushi ya cigaba da kallonta, sai da taga fitowan Faruk yana nufan Ahmad din tace "Allah ya kaiku lafiya" ya gyada kai tareda cewa "Amin, take care" da haka sukayi sallama ta koma cikin apartments din nasu....
A washegarin ranan su Na'iman suka kama hanyar barin Oxford bayan sun karbo certificate dinsu a inda ta samu distinction Nafisa kuma ta samu second class upper amma, Abba yayi farin ciki sosai ya rinqa shafa kansu yana cewa "I'm proud of you my kids", wani farin ciki Na'ima ta rinqa ji ganin murnan iyayen nasu, tana ganin soyayyarta a idanunsu, a zuciyarta tana fadin "What more could she wished for after this?"....
Ranan da suka dawo Nigeria daman ko gyara kayansu basuyi ba su ka rinqa bacci a dakin Nafisa dan a dakin Na'ima suka loda kayan nasu, da safe basu tashi ba sai guaren 9 sannan suka fito yin breakfast, suka samu Mami na zaune da Faruk suna cin abincin, ganinsu yasa Mami cewa "Kun tashi" Nafisa ta gyada kai tana hamma tareda jan kujera ta zauna, da Na'ima ta zauna sai Mami ta zuba abinci a plate ta miqa mata sannan ta zubawa Nafisa itama, suna ci Faruk yace "Yara welcome to labour market" Nafisa ta ajiye cup din tea dake hannunta tace "Sai nayi shekara ina hutu tukunna" Mami na murmushi tace "Ji lalaci" sai Faruk ya kalli Na'ima yace "Na'ima kefa" cikin sanyinta tace "Duk abunda Allah yayi" Mami tace "In sha Allah ko wanne aiki kikeso, matuqar bai sabawa addini ba zakiyi Habibiti" Na'ima tayi murmushi sai Nafisa tace "I thought we were a team Na'ima, i rest...you rest" dariya su Mami suka fara Faruk yace "Sannu mamanta" sai Na'ima tace "A'a zan huta din nima Yaya" ware ido yayi ganin zasu hade masa kai sai Mami tace "Kwaji dashi dai, bari sai kun dawo daga Umrah muji me Abbanku zaice akan batun aikin" Na'ima na murmushi tace "Toh Mami" su Lamin ne suka shigo falon, Mami tace "Wai dama baku tashi ba kuma" dan tun asuba ta gaisa dasu, amsa mata sukayi tareda zama, Na'ima ta miqe tayi serving dinsu abincin sannan aka cigaba da hiran dasu....

Zaune Ahmad yake cikin wani tsadadden Bar dake cikin garin Lagos, ya kishingida jikin leather seat din tareda crossing legs dinsa yana kurban champagne cikin glass cup din hannunsa, ta gefensa wani inyamuri ne shima adan jingine da kujeran wanda duk jikinsa yasha tattoo da chain a wuya yana zuqan taba, Bar din babban ne wanda kana gani kasan ba wajen zuwan yaro bane sai wanda yakai, magana Ahmad din keyi sama sama da inyamurin me suna Don Mazzy, wata mace ta zo cikin yari yarin kaya ta zauna a gefen Mazzy din wanda ko kallon inda take Ahmad beyi ba yana danna wayarsa da hannu daya, sai da ya gama typing message din da yake yiwa Na'iman sannan ya ajiye wayan ya kai hannu gurin qaramar brief case dinsa dake gefensa ya ciro wani folder ya jefa akan glass table din da ke gabansu, yana kallon Mazzy yace "I need every details on them, Everything..." Mazzy yakai hannu yana ciro hotunan da suke cikin foldern sannan ya zubasu akan table din, Hotuna ne kusan guda shida, tun daga kan Bilal har iyayensa da Nasir sannan na Stella, Mazzy na kallon hotunan yace "My, My, what do we have here?" sai ya dago kai yana kallon Ahmad din yace "Boss, you know it's gonna cost you big, right?" Ahmad yace "Name your price" sai Mazzy yace "10 M, scratch that..15" sai Ahmad ya gyada kafada yace "Done...I'll make it 30 if you conduct everything in a week and deliver it to me with a package" sanin me package din yake nufi yasa Mazzy yin dariya yace "Ahmad you're a Bad guy" sai Ahmad yakai hannu yana zaro hoton Bilal sannan na Nasir ya turasu gaban Mazzy yace "I want them in wrapped package" Mazzy yace "Let me handle them for you nah, let me end them in one go" sai Ahmad ya girgiza kai yayi sipping champagne din sannan yace "No Man, i want them to taste something different" ya qarasa maganan yana kallon Adam dake nesa dasu yana buga snooker da wani friend dinsu bahaushe..Bayan sun fito daga Bar din zasu koma gida sai Adam yace "What's with you and Mazzy again?" Ahmad bai kulasa ba ya nufi wajen baqar jeep dinsa dake fake a gaban gurin, bin bayansa Adam din yayi ya sake cewa "Ahmad" sai sannan ya juyo ya kallesa, sai Adam din yace "Banaso kasani, the last time da na ganka tare dashi, you almost killed Saddam after that" anutse Ahmad yace "Kana ganin ina shiga gonar mutum in bai shiga tawa ba?" da zafi zafi Adam yace "Abunda ya faru tsakaninka da Saddam yawuce abadan sannan ka rama Ahmad" rai abace shima Ahmad yace "Yeah.. that's the problem with me Adam, i don't tend to forget things easily, kuma Billahi..ko waye ya shiga gonata sai na masa iyaka" shiru Adam yayi yana kallonsa da mamaki sai yace "Who is it this time?" Ahmad bai amsa ba ya bude motansa ya shiga tareda tayarwa ya figeta yabar Adam din nan tsaye shima ransa na baci, a sannu ya nufi tasa motan yana tuna incident din da ya farun tsakanin Ahmad da wani competitor dinsa da ya masa wani tuggun da ya taba Ahmad din sosai....