BAFULATANA🐄

Chapter: 4

by @zmchubado

🐄BAFULATANA🐄

Z.M~CHUBAƊO✍️

          04

A nitse moddibo ya Ƙarasa kusa da matashin ya sinkuya da murmushi  a kan fuskarsa ya ce "sannu da jiki Yaro kashe doguwar jinya."

Cikin harshen fulatanci moddibo ya yi maganar. 

Da ido kawai matashin ke bin moddibo ba tareda ya san abinda yake faɗa ba. Kallon Rabe Baffa ya yi ya ce,"da alamafa ba yajin abinda muke faɗa." ya ƙare maganar da damuwa akan fuskarsa.

Ita dai ba tace komai ba ta zuba masu idanu kawai tana kallonsu, don bata san abinda zata ce ɗin ba. Shiru Baffa ya yi yana nazari na ɗan lokaci, musamman da ya fahimci  matashin baya gane abinda yake faɗa saboda banbanci yare, can sai dabara ta faɗo masa ya kalli matashin cikin kwaɓaɓɓiyar Hausarsa wadda bata fita sosai ya ce "Shannu yaro ya shikejin ƙarfin jukin naki?"

Tunda Baffah ya fara magana matashin ya yi shiru yana  kallon motsin bakinsa har ya kai ƙarshe, ajiyar zuciya ya sauke sannan ya buɗe baki da nufin ya amsa tambayar da ya yi masa amma muryanshi bata fita sosai saboda sanyin rugar daya jima da toshe masa ƙirji ya ce"Alhamdulillah I'm feeling better."

A ɓangaren Baffah ba abinda ya tsinta a maganar matashin sai Alhamdulillah, sauran maganar kam bai ji abinda ya ce ba balle ya fahimta, anitse shiru ne ya ƙara ratsa gurin sannan Baffah ya katse shirun ya ce,"
"Yaro na san zuciyarka a cike take da tambayoyi akan yanda akai kazo nan, na san cikin ranka za kaso ka san dalilin da ya kawoka wannan gurin?"  shiru ya ƙarayi sannan ya ci gaba da cewa,
 "magana ta gaskia yanda akai kazo nan ba kowa bane sila sai ni, ina  kan hanyata ta dawo da ga kiwo Allah ya haɗani dak ai acikin mawuyacin hali  kwance cikin jini. Haɗuwa ta da kai tsarin Ubangijine wannan dalilin ya sa nafi hanyar dana jima banbi ba, amma da ya ke Ubangiji mai hikima ne a cikin al'amarinsa sai ga shi ya  nufeni da bin hanyar saboda ya ɗora nauyin ceton Rayuwarka a wuyana. Madalla da Ubangijin alheri wanda baya bada komai sai alheri.

A lokacin da na tsinceka  Ban taɓa zaton zan sameka da sauran numfashi a tareda kai ba, amma da na taɓaka sai na fahimci da sauran rayuwa a tareda kai, a haka na ɗakko ka a daji na kawo nan  mu kaita kula da kai tareda raunikan jikin ka na tsahon lokaci har Allah ya nufeka da farkawa  yanzu."

Jikin matashin ne ya yi sanyi lokacin da ya tuna irin baƙar azabar da ya sha a wancan lokacin da abin ya faru, gabaɗaya ya cire tsammani da rayiwa amma jin labarin da Baffah ya bashi lokacin daya tsinto shi sai ya ƙara masa ƙaimi, ya jima da cire rai akan mutane saboda muguntarsu amma ganin modibbo da ɗiyarsa yasa zuciyarsa ta yarda akwai bayin Allah masu zuciyar alheri a cikin wannan duniyar.

Lumshe idanunsa ya yi yana jin yanda ƙwalla ke samawa kanta gurbi a ƙwayar idanunsa, ba komai ne ya sabbaba masa haka ba sai karamcin da moddibo ya yi masa. Haƙika ba shi da abinda zai iya biyansa dashi sai fatan alheri da kyautatawa.

