KUNCIN ZUCI

Kuncin zuci

by @bintuuu

Har Na'ima ta bar gidan bata daina murmushin ba wanda hakan ne yasa bata ma lura da motan da ta bi bayanta ba, ahanya bini bini zatayi murmushi ta dan jijjaga kai in ta tuna abunda Ahmad din ya fada mata, tasani wannan wani side dinsa ne da in ance ita kadai yake nunawa, zata yarda da hakan, but above all this, meyasa take qara sonsa despite duk abunda zai fada, meyasa irin maganganun nan da yake mata suke hautsina mata lissafi da zuciyarta ne madadin ta kallesu a wata fuska daban, sai tayi murmushi tana dan jijjaga kai bata daina kallon titi ba, har ta isa babban bankin zuciyarta bata daina annushuwa ba, a can nesa da bankin tayi parking saboda bata da cikekken permit na shiga ciki da motan nata, a lobby tayi tambaya aka kwatanta mata office din Mr Adekunle din ta wuce ta hau lift din da zai kaita floor dinda yake, isar ta nan ma ta samu ba ita kadai bane a line din and to her suprise sai ta samu wa'inda ke zaman jiran duk da suits ajikinsu har matan, ai atake taji kalli jikinta amma ga mamakinta sai taji secretary din ta kirata, da taje sai ta tambayeta tace "Are you Na'ima Yusuf Dabo?" ta amsa da "Yes" sai secretary din ta miqe ta wuce babban office din Mr adekunle din, bata dade ba ta fito tace Na'ima ta shiga, lallai qasar mu in kanada gata da wanda zai tsaya maka an wuce gurin, dan Na'ima acikin mintunan da basufi talatin ba ta gama magana da adekunle, shima dan kar ace bata je bane if not straight zata samu aikinta daman, haka ta fito ta wuce masu jiran shiga office din kiran Abba na shigowa wayanta, tambayanta yayi ya sukayi dashi Adekunle din saboda yanason ya kirashi, a hanyar ta na fita daga bankin ta masa bayanin komai sannan sukayi sallama, fitowanta daga gurin gaba daya ta hango Bilal a jikin motanta a tsaye alamun yana jiranta, sai batayi mamaki ba tunda har a England ma sai da samota balle qasar nan, dakewa tayi ta qarasa gurinsa sai ya cire shades din idonsa yana kallon ta yace "Nice car Na'ima" batace komai ba ta zagaya ta shiga driver's seat, kawai taga ya buge dayan side din ya shiga shima, ta juyo tana  kallonsa tace "Ka fita" sai ya rinqa kallonta yace "Na'ima we need to talk" juya kanta tayi tace "Talk then" sai ya kwantar da murya yace "Mu samu wani gurin, I'm hungry" bata ce komai ba ta tada motan suka bar bakin bank din, har suka isa Bilal sai kallonta yake, he still can't believe wannan wai Na'iman daya taba rayuwa da ita a baya ce, idanun Na'ima na kallon titi har suka isa bakin wani open restaurants tayi parking suka fito, kanta tsaye ta shige gurin yana biye da ita, sai da suka zauna a table waiter ta kawo abinci a Bilal din shi kadai dan Na'ima tace bazataci komai ba kuma har sannan taqi kallonsa, sai da yayi nisa da cin abincin ganin sunyi shiru ya ajiye spoon din yace "Na'ima ki dawo gidana, ki manta komai kamar yanda na manta ki dawo, na yafe miki abunda kikayi da Nasir sannan nima ki yafemin komai" Na'ima tayi wani murmushi me ciwo tana shafa tafin hannunta , sai ta dago kanta tana kallon idanun sa tace "Ban yafe maka ba, bazan taba yafe maka, bazan taba manta komai ba, duk abunda kayi min ban yafe ba Bilal" sai ta daga murya ta sake cewa "Ban yafe ba Bilal" kawai sai ga hawaye suna zubo mata, cikin bacin rai Bilal yace "You've hurt me too Na'ima, rashin bani kanki da kikayi kin dauka nima zan yafe ne, you're willing to give yourself to Nasir" sai ta dago idanunta da ke zubar hawayen tace "You know what? sai daga baya nayi tarin godiya ga ubangiji akan hakan, in sha Allah tun a duniya sai Allah ya sakamin akan duk cutarwan da kamin" rai a bace yace "Karki yafe din, f*ck you Na'ima, i said damn you, kuma kisani ko zaki mutu, duk inda zaki shiga sai kin koma gidana, ki gama maulan naki gurin wa'ennan pathetic people din, we are your blood Na'ima, nothing changes that" ji tayi zuciyarta na zafi, sai ya sake cewa "Wait...kina tunanin akwai me auren ki after all you've done Na'ima" sai tayi murmushi me ciwo tace "Zanyi aure nan ba da jimawa ba Bilal, zan auri wanda nakeso, zan auri wanda yake mutuqar sona wanda yasan daraja da kimata, let's see in kanada halin hana hakan" aikuwa be san lokacin da ya tunkudar da plates din gaban sa ba, cikin huci yace "Damn you, I'll kill him, and I'll kill you Na'ima" sai mutanen gurin suka fara kallonsu, da gudu waiter tazo tana fadin "Violence is not allowed here sir" Na'ima ta girgiza kai sanin Bilal bazai taba chanja wa ba, duk nutsuwar da zeyi ta bogi ce, sai ta miqe ta dauki jakanta ta barshi anan zaune yana kallonta, wani irin turirin kishinta ne yakejin ya taso masa a zuciya, awannan lokacin ji yake zai iya kashe duk wanda yayi gigin auren Na'ima, yana nan zaune sai ya tashi kamar an mintsinesa yayi saurin bin bayanta....

