HAWAYEN MARAICI

3

by @asmybaliyu

HAWAYEN MARAICI

By

Asmy b Aliyu

3

hajja ta shiga ciyar dashi kallon cikin fuskarta yakeyi Wanda yake hango tarin damuwa acikinta hannunsa yasa ya debo dakakkiyar sakwarar da taji Jan miya a hankali ya isa kan bakinta daita haka ya tsareta da manyan idonsa ,babu musu ta buda baki ya saka mata da haka suka shiga ciyar da junan su.

Aunty sadiya da Aunty salma na gefe suna kallon su soyayyar da hajja da Abdulhakeem sai Allah bayan sun kammala cin Abinci ya dan kalli aunty salma da murmushi Aunty yaushe kika xo??

"Daxun nan ta jirgi ma na biyo daga kano xuwa Bauchi jia da dare Aunty sadiya ta kirani take sanarda ni Aurenka " Ashe ka canja ya'n uwa bamu sani ba Abdulhakeem ??"murmushi yayi a hankali gamida cije leben sa na kasa haka ya kama kunnensa duka biyu ya langabe kansa yana kallon Aunt's din nasa am sorry nayi laifi kaina bisa wuyana ni na isa na canja mahaifina."

Aunty sadiya ta zabga masa harara nikam na fasa basa Rukaiyya yanxu kam Rukaiyya tafi karfinka kamata tsufa sai kai sai jawaheer waya sani ma Age mate dinka ce."

Ya kalli Aunty sadiya sai kuma ya dan tabe baki ni mezan yi da Rak! Ae tayi min karama."

ya mike tsaye ya kallesu xanje na huta.

Ya dan subbaci goshin hajja I love you hajja ." murmushi hajia tayi a hankali gamida Shafa lallausar sumar kansa tareda fadin " may Allah bless you my child da sassarfa ya bar part din hajja .

Hajja ta maida hankalinta kan ya'yan nata ajiyar xuciya ta sauke yaron nan tausayi yake bani ,kunsan meyasa na kasa yimasa magana?? Gabadayan su suka girgixa kai lokaci daya haka suka xuba ma mahaifiyar tasu Ido idan muka nuna masa bama so ,xai daga hankalinsa ne ina tsoron ciwonsa ya tashi kawai muyi masa fatan Alkhairi .Allah baya bacci Allah ya shiga tsakaninsa da duk wani makirci na jummai."

Abunda nakeso yanzu

Ku tashi ku shiga wajen jummai cike da bin umurni suka mike dukan su xuwa part din mum.

Yana kwance akan coach farar best ce ajikinsa sai bakin wandon Tree quarter wayar sa dake gefe tayi kara ganin sunan dake yawo akan screen din wayar yasa yayi banxa da mai kiran.

Karo na biyu wayar ya kara shigowa a fusace ya daga wayar me kuma ya faru??"

Sassauta murya sagir yayi kana Ina ne gani a gida ina ta Neman ka mum tace ka shigo amma ka fita ,ina son muyi magana."

Dan shiru AY yayi kamar bazai ce komai ba kafin yace ina part dina"Okey gani nan zuwa ." Katse Kiran yayi cikin minti biyar sai gaya shi part din nasa da sallama ya shiga kira'ar AbdulRahman Sudais kawai ke tashi a kayataccen falon nasa wandda aka kawata sa da komai fari Sol.

Sagir ya xauna daya daga cikin kujorun da suka kawata falon yana fuskartar abokin nasa ,Remote ya dauka ya tsayar da karatun .

Wai meke faruwa ne AY??"

Da yake haka friends dinsa suke kiran sa Nigeria da wajenta ga jawaheer can tana kuka da sauri ya kalli sagir,

Kana son ka sani ? Ya

yi mganar fuskarsa bbu walwala

Baxanje Dinner ba shine kawai amma gobe su hajja xasu hada kayatattar waleema nifa kasan duk wannan bidi'ar baya gabana sageer!!

