BLOOD CROWN (THE HEIRS APPARENT)

PAGE _______12 & 13

by @swrites22



Daga bayan ta taji ance, "sannu ƙaramar ɓarauniya"..........Juyawa tayi idonta ya shige cikin na yarinyar nan da tayi sata a starlight beauty co. sannan ta nemi ta ɗaura mata, Saida ta ƙare mata kallo sannan ta ce, "Yauwa sannu babbar barauniya".........."Ina kudi na ?"........ Yarinyar ta tambaya.

"Dama kin bani ajiya ne?"............ Itama Hushaiman ta maida mata tambayar tana binta da wani kallon banza. "Kuɗin da kika sata jiya, suna Ina?".

"Haa ikon ALLAH, au da kika sata kin bani ne kince na ajje Miki?".

"Amma dai kinsan ba naki bane meysa kika ɗauka, meysa baki maida su jakar tawa tare da Abun hannun da zoben ba, kika sani ramakon kuɗin da banci ba".

Wani gafalallen murmushi Hushaima tayi tare da faɗin, "Ke kina da kuɗi makamancin wancan ɗin kikayi sata".

"Amma dai kinsan ko kogi baiki daɗi ba, kuma abinda na sata ɗin da nayi a Sa'a ai kinga yafi abinda nake dashi ɗin, kawai ki ragemin zafi mu raba asara".

"Zancen banza ma kenan, kinga ni shawarar da zan baki shi ne ki nemi Abun yi domin sata ba sana'a bace dan sai wani ya ajje kin gani zaki ɗauka, in Bai ajje ba Kuma rayuwar ki tana cikin gararin babu, Dan haka ki maida hankalin ki tun da sauran mutuncin ki kafin a samu wasu su ankare dake su Miki dukan da baza ki moru ba"........ Tana kaiwa Nan ta juya da niyyar Ƙara gaba yarinyar nan ta riqo kafaɗarta tare da juyo da ita da ƙarfi tana faɗin, "Whl baki Isa ba ɓarauniyar banza ke har kina da bakin bawa wani shawara, ko kema ba satar kikayi bane?".

Hushaima na juyowa ta buge hannun da ƙarfi tare da nuna ta da yatsa ta ce, "kinga karki ɓatamin rai whl zan iya janyo miki Abun kunyar da har ki mutu baza ki manta ba, sannan ni ban taɓa sata ba, kyauta ce kika ɗauka kika ban tunda ke kika sakamin a jaka Kuma kika biya a asusun ki. Sannan Kuma gargadi na ƙarshe ko a titi kika ganni kika nuna kin sanni sai kin gwammace mutuwar ki kafin wanna ranar, banza Mai matacciyar zuciya, ki rufawa kanki asiri ki wuce ki bar kasuwar Nan tun kafin masu kaya su fara nemanki"............Ta Ƙarashe tana wucewarta ta bar yarinyar tsaye sake da baki cike da mamakin yadda akayi Hushaiman ta san tayi sata a kasuwar, jijjiga Kai tayi cike da borin kunya ta ce, "Zaki San sata gidan barawo rance ce"........... Ta ƙarashe tana saka hannu cikin hijab ɗin ta ta gyara zaman jakar dake kugunta Wadda take cike da hakkin mutane data sanfe.

 Ita kuwa Hushaima tana gama sayan abinda zata saya ta tari abun hawa ta wuce gida, tama manta da batun wata ɓarauniya. Ganin me tuktuk ɗin na ƙoƙarin ɗaukan wata hanya daban ya sata faɗin, "Miqewa fa zamuyi"............ "Eh hajiya ai na sani zan biya ne na karɓi saqo sai mu wuce".

"Kaga Malam tunda mun kusa kawai mu ƙarasa ka saukeni sai ka wuce".........Hushaima ta faɗa.