Rai abace Na'ima ta isa gida, shigan ta compound din da motanta sai taga na Ahmad a fake nan cikin parking lot din, da dan mamaki ta fito sai murmushi ya subuce mata tuna kashe wayan da tayi suna magana dazu, ahankali ta qarasa entrance din gidan tana gyara gyalenta, aikuwa sai ta samu Ahmad din tareda Mami har da Faruk a zaune suna hira, a sannu ta qarasa falon Mami tace "Har kin dawo Habibti" ta amsa da "Eh" tareda zama anan falon tana gyara gyalenta ganin Ahmad din, duk yasa ta fara tsarguwa in his presence kuma, Faruk yace "Sun miki interview din?" tace "Eh Yaya, Abba yace zasuyi magana tukunna" sai ya gyada kai, Mami na murmushi tace "Masha Allah Habibiti" Ahmad dai yana ta danna wayarsa bai dago kai ba har sannan, cikin sanyin murya Na'ima tace masa "Ina wuni" ya dan dago yace "Lafiya, ya aikin?" Mami tace "Interview taje yau din tukunna" sai yace "Ma Sha Allah" Na'ima sai danne murmushi takeyi ganin yanayinsa, sai Mami tace da Na'iman "Mutanenki sun tafi dubo site din ko jiran Yayan nasu basuyi ba" Faruk yayi dariya yace "Nima sai na bata musu lokaci kafin naje ai" Mami na murmushi tace "Kayi hakuri" sai ta sake kallon Na'ima tace "Ki debo abinci Habibti" tace "A'a Naqoshi" da haka Mami ta cigaba da magana da Faruk, Ahmad na saka baki jefi jefi, Na'ima dake zaune a falon ta rinqa kallon Tv tanajin kaifin idon Ahmad akanta bata juyo ba, wayanta dake jaka taji yayi qaran shigowan text amma bata kula ba, again ta sake jin wani ya sake shigowa sai tayi murmushi wanda se a dauka a tv taga abun dariya, Ahmad na shirin tura mata wani text din kira ya shigo wayansa sai ya miqe yana cewa "Mami bari na dau kira" tace "Toh son badamuwa" da haka ya fice daga falon, yana isa compound din gida ya daga tare da cewa "Talk Mazzy" daga dayan bangaren Mazzy yace "Man this job is huge, i should've said 20" sai Ahmad yace "That's not my answer, I've given you a week to finish everything" sai Mazzy yace "Boss, I'm trying everything i could, munyi binciken tun daga diddigi ne, six people fa" sai sannan yadan sauqo sanin Mazzy baya disappointing dinsa, gashi aikin mutum shida cikin sati yasan dole sai sun sha wahala, sai yace "Zan qara maka kwana biyu, max shine uku" Mazzy da daman ya iya Hausa sai yace "Mun hada details na komai, one package is here with us, but i had a tip up yesterday, saying that...the other package is there in Abuja" confusedly Ahmad yace "What? here in Abuja?" Mazzy yace "Yes, but i've sent my guys to wrapped it up, do you want it back here in Lagos or Abuja?" sai Ahmad yace "Bring the other one here, kasan inda zaka kai mun ai" Mazzy yace "All done Boss" da haka sukayi sallama sai Ahmad ya dago wayan yana kallo ransa na baci, so yananan Abuja, jikinsa ya basa Bilal ne, hakan na nufin ya hadu da Na'ima kenan, lallai kuwa lokaci yayi da tsayar da rainin nan, dan hakan raini ne a gurinsa..Yananan tsaye ya danna kira a dayan wayansa da ya bari a falon da zai fito, su Mami dake zaune a falon har sannan ta kalli wayan itada Faruk, sai tace "Habibti kaiwa Ahmad wayarsa a waje" asannu Na'ima ta miqe tareda daukan wayan ta nufi wajen, fitanta ta hango sa tsaye kamar me jiran fitowan nata, tana qarasowa gurinsa ta hau gyara gyalenta, Ahmad na kallonta ya danyi murmushi sai yace "Idanun ki nake kallo