013
by @gureenjoh
SAFARA A TAƁO
FATIMA MUHAMMAD GURIN
*GUREENJOH*
*ADABI WRITERS ASSOCIATION*
*PAID BOOK*
*013*
"Yaya Nasir? Yaushe a gari?"
Tayi tambayar tana murmushi yace
"Tun jiya sai dai Hotel na sauƙa, aiki ne ya kawo ni branch namu na nan. Lafiya kike kam?"
Suna ƙarasa wa cikin babban parlorn tace
"Lafiya ƙalau fa, ya ka baro su Yaya Zaitoon?"
Momma dake fitowa tace
"'yar uwarki kawai kika sani ko? Nasir barka da shigowa ya Yayata?"
Daga shi har Hibbah suka yi dariya, Aina'u da ta fito taje ta kawo mishi ruwa da snacks nan suka zauna suka shiga hira abinsu, zai dan yi kwana biyu amma ba gidan zai zauna ba saboda idan suka sauƙa gidan basa jin daaɗin su Hajiya kamila don haka suke sauka Hotel abinsu ko sun zo gidan ziyara ne, ya jima don har bayan isha yana nan tana tsaye da Dr. Najeeb da zai koma bayan hira da suka yi ya fito tace
"Dr. Ga yayana Yaya Nasir"
Miƙa mishi hannu yayi suka gaisa kan tace
"Wai zaka wuce kenan?"
Kai ya gyaɗa
"Zan tafi sai zuwa wani sati ma kila zan sake shigowa saboda daga gobe aikin da ya kawo ni zan fara"
"Toh Allah ya taimaka sai da safe"
Ya je ya ɗauki motar Momma ya bar gidan, basu jima tsaye da Dr. Najeeb ba ya tafi shima tana bashi saƙon gaisuwa zuwa wurin umma kaman yadda itama bata taɓa gajiya da aiko mata da saƙon gaisuwa ba.
Tana shiga cikin parlor ta tarar duk ba kowa ma sai mai aikin dake gyarawa ta haura sama kai tsaye zata shiga ɗakinsu Fareed ya kirata
"Momma wai ki zo Yaya Twinee"
Kai ta gyaɗa ta juya zuwa ɗakin momman ta samu ma Aina'u na janyo fadeel akan su tafi taje ta shirya su su kwanta yana ƙi, masifeshi tayi da sauri ya riƙe hannun Aina'un suka fita Momma ta dube ta
"Ki dinga kokarin bin yaran nan a hankali mana don Allah ji fa yadda duk kika tsorata min ɗa"
Ta taɓe baki kaɗan tana zama
"Momma Allah raini ne ban cika so ba, ki ga fa abin da yake yi wa Aina'u kaman wata sa'arshi amma kin san ina son yara"
Momma tayi kwafa kan ta ce
"Shi wannan dake zuwa wurinki waye ne?"
Dukda tana tsammanin titseyen sai dai da taji daga bakin momman sai da gabanta ya faɗi, kanta ta mayar ƙasa
"Momma Dr. Najeeb ne"
Fuskar Momma a ɗan washe tace
"Wannan likitan dake duba ki a asibiti?"
Kai ta gyaɗa Momma ta ce
"Masha Allah yana da hankali kuwa, ga mahaifiyarshi mai kirki ko ba ita muka samu a ɗakin asibiti kwanaki chan da baki da lafiya ba ta zo duba ki?"
"Ita ce Momma, ai kirkinta ya wuce nan, har fa layina ta karɓa wurinshi ta kirani rannan daga haka nayi saving idan nayi kwana biyu ban ƙira ba ita za ta ƙirani mu gaisa"
"Masha Allah! Allah ya kara mata lafiya"
Hibbah ta amsa da Ameen.
"Babanku ya ce ki ce mishi ya iso idan da gaske yake saboda ya ganshi ba sau ɗaya ba ba sau biyu ba yana zuwa wurinki."
Da sauri ta ɗago tana kallon Momman
"Mene? Ba da aure yake sonki bane?"
Kanta ta mayar ƙasa gabanta na cigaba da bugawa
"Da aurene ya jima ma yana min maganar turowan ni ce dai nake ta kwana kwana, Momma tsoro nake ji sai in ga kaman shima auren ba zai yiwu ba!"
"Me zai hana shi yiwuwa Hibbah? Ke ba mace bace kaman kowa? Kuma ina ce babu abin da bai sani ba akan abin da ya faru a baya hatta mahaifiyarshi ma ta san komai to tsoron me kike?"