Yanzu babbar damuwarsa A yanzu  bai san halin  da iyayensa suke ciki  ba, duk inda su ke ya tabbata damuwace abokiyar rayuwarsu. Amma da ya tuna rayuwarsa ta baya sai ya ji zuciyarsa tayi nauyi komai ya tsaya masa cak, rayuwarsa ta baya a cike take da tarin ƙalubale mai rikita tunani wanda ya sa aka fara farautar rayuwarsa ta ƙarfi da ya ji, don haka ya zama waji bi a gareshi ya manta da rayuwarsa ta baya ya fara sabuwar rayuwa tareda waƴannan mutanan da ya buɗe ido ya ganshi a tsakaninsu...

Cike da kulawa Baffah ya kai hannu ya dafa kafaɗarsa ya ce" kayi haƙuri yaro nasan dole zakayi kewar gida tareda ƴan uwanka, amma ka Ƙara haƙuri jikinka ya yi ƙwari sai ka koma gida  Kaji?"

Ɗaga masa kai matashin ya yi ba tare da yace komai ba ya mayarda idanunsa ya lumshe. mikewa Baffah ya yi sai  kuma ya sinkuyo ya ce da matashin "yaro ya sunan ka?" 

Gabansa ne ya faɗi a lokacin da ya ji tambayar da Baffah ya yi masa, nan da nan wani ɓangare na zuciyarsa yace masa "karka sake ka faɗi cikakken Sunanka dana mahaifinka, idan ba haka ba Mutanan nan zas u gane waye kai cikin sauƙi kuma su mayar dakai hannun maƙiyanka waƴanda suka jefaka a cikin wannan halim da kake ciki."

Ajiyar zuciya ya sauke me nauyin gaske Still idanunsa a lumshe ba tareda ya buɗe ba ya ce," Muhammad Ali. shine cikakken sunana!"

Ɗan jim Baffa ya yi yana kallonsa sannan ya yi murmushi ya ce"Masha Allah Muhammad ai babban Sunana, Allah ya ƙara maka lfy."

Duk wannan hirar da sike Rabe na jinsu a nitse ta matsa kusa da shi har ƙafarta na gugar tabarmar da yake kwance a kai ta kai hannu ta mintsini kumatunsa don dole ya buɗe idanunsa yana kallonta, ƙura masa idanu tayi sannan ta ce," "Anya sunan Muhammad ne?"
Da sauri ya janye idanunsa da ga kallonta  gabansa na faɗuwa,  murmushi ya yi a karo na farko tun farkawarsa ya ce,"That’s my name, just as you heard me say it." ya firta haka ts tsakanin kyawawan laɓɓansa wanda jinya ta sa sika bushe har suna tsagewa saboda rashin hydration.
Tun da ga lokacin da Muhammad yayi mata murmushi har zuwa sanda  ya gama magana  take kallon sa, ba komai take kallo ba sai tsabar kyau Da tsarin halittar da Ubangiji ya ƙawatashi da ita,  ba ta tabbatar da shi kyakkyawa bane sai da yayi murmushi a iya  rayuwarta zuwa yanzu ba ta taɓa ganin mutum irinsa ba. Mutane da yawa su na fada mata cewar tana da kyau amma yau Kam taga  Wanda ya fita kyau.

Sai da Baffah ya taɓata sannan ta dawo daga duniyar tinanin data afka,
a daburce tace,"Baffa yaushe za'a kuma bashi abinci?" maganar data fito bakinta kenan saboda
har ga Allah ba abinda tayi niyar faɗa kenan ba.

Kallon tsaf Baffah ke binta dashi kuma tsaf ya fahimci halin data Samu kanta a  ciki  amma kawai sai ya yi murmushi ya fita daga Ɗakin, zuciyarsa a cike da tsoron abinda ya gani kwance a idanun ɗiyarsa. Fatan sa Allah yasa abinda ya gani kar ya zama gaskiya saboda ba zai iya mallaka mata abinda take so ɗin ba.

Jin alamar Baffah ya fita ne ya sa Muhammad ya buɗe idanunsa a hankali ya kalleta, cikin muryarshi da bata fita sosai ya ce,"What is your name?"