kadai fa" tace "Uhm Uhm, toh ka juya kanka" sai ya kauda kan yana dan dariya tareda cewa "Toh ki ban wayan" miqo masa tayi sai ya hada da hannunta wajen karba, dan jawotan da yayi sai ta taho gaba daya garesa har kanta na kusan bugewa da qirjinsa, sai ta ganta 'yar qarama a qasan sa ta kasa dago kanta sai Ahmad ya sunkuyo yana kallon ta nan ta damqe idanunta duka tana jin numfashinta na fita da sauri sauri, kallon lashes dinta ya tsaya yi baya ko kifta ido, sai ya rinqa kallon features din fuskanta admiringly har sannan bata bude idon ba, Jin kamar numfashinsa na sauqa a fuskanta yasata kai hannu qirjinsa da nufin ta turasa baya, amma sai ta samu kanta da barin tafin hannun nata akan qirjinsa dalilin jin bugun zuciyarsa da tayi a hannun nata sai  ta bude idonta ya fada cikin nasa yana kallonta har sannan, saurin kauda kanta tayi jin idanunsa na mata kaifi dayawa tayi gyaran murya da dan qarfi, murmushi Ahmad yayi yace "Ki juyo in kalli idon naki ko in kalli inda bakyaso" da sauri ta juyo tace "Nidai ka rufe idonka please" dan dariya ya fara qasa qasa, sai ya duqa kamar ze mata rada kawai sukaji an banko qofar dake jikin gate din gidan, Bilal ya shigo cikin diri yace "Na'imaaaaa" da sauri suka juya itada Ahmad suna kallonsa yana tahowa kamar wani mahaukaci, Ahmad na kallonsa kansa na ringing "So the package is right here in front of me" aikuwa da sauri Na'ima ta fincike hannunta daga na Ahmad din ta nufi Bilal, sai yabi bayanta da sauri shima, da sauri ta taho tana fadin "Bilal stop" sai yace "I'll kill him, so this is him" tana isowa gabansa ya hankadata da karfi kamar yanda ya saba sai tayi baya ta fada jikin Ahmad daya tarota da sauri ya miqar da ita, Ahmad beyi wata wata ya sauqewa Bilal naushi a fuska, kafin ya farfado ya sake qara masa wani yana huci, nan ma yasa kafa ya debeshi sai ga Bilal a qasa shima tiim, Na'ima na kuka ta fara jan rigan Ahmad da ya duqa yana sauqewa Bilal duka ta ko ina kamar yasamu punching bag, Bilal na karban naushi yana fadin "I'll kill you, wallahi yau ko ni ko kai" Ahmad dake huci yace "Sai dai niiii" Na'ima na ihu ta sake Ahmad din ta nufi cikin gida da gudu tana fadin "Mamiiii, Mamiii" sai sannan maigadin ya dawo gidan shima da gudu ya nufi gurinsu ganin Ahmad na dukan Bilal kamar ba mutum ba, da gudu su Mami suka fito da Faruk, Mami na fadin "Na shiga uku, Ahmad ka dagashi zaka kasheshi" Faruk dake jan Ahmad din baya yace "Ahmad meye haka wai" dakyar maigadi da Faruk din suka rabasu, Bilal na kwance hanci sai jini da baki, da Ahmad ya miqe yana huci yace "Dan uw*rka a gabana zaka taba ta, waye baban ka ma dan bantan ub*nka" sai Bilal ya miqe dakyar Maigadin na riqesa yace "Ka shammace ni ne amma duk ranan da mukayi gamo na biyu sai na kasheka" Ahmad yayi murmushi Faruk na riqesa shima yace "Zaka maimaita maganan nan a gamuwata da kai next time, sai ka maimaita wallahi, yanzu ma ban barka ba" cikin tsawa Mami tace "Bilal Get out before i call the police" sai Bilal yayi kururuwa "Babu inda zanje kun riqemin mata ta" Ahmad yace "Sai kayi claiming dinta yanzu ma in ka isa" kawai Bilal yayi murmushi yace "You're late... you're late motherfucker, kaganta nan" ya nuna Na'ima dake tsaye gefe tana kuka, yace "I've touched every core of her, you hear me?" "I've f*cked