So please mubar ma wannan maganar haka na fadawa mum

sagir ya xubawaa abokin nasa ido

yasan halinsa fiye da sauran friends dinsu idan yace no babu mai sashi yayi haka ma idan yace yes bbu Wanda ya isa ya canja sa .

Sageer ya mike tsaye hannayen sa duka xube cikin aljihun wandonsa

Alright !

Ni xan tafi gida na huta

Su tafida suna hotel xuwa anjima dai xamu hadu.

anan yasa kai yabarsa batare da ya jira amsar daxai basa ba.

Waya ya daga ya danna wa hajja kira akan A kawo masa ruwan lipton,

8:30pm.Na dare dukan su suna a harabar gidan su biyar ne da alamar friends din AY ne sageer Tafida ,farook ,jalal, Nura . AY Yana a tsakiyarsu ya hade cikin wani tattausan bakin yadi da babbar Riga taji dinkin xamani,Shigen baka ramin karbarsa yayi ba kasancewar shi mutum ne mai son shigen manyan kaya kananan kaya ma bai fiye saka suba,

sae a lokacin zafi .

Tafeeda ya kallesa

ango kar kaje ka saki baki kana barci gobe flight din karfe goma zamu bi xuwa Abuja nida jalal hakama Nura xa yabar Bauchi xuwa kano ,sauran farook da Sageer xa'a barku tare ne kuci amarci koya kukace guy's?? "

Gabadaya suka fashe da dariar shakiyanci yau gaka ga macce ,sai muga ya xakayi xuba mata ido xakayi ko yaya Tunda anki ba su Tina da leesa dama."

Dunkule hannunsa AY

yayi da nufin yakai wa Tafeeda duka da sauri ya gofce ya naushi iska kai dai Dan iskane Tafida naga sanda xaka canja jalal yayi saurin amshe xancen da fadin nidai Ticket din Honey moon na nan na jiran Ku ko wace kasa kukeson xuwa mijin jawaheer!!!

Gabadaya suka fashe da daria insha allahu soon xamuje honey moon. " Ku xauna nan a matsayin tuxurai

mukam mun shige daga ciki.

Abdulhakeem ya fada yana gyara babbar rigar sa sageer, ya duba agogon hannunsa mukam suna bata mana lokaci muna so muje mu Hutu tunda ango ya hana aje dinner.

Sageer yayi maganar yana kallon AY ta gefen ido nidai ban hana kowa zuwa dinner ba ."nidai kawai nace baxan jeba."

Wayar AY tayi kara yana duba kiran yaga aunty sadiya ce ,ya daga wayar Abdul kana ina??

Ganinan tareda su sageer kaxo ka dauki amaryarka a side din hajja mun gama .ohkey Aunty ya kalli su sageer guys sai Allah ya tashe mu lafia xanje na dauki amaryata gabadaya suka kalli juna tareda hada baki gurin fadin "Abun harda su kora da hali anan suka shige motocin su Ay yana daga masu hannu gamida sakar masu kayataccen murmushi har ya daina ganin su kai tsaye part din hajja ya nufa...

Masu karatu idan nace zan tsaya na fada maku haduwar part din Abdulhakeem xai daukeni tsayin lokaci ban gama ba amma bara na Dan takaita .

Babban falo ne wandda komae nasa dark purple ne da white yana dauke da katon bedroom har kwara hudu acikin sa sae gefe kitchen da katon store wandda yake lode da kayan abinci .akwai katon bene acikin falon inda xai daukeka zuwa part din AY Wanda komae nasa white ne ..

Duka suna xaune a falonta itada friends dinta sai yaba gidan nata sukeyi billy CE tayi saurin katse ya'mmatan zip din Jakarta ta zuge ta fito da wata ya'r karamar kwalbar turare ta damka ma jawaheer a hannunta ,meye wannan??

Cewar jawaheer ta fada tana ya tsine fuska.

