Kuncin zuci
by @bintuuu
A week Later..
Na'ima ce kwance a gado bayan tayi sallahn asuba da azhkar dinta ta qudun dune cikin blanket kamar wata Baby, waya ce a kare kunnenta tana magana da Ahmad, shiru tayi tana sauraron abunda yake fada, sai tayi murmushi batace komai ba, daga bangaren Ahmad dake kwance shima a nashi gadon ya sake kwantar da murya yace "Babe answer me" sai ta sake yin murmushin tace "Nidai uhm uhm" sai yace "So kike na bar komai na dawo ayau ko?" Na'ima tadan ware ido sai tayi dan dariya tace "Ai kace zaka dawo satin nan" sai yace "Kinason in dawo?" tayi qasa da murya tace "Uhm" sai yayi murmushin da har tana jiyosa, shiru sukayi Na'ima na kallon pop na dakin, wani irin abu takeji yana mata yawo a zuciya a duk lokacin da take waya da Ahmad, ahankali taji yace "I dreamed a life with you Na'eemah, A life where you and me will build everything together, only you by my side Na'eemah...Side by side" ji tayi hawaye na kawowa idonta, tayi shiru tana tuna yanda rayuwanta ya zamo bari biyu, ta inda past dinta Namiji ya nuna mata tsana mai qarfi sannan present dinta kuma wani Nimijin yake nuna mata qauna mai tsayawa a zuciya, Namijin da keda burin yin rayuwarsa tareda ita, Jin Ahmad din yayi shiru ya sata cewa "Nima inason yin rayuwa dakai" sai yace "And we'll have our kids Na'eemah, beautiful ones like you" murmushi tayi me sauti sai ya qara cewa "Duka mata nakeso kuma masu irin gashin ki" tadan ware ido cikin kunya tace "Son kai ne hakan fa" yace "Na yarda i'm selfish akanki, i want you all to myself Babe" tana murmushi tace "What about Simba?" sai yace "Kinason in kawo miki shi bayan aurenmu?" ta gyada kai tace "Uhm" sai Ahmad ya gyara kwanciyarsa yace "Then angama Babe"...Hira sukayi me sanyaya musu zuciya a wannan asuban, hiran da shiru yafi yawa acikinta, amma jin shirun suke shima wani muradi na daban wanda basa gajiya da yinsa, shiru kan zama boring while on call amma ba'a gurinsu ba, in the sense that jinsa suke kaman wani maganar zucin me zaman kansa... Na'ima ce ta fara masa sallama dalilin zata je su gaisa da Mami dan tasan tana falonta, da haka sukayi sallama ta nufi dakin Mami sai ta samu Nafisa acan tareda Mamin suna gaisawa, zama tayi anan qasan carpet din itama suka gaisa da Mamin har da Nafisan sannan sukayi karatun Qur'ani, Nafisa ce ta fara miqewa ta nufi dakin Mami sannan Na'iman ta bita suka kwanta bacci anan din, wanda basu tashi ba sai kusan qarfe tara saura, Na'ima dakinta ta koma tayi wanka ta shirya cikin kaya mara nauyi sannan ta fita downstairs yin breakfast, Mami ta gani zaune a falon tareda lantana suna magana, sai tace mata "Habibti kije falon Abbanku, Nafisa nacan ta kai muku breakfast dinku can yau bai fita ba tukunna" ta gyada kai tareda gaishe da lantana sannan ta nufi can din, Abba da Abu tareda Nafisan ta samu anan falon suna hira sai Abba yace "Na'ima antashi" ta amsa da "Eh Abba" tana murmushi tareda zama nan qasan carpet din kusada Nafisa sannan ta gaishesa ya amsa, Abu ma gaisheta yayi ta amsa sai Nafisa ta miqo mata cup "Bobo ga tea dinki kar yayi sanyi" karba tayi sai Nafisa ta fara serving dinsu abincin suka fara ci, Hira sukeyi da Abba sama sama yana kallon news shi da Abu, dan shi kadai ne me taya Abban kallon tashoshin labarai a gidan, sai Na'ima wani lokacin itama tana gani in suka zo gurin Abban, Mami ce ta shigo falon ta samu guri ta zauna itama, tana kallonsu Nafisa tace "Yau ku mana sakwara, zan yi baqi anjima" Na'ima