Ƙura masa idanu tayi tana kallonsa hakan ya sa ya ce,"Don’t you have a name, that you’re just staring at me like that?" ya ƙara faɗar haka yana tsareta da nasa idanun kamar yanda tayi masa.

Murza goshinsa ya yi a lokacin da ya tuna inda yake, don haka ya ce,"sunanki, ya sunanki?" yayi mata maganar ta yanda zata iya fahimtarsa

Murmushi ta yi sannan ta ce,"Sunana Rabe."

A hankali ya kuma maimaita sunan yana wani yamutsa  fuska ya ce "what's that does mean?" 

Ƙura masa idanu tayi tana kallonsa, hakan  yasa ya taɓe baki ƙaɗan yace" ni wllh I can’t call you by that meaningless name, I’ll just keep calling you Fulani." A taqaice Ya sake kallonta still itama kallonsa take ba tareda ta san abinda yake faɗa ba.

Ya ce,"na gode sosai da ɗawainiyar da kikayi dani."Ya faɗi hakan yana mayar da idanunsa ya lumshe.

ta jima tana juya kalmarsa ta ƙarshe a ranta duk da cewa bata San mai yake nufi da ita ba, amma sai taji Kalmar tayi mata dadi Kuma ta tsaya mata a rai. A haka taɓar ɗakin tana ta juya maganar a ranta.

har yamma ta yi Rabe ba ta ƙara dawowa ɗakin ba har lokacin shafa masa magani yayi, ganin lokaci yana tafiya ne yasa Baffah ya fito da maganin ya haɗa sannan shafa masa, sai da ya gama shafa masa sannan ta shigo cikin Bukkar. Kallota Baffa ya yi sannan ya sa ta ɗora masa ruwan zabi ta kawo masa, ba ta jima ba ta dafo ruwan zafin kai masa ta na ajiyewa tayi waje abinta.

Baffa ya tashi ya nufi inda  matashin ke kwance  a hankali ya fara kiran  sunan sa.

A nitse ya buɗe kyawawan idanunsa a fiskar moddibo,
Murmushi Ya yi masa sannan yace ka gyara zan goge ma jikin ka, a nitse ya fara Ƙoƙarin tashi amma ya  kasa tashi da taimakon Baffah ya tashi ya zauna da ƙyar.

wani farin saki Baffah ya ƙara ɗakkowa ya tsoma a cikin ruwan ya fara gasa Masa jikinsa, dik da cewa jikinsa yana ciwo sosai hakan be hana moddibo gasa masa shi da kyau ba,
Yana gamawa ya ɗakko maganin shafi ya shafa masa sannan ya taimaka masa yayi alwala, Cikin mintunan da ba zasu gaza 5 ba ya shiga  rama sallolin dake kansa.

ya daɗe yana yi dik da bai san adadin kwanakin da ya Kwashe baya cikin haiyacinsa ba a wannan Ruga.

Duk abinda ya ke hankalin Baffah yana kansa, nutsiwarsa da kuma yanda yake karanta alƙu'ani a cikin sallar shine babban abinda yaja hankalinsa gareshi, gabafaya sai yaji karatun Muhammad da yanayin nutsuwarsa a sallah ba irin nasu bane, komai nasa a nitse yake yi dedai da koyarwar alƙur'ani da sunnah.

Sai da ya Ɗau lokaci mai tsayi sannan ya idar, Baffah ya taimaka masa ya kwanta sannan ya Ɗakko wani zanin saki ya lullube shi saboda iskar dake kaɗawa, ba'a Ɗau lokaci mai tsayi ba ba bacci ya yi a won gaba dashi.

          *****
Ɓan garen  Rabe kuwa tunda ta fita bata sake dawowa Ɗakin ba 
Sallah ta gabatar sannan ta fito ta yi aiyukan da ta saba yi kullum, sai da ta gama tsaf sannan ta koma daki da nufin ta gabatar da sallar ishsha'i, bayan ta idar ta jima a zaune amma ba ta san abinda zata roƙi Ubangiji ba saboda ba ta iya ba, ba ta san ladduban addu'a ba amma dai tana jin rayuwarta da wani giɓi wanda har yau ta rasa menene.