"To Hajiya ai nan gaban mu ne zan karɓi saqon duk kan hanyar ne "............wata wadda Hushaima ta tarar a cikin tuk tuk ɗin ta ce, "Ni mun ma iso, sauke Ni anan" ..............."Gsky bazan tsaya ba ai ba nan mukayi dake ba".

"Kamar ya baza ka tsaya ba tace ma ta iso haa"........ Hushaima ta faɗa a fusace.

"Whl ko me zakuyi bazan tsaya ba sai na kaiku in da zaku".......... hankali tashe matar ta ce, "Malam nace ma na iso ka tsaya na sauka ko na ma ihun ɓarawo Whl" .

"Whl bazan tsaya ba"............ screwdriver Hushaima ta kafa masa gefen wuya da faɗin, " ko ka tsaida mashin ɗin nan ko na burma ma ita whl"........... Gefe guda kuwa matar nan leqowa tayi tana ihun faɗin ɓarawo jama'a ɓarawo ku taimaka. Jin haka ya sashi ƙara gudun mashin ɗinsa ɗan yasan yana tsayawa in mutane suka rafke shi sai sun halaka shi saisa kawai ya gommaci in ma caka masa Hushaiman zatayi saidai ta caka masa. Wani irin bugu Hushaima ta daddage ta kai masa a gefen wuya, rawa kan tuk tuk ɗin ya fara masa a hannu saboda a bazata yaji bugun, take jijiyar muqamikin sa ta riqe yayinda gudun tuk tuk ɗin ya sassauta, kafin ya gama dawowa hayyacin sa Hushaima ta kudunduni kayanta tayi tsalle ta dira a waje ganin haka yasa ɗaya matar ma bin bayanta. Nan mutane suka rufarwa tuktuk ɗin saidai ko da sukayi nasarar isa gareta me tuk tuk ɗin ya suma, ita kuwa Hushaima ba tare data damu da yan raunikan data ji ba ta tsari wani me tuk tuk ɗin ta wuce gida tana godewa ALLAH da ya taimake su.

Tana shiga ta samu Sahnish tsaye a tsakar gidan yanayin fuskar sa ne ya shaida Mata kamar yana cikin damuwa, ƙarasa shigowa tayi kallon furkarsa ta ce, "Sahnish lpy meke faruwa?"

"Meysa kike da taurin Kai ne Hushaima? Meysa duk abinda kika sa kanki sai kin yi ? Meysa in kina Abu bakya tunanin abinda zaije yazo"...........Cikin Rashin gane Kan zancen sa ta ce, "me.. me kuma ya faru?"

"Meysa zakiwa su karafiya shu ne idan kuma suka gane da sa hannun ki ciki fa? Whl baza su barmu ba kuma kin sani ".

"Shu ne kuma? Ni ? To ina ruwana dasu, ni ai tun ranar da suka ma wannan dukan naje mukayi cacar baki ko kallon inda suke zama ban sake yi ba, to uban wa ma yace ni na musu Shu ne?".

"Ba uban daya gayamin Sarkin masifa, kawai naje shagon Juma ne zan saya katin waya, sai naji wani yana faɗin wai hukumar yaqi da miyagun kwayoyi ta ƙasa ta kama su karafiya,  kotu ma ake shirin kaisu saboda an same su da kwayoyi masu hatsari".

"Eh shikenan kuma sai zuciyar Ka tace ma ni nasa a kama su ko, saboda nice kullum cikin rigima ko Sahnish? Wai meysa Baka kyautata min zato ne? kullum a cikin zargi na kake nayi kaza nayi kaza".

A sanyaye ya ce, " kiyi hakuri, yadda kika fita ranar da qudurin fansa yasa nayi zaton haka".........bata ce masa komai ba ta ajje jakarta tana kokarin cire gyalenta suka ji ana kwankwasa ƙofar gida, kallon ta yayi da faɗin, " waye ne?".

Wucewa tayi ciki tana Kiran Shazeen ta ce, "Ina cewa tare dakai muke tsaye, kaje Ka duba mana".