ta amsa da toh sai Nafisa tace "Ni zanyi miya ai ko Bobo" tana murmushi ta amsa da "Toh badamuwa" Mami tace "Baby ki fita daga idona da lalacin nan naki" dariya Nafisa ta fara Na'ima na girgiza kai tana murmushi sanin miyan ma ita zatayi daman, sai da suka gama yin breakfast din suka tattare komai sannan Abba ya fara musu magana Umrahn nasu da aka samu delay din visan Na'ima har sannan, sai ya fara musu tambayoyi akan ra'ayinsu na batun aiki, Nafisa ce ta fara cewa "Abba dream job dina nakeso" Abu na kallonta yace "Boutique din" ta gyada kai sai Mami tace "Bakya son aikin office ne Baby" nan ma ta girgiza kai tace "Nafi son nawa Mami" sai Abba ya sauqe numfashi yace "Ina sane da wannan daughter, i thought kin chanja shawara ne" tace "A'a Abba, i want a big luxury boutique, so i can be my own Boss" murmushi iyayen nata suka fara, Abu na dariya yace "Anty Boss" takai hannu zata ranqwashesa ya kauce, Mami tace "A sannu zaki fara sai ya zama babban ai Baby, Allah ya dafa miki kinji" Nafisa ta amsa da Amin tana murmushi dan har ta hango location din da takeson fadawa mahaifin nata ya siya mata shago agurin, Na'ima sai kallon Nafisan take tana murmushi admiringly, aduk zaman da sukayi a Oxford in Nafisan ta fada mata wannan burin nata dauka take wasa ne saboda ganin yanayin Nafisan na rashin daukan abubuwa serious, but right now Nafisan da take gani a gabanta wata ambitious lady ce mai cike da burin son gina kanta, Abba ne ya kalleta yace "Na'ima kefa?, inason jin naki ra'ayin" sai ta sunkuyar da kai tace "Duk abunda Allah yayi Abba" Mami tace "Ki fadi abun da kikeso har ranki Habibti" nan ma ta qara girgiza kai tace "Babu komai" dan har ranta take nufin hakan, sai Abba ya sauqe numfashi yace "Ma sha Allah, akwai request din da Adam yazomin da ita na son kiyi aiki a company'n su dake nan Abuja, sannan akwai wanda nake nema miki anan CBN matsayin data analyst in kinaso" sai Na'ima ta gyada kai tace "Inason na data analyst din Abba" yace "Ma sha Allah, zan miqa takardun naki, duk abunda ya biyo baya sai kije can din, Allah yayi muku jagora gaba daya" duk suka amsa da Amin aka cigaba da wata hirar kuma.
Washegari da sassafe Mami ta tafi gurin rasuwa, na yar wata distant kawarta da sukayi zaman mutunci, da su Na'ima suka tashi ma basu sameta a gidan ba sai lantana ce ta fada musu, gidan shiru babu kowa sai itada Nafisan dan su Al'ameen ne suka tafi kai Mami gidan rasuwan, bayan sun yi breakfast din Nafisa ta koma dakinta waya kare a kunnenta tana magana da Lamin, Na'ima na cikin wanke dishes din Faruk ya shigo kitchen din sai ta kallesa tace "I thought baka nan fa Yaya" idonsa da alamun bacci yace "Yau ina hutu Habibti, akwai sauran breakfast din ne" ta gyada kai tana nuna masa food flask dinda ke kusan cike da peppered soup, sai yace "Good..hadamin da tea and bread with two plates, sai ki kaimin side dina akwai baqo" ta amsa da toh sannan ya fice, saida ta ta gama dauraye kwanukan sannan ta tafi dakinta ta dauko babban hijab, data fito zata je side din nasu sai taga Faruk din a parking space yana pressing wayansa zaune akan boot din mota ya saita daidai hasken ranan safiya yanashan hantsi kansa duqe, dan qarasowa gurinsa tayi tace "Yaya gashi na gama" sai ya dago yace "Yauwa thank you, kaimin ciki" ta gyada kai sannan ta wuce yana bin bayanta da kallo, saida ta shige sannan ya maida hankalinsa kan wayansa, shigan Na'ima falon su Faruk din sai tayi stiff tana kallon wanda ke zaune