Numfashi ta sauƙe
"Hakane zan faɗa mishi Momma"
"yauwa. Ki cire duk wani shakka ko tsoro a ranki babu abin da zai hana ki samun farin ciki, akan ciro mace ma daga gidan karuwai a aureta kuma ayi zaman lafiya da ita bare ke da hotuna ne su ɗin ma kuma ba tumbur haihuwar uwa ba. Zuwa yanzu duk komai mu barshi a baya mu yi adu'ar Allah ya tabbatar muku da alkhairi a tsakaninku"
Kai Hibbah ta gyaɗa bata wani cigaba da zama ba ta yiwa momman sai da safe ta wuce ɗakinsu.
Shirin bacci tayi tana ƙarewa kaman yayi timing sai ga ƙiran shi
"Ka je gida lafiya?"
"Ba ƙalau ba"
Yayi maganan kaman baby
"Subhallah wani abu ya faru ne?"
Kai ya girgiza
"I wished cewa da na dawon nan ke zan tarar zaune cikin kwalliya ki tarbe ni da murmushin nan naki mai kyaun gani da narkarwa"
Murmushi tayi mai sauti
"Soon in shaa Allah, yanzu ma da albishir a baki na"
"Haba? Faɗi mu ji"
"Uhmm uhmm sai an ba ni goro fari kallll"
"Na ji za ki ga goronki fari kalll ni dai ba ni in shaa"
"Daddy ya ce ka turo"
Karamin ihun murna yayi
"Yessss Alhamdulillah Alhamdulillah"
Murmushi take yi jin farin cikin da ya shiga haka suka cigaba da soyewa kan su yi sallama ya tabbatar mata zai tuntubi Baba gobe da safe suna saka date na zuwan nasu zai faɗa mata ta faɗawa Daddyn.
****
Da ciwon kai yau ta yini tana girkin ranan ma tana jin jiri jiri na damunta, miyan tayi tasting taji ba gishiri ta dibo ta ƙara ta sake tasting bai fita ba ta sake ƙarawa Dukda kadan ta yi niyyar sawa saboda Hajiya dake fama da hawan jini a kwanakin don haka bata buƙatar gishiri mai yawa amma jin miyan bai fitar da gishirin ba kuma ta gaji da ƙarawa ya sa ta rufe ta ƙarasa duk abin da zata yi ta zuba na su hajiyar ta fito da su a basket ta nufi wurin hajiyar.
A ƙasa ta zauna ganin Mu'azzam shima zaune yana matsa mata kafafu, ganin abincin yace
"Yauwa Hajiya dama yanzu kika gama zancen yunwa kike ji ga yarinyar nan bata gama girki da wuri ba bari na zuba miki wannan kawai sai ki ci ki sha maganin"
Zai ja basket ɗin Huda ta matsa gangarshi ta buɗe ta shiga serving a natse bayan ta gama ta ajiye gaban Hajiyar ta koma ta zauna.
Cokalin Hajiya ta ja tayi bismillah a fili ta kai loman farko... Wani irin furzarwa ta yi tana kakari
"Ba ka ga ba Mu'azzam? Ba ka gani ba? Na ce maka matarka bata ƙaunata kasheni take son yi ka ƙi yarda yanzu idan ba baƙar mugunta ba me na labta gishiri alhali ta san ba ni da lafiya??"
A ɗan ruɗe Hudah tace
"Hajiya me yasa zan kashe ki? Wlh ko kadan gishirin abincin nan bai fita ba, wallahi ba zan iya cutar dake ba ko menene kuwa kika min..."
Mu'azzam ya janyo cokalin ya ɗanɗana abincin da sauri ya furzar yana kallon Hudah
"Amma baki san an hanata cin gishiri haka bane? Meyasa za ki zarge ta da miki karya Hudah alhali gaskiya ce? Wannan gishiri ko ke ba na tunanin za ki iya cin abincin nan..."
Hajiya na sharce hawaye take cewa
"Ai wannan watarana sai dai ta zuba min maganin ɓera in ci in mutu..."
Da sauri Hudah ta karɓi cokalin ta ɗanɗana hawaye na cika idanunta ganin irin kallon da suke mata ta ɗanɗana bata ji komai ba
"Wallahi ban ji komai ba, yanzu menene a abincin nan?"