Juyawa yayi ya fita zuwa ƙofar gidan dan ganin waye ita kuma ta shige ɗakin su. Yana fita ya tarar da wasu maza biyu tsaye sai wata makociyar su. "Lpy dai?".......... Ya tambaya yana binsu da kallo. Matar ta ce, "Gashi nan tun ɗazu ya Kafa min a ƙofar gida yana neman haɗani rigima da mijina, wai sai na fito masa da Hushaima nace masa ba nan bane yaqi yarda, to kai kaga gidan nata karka ƙara dawowa ƙofar gida na".

Kallon sa Sahnish yayi da faɗin, "To lpy dai?"..........."Eh lpy ba lau ba nayi mata kayan ɗaki ne sai ta bani rabin kuɗin tace zata cikamin rabin daga baya na bata kayan, to kusan sati kenan dana haɗota da yara na suka kawo Mata kayan, dake Babbar mota bata shigowa sai suka ajje daga bakin layi ita kuma tasa aka ɗauko mata kayan aka shigo dashi nan layin, to naji shiru kuma bana samun layin ta shi ne na ɗauko yaron da suka zo tare ya nuna min gidan wannan matar, ita kuma tace ba nan bane".

"Kayan ɗaki ? Kuma anan gidan? Sannan kace Hushaima?"........... Ya tambaya cike da mamaki.

"Eh, kaga ka shiga ka kirata kawai"..........Jijjga kansa yayi da faɗin, "kwantar da hankalin ka, zan kirama ita mana"...........Ya faɗa yana juyawa ya wuce ciki har lokacin mamaki yake. "Hushaima!, Hushaima!".

"Wai Sahnish lpy kake ta ƙwalamin Kira haka, wanka fa nake son shiga".........Ta ƙarashe tana leqowa.

"Eh wasu mutane ne suka zo neman ki, suna ƙofar gida "..........."Wasu mutane kuma? To uwar me zan musu?". 

"Ah waqa a bakin me ita ai tafi daɗi, ki leqa dai ki gansu tukunna".

"Kai dallah in zaka faɗamin su waye ka faɗamin bana ciki da iskanci".

"Ya hakuri bani na kar zomon ba, wai wani kafinta ne da ya haɗa Miki kayan ɗaki, kika karɓi kaya kuma kika gudu baki cika masa kuɗi ba".........ya ƙarashe yana dariya ƙasa ƙasa.

"Kai kaga inda aka shigo da kayan ɗaki a gidan nan ne?"...........ƴarfa hannu yayi da faɗin, "To ni na san muku ne, yanzu dai kije ki sallamesu".

Ƙwafa taja ta nufi ƙofar gidan, tana fitowa matar ta ce, "Gsky zan gaya Miki karki Ƙara taro rigima ki turomin gidana wannan ai sai ki kashe min aure"........... Matar ta faɗa cikin ɓacin rai.

Saqale Hushaima tayi baki buɗe tana kallon ta kafin cikin ɓacin rai ta ce, "Ke da ALLAH malama dakata ni na nuna masa gidan ki ne, ke kinsan ba gudun rigima nake ba bare kice tsoron hakan yasa na turoshi gidan ki. Ki kama kanki Bana shiga harkar kowa a unguwar nan duk kuma wanda ya shiga tawa to whl rashin mutuncin da zan keta masa ko karai bazai shishina ba , Kai kuma uwar wa kayi wa kayan ɗaki?"......... Ta ƙarashe tana zaro masu rikitattun idanun ta. Duk wanda ya kalle ta a wannan lokacin yasan tabbas ba karamar yar rigima bace ba kuma tsoro a tattare da ita daidai da misqala zarratin.

"Dan ALLAH kiyi hakuri"...........Ya faɗa yana juyawa wurin matar ya ce, "Ni fa ba wannan bace wadda nake nema".

