SAFARA A TAƁO

012

by @gureenjoh

SAFARA A TAƁ


FATIMA MUHAMMAD GURIN 

*GUREENJOH*


*ADABI WRITERS ASSOCIATION*


*PAID BOOK*


*012*


Gaban madubi ta ƙarasa ta dafe, kanta a ƙasa tana ƙoƙarin saita gudun da zuciyarta ke yi kaman zai ratso kirjinta ya fito, haka kawai take jin kaman jininta na hawa bata san me zata yi ba, she's feeling not safe about this kaman something is not right, ta ɗauki tsawon lokaci kan ta iya saita kanta ta ɗago ta kalli madubi, babu abin da ta ƙara ko ta chanza haka ta juya ta nufi ƙasa hannunta riƙe da wayanta, a parlorn ta tsaya kusa da Momma tace a hankali 


"Momma na yi baƙo ne yana so in fita mu gaisa..!"

Da sauri Momma ta ɗago tana kallonta amma ganin tension a yanayinta da alamu tana cikin sarkakiya ko wani damuwa ya sa bata ce komai ba bayan 

"Sai kin dawo"

Juyawa kawai tayi ta fita cikin sassarfa tana fita harabar gidan motarshi na shigowa daga bayanshi Nadiya babbar 'yar Hajiya kamila kuma ita ce babba a gidan gabaɗaya a yaran Daddy ta shigo bayanta goye da ɗiyarta, motar na parking ya fito yana kallonta ta mayar da kanta kan yatsunta tana wasa da su, shi kuwa ya narke a kallonta maganan Nadiya ya katse su...


"Hibbah baƙo aka yi?"

Juyawa yayi kaman yadda Hibbah ta ɗago tana kallonta, ta san da gayya ta tsaya ba arziki ne ya tsaida ta ba.

"Eh, sannu da zuwa"

Ta faɗa tana ɗauke kanta a lokacin Dr. Najeeb ya jefa mata gaisuwa ta amsa ta sake kallon Hibba 

"Ya kufayin jikin dai? An ce wai ɓari kika yi ne ko Haihuwa ma?"

Daga Dr. Najeeb har ita da sauri suka kalleta sai Hibbah ta mayar da kai kanshi shima ya ɗan juyo yana zuba wa yanayinta idanu, sossai ta haɗe rai tace 

"Idan kin faɗa domin ki ɓata ni ne shi wannan da kike gani tunda abinda ya sameni ya faru bana rufa sati biyu bai ganni ba idan ma haihuwar ne shi ya kamata ya fara sanar wa don na tabbar shi zai karɓa kan ya iso kunnuwanku. Dr. Mu isa ciki na barka tsaye Afuwan!"

Tana kai nan ta juya ya bi bayanta bayan ya juya ya kalli Nadiyar, seating room na Daddy ta mishi iso suka zauna kanta ƙasa zuciyarta na ƙuna akan abin da Yaya Nadiyar ta yi mata, numfashi ya sauƙe a hankali ya ce 


"kin manta you promised ba za ki bari maganar kowa ya yi hitting ɗinki Hard ba? You are a strong woman Hibbah sincerely speaking yadda kika amsa mata ya burgeni ƙwarai i like ur confidence"

Ta ɗan kalleshi cikin sigar Harara yayi dariya itama ta yi murmushi bai tambayi alakar su da Nadiyar ba kuma bai damu ya sani ba abinda kawai ya sani bata son Hibbah kuma shima baya sonta ko wacece ita ga hibbar.

Miƙewa Hibbah tayi ta kawo mishi ruwa da lemu daga frigde na Daddyn ta tsiyaya mishi five alive a glass cup ta miƙa mishi, fararen yatsun ta dake ɗauke da jan lalle da ya rufa maroon sharr ya bi da kallo.


"Thanks love!"

Ta ɗan yi murmushi kan taje ta zauna inda ta taso, sai da ya kurba kan ya ce 

"Ya kike? Kin yi min wuyar gani"

"Eh ai ku ganinku sai dole, in ba dole ba wa zai so rashin lafiya?"

Suka yi murmushi a tare 

"Hibbah"

Ta kalleshi

"I Miss you..."

Zuciyarta ya doka ta mayar da kanta ƙasa 

"Na zo ne in ji amsata shin wannan ɗan bawan Allahn ya samu karɓuwa? Ko in je in rungume tramsfomer?"

Dariya ta yi shima ya cigaba da murmushi yana kallonta.


"Ɗan umma ya yi nasara akan Hibbah. Don Allah ka riƙeni amana do not betray me kar ka ƙarasa zuciyar da ta riga ta gama tsatsagewa tarwatsewa ne kawai ya rage...."