every inches of her" Faruk ne ya dauke Bilal da mari wannan karon, cikin ihu Mami tace "Bilal ka fitaaaa" shi Ahmad ma daskarewa yayi yana kallon Bilal din, ji yayi komai na jikinsa ya daina aiki na wasu daqiqu, Faruk ya sake marin Bilal din tareda hankadasa baya yace "Durun uwarka, Durun Uwarka nace" Bilal na dariya yana kallon yanda jijiyoyin kan Ahmad suka tashi, ji yayi he has won this fight, yasani ya daki Ahmad din a zuciya ba kadan ba, maigadi na turasa waje yana tafiya da baya da baya ya sake cewa "Tell him Na'ima, tell him how we do it every single night" Na'ima ta damqe idanunta tana kuka da qarfi, sai a sannan Ahmad ya zaburo kansa Mami ta riqe rigansa tana fadin "Don't let him get into your head, Ahmaaaad" da sauri Bilal ya juya ya fice daga gidan, aikuwa sai ga hawaye sun kawo idon Ahmad ya daga murya da qarfi yace "You'll scream my name while i slaughter you, I'll slaughter you like the pig you are" Faruk ya dafa bayan Ahmad kawai dan shima ya gagara magana, qoqarin tafiya Ahmad din ya fara Mami tace "Kar kaje Ahmad, banason fadan nan" sai yace "Gida zan tafi Mami" Na'ima na kuka a gefensa yana jinta amma yanda zuciyarsa ke zafi sai ya kasa juyawa gurinta, Mami tace "Muje ciki Ahmad, you're not yourself, kar ka bisa kisa ya biyo baya" ahankali ya sake cewa "Mami i need to go" sai tace "Faruk ka tuqasa" sannan ta juya ta riqo Na'ima dake hawaye har zuwa sannan tarinqa shafa bayanta, har suka tada motan suka nufi gate Ahmad na jingine da kansa a kan seat yaqi kallon inda Na'ima take, Na'ima kallonsa tana kuka suka fice tanajin zuciyarta na breaking into pieces... Da haka Mami ta jata suka shiga cikin gidan tana bata hakuri, har dakinta ta kaita suka zauna bakin gado, kuka sosai Na'ima takeyi tanajin zafi a nata zuciyar dan ji take kamar Bilal din yaci galaban rabata da Ahmad din, Mami ta rungumeta tana cewa "He'll pay for everything, shari'an da mukace zamuyi dasu din za'ayi" batace komai ba ta cigaba da kuka....Dakyar Mami ta samu tayi shiru, tana nan kwance a gadon taja mata blanket ta rage qarfin Ac din sannan ta fita, dago kai Na'ima tayi hawaye na kawowa idonta dan ba bacci tayi ba daman, har yamma tana dakin Mami na zuwa dubata akai akai, dasu Nafisa suka dawo tana jiyo hayaniyar su a falon amma ta kasa tashi bayan wasu lokuta Nafisa ta shigo dakin tana fadin "Bobo bakida lafiya ne" taja bargon tana kallon Na'iman, aikuwa nan taji jikinta yayi zafi sai ta fita kiran Mami, kiran likita akayi da wannan yammacin yazo ya mata alluran zazzabin da ya rufeta gashi bini bini sai hawaye, da dare Nafisa na zaune gefenta bayan ta kawo mata abinci, Abu kuma yana zaune kan stool din mirror, sai Nafisan tace "Wai daga dawowan ki daga bankin ne zazzabin ya rufeki kenan" Na'ima ta gyada kai ahankali tace "Yayi sauqi ai na daina jin komai ma Nafee" kafin Nafisan tayi magana Abba ya shigo dakin tareda Mami da Faruk, dan zuwa sannan Mami sun fada masa komai da ya farun, yayi ta fada akan meyasa basu kira polisawa ba anriqe masa yaron kafin yazo, sai Mami tace "Har da Ahmad din za'a kama kasani, which will link to su Baba su sani, and yarinyar nan har yau mun boye wa kowa wacece ita gudun maganganun cikin family", da wannan Abba ya fito ganin Na'iman a daki, yana tsaye a dakin Na'ima ta fara qoqarin