"Kai malam karfa ka rainamin hankali, wannan dai itace Hushaima kaɗai a unguwar nan".

"Hushaima ne sunan ta amma ba wannan bace"......... Carpenter ya faɗa, Hushaima data maidasu TV ta buɗe baki zatayi magana dan tuni ta gano wata ce kawai ta damfare shi a layin ta kuma yi amfani da sunan ta, Kuma duk yadda akayi ta mata farin sani ne, bata kai ga yin Magana ba ta hango wata matashiyar budurwar na fitowa daga wata arniyar BMW i5 sedan, tana sanye da wasu shegun English wears riga da wando, fuskarta manne da wani makeken glass, kyakyawa ce sosai gashi kallo ɗaya zaka mata ka hango class a tare da ita daga yanayin takunta ma. Da wani irin kallo tabi mutanan dake ƙofar gidan kamar taga wasu sabbin halittu daga wata duniyar kafin ta maida kallon ta ga Hushaima data ɗan saki fuskar ta duk da ba wai murmushi take ba. "Mutan new york saukar yaushe? Bismillah shiga daga ciki mana Ina zuwa".

"Ke dai bari tun last week na dawo ban faɗa Miki bane saboda dama surprise nake son miki"......... Ta ƙarashe tana sake kallon mutanan sannan ta shige ciki tana faɗin, "Saikin shigo".

Ita kuwa Hushaima baquwarta ta na ida shigewa ta fara tijare mutanan nan tare da yin jam'u ga dukkan mutanan unguwar ta musu tas sannan ta ce ALLAH yasa wata ta sake amfani da sunan ta whl sai taci mata uwa, duk ta tara mutane a ƙofar gida daga karshe ta ce, "ku Kuma ku daibi kafuran ƙafafunku ku bace min daga ƙofar gida tun kafin rai na ya ida bacewa"...........sumi sumi suka wuce, da kallo ta bisu kafin ta ce, "Munafukan mutane da ana ruwa suna irgawa tsabar sa ido, ALLAH yasa wani me tsautsayin ya sake daibo kafa yazo ƙofar gidan Nan"..........Ta Ƙarashe tana juyawa ta shige tare da gabzo ƙofar.

A tsaye ta samu baquwarta ta tana danna waya, ɗaki ta wuce ta ɗauko tabarma ta shimfiɗa tana faɗin , "Ya hakuri Amla na barki a tsaye kina jira".

 Sai da ta zauna sannan ta kalli Hushaiman data zauna ita ma, ta ce, " ƙawata meke faruwa Wai?".

"Mtwee barni kawai, mutanan unguwar Nan ne suke neman su tsokano ni, kinsan mutane baka shiga harkar su ma nema suke su taqale ka, wai wata ce akayiwa kayan ɗaki bata cika kuɗin ba ta gudu Kuma Wai sunan ta Hushaima shi ne suka kawo carpenter nan".........."Yanzu ya kukayi dasu?"

"Ai kema kin sani, na saita musu hanya mana, to ni akwai wata sabuwar buɗewar ido da za'a nuna min ne".

Dariya Amla tayi da faɗin, "ƙawata kenan baki da dama, nayi missing dinki sosai whl".

"Ki bari kawai, ai Ina ganin videos ɗin ku a yanar gizo, naga kin sake karɓo mana lambar yabo, ALLAH ya sanya alheri".

Murmushi tayi me ƙayatar wa kafin ta ce, "Ameen ƙawata, Ina su Shazeen ne naji gidan shuru ko tana makaranta?".

"Duk suna Nan, Shazeen!, Shazeen!".

"Naam".......... Ta amsa tana fitowa daga ɗakin ganin Amla yasa ta taho da gudu ta faɗa kanta tana dariya, itama rungume ta tayi daga zaunen da take tana murmushi ta ce, "Sweetheart ykk ya scul ?".