a kujera yana kallonta, miqewa yayi yana dan murmushi ya qaraso gareta ya miqa hannu da nufin karban tray dinda ta riqo, ganin yanda yake kallonta yasa ta yin murmushin itama sai taqi bashi tray din ta qarasa ta ajiye akan glass table din da ka falon, bin bayanta Ahmad yayi ya zauna a kujera yace "Gani na dawon Babe" sai ya dan bubbuga hannunsa a gefensa alamun ta zauna, ita kunyansa ne ma ya rufe ta sai ta duqar da kai tana murmushi ta zauna din, ganin taqi kallonsa ya sashi kwantar da murya yace "Bazaki kalleni ba" sai ta juyar da kai, ahankali yace "Gosh...i missed Na'eemah" sai sannan ta kallesa cikin ido tanajin zuciyarta a amsawa, kallon cikin idonta shima yake sai ya kamo hannun ta cikin nasa ahankali yace "I really missed those Eyes" kauda kai tayi tana murmushi, sai ya sake cewa "Babe baki karbi request din ba fa" ta kallesa tace "I knew it was you daman" dan dariya yafara sannan yace "I want you by my side in na dawo nan din" sai ta girgiza kai tana murmushi, ya sake cewa "Shikenan, Allah ya tabbatar da abunda yafi alkhairy, Abba told me you chose CBN, hope aikin bazai shiga lokacin mu ba nan gaba" cike da kunya ta duqar da kanta tace "Duk daya ne fa da aikin naku company din" sai yace "Shiyasa nakeson kije can saboda banason kisha wahala Babe" dan dariya tayi tana kare bakinta da hannu tace "I knew it, ba aiki zanyi ba hira zamuyi tayi in naje can" yana dariya shima yace "I'm serious zakiyi aikin, amma kadan" tace "Uhm uhm nikam" ahankali yace "Ba damuwa sweetheart, Allah ya taimaka aduk in da kikaje din" ta amsa da Amin, sai tayi serving dinsa abincin ya fara ci asannu, kallon ta yayi yace "Kici kema" sai tace "A'a naqoshi" da haka sukayi shiru, can ta fara qoqarin miqewa, sai yace "Ina zakije kuma?" da sanyinta tace "Zan koma cikin gida, Yaya Faruk yana waje" sai ya girgiza kai yace "Karki damu ki zauna muyi hira, i just come here straight from Airport" dan ware ido tayi tace "Yanzu dawowanka?" ya gyada kai yana cin abincinsa hankali kwance tana kallonsa, Na'ima bata yarda ta zauna ba tace masa zata koma ciki dan aranta duk nauyin Faruk din ne ya cikata shikuwa gogan ko a jikinsa sai da ya gama sannan ya miqe yace su fita taren, aikuwa tace "A'a please kabari sai na tafi tukunna" dariya ma ta basa sai yace Toh, da haka ta juya ta fita yana kallonta, acan gurin maigadi ta hango Faruk din zaune suna magana sai duqar da kai ta nufi entrance din gidan da saurinta, Faruk da ya lura da itan sai be kalleta ba har ta shige sannan can shima ya tafi side din nasu, a falon ya tadda Ahmad din har sannan yana shan tea dinda ya qara a cup, sai Ahmad din ya dago kai yace "Thanks Man" tareda miqa masa hannu sukayi shake, murmushi kawai Faruk din yayi ya zauna tareda serving kansa abinci suka fara hira jefi jefi..A washegarin ranan Mami tace su shirya su je gidan Baba da Daddy su gaishe da 'yan'uwan nasu, ranan Nafisa batayi raki akan zuwa gidansu Laila ba wanda hakan ya dan bawa Na'ima mamaki, ranan ma haka Nafisan ta saka ta yin driving dinsu har sukaje gidansu Ahmad din, time din baya nan dan tayi waya dashi yana office a lokacin, Mamma suka samu tareda Anty sai twins da Husna a babban falon gidan, da fara'a Husna ta taso tana musu oyoyo, suna murmushi suka qarasa falon tareda gaishe su, Mamma ta amsa tana cewa "Yanzu dai kun cire gajiyan makarantan gaba daya" Nafisa tace "Aikuwa munyi sosai Mamma" Mamma tayi murmushi tana kallon Na'ima dake sunkuyar da kai tace "Na'ima ya