MATACCEN RUHI

MATACCE RUHI 2

by @109696625203084497219

*MATACCEN RUHI*

*2026*

*Aysha D Fulani*

*BABI NA BIYU*

Najma ce zaune ta gefenta kuma abokiyarta Aminatu ta kasa ta tsare sai zuba ruwan rashin mutunci take ido rufe, wacce aka maƙure a cikin lungu na hango ido ya yi jajir sai faman nishi take gaba daya ta firgice da Inna uwasu mai jigida da tayun boris wato Najma. Tsawar da Aminatu ta bugace ta bani tsoro ni kaina sai da alkalamin nawa ya fadi da sauri na dauka na cigaba da bin sahu su don rubuto muku abin da ke wakana. 

“Zaki gaya mun gaskiya ko sai na sauke ya tsuna biyar akan wannan fuskar taki?”

 Baki na kakkarwa take fadin
  "Wallahi karya nake yi kawai na kirkira ne da kaina amma ban taba jin Malam Hashi yace yana sonki ba, kawai karya nayi ma su Hansai wallahi na tuba Najma kiyi hakuri wallahi bazan ƙara kwatanta yi miki ƙage ba don Allah” 

    Tsaki Najma taja tana fadin 
    “Kin ceci kan ki da ki ka fadi gaskiya munafukar Allah ta’ala zo ki wuce kona shure ki a wurin wallahi ko da wasa ki ka sake mun wannan shashancin sai na karya ki gida biyu” 
     Da sauri ta fice daga lungun da suka sakata tana ta faman haki, dariya Aminatu ta saka tana fadin
     “Hanya ba kyau Najma kin bani dariya yadda ki ka tsare gida kina hura hanci sai kace wata babba amma Allah ya shiyar mun ke mu wuce aji kinga an koma ma ashe” 
     Karfe biyu daidai a ka taso su daga makaranta tafiya suke suna hirar har suka fara isowa kofar gidansu Aminatu wanda shine na farko sannan na biyu na su Najma, gidajene daidai na rufin asirin bawa irin namu na talakawa sallama sukai da juna suka shige gida. Da sallama Najma ta shiga cikin gidan nasu ta na fadin
     “Wash Allah na wallahi nagaji Allah yasa dai Innamu ta gama abinci”
      Inna dake fitowa daga cikin ɗaki ne ta amsa mata sallama tana mata sannu da dawo wa. Amsawa tai ta nemi wurin akan bakin kofah kan kujera yar tsuguno ta zauna tana duban Inna dake ƙokarin zama akan tabarma fadi take 
     “Inna Allah yasa kin gama abinci wallahi da yunwa na dawo nifah yau ko kudin tara baki bani ba gashi na kwaso yunwa” 
     Dariya Inna tai tace 
    “Haba uwata ai dole na gama abinci nan domin kuwa nasan baki ci wani abun kirki ba kosai ki ka ci fah kunun ma ki tsaya na saka sugar ki sha amma ina sai fitowa nai na tadda abata akan tabarma”
      Hijabi ta cire gefe ta sauko da jakar makarantar tana kokarin zare takalma take fadin 
    “Inna yi hakuri sauri nake ne a lokacin na kosa na tafi makaranta don bani so amun bugun latti wallahi manyan mu ne basu da imani, ko ya ya ka wuce lokaci sai ace kayi latti kuma kin san ni ba kaunar duka nake ba amma fah ni zan daka idan mutum ya yi mun wallahi”
     “Sai kiyi dukan ga wanda ki ka raina ma wayau ai ke wato baza’a dake ki ba amma ke kina son cin zalin mutane muguwa kawai Allah yasa gobe ki shafka latti a zaneki wallahi”
     Jamilu da ke shigowa daga makaranta yake rattafo na shi zancen. Tsaki Najma tai ta jawo kwanon abincinta sai da tai bismillah sannan ta soma ci, ba ta kalli Jamilu ba bare ya sakaran cewa zata kulashi ma.
     “Ka dawo zaka fara tsokanar nata ko wallahi ka fita idona sai ta jibgeka ka zo kana bare ma mutane baki, ka kiyaye ni, haba wannan raini naka har ina bana son wannan halin wallahi ka kiyayr ni na dai gaya maka.”
     Inna ce ke zazzage masa, bata rai ya yi ya nemi wurin zama kusa da Inna. Ita ko Najma ko takansa bata bi ba abincinta kawai take aikawa baki domin ba karamin yunwa ta kwasa ba daga safiya zuwa yanzu. Sai da ta kamallah sannan ta miƙe ta debi ruwa a randa tasha ma’ishi ta tattare kayanta ta shige cikin daki wanda yake mallakinta ita da ƙannanta mata biyu. Saman katifah ta kai kwance tana jin wani irin dadi na ratsa mata gabobin jikinta,wani irin yanayi take ji mai dadin gaske domin kuwa dama ta debo gajiya ga yunwa.
      Jikinta ne ya soma saki daga nan bacci mai dadi ya dauketa. Inna na zaune suna hirrar makaranka da Jamilu su Maryam da Fauziya suka shigo bayan su goye da jakunkunan makaranta, sannu da gida sukai ma Inna suka cire nasu kayan makarantar suka nemi wuri suka zauna suna ci abinci su. 
    Bacci sosai Najma take wanda ko farkawa ba tai ba, har akai kiran sallar la'asar, jin shiru bata fito ba ga lokacin sallah na neman fita yasa Inna lekawa da kanta don tadota.
    "Najma! Ta bubbuga bayanta ta cigaba da fadin "Ki tashi kiyi sallah lokaci na neman shigewa, kinga yaranan duk sun tafi Islamiyya, ki yi sallah ki kaima su Malam abinci can gidan gona nasan yanan yana tsumayen ki"
     Mitsike ido Najma tai bakinta dauke da salati ta miƙe zaune tana kallon Inna tana,nazarin abubuwan da ya fadi, ciki da jin dadi ta mike tana jin farin ciki na mamaye ruhinta. Cike da farin ciki ta dauro alwalah ta gabatar da sallah, hakan ta tsinci kanta cikin yanayin nishadi kuma ta san ba don komai ba ne saboda ance zata gidan gona.
   Tana idarwa ta dauki hijabi mai tsabta wanda yasha karin gugu ta saka, kwandon da Inna ta jera abincin ta dauka tai mata sallama ta kamo hanya.
    Tafiya take tana ƙiyasta yadda zata kamashi yau don kusan wata kenan basu hadu ba. Zuciyarta ce ta jefeta da tambayar to idan yau ma bai zo fah kamar sauran kwanakin.
    Tsaki taja tana ɓata rai "Allah ka cece ni yau dai yazo ko zuciyata zata samu salama daga zugin da take mun" ta fada tana yin kwanar da zata sadata da hanyar gidan. Addu'a take yi don cikar muradinta na son ganinshi, aiko tai sa'a tana sake shawo kwana tai arba da daleliyar matarsa mai matukar kyau da daukar idon duk wanda ya kalla.
   Daga kafah tai don zuciyarta sai azalzalarta take akan shi burinta taga yadda ya koma tsahon kwanakin nan da basu hannu.
    Da Dutsen da ta dauka tun kusan karasowarta ta soma bubbuga gidan, mahaifinta ne ya amsa da "Ana zuwa" hakan yasa tai saurin tattaro duk wata natsuwarta ta dawo da ita jikinta don ta san halin Malam muddun yaga wata alama ta rashin gaskia a tare da kai to wallahi sai ka gaya masa dalili ko kuma yai maganin mutum.
       Tattaro dukkan natsuwa tai ta gaida shi tare da nuna masa kwondon da aka aiko ta dashi wanda ke dauke da abinci mai yawa da kayan lambu sai cokali da farantin zubawa akai.
      Matsawa yai daga bakin karamar kofar ya nuni da alamun ta shiga ta ajiye masa a inda aka saba ajiyewa.
     Aiko da sauri na shige domin kuwa burina kenan dama in gani cikin babban gidan wanda shuke-shuke su kai masa ƙawanya ta kowacce kusurwa. Ga dabbobi tunda ga kan Shanaye har zuwa kan kaza yar gida, ta can gefen kuma wani irin tafki akai mai girma aka zuba kifaye na tarwada wanda sai sun kai wata takwas ake cire su a siyar gaba ɗaya.
    