Da sauri ta miƙe ta cire  mayafinta wanda saboda dauɗa da ga fari ya koma ruwan madara, ta nufi katifar ciyawar dake ɗakin dan ta kwanta sboda sanyin daya fara busawa, Kamar daga sama  taji an banko cikin Bukkar wannan ya sa ta ta miƙe da sauri sabda sanin wadda ta shigo, saboda idan da  sabo yaci ace ta Saba da halin Jaddah.

Masifa fal ranta  ta shiga sannan ta haskata da fitila tana binta da wani wulaƙantaccen kallo ta ce"fita za kiyi kimin aiki  da kike Koƙarin kwanciya bacci ƴar mowa, wato ga baiwa Ubanki ya ajiye inyi muku wahala ko? To wllh baki isa  kiyi bacci yanzu ba sai kin gamamin aiyukan dake cikin gidan nan."
Ba ta jira cewarta ba ta fincikota sukayi waje, wasu tarin kwanuka ta gani an jibge su a gefe sai wata ƙatuwar ƙwarya da aka cika da ruwa kana gani ba sai an faɗa maka ruwan ya dau sanyi ba, ka san da biyu aka ajiyeshi ya sha iska don tayi mata azaba da sanyi da wannan uban duhun daren.

Kallo ɗaya za kayiwa kwanukan ka fahimci babdatti ko kadan a jikin su kawai tsabaragen mugunta ne ya sa Jaddah ta Fito dasu.
Ba musu Rabe ta sunkuya ta fara ɗauraye kwanukan tana yi jikinta na rawa  saboda sanyi dake busawa har taci Ƙarfin kwanukan, da Jaddah ta ga ba zata Iya jure sanyin ba sai tai shigewarta ɗaki tabar Rabe a waje tana fama da sanyi,  ta ɗau lokaci mai tsawo ta na ɗauraye kwanukan sannan ta gama ta kife mata su,
ta wuce tata bukkar jikinta sai rawar sanyi ya keyi, tana shiga  ta kwanta dikda cewa ta lulluɓa amma Sam bata dena jin sanyin ba.

Abu kamar wasa  Haƙoranta suka fara haduwa da juna Suna fitar da wani sauti na daban, nana da nan zazzabi mai zafi ya rufeta, da ƙyar ta samu bacci ya ɗauke ta
ba ta farka ba sai bayan an gari ya yi haske sosai, da yake bata san mahimmancin sallar Asuba ba sai bata matsawa kanta akan dole sai tayi ba, hasalima ba kullum takeyi ba saboda malam Iro yace masu ba kullum ake salla ba har sai mutum ya yi aure tukuna. 

Komawa ta yi ta kwanta duk sai jikinta ya yi mata nauyi, ta kasa tashi da ga inda take taje gun baffah saboda wani irin azababben jirin da takeji. Har gari Yayi haske  sosai kowa ya fara harko kin Gabansa amma Rabe bata fito ba.

A ɓangaran Baffah kuwa Sosai ya yi mamakin rashin ganin giftawarta,  a zatonsa ko bacci takeyi  shiyasa be wani damu sosai ba.

A nitse ya gama gabatar da komai na karin kumallonsu wanda Matashin zeci saboda Jaddah ta rantse akan ba zata bashi abinda ta dafa ba saboda bata yarda da yaron ba har cikin ranta, amma har ya gama bai ga  idon Rabe ba sai kuma abin ya fara damunsa. 

Ɓangaren Matashin saurayin kuwa tunda ya tashi da ga baccin safen da yayi ya afka duniyar tunanin "mai yasa Yakeda tarin maƙiya ne a Rayuwarsa?  Mai ya tare masu suke son ganin bayansa ?"

Baffah ne ya katse masa tunanin ta hanyar shigowarsa ya ce," ya kamata ka tashi kaci abinci don kasha maganin ka Muhammadu."