gida" cikin sanyinta ta amsa da "Alhamdulillah", sama sama Anty ta amsa gaisuwan nasu tana kallon Na'iman dan bilhaqqi ita ta manta ta, dakin Husna suka tafi nan sukayi ta hiransu Na'ima na saurarensu jin sun dauko hiran IG da kawayensu, Husna ta kalleta tace "Sis kinyi shiru fa?" Na'ima tayi murmushi tace "Babu komai" sai ta kalli Nafisa tace "Nafee ki bamu labarin Lamin" da mamaki Husna tace "Lamin abokin Yaya da yaje gurin graduation dinku?" Na'ima ta gyada kai tana murmushi, sai Nafisa tace "The guy is sweet, jiya yace min zai dawo nan ai" Husna tace "Yaushe hakan ta faru bansani ba, shine baku fadamin ba" Na'ima tace "Ni ma bata bani labarin in details ba sis" sai Nafisa na dariya tace "Guy's ku tsaya, bari kuji me ya faru" suna kallonta ta hau basu labarin haduwanta da Lamin ranan da zasu je Italy, da kuma ranan da suka fita dinner gaba dayansu a restaurant, anan ne tayi dan dogon magana dashi har ya karbi contact dinta suka fara waya, Husna tace "Kuma dai daga ganinsa zai fi Umar, ke ni yafimin Umar din ma" Na'ima tace "Ya fisa sosai sis" sai Nafisa ta dafa qirjinta da hannu biyu tana juya ido dramatically tace "And he loooves me" kawai suka kwashe da dariya dukansu ganin draman Nafisan, Na'ima tace "I'm so happy wallahi" Husna ta qara da "Wallahi nima haka, in sha Allah you've finally found your Mr right sis" Na'ima ce ta fara amsa wa da Amin sannan Nafisan...
Da suka tashi tafiya sai Nafisa ta nufi gidan Anty fatima dasu, basufi 30mins ba suka isa gidan nata daya kasance babba sosai cike da alatu, a babban falonta suka zauna Na'ima ta dauki 'yarta hamra da tayi wayo zuwa sannan, Anty Fatima tace "Ko ta ganeki ma?" sai Na'ima tayi murmushi tana wasa a hamra dake ta babbaka dariya, gaisawa sukayi Anty Fatima ta miqe ta nufi kitchen bata dade ba ta da kawo musu refreshments sai ta hado da wasu fluffy milky cakes qananu, Nafisa na gutsira tace "Anty Fatima amma yanzu kikeyi ko, naji da dumi" sai tace "Ban gama ba ma ga sauran can inayi, Yaya ne ya sani in masa jiya, so inaga anjima zan kai masa can gidan ma" Nafisa ta amsa mata, tana santi ta miqawa Na'iman tace "Bobo ci kiji, yayi dadi sosai wallahi" karba Na'ima tayi Hamra dake jikinta ma ta miqo hannu zataci sai ta gutsira mata sukaci taren, sai da taci tace da Anty Fatima "Yayi dadi sosai Anty" sai Anty Fatima tayi dariya tace "Karki ce min Anty baruwana" dariya Nafisa ta fara sai tace "Kema kin gane komai ko Anty" tace "Ai Yaya baya boye boye shi daman, straight ma ya fada mana komai ranan da muka koma London daga gidanku" sai Na'ima ta duqar da kanta kunya na cika ta, Nafisa tace "Ni dama tun zuwan mu bikin salma dazamu koma na fara gane komai" Anty Fatima na murmushi tace "Abu yayi kyau Anty Na'ima, he loves you alot, dan har Mamma ya fadawa, we are so happy about it" itadai Na'ima har sannan kanta yana qasa batace komai ba tana murmushi, Nafisa sai grinning take from ear to ear, da haka suka taya Anty Fatima ta qarasa sauran snacks din, aikuwa tana gamawa sai ga kiran Ahmad a wayanta yace mata yana waje, sai da ta amsa masa sannan tace musu "Nafisa tayani dauka mukai masa wai bazai shigo ba, daga office yake, kinga ya hutar dani zuwan ma" Na'ima bata bisu ba ta zauna anan falon suka tafi kai masa sannan suka dawo, aikuwa basu gama zama ba sai gashi ya shigo falon hannunsa riqe da leda daya, anutse yace "Fatima wancan ma ya isheni, yamin yawa" sai ta miqe tace "Toh Yaya" sanin me ya kawosa yasa Nafisa tayi murmushi