sauqowa daga gadon yace "Yi zaman ki daughter, Allah ya baki lafiya" ta amsa da Amin kanta a qasa, da Abba ya gama mata sannu sai ya fita ya barsu Mami, ta qaraso gurin Na'iman tace "Daughter ya jikin" ta amsa "Na warke Mami" sai duk yan dakin sukayi murmushi, Mami ta shafa kanta tace "Haka akeso, Good night" Faruk dake kallonta yace "Sannu Na'ima" sai tayi masa murmushin dole, da haka duk suka fice daga dakin aka barta da Nafisa dake gyara kwanciya a gadon dan anan zata kwana, cikin dare Na'ima ta farka ta jawo wayanta tana duba wa amma bataga miscalls din Ahmad ba kamar yanda ya sabar mata, zuciyarta na nauyi ta danna kira a line dinsa sai taji baya tafi, the line is unavailable, hawaye taji ya kawo idonta kawai ta kwanta tareda jan blanket din har kanta....
Zuwa safiya Na'ima ta warware sai dai nauyin da takeji kawai a zuciya, like every morning haka sukayi breakfast dinsu dan ranan kaman hadin baki duk an tashi tare a gidan, suna hira har aka gama breakfast din su Na'ima suka tattare gurin tsaf...Har la'asar su Na'ima na falon Mami, tana cikin hira da Nafee sai taga tana danna waya tare da dan ware ido, da sauri Nafisan ta dago kai tace "Bobo kinji wai Yaya Ahmad ya fadi da bike jiya?" sai da zuciyan Na'ima ya buga, ahankali tace "Wa ya fada miki?" Nafisa tace "Yanzu Husna ke fadamin, wai jiya Yaya Faruk ya maidashi gida hannunsa duk jini" jin haka yasa Na'ima taji nutsuwa sanin jini menene a hannunsa nasa ba faduwan bane, sai Nafisa tace "Bari muje dubasa Bobo" ahankali  tace "Allah ya basa lafiya" da haka tayi shiru amma har zuciyanta itama tasan tanason ganinsa, zuciyarta na mata wani nauyin da in ba ganinsa tayi ba tasan bazata daina ji hakan ba, Mami ce ta shigo falon sai Nafisa ta juya ta kalleta tace "Mami munason zuwa duba Yaya Ahmad wai jiya ya fadi da bike" dan stiff Mami tayi ta kalli Na'ima da kanta ke duqe, sai tace "Ku dawo da wuri Baby, lantana batanan zakuyi girkin dare" cikin sanyi Na'ima tace "Zan zauna nayi Mami" sai tace "No Habibti kije ku dubosan" da haka ta nufi cikin dakinta yin uzurin da ta shigo yi, su Abu daman basa gidan ranan sun fice gari shida Al'ameen, da motan Nafisa sukaje gidan, Nafisa nata yiwa Na'iman hira tana amsa mata akai akai dan tasan in tayi shiru yanzu zata shiga damuwa ta fara tambayanta, ita kuma ganin su Mami basu fada musu ba yasa tayi shiru itama, isarsu gidan suka fara zuwa gaisheda Mamma sai suka samu tana aikin abinci a kitchen tareda Husna da Ummi last born din dakinsu Ahmad, a kitchen din suka fara gaisheta tace bakomai su zauna a falo tana zuwa, sai da ta fito suka gaisa kan Na'ima na duqe tayi shiru sai Nafisa tace "Ya jikin Yaya" Mamma tace "Wannan har ya fita ma da safe, kaman dai ya dawo dazu yana side dinsa" Husna ta fito tana fadin "Muje ku rakani zan kai masa abinci" sai Nafisa ta fara miqewa Na'ima na zaune bata tashin ba, ganin hakan yasa Mamma tace "Daughter kije ku dubosan" Na'ima ta gyada kai sannan ta miqe ahankali suka fita, da suka fito compound din zasuje side dinsa Husna tace "Baba fa sai da ya hanasa fita yau wai ko akwai internal injuries tun da babu ciwon komai a jikinsa, amma inaga Baba yana fita Yaya ya bisa a baya" Nafisa tace "Ai dai mayyar can bataji labari bako" Husna ta amsa da "Anty tasani ai to dole su salma