"Lpy kalau aunty Amla, kullum Ina tambayar Aunty Hushaima Ina kika tafi, tace min kin tafi New york, har mafarkin ki nayi jiya".

Kallon Hushaima tayi tana murmushi ta ce, "kinji ko, ni Anya bazan daina ƙawancen nan dake ba, oh sweetheart nima kullum sai na tambayeki, yayar nan taki ce baƙin hali ya mata yawa, taƙi haɗamu mu gaisa".

"Can ta matse muku kuma, sai ki ɗaga ta ai kije ki faɗawa Sahnish ga Amla ta zo ya fito su gaisa".

"Dama Sahnish Yana Nan?"........."Yana ciki, saidai in wani Abun yakeyi"..........Tashi Shazeen tayi ta wuce ɗakin Sahnish domin sanar masa saqon Hushaiman.

Gyara zama Amla tayi tare da zaro wani form a jakarta ta ce, " Nayi wani karambani, Amma karɓi dai ki gani".......... Karɓa Hushaima tayi ta zubawa takardar ido sai Kuma ta ɗago tana kallon Amlan da yanayin neman Ƙarin bayani. "Form ɗin neco ne da aka fara siyarwa shi ne na siya Miki, kinga in results ɗin ya fito sai a samu wata higher institution ki jo na".

Da wani irin yanayi take kallon Amlan har tagama maganar sannan ta furzar da zazzafar iska, "Amla naji dadin karamcin ki a gareni, Amma da kinyi shawara dani baza ki siya ba domin ni inaga asarar kuɗin ki kawai kikayi, dan bazan iya zama na rubuta komai ba".

"To in baza ki iya ba, ba sai asa a rubuta miki ba, ai ba abinda zai gagara".

Sunkuyar da kanta tayi kamar me jin kunyar abinda zatace, kafin ta buɗi baki ta ce, "Amla taya zan nuna shaidar gama secondry sannan na kasa kare Kai na".......Da fuskar tambaya Amla take kallon ta saidai kafin tayi magana su Sahnish suka iso. "Ahh yau kuce manyan baki ne a gidan namu".

Yar dariya tayi da faɗin, " Kaji Sahnish Kuma da wani batu, ni ai ba baquwa bace, ya kake ya gidan?".

"Ni dai karki canza min zance ba haka nake nufi ba, Alhamdulillah kin iso lpy?".........."Lpy kalau alhamdulillah, meya same ka? ciwo kaji ne ?"

Hushaima ce ta karɓa maganar da faɗin, "Me machine ne ya bugeshi"..........."Subahanallah, ALLAH ya kare gaba, sannu Sahnish".

"Yauwa amla nagode, Bari na koma daga ciki kafin Ku gama".

"Ah ah, kaga bama jimawa zanyi ba, tunda na dawo ban fita ba sai yau shi ne nace Nan zan fara zuwa".

Murmushi yayi da faɗin, "Mun gode sosai, ALLAH ya bar zuminci".........Tashi Hushaima tayi ta shiga ɗaki ta ɗauko dan kwalin ta suka fita raka Amla ɗin gabadayan su, tana ƙarawa Hushaima bayani Kan maganar neco ɗin da Kuma amfanin ilimin, anan Sahnish yaji, sosai ya nuna jin dadin sa tare da mata godia. Har wurin motar ta suka rakota, buɗe bayan motar tayi ta ɗauko wasu shopping bags guda biyu masu kyau ta miqawa Shazeen ɗaya sannan ta miqawa Hushaima ɗaya da faɗin, "Tsarabar New York ce, ba yawa gashi Nan ke da Sahnish"......... "irin wanna dawainiya haka Amla, mun saki wahala da yawa ai".

"Kinga madam ba fa Dan ke na kawo ba, kawai dai dan karki sawa na kannen na ido ne saisa kawai na Dan Kara dake".