tace "Yaya ka bamu toh mu qara akan namu" sai ya miqa mata ledan yana kallon Na'ima da taqi kallon gefen sa, da haka ya juya ya fita daga falon Nafisa na masa godiya...sun dauki lokaci kafin su bar gidan Anty Fatima sai Na'ima taga Nafisan ta juya kan motan sun dauki hanyan komawa gida, kallonta tayi tace "Nafee kinsan fa Mami tace muje har gidan Daddy" Nafisa tace "Karki fada mata bamuje ba dan Allah, wallahi banason ganin banzar can yau, I'm in good spirit" murmushi Na'ima tayi tace "Ni dai baruwana, sai munje" sanin Na'ima zata iya fadan gaskiya agurin Mamin yasa Nafisa tayi tsuka tareda kai wa Na'iman duka tana kaucewa, sai tace "2 minutes zamuyi wallahi" Na'ima ta gyada kai tana murmushi ta kalli window, itama har ranta batason zuwa amma saida Mami ta musu gargadin zuwa can din, shiyasa babu yanda ta iya itama, message din Ahmad ne ya shigo wayanta through WhatsApp, sai tayi reply daganan kuma ya kirata, har suka isa gidansu Lailan waya suke, sai da sukayi parking sannan tayi masa sallama suka qarasa cikin gidan shima a falo suka tadda Mummy da Anty Murja da tazo wuni gidan, zama sukayi fuska adinke Nafisa ta gaidasu, suka amsa sama sama Murja tace "Ke dai Nafisa inaga in muka hadu a hanya ma zakice baki sanni ba" sai tace "Nasanki mana Anty, kawai dai haduwata dake a gidanmu ne bata yiwuwa shiyasa" sanin me take nufi yasa Mummyn cewa "Ke zuwa gaida uwarta kikeyi ne, uwar yan raini" Nafisa ta juya kai ranta na baci batace komai, sai Mummy ta kalli Na'ima tace "Ita kuma wannan din ta yafe danginta na nijar dinne da har kuka gama makarantan ta biyoku nan din" ci kanka Nafisa batace mata ba sai ta kara waya akunne tana fadin Hello alamun an kirata, Murja tace "Zanyi maganinki asannu Nafisan" Na'ima dai kamar ta arce daga falon takeji, sai lokacin tayi dana sanin fadan suzo din, Laila ce ta shigo tana waya sai tayi stiff ganin wa'inda ke falon, cikin kashe murya tace da Luba da suke wayan "Bari zan kiraka Yaya" sai tayi dan dariya ta sake cewa "I promise dear zan kira" da haka ta kashe wayan ta qaraso falon Anty Murja tace "Ke da wa kuke wayan sis" sai da ta zauna a gefen Mummy cike da isa tace "Yaya Ahmad, shi ya dawo dani ma yanzu" kadan ya rage Nafisa tayi dariya a falon, sai ta daure ta danne gashi ba'a basu ko ruwa ba balle tasha ta maida dariyan, Na'ima dai jinta kawai take sai ta samu kanta da motsa bakinta alamun murmushi kawai, Anty Murja har da fadin "Love wan tin tin sis, Allah ya kauda idon maqiya kinji sis" sai Laila tace "Amin wallahi" tana kallon Na'ima tace "Baqi kukayi ne" sai Mummy tace "Yanzu nake tambayan Nafisa ko wannan din ta yafe danginta na nijar din" Nafisa tace "Yar qanin Mami ce fa, jininmu ce Mummy" Laila ta tabe baki tace "Su jini da Nijar manya, ana tafe dai" sai Nafisa ta mata wani irin kallo tace "Bangane ba?" sai Laila ta miqe tana fadin "Bari naje nayi wanka Mummy" da haka ta nufi stairs ranta na zafin ganin Na'iman, ran Nafisa in yakai dubu to ya baci a wannan lokacin sai kawai ta miqe tace "Zamu tafi" Na'ima ma tayi saurin miqewa suka nufin hanyar fita su Mummyn na bin su da kallo..Rai a bace suka koma gida ranan, aikuwa suna isa Nafisa ta fadawa Mamin yanda akayi, sai tace "Na hanaki biye shirmen Laila amma bakyaji Nafisa" ran Nafisa ya sake baci anan ma, sai Mami ta kalli Na'ima tace "Habibti kar kisa damuwan komai aranki kinji, haka hausan Maman Lailan yake" sai Na'ima tayi murmushi tace "Toh Mami" da haka suka kama wata hirar daban