Ta ƙarasa hawaye na silalo mata 

"Amsarki kawai ta isa na cigaba da kasantuwa a cikin farinciki a raina lallai na yi babban dace wanda ba zai misaltu na iya bayyanawa ba, na zamo mafi sa'a da samun ki kuma na miki alkawari mutuwa ce kawai ta isa raba wannan alaƙa sai kuma wanda ya haɗa"


Daga wannan lokaci Hibbah ta buɗewa Najeeb zuciyarta ya shiga ya yi kane kane, soyayya suke zubawa ba na wasa ba yayi nasara ƙwarai wurin mantar da ita duk wani burbushin damuwarta, Momma ma hankalinta ta kwanta ƙwarai ganin yadda Hibbah ta dawo da walwalarta kaman komai bai faru ba Dukda har yanzu ta ƙi komawa makaranta.


Safiyar Asabar ne sun gama karyawa suna zaune gabadayansu kawai Hajiya Kamila ta dubi Daddy

"Jiya mijin Amal ya kirata Alhamdulillah komai na warwarewa bisa tashi tsaye da muka yi mu ma, ya ce ta shirya komawa wani sati zai zo har nan ya ɗauketa"

Amal ɗin da ke zaune tana ta murmushi Hibbah ta kalla ta ɗauke kai. Daddy ya ce

"Toh Alhamdulillah tunda komai ya warware dama haka ake fata sai ta hau shiri"

Momma ta musu barka suka amsa a gatsine.

Hajiya kamila ta sake cewa 

"Sai Nadiya ta ce ɗiyarta ba lafiya tana so Mujiba ta je ta ɗan kama mata aiki samu ta kaita asibiti"


"Meyasa sai Mujiba? Sauran yaran kam ba ƙannen Nadiya bane? Meyasa kuke so a koyaushe ku ga kun raba mini kan yara ne kam kamila?"

Hibbah ya kalla

"Ki shirya ki je gidan Nadiya ki kama mata aiki ta kai yarinya asibiti"

Har ranta bata so ba amma wacece ita da zata Musa? A hankali ta amsa da Toh ta miƙe ta fice daga parlorn ko ta je ma rigima ne zai biyo baya su da ba'a raba su da rigima.


Sama taje ta ɗauko wayanta da car key ɗinta ta fice daga gidan kai tsaye ta nufi Gidan Nadiyar, tana shiga parlorn a kan idanunta Mijin Nadiyar na tsinketa da mari har ɗiyar hannunta na faɗuwa a ƙasa ta fasa ƙara, wani irin zaro idanu Hibbah tayi ganin Nadiyar jiki na rawa ta shiga kokarin bashi haƙuri shi kuwa yana sake harzuƙo wa yana yunkurowa zai sake 

Kai mata hannu.


Wani irin tsalle hibba tayi ta dira tsakiyarsu ba tare da ta sani ba ta sa hannu ta ture shi da ƙarfin gaske

"Baka da hankali ne? Kai dabba jakin wani garin ne???"

Da ƙarfi tayi maganan har Nadiya na maƙalewa bayanta cikin kuka.


"Wacece ke da za ki shiga abin da babu ruwanki? Ke kin san wan..."

"Ko uban waye kai baka da right na sa hannu ka daki matar aurenka, kai ko ma wanene kai you are very, very stupid..."

Hannu ya ɗaga zai daketa ta mishi ihu 

"Kana taɓa ni wallahil azeem daga yau ba zaka sake marmarin taɓa wata mace a duniya da sunan duka ba, zaka ga danyan hauka da jahilci wanda ya ci uwar naka.... Gidanka gidan 'yan dambe ya zama da zaka daki uwa ka daki 'ya? Idan damben kake ji ka je ka shiga wrestling mana ka yi da maza masu jini a jika!"


Ta juya ga Nadiyar dake shaking cikin kuka take cewa 

"Ke kuma wa...."

Ta ja dogon tsaki ta ma kasa ƙarasa wa ta kusa zaucewa wani irin namiji ne Nadiyar ke aure? Ashe da suke ta pretending tana zaman lafiya tana cikin jin daaɗi suna yi ne don kawai kar a musu dariya? Ba gara dariya ba da zama ciki assault? Bare ma wa zai yiwa ƙaddarar wani dariya idan ba su ba jahilai da kwakwalwarsu ke dankare da tarin wawanci da rashin sanin ciwon kai?


"Yaya Nadiya tashi mu tafi"

Ta ɗauki yarinyar da har lokacin bata yi shiru ba jikinta rau kaman wuta za su fita ya ce 

"Wallahi Nadiya kina fita a gidan nan a bakin aurenki"


"Sai me??? Sai me?? Dama wannan aure ne? To hell with you da auren naka da ma gidan gabaɗaya. Ki tashi mu tafi...."