  Sahnish ne ya amshe da. "Kinga Amla rabu da wanna baki ne da ita kamar aku"........ Duka ta Kai masa ya kauce Yana dariya, juyawa tayi wurin Shazeen da faɗin, "Shazeen kiyi wa aunty Amla Godia".

"Ina ruwanki, tun kafin ki faɗa tayi ai Madam"......... one side smile ta saki wanda ya sake fito da kyanta saboda ba ko yaushe takeyin murmushin ba saisa in tayi yake mata kyau. "Muna ƙara Godia Amla, ALLAH ya saka da khairan".

"To Ameen"........ Amla ta amsa tana shiga mota, daga nan sukayi sallama tare da dan matsawa gefe shi kuma Sahnish ya shiga duba mata hanya da zatayi reverse ta fita daga layin. Saida ta fita a layin sannan suka juya gida.

A tsakar gidan suka zube nan kan tabarmar suna duba kayan. Sahnish riga da wando ne masu kyau da turare sai Hushaima data sako mata dogayen riguna uku, ɗaya armless sai long sleeve ɗin da take tafe da ita a ciki, biyun kuma jacket suke tafe dashi wanda ta tsaya iya ciki, sai turare da veil ƙarami. Na Shazeen kuma English wears ne masu kyau na yara daidai shekarun ta tare da hair oils da ribbons sai su chocolates. Ita dai Hushaima tattare nata tayi ta wuce ɗaki ta ajje tare da form ɗin da Amlan ta bar Mata su cike zata dawo ta karɓa, sannan ta cire kayanta ta ɗaura zani ta fita ta shige wanka.

 Har ta fito su Shazeen na tsakar gidan, sai gwada kayan take, tana ganin Hushaiman tayi saurin matsawa tana faɗin, "Aunty Hushaima kinga yadda kayan suka min kyau"........ Cikin Jin dadi ta ce, "Naga kayanki Shazeen, Kaya sunyi kyau sosai, ALLAH yasa a kashe lpy, mun godewa aunty Amla".......Tsallen murna tayi ta koma wajen Sahnish ita kuma ta shige ɗaki dan shiryawa, wata yaloluwar doguwar riga ta material marar nauyi ta saka tare da jan robar wandon data ke daure gashinta da ita, fatabarakar Rahman shi ne abinda baki na ya iya furtawa ganin yalwar gashin Kan Hushaima Wanda dama tun daga fuska zaka shaida  akwaishi Amma baza Ka taba tunanin zai Kai haka ba, dogo ne sosai dan ya kusan wuce kugunta gashi da tsantsi saidai bashi da cika can can kuma ba baƙi bane, light brown ne. Masarci ta dauka ta taje sannan ta daure shi in a sleek bun style. Juyawa tayi da niyyar fita Shazeen ta shigo da jakar kayan ta ɗaya hannun kuma ledan sweets ɗin ne, karɓar jakar kayan tayi ta ajje sannan ta karɓa na sweet ɗin ma ta eba mata kaɗan daga ciki ta bata sannan ta boye sauran ta juya ta fice.

Yana zaune a inda Shazeen ɗin ta barshi, zama tayi kusa dashi sannan ta kira sunan sa , "Sahnish!"........... Ɗagowa yayi yana kallon ta ba tare da ya amsa ba. "Kai za'a cikewa form ɗin nan bani ba".

"Kamar ya bangane ba?" .........Ya faɗa yana bata dukkan hankalin sa.

"Kai zaa zanawa bani ba, Kai zakafi buqatar ta"........ Dan shuru yayi kafin ya ce, "Dani dake fa duk Abu ɗaya ne, kinfi kowa sanin abinda baza ki iya ba to ni ko tunanin somawa ba zanyi ba, ni inaga kawai mu faɗawa Amla gsky".