anan falon Mamin..Washegari da safe Ahmad ya aiko motan Nafisa gidan, to their utmost suprise sai ya hado da wata irinta sak amma white color yace ta Na'ima, da suka fito kallon motan a compound Nafisa ta rinqa tsalle tana kama Na'ima tace "Wayyo our first matching car Besty" sai ta sake wani tsallen Na'ima na dariya, Mami na murmushi tace "Ma sha Allah, maza ku kirasa ku masa godiya sosai" suka amsa da Toh sai Nafisa ta kalli Al'ameen dake zaune a driver's seat yana duba features din cikin motan tace "Bro ka sayi irin ta kaima" sai ya dan bugi sitiyarin motan yace "Ai dole ma, amma sai na dawo wani hutun tukunna" Faruk na murmushi yace "Sai ku cika mana parking lot da wrangler jeeps kenan" Abu yace "Nima sai na siya gaskiya" nan Nafisa ta juyo tace "Kana siya zan saida tawa" kowa sai da yayi dariya a gurin, Na'ima ta matsa kusa da Abu tace "Ka riqe tawan toh, daman ban cika driving sosai ba ai" sai Abu yayi dariya yana girgiza kai, Faruk yace "A'a Na'ima ki tuqa motan ki kinji, da haka zaki saba, I'll buy him the latest model shima" Mami na kallon Na'ima tana murmushi sosai, sai ta shafa kan Abu tace "Rabu da Nafisa Babana, kaji abunda Yayanku yace ma" aikuwa aranan Faruk yayi ordern motan Abu yace it's high time shima Abubakar din ya fara tuqa mota tunda ya shiga shekararsa ta sha takwas shima, da Abba ya dawo da dare yasha surutun akan motocin ranan, yana zaune sai murmushi yake yana sauraron kowanne daga cikin iyalin nasa, sai da suka gama zancen motan sannan yace da Na'ima "Daughter nayi waya da Adekunle yace you can go for an interview tomorrow" cikin ladabi ta amsa da "Toh Abba, nagode" sai yace da Nafisa "Kema nasa Yayanki ya yi magana da constructors na shagon naki, an samu location mai kyau, sai kuje da qannenki ku gani" da fara'a Nafisa tace "Toh Abba in sha Allah" Faruk yace "Gobe ki sameni a part dina muyi maganan komai"..
Washegari da Na'ima ta shirya tafiyan sai su Mami da Nafisa suka ce taje da motan nata itama, haka ta fito cikin shirin abaya, dan Na'ima na son Abayas sosai, da ta shiga motan sai ta tsaya tana kallon interior din, sai lokacin ta lura everything about the car scream luxury, no wonder Nafisa takeson motan ashe, wani kiran ta sake yiwa Ahmad dan sun gaisa da safe, bugu biyu ya dauka lokacin yana office shima, sai tace "Thank you once again, i love everything about the car" daga dayan bangaren Ahmad ya kishingida jikin executive chair dinsa, anutse yace "Babe inata tunanin yanzu zata rinqa hanani daukoki" sai tayi murmushi tace "Kaga na hutar dakai ai" yace "Ki riqe hutun ki" dan dariya ta fara sai ya sake cewa "Da yaushe zaki koma gida?" Tace "Bansani ba, duk lokacin da suka sallameni" sai ya kwantar da murya yace "Should i order food for us sai ki biyo ta office dina?" cikin shagwaba tace "Uhm uhm" yace "Idanun ki kawai zan kalla i promise" sai tace "Okay ba idanuna kadai kake gani ba dama in muka hadu?" shiru Ahmad yayi har sai da ta dago wayan taga kiran is still going, ta sake cewa "Hello" ahankali yace "Your figure is so mesmerizing Na'eemah" cike da kunya takai hannu idonta tana rufewa bata bar murmushi ba, cikin rada tace "Ahmad...what is this?" yana murmushi yace "I told you kina turning dina on baki yadda ba ko" bata ce komai ba sai ya sake mata rada "Watarana zan nuna miki hakan kinji" ai da sauri ta kashe wayan tana dan dariya, tana mamakin halin Ahmad wanda in zata kwana dubu tana fadin haka gurin 'yan'uwansa bazasu taba yarda ba....