    Kutsa kaina nayi ciki sosai don inga ko yanan, aiko da turarensa nafara cin karo wanda ɗaddan kamshinsa yasa ni lumshe ido hadi da ajiyar zuciya.
    Zaune yake akan tabarma mai kamar kafet hannunsa rike da waya kirar kamfanin apple, ya amai da hankalinsa sosai kanta sai faman sarrafa ta yake. Sanda na samo yi a hankali har na isa bayansa.
    Gashin kaza na dauka na shiga shafamasa a gefen kunne. Da farko hannu ya kawo ya sosa a karo na biyu kuma ya sake mai da hannun wurin yana karkaɓe wurin. Da yaga dai ba sarki sai Allah ya jiyo yaga mai ke hawa masa wuyan riga.
  Tsorata yai da sauri yai baya yana kallonta da kyawawan idanunsa masu matukar isar da sakonin soyayyar sa garrta.
    Haɗe rai ya yi yana dubanta a alamar yaji haushin abun da taimasa.
  Langabe kai tai ta kama hannunwanta sama ta rike kunne ta soma kai ƙafafuwanta kasa. 
    "Kina zubewa a wurin zan dauke ki cak yau sai dai Malam yace na lalata masa ke " ya fada yana dubanta
    Dariya tai a hankali tace "To afuwan ka yafe mun har a gurin Allah"
    Yadda ta tsare shi da fararen idanuwanta masu kyau da daukar hankali abun gwanin sha'awa.
Samun kansa ya yi da sakin mata murmushi irin na sannu da zuwa ɗinan.
      Tamke fuska tai tana dubansa ta rausayar da kanta gefe tana fadin 
       "Shi mutum din bai san halin da ake shiga ba ne yake ƙin zuwa wurin mutane sai ya gama jamusu rai sannan zai zo ko?"
    Yadda tai masa maganar a shagwaɓe shima haka ya langabar da nasa kan gefe yana yin yadda ta mashi ya bata amsa da "Ayi hakuri domin Allah balaguro ce ta kamani kuma aiken na Mami ne zuwa wata kasar kinga fah har tsaraba nayi miki"
      Kyalkyalewa da dariya tai ganin yadda ya kai kaice yana kallonta kuma yana kwaikwayonta.
    "Inalillahi yau naga abin da ya girmi tunanina wai namiji da shagwaɓa kai amma fah tai maka kyau kamar wani babyn roba"