"Ban gane a faɗawa Amla gsky ba, kana so ka kunyata mu ma kenan, nace mata iya jss muka tsaya sannan yanzu kuma muce mata bamu taba zaman aji ba ko me ?".......... Ta ƙarashe tana wurga masa wani kallon cikin ido, shi ma kallon nata yake, tsawon two minutes suka ɗauka kafin ya ɗauke kansa da faɗin, "Shikenan duk abinda kika yanke, amma ki tuna shi dai karatu ba abu bane dake ɓoyuwa ina gudun ranar da Amla zata gane muna mata ƙarya, saboda ta ɗauke mu kamar yan uwa". 

Dan shiru tayi tana tunani kafin ta ce, "A tsawon lokacin da mukayi duk bata taɓa fahimta ba sai yanzu, kai dai ka bari ɗin a zana makan kawai"......... Bai sake cewa komai ba ya tattare kayan sa ya wuce ɗaki, ita kuwa gyara zama tayi tare da nutsawa cikin duniyar tunanin rayuwar su.



-------------------------√




Tsaye yake kunnen sa maqale da waya, kallo ɗaya zaka masa Ka tabbatar da ba'a cikin dukkan nutsuwar sa yake wayar ba. "So nake kawai Ka binciko min ta yadda akayi har ya samu visa ya fita wata ƙasar, kuma ma ya akayi ba wanda ya sani bayan kuma a yanzu bashi da ikon ƙetara ko da iyakar ƙasa ne bare kuma ya yi tafiya wata ƙasar a jirgi".........Daga daya bangaren akace. "Oga Awais duk iya binciken da zanyi nayi shi a dai bangare na amma babu wata shaida data bayyana mana cewa Amjad ya fita daga ƙasar Nifaz, domin ɗazu na aika yarana airport ɗin su min bincike kwata kwata bama sunan sa a list ɗin mutanan da suka tashi daga birnin Nifaz a ranar da kuma satin nan gabaɗaya".

"Amma an tabbatar min ya shiga WorldLink international airport a shekaran jiyan da yamma"......... Awais ɗin ya faɗa cikin yanayin dake nuna a qage yake da samun bayanan da yake so.

"Tabbas ya shiga airport Amma saidai wani abun yaje yi, dan gaskiya bincike na ba kuskure a ciki".........takaici yasa ya ƙasa bashi amsa sai kawai ya Kashe wayar tare da dafe Kai cikin takaici ya furta, "Oh sh**t yaron nan Yana son wargaza mana lissafi fa".........Wata number ya sake dialing ana ɗagawa ya ce, "akwai wani labari ne ta wajen Ka?".

"Akwai matsala dai, dan ni whl kai na yana barazanar rabewa biyu, idan fa harta tabbata Amjad ya fita alkadarin mu ya karye, burikan mu sun watse, sannan sirrikan mu na barazanar bayyana, gashi ina ta neman number Julaybin bana samun sa na kirawo Atiq yace min shi tun safe ya fita, na kira Bisma kuma ta shaida min julaybin din ya dade da fita, nayi tunanin har kaina ya kama ciwo".

"Tsaka mai wuyar da kake ciki Nima ina cikin ta Nuhail ko nace muna cikin ta domin duk mu ukun nan shirin mu ne silar tarwatsewar farin cikin sa, aikin mu ne yayi sanadiyyar watsewar alqiblar rayuwar sa tare da sanyashi a tsaka me wuyar da yake ciki a yanzu, shin ya kake tunanin makomar mu wurin al'umma da kuma dada da zan iya cewa sanadiyyar abinda mukayi ne baqin ciki ya kwantar dashi saboda kasan yadda yake ƙulafuncin shegen Amjad ɗin nan".

"Haqiqa muna cikin tashin hankali ba wai, amma yanzu miye mafita?".

"Mafitar mu ɗaya ce shi ne muyi fatan Kar zancen tafiyar da aka faɗa ya fita wurin Al umma, ALLAH kuma ya rufa masa asiri ba'a samu wani dan media ya masa hoto ba a airport ɗin"..........."Kuma Awais da gasken yayi tafiyar?"........Nuhail ya tambaya.