Murmushi billy tayi wannan xaiyi maki matukar amfani kawata shixai daga darajar ki a gun mijinki basai na tsaya yimaki dogon sharhi ba keda kanki xaki bani labari idan komai ya kankama.

Mun barki lafia sai xuwa gobe anan suka tafi suka barta nan ta mike tsaye ta fara zagayen gidan ,Wanda har lokacin bata ji motsin AY ba duk da ranta a mugun bace yake da Ay din yadda ya ruguza Mata duk wani doki da take

Akan dinner party din da ta tsara itada friends dinta ,Sai da mum dinta da hajiya jummai suka sakata a daki

Dan lokaci daya ta birkice masu.

kai tsaye bedroom ta ta nufa wandda komai na ciki lemon green ne kasan cewar tana son Abu green shiyasa mamin ta tasaka aka saka mata komai green da ratsin fari.

Kayan jikinta ta rage ,tareda Dora Dan karamin towel anan ta shige wanka.

Yana kan sallaya da alamar yanxu ya idar da sallah kaidar sa kenan baya sallah Shafa,i da wutri sai xai kwanta barci ya daga kansa ya xubama agogon bangon dakin ido karfe goma sha daya dai-dai na dare.

A hankali ya dan ja tsaki baya son ya shiga hakkin mutum ko kadan A rayuwar sa balanta na matar da take karkashinsa bedshoe dinsa ya saka kai tsaye ya nufi down stair xuwa part dinta.

hannunsa ya aza akan kofar dakin yafi minti biyu a haka kafin ya tura kofar dakin wani sanyayyan kamshi ya daki hancin sa ,hada ido kawai da sukayi daita gabansa sai da yyi wani irin buguwa tana cikin wata rigar barci Mai daukan hankali kalar maroon wacce ko cinyoyinta bata gama rufewa ba.

A nan ya shiga karema halittar ta kallo jawaheer irin fararen mutanen nan ne mara su kiba Amma tana da cikken kugu haka tana da cikar dukiyar Fulani ..murmushin mugunta ya saki lokaci daya Dan da alamr jawaheer baxata iya da yawan bukatar sa ba dan shi mutum ne Mai yawan bukata dan haka ma yake azumin litinin da Alhamis.

Tana taje gashinta tana hangosa ta dressing mirror tana kallon yadda yake kallonta yau ne rana na farko da ya mata kallon tsaf!

Bbu laifi tana da tsayin gashi sai dai kuma bai fiye baki ba.

Sallama yyi gami da shigowa cikin dakin gaba daya, a hankali ta amsa batareda ta kallesa ba gefen bed yayi wa kansa mazauni sunfi minti biyu a haka ba wandda ya kara cewa uffan har jawaheer ta gama dunkule gashin kanta guri daya taxo ta xauna gefen sa .kamshin turarenta yana fisgarsa nan take ya fara jinsa cikin wani irin yanayi .

Kana bukatar wani abu ne??" Ta fada fuska babu walwala Dan har lokacin fushi takeyi dashi ,ki hada min ruwan lipton haka Leda na nan a kitchen ki gyara kayan dake acikin a katon faranti ki sameni A part dina.

Yana maganar ne batare da ya kalleta ba itakuma tayi nisa gurin kallon kyakkyawan fuskarsa musamman bakin sa ,da yafi tafia da imanin ta da sauri ya mike tsaye har yakai bakin kofa

idan xaki fito kifito da kayan sallarki da haka yaSa kai ya fice daga dakin ..

Murmushi jawaheer tayi wandda tarasa ko na menene lokaci na farko kenan da yayi mata magana mai tsayi haka ,abun tambaya anan shine ko yafara Sonta ne??

A yadda yake maganar tamkar maganar yana masa wahala komae nasa burgeta yakeyi.itakam tana son Abdulhakeem tana addu'a Allah yabar mata shi har karshen numfashinta.

#HAWAYEN MARAICI

#HAUSA NOVEL

#LOVE STORY 2026

#JAWAHEER TAUFIQ

#AY MAI KEKE

#ASMY B ALIYU

#***