Haushin musun da take yi ya kama Mu'azzam bai san ya rufeta da masifa ba kaman zai ari baki, a rikice ta ɗauki abincin tana cewa bari taje ta chanzo taku biyu ta yi zuwa uku ta faɗi a wurin a sume.
****
Nasiha Daddy da Daddy Rabi'u suka saka alqasim a gaba suke mishi na haƙuri da rayuwa da kuma jarrabawa don ya ce musu kusan ya rasa komai nashi sai dai adu'ar Allah ya dawo mishi da arzikin, sun tausaya mishi ƙwarai daga Daddy har Daddy Rabi'u sun bashi kyauta masu tsoka akan ya riƙe hannunshi kan aka turo Amal don su wuce.
Har tsakar gidan su Hajiya kamila suka rakota, baki har kunne cike da nishadi ta shiga jar motar dake parke yana jiranta, shima Alqasim ya shiga suka fita a gidan a hankali.
Suna fita daga gidan ya riƙo hannunta cikin kulawa
"My love na yi kewarki"
Ta langwabe tana kwantar da kanta jikin kafaɗarshi
"Ba zaka gane yadda nayi kewarka ba don faɗa ma ɓata baki ne Sweetheart"
Murmushi yayi yana shafa kanta suka cigaba da zama ganin ba'a ɗauki hanyar gidansu ba sai ma wani uban tafiya da suka ɗauka ya sa tace
"Ina kuma muka nufa Sweetheart?"
"Gidanmu za muje, kin san abin da ya faru a yanzu haka gidana bai dawo hannuna ba zan kaiki wurin su Inna ne ku zauna tare kafin komai ya daidaita ina fata za ki bani haɗin kai?"
Kai ta gyaɗa tana komawa kishingiɗe
"Babu matsala my love ai mahaifiyarka tamkar tawa take, Fatana dai Allah ya dawo maka da duk abin da ka rasa cikin sauƙi."
Ya amsa yana murmushi, tun suna tafiya tana gane ma hanyoyin da ake bi har ta ɓace, ba su suka tsaya ba sai cikin wani ƙaramin kauye mai dauke da jar ƙasa da ma gine gine irin na jar kasa, yara ne yuuuuuuu suke biye da motan suna ihu daga marasa wando sai masu majina duk sun yi futu futu kaman dodon wasannin yara.
"Ga qasimu! Ga qasimu..."
Kallonshi tayi cikin tsantsar mamakin da ya kasa ɓoyuwa a fuskarta ta kalli kofar gidan da suka tsaya da buhu ne madadin kyauren wani wurin ma a fashe kwata ne mai girma da sai ka tsallake kan ka shiga cikin gidan, hankalinta a tashe tace
"Ina ne nan Alqasim?? Me muke yi anan?"
"Yanzu fa na gama ce miki wurin inna zan kawo ki ku zauna kafin komai ya warware"
Idanunta kaman za su faɗo ta kalli kofar gidan ta sake kallon Alqasim a rikice
"Naan.....nan shi ne gidanku?"
"Eh mana anan aka haifeni, nan ne gidan iyayena"
"Innalillahi wainna ilaihi rajiun Na shiga uku! Alqasim mayar da ni gidanmu, mayar da ni gidan iyayena wallahi ba zan iya zama anan ba"
Buɗe kofa yayi ya fita ya zagaya ya buɗe ɓangaren ta ya janyo hannunta
"Ai kuma zancen kike so, tunda kina aurena ai zama a gidanmu dole...Na ma yi miki da sauƙi da kika kwashe watanni gidanku"
Turjewa take tana kuka akan ya saketa ita gidansu zata tafi shi kuma yana janta har ƙasa ta zube tana kuka ita ba zata iya shiga ko gidan bane shi kuma ya dage sai da ya kaita har ciki duk matan kauyen suna tsaye ana ta kallonsu, yana shiga innar shi ta taso
"Lafiya kuwa Qasimu?"
"Inna bata da lafiya ne a kawo ruwa ta sha ko zata watsake"
Da hanzari innar taje ta kwalfo ruwa a randa ta kawo mata, ganin jan ƙasa dake kwance ciki ga ruwan jajazir kawai ya tayar mata da zuciya duk kwanon tsatsar lamba ne haka ya kai mata baki da karfi ta Buge ya faɗi sai amai.