Yadda take tafasa za ka zaci ma ita ce yayar Nadiyar ce ƙanwar.

Janyeta tayi suka fice daga gidan Nadiyar na ta kuka har mota ta ja ta bar gidan, rasa ma me zata fara yi tayi don yarinyar na bukatar ganin likita haka kuma tana son ganin Daddy cikin gaggawa.


Asibiti ta fara yi wurin su Najeeb kan ta isa ma ta kirashi akan suna zuwa ganin Pediatric dr saboda yarinyar ma is at state of emergency, duk abin bukata ya sa aka tanada suna isa aka karɓi yarinyar Nadiyar na tsaye daga gefe tana kuka, kallo ɗaya yayi mata ya ganeta bai cewa Hibbah komai ba har sai da yarinyar ta zama stable ya zo yana tambayar 

"Meyasa yarinyar nan zazzabi na jikinta ba'a iya an kawo ta asibiti ba sai da ya ci karfinta har ya ƙone ruwan jikinta? Wasu irin iyaye take da su da basa aiki da hankali?"

A matsayinshi na likita faɗa ya ringa yi Hibbah ta kyale shi da Nadiyar da take ta kuka kawai tana roƙon ya taimaka yarinyarta kar ta mutu ta rasa yara har biyu cikin sakaci irin wannan da tsoron mijin nata. ya ce

"idan ta mutu ma ai sakacinki ne ba na wani ba"

Yana kai nan ya wuce Hibbah tayi murmushi ta juya gareta.


"Na kira Daddy ya ce ana samun kan Amatun mu je gida yana son ganinki"

Bata ce komai ba jiki a sanyaye ta juya suka fice.


Babu hijabi duk abin da ya faru sai da Hibbah ta faɗawa Daddy da Brothers ɗin shi dake zaune, shi dai Daddy Z bai ce komai ba don ya riga ya fitar da kanshi a abinda ya shafi yaran Hajiya kamila tunda ta ce ba ruwanshi Daddy Rabi'u ne ya ce 

"Ke Nadiya dama hakan ya jima yana faruwa ne baki iya kin kawo batun gida ba?"


Hajiya Kamila dake ta maka mata Harara ta kalla kan ta mayar da kanta ƙasa tana zubar da hawaye.

"Ba magana ake miki ba kin mayar da mutane banza??"

Daddy Z ya daka mata tsawa, jiki na rawa tace 

"Eh Daddy amma Hajiya ce ta hanani faɗa muku saboda bata son kishiyoyi su yi mata dariya idan aurena ya mutu"


"Ba ka ji dabbanci da rashin hankalin ba? Ba ka ji ba Yaya..."

Daddy ya faɗa cikin tsantsar takaici ya juya ga Hajiya kamila

"Wace iriyar uwa ce ke? Ni da na haifi yaran nan kin taɓa gani na saka su gaba ina jibga har sai da na aurar da su da girmansu, iliminsu daidai gwargwado da hakwaransu talatin da biyu wani chan gardi yaje yana jibgarsu ki ce kar su faɗa? Dariyar banza dariyar wofi... Yanzu idan da Hibbah bata je gidan ba sai kenan ya kashe yarinyar ita ma ya kasheta a banza?"

Ta inda yake shiga ba ta nan yake fita ba zuciyarshi har zafi zafi yake mishi saboda bacin ran Hajiya Kamila da ko a fuska bata nuna wani damuwa ba hasali ba wani haushin Hibbah da Nadiyar ne ya zo mata wuya, tana ganin ai Nadiyar ta gama sunce mata zani a kasuwa ne.


"Zan yi ƙarar wannan marar mutuncin wallahi he must pay na taɓa yarinyar nan"

Daddy Rabiu da shine waliyyinta ya faɗa a hasale, Daddy ya sallame su suna fita Hajiya kamila ta bi Nadiya da zagi da masifa hibbah na kallonsu har suka ɓace mata kan ta girgiza kai ta nufi nasu sashen.


Ko a mafarki bata yi tunanin rashin wayon Nadiya ya kai ta zauna wani na jibgarta ba, da ilimin ta da gatanta da komai saboda karamin tunaninsu, ta tuna fa itama Nadiyar auren soyayya suka yi da Baban Amatun don tana tuna har choculates da sweets yake kawowa in ya zo hira a raba ayi ta iyayi a wurin wasa musamman su Amal, ashe soyayyar duk na bogi ce to anya akwai auren da yake da daaɗi kuwa a wannan duniya? Ita dai duk inda ta juya matsaltsalu take hangowa dake ƙara tsinka zuciyarta da al'amarin mazan da ma kanshi rayuwar auren.


"Ke lafiyarki kuwa?

Taji an faɗa daga bayanta da sauri ta juya...