zasu sani, amma kaman batazo ba, dan banganta acikin gida ba" Na'ima na jinsu batace komai ba har suka qarasa side din nasa suka shiga falon tana baya, aikuwa shigansu suka ga Laila a agabansa tana zuba masa abincin da takawo ga Adam ma zaune a falon da wani friend dinsu daya shima, dan stiff sukayi dukansu a bakin qofan, Na'ima ta sauqar da kanta qasa tana dana sanin zuwan ma, Ahmad na dagowan kai ita ya fara gani, sai ya kasa dauke idonsa akanta har suka shigo suka zauna, Husna ta ajiye masa abincin tana fadin "Yaya gashi Mamma tace kaci wannan saboda ta dafashi yanda kakeson" sai ya gyada kai ya sake juyawa yana kallon Na'ima dake kallon gefe ma, zuciyarta quna taji nayi kamar wuta a lokacin, bayan sun gaisa da Adam sai ta dan kallesa idonta ya fada cikin nasa, atake ta sake dauke idonta, bai dena kallonta ba Laila ta zauna a gefensa tana fadin "Sannunku da zuwa Nafee" Nafisa na kallonta da mamakin yanda take musu abu kamar wasu baqi, sai bata kulata ba ta kalli Yayan nasu tace "Sannu Yaya, ina wuni" yace "Lafiya Nafisa" shiru tayi bata amsa ba ta juya gurin Na'ima tace "Muje sis" sai ta miqe Husna tace "Har zaku tafi kuma" Adam yace "Nafee wannan gaisuwa taqu miqe ce" tana murmushi batace komai ba, miqewa Na'ima tayi itama, sai sannan ma ta tuna batace masa ya jikin ba amma haka tabi bayan Nafisa suka fice daga falon, ahanyarsu ta komawa sai Nafisa batace komai ba ganin sanyin da Na'iman tayi, da sukaje gidan sai suka samu Mami a falo tana zaune ita kadai tana waya, zama sukayi gurinta sai da ta gama tace "Har kun dubosan" Nafisa ta gyada kai kawai, sai Mami tace "Abbanku yadawo shima yana falonsa" sai Nafisa ta fara qoqarin miqewa tana cewa "Jiyan ban masa maganan site din bama Mami" sai Mami ta amsa da "Yanzu dai kuyi abincin tukunna akwai anjima ai" Na'ima tace "Zanyi Mami, me za'a girka" ta amsa da "Ki duba dai, Abbanku na masa, naku kadai zaku girka" Na'ima ta gyada kai sannan tace da Nafisan "Ki je gun Abban zanyi" sai Nafisa ta miqe tana fadin "Yauwa Anty Na'ima naa" suna murmushi itada Mami suka bita da kallo ta shige bangaren Abba, sai Mami ta kalleta tace "Are you okay Na'ima? ki fadamin meyake damunki kinji" hawaye taji yana zuwa idonta sai ta danne tace "Babu komai Mami" sai Mami tace "Karki sa komai aranki kinji daughter, hakan bazai sake faruwa ba i assure you, jiyan ma Abbanku yasa a binciko masa shi duk inda yake" ta gyada kai ahankali sannan Mami tace "How's Ahmad?" cikin sanyi tace "Yana lafiya" sai ta gyada kai tana kallon Na'iman, miqewa Na'iman tayi ta nufi kitchen zatayi abincin sai Mamin ta miqe itama ta nufi falon Abban, da tashiga kitchen din sai ta maida hankali tana ta aikin nata har ta gama bata daina jin zafin ganin Laila gurin Ahmad ba, like how is she feeling this way ne ma? Bilal da ya kasance mijinta abaya ma da ya kawo karuwarsa gidan bataji komai ba sai wannan da ba mijin ta ba, kuma wadda ta gansu taren ma 'yaruwarsa, sai ta jefar da soson da take wanke plate din hannunta ta daga kanta tana kallon sama da nufin ta hana hawayen idonta fitowa, ji tayi an bude kofan kitchen din amma bata juya ba, sai kuma tayi stiff jin turarensa, ai da sauri ta juya tana kallonsa yana tsaye jikin qofan bayan ya rufe shima yana kallonta cikin ido....


Follow my account please