Ba musu  ya fara Ƙoƙarin tashi duk da cewa ba iyawa zeyi ba.

Murmushi Baffah ya yi ya ce," yaro gaskiya kana da Ƙarfin hali sosai  ka Ƙara haƙuri In sha Allah ka kusa fara tashi da kanka." tunda Baffah ya fara magana idon Matashin ke kansa sai kuma ya yi murmushi ya ce"to baba Allah yasa Hakan, ba zan gaji da ƙara jaddada godiyata a gareka ba sabda ka taimaki rayuwata,a lokacin dana jima da fitar da rai akan rayuwa." Shiru ya ɗanyi  sannan ya sake kallon Baffah ya ce"thank you for saving my life." ya Ƙarashe maganar idanunsa suna canza launi.

Da sauri Baffah ya dafa kafaɗarsa ya ce"kar ka damu yaro duk abinda nayi maka nayi ne don Allah ba don kayi min godiya ba, kai tamkar Ɗa kake a gurina kuma zan kula da kai har zuwa ranar da zaka Samu sauƙi ka koma ga iyayen ka." ya Ƙare maganar da murmushi A kan fuskarsa.

Canza fuska matashin ya yi a lokacin da Baffa ya yi masa zancen komawa gida, Sosai yake jin kalaman Baffah sina huda zuciyar sa saboda har cikin ransa ya ji yana ƙaunar dattijon kuma ya shiga  ransa sosai. Kwanon da ya shigo dashi Baffah ya buɗe sannan ya sa ludayi ya juya kunun ya ɗebo ya kai masa bakinsa, a hankali ya buɗe baki ya kurɓi kunun har yana lumshe idanu saboda yanda ya yi masa daɗi. Haka ya buɗe ciki sosai ya sha kunun har ya Ƙoshi.

murmushi Baffah ya yi ya ce,"masha Allah tunda yanzu ka Ƙoshi bari na shafa maka magani ko?"

Matashin yace,"okey!"
Sai da moddibo ya gama shafa mai maganin sannan ya bashi na sha shima ya shanye. yana gamawa bashi kulawar data dace yace,"to yaro bari in je  inga Rabe ko lafia naga har yanzu bata fito ba."

Matashin ya ce"ya kamata a duba agani ko lfya."
Da ga haka moddibo yay waje  ya nufi Ɗakin Rabe,  tana nan a Inda ta kwanta jikinta sai rawa ya ke duk ta gama ɓata jikinta da amai, da sauri moddibo ya nufeta yana tambayar ta "Meya sameta?"

yana taba jikinta ya ce" subahanallah!
Rabe meya sameki haka?" be jira cewarta ba ya kinkimeta yayi Ɗakinsa da ita,  banda hawaye ba bu abinda ke fita a idonta a haka ya Ƙarasa ɗakin da ita, sannan ya kwantar  da Ita.
tun da suka shigo ɗakin gabansa ya faɗi ganin wadda moddibo ya kwantar a nesa dashi kaɗan, a rude yake tambayar Baffah abinda ya sameta har yana Ƙoƙarin tashi daga inda  ya ke zaune.

Sosai moddibo ke kallonsa yana girmama sanin yakamata irin na matashin a cikin ransa, cikeda  tsantsar so da Ƙauna Moddibo yace "yaro ka kwantar  da hankalinka  ba wani Abu bane zazzabi ne kawai Kuma zata samu sauƙi da izinin Allah." Ya faɗi hakan yana kallonsa.

Har ga Allah moddibo yaji Matashin ya Ƙara kwanta masa a rai musamman da yaga  ya nuna  kulawar sa a kan tilon ƴarsa guda daya!"



Wai shin wanene wannan matashin ne?

menene cikaken sunansa🤔?

Sannan me yasa yake fargabar komawa ga iyayensa ?

Menene hujjarsa na ƙin gayawa modɗibo sunansa a lokacin daya tambayeshi Ya gaya masa wani sunan na daban?

ZMC
***

Comment 
And 
Share