"Ashaaa Ashaaa jikin ashe yayi tsanani haka? Taho in taimaka miki zuwa ɗaki"
Ture matar tayi tana ihun kar ta taɓa ta cikin kuka da karaji.
****
"Ai tunda kika zaɓi kashe aurenki ki dawo ki zo muna haɗa kafada babu abin da ba za ki gani ba, ba dai ni kika zaɓa a yi wa dariya a gidan nan ba? Za ki faɗa min idan bakin ciki kike da ni...ki wuce ki ɗaura mana abinci babu mai miki girki ki ci a gidan nan"
Kallon Mujiba ta yi
"Hajiya fa kina ji yarinyar na min rashin kunyar da ta ga dama kuma ki ce ba zan yi magana ba? Gidanmu fa na dawo amma daga kan shara, wanke wanke da girki, gyaran dakinki hatta wanki duk yaran nan sun nade hannu sai ni zan yi? A kaina aka fara mutuwar aure? Idan ban bar baban su Amatu ba mutuwa zan yi kafin ki gane ina cikin ƙuncin rayuwa?"
Miƙewa tayi ta nufeta cikin masifa da tsawa
"Da kina gidanki uban wa zai saka ki hakan? Tunda kin zaɓi ki kashe auren ai kin shiryawa zama da ni da bauta mini don duk wanda ya ki sharar masallaci zai yi na kasuwa tunda ba ladar za ki samu anan kaman dakinki ba... Mujiba kuma ba zata yi ba ke za ki yi don ubanki"
Gabaɗaya hajiyar ta sauya mata, bata da sukuni da farin ciki a cikin gidan kaman wacce ke gaban kishiyar uwa, abu kaɗan zagi da cin mutunci bata la'akari da yanayinta ko ciwon dake cinta a cikin rai kuka take yi sossai kaman 'yar goye don ta fara gundura da zaman gidan tana jin gwara dukan Mijinta da irin abin da mahaifiyarta ke mata.
Miƙewa kawai tayi ta fice daga sashen tana kuka sossai ta nufi sashen Momma duk irin kira da ihun da Hajiya kamila ke mata akan ta zo kar ta taka kafanta wajen gidan bata waiwayo ba ta fice.
Momma na zaune da su Hibbah suna hiran su kawai suka ji Shigowarta ko kan Momma tayi magana taje gabanta ta tsuguna tana kuka
"Subhallahi... Nadiya? Lafiya me ya faru haka? Menene?"
"Momma haka kowace bazawara ke fama ne ko ni ce kaɗai? Momma ba gwara in koma in cigaba da karɓar duka ba da irin maganganun Hajiya marasa daaɗi? Momma ki ba Daddy haƙuri ya sa a bar ni na koma kawai na gaji wallahi ba zan iya cigaba da zama da Hajiya ba"
"Ki natsu Nadiya, a yanzu wannan kukan duk saboda Hajiya kamila ne? Share hawayenki ba za ki koma gidan da za'a cigaba da assaulting ɗinki ba har abada, ki tashi ki je ki zaɓi ɗakin da za ki zauna babu mai takura miki anan bare ya gayamiki baƙar magana kin ji?"
Kuka kawai ta sake fashewa dashi tana ɗora kanta kan kafafun momman saboda abu ne da bata taɓa zato ba, duk irin cin kashi, rashin kunya da fitsaran da suke yiwa matar nan ta iya samun wuri a zuciyarta ta yafe musu kuma take marabtarsu a gangarta? Lallai zuciyarta mai kyau ne dole ta nemi yafiyarta sun zalunce ta bisa rashin sani da hurewan kunnen Hajiyarsu da ta nuna musu Momma bata taɓa ƙaunarsu ba kuma burin ta shine ta raba su da mahaifinsu...
Wayan Hibba da yayi ƙara ya sa ta mayar da hankali kai tare da ɗauke kanta daga magaganun su Momman, Dr. Najeeb ne picking tayi tare da sallama suka gaisa a natse yace
"Babe kin kusa zama tawa... Tawa ta har abada"
Murmushi tayi softly
"Allah ya nuna mana"
"ba za ki tambayi me yasa na ce hakan ba?"
"To me yasa ka ce hakan?"
"Na riƙe maganata tunda bakya son ji"
"Da gaske ina son na ji"
"Su Abbana za su zo wani sati lahadi in shaa Allah, za'a zo a tambaya min aurenki"
Kunya ne ya rufeta ta rufe fuskarta tana dariya a hankali.