"Ba zan iya ce ma komai ba Nuhail, bangare biyu sun tabbatar min da Amjad yayi tafiya bangare uku kuma sun tabbatar da babu jerin sunan sa a wa anda suka tashi ma".

"To yanzu a wace matsayar zamu tsaya, Nima bangare na na saka a bincika mi........" Bai ƙarasa maganar ba ƙira ya shigo, "To gama shi nan ana kirana".

"Karka kashe ɗaga nima inaso inji".......... Picking Nuhail ɗin yayi da faɗin, "kawule ya Ake ciki?".

"Ranka ya dade daga farkon titin airport ɗin zuwa cikin sa gabaɗaya ɗauɗauku 15 ne, a kowacce kuma result ɗaya ne an shiga dashi airport ɗin daidai karfe 4:40pm a mota kirar range rover silver colour tinted glass, saidai an samu ɗaukewar wasu daga cikin cameras ɗin daga shigar sa wa'anda sune suka wargaza mana lissafi a yanzu, kasancewar baza mu iya tantance ya shige cikin filin tashin jirgin bane ko kuma bai Shiga ba, saidai an auna nauyin tayar motar da suka shiga nauyin ya ragu akan yadda ta shiga hakan ya tabbatar da ya sauka daga motar kenan"......... Duka nuhail ya kaiwa bango cikin qunar rai ya ce, " Duk yadda za'ayi Ku gano cewa ya tashin ne ko kuma bai tashi ba ko nawa ne zamu biya kasan kuɗi ba matsalar mu bane".

"Haka ne yallabai Amma kasan dokar daka ce akan aikin, so munayin sa ne ta sirri idan har zamuyi da zafi zafi to tabbas zance zai iya fita"......... Awais ne ya tare maganar da faɗin, "kaga Kubi a hankali Ku dai kawai Ku gano mana ya fita ko kuma yana cikin birnin Nifaz ne har yanzu"..........."Shikenan ranka ya dade zamuyi iya kokarin mu".

"Zan tura ma na mai yanzu"........... Nuhail ya faɗa, shi kuma ya shiga zuba masa godia,  katse kiran yayi, yayinda Awais ya ce, " Nuhail kana ganin baza mu gwada Kiran Amjad ɗin ba ".

"Mu kirashi mu masa uwar me, zamu bada Kan mu ne kawai, kuma hakan zaisa yayi zargin wani Abu tunda ba saba kiran sa mukayi ba, kasan shi da brain".

"Shikenan, Bari muga abinda hali zaiyi, in na gama abinda nike anjima maybe zan shiga gida wurin hajiya ".

"In Ka fito daga gida Ka kirani sai mu haɗu a can".......... Da haka sukayi sallama tare da katse wayar.

TO FA, MY PEOPLE NI KAINA ABUN NAN YA FARA ƊAURE MIN KAI FA🤔 TO WAI SHIN TSAKANIN SU AWAIS DA SU HAJJ ZAWAAD SU WAYE KE DA ALHAKIN DUSASHE TAURARIN AMJAD? GASHI DAI KOWANNE BANGARE SUNA IKIRARIN DA SA HANNUN SU A CIKI? TUKUNNA MA MIYE MATSAYAR DA SUKE SAN CIMMA A KANSA? MEYSA SU DUKA SUKE FARAUTAR ABU ƊAYA? WANI IRIN SIRRI NE KE LULLUBE DA AMJAD DIN? SHIN SU HAJJ ZAWAAD SUN SAN CEWA SUNA FARAUTAR ABU ƊAYA DASU AWAIS NE ? TO WAI AMJAD YA BAR ƘASAR DA GASKE KO KUMA DAI AKWAI WANI ABUN DA YA FARU DA MU BAMU SANI BA?🤔


MU TARA A NEXT PAGE  DOMIN SAMO DUK WANNA AMSOSHIN TARE DAKU.