A CIKIN IDO...

Shafi Na 1

by @sanazty

A CIKIN IDO...

Ake tsawurya

Wattpad @SaNazdeeyah_

Arewapen@sanazty

Facebook @Habibtyn Habibi

Heart touching love story🥰

KARAMCI WRITERS ASSOCIATION

[karamci tushen mu'amula tagari]

*Bismillahir rahamanir rahim, gani tafe da wani ƙayataccen labari fatan zai amfane mu baki ɗaya.*

11 May 2022

Shafi Na ÆŠaya

_________Da gudu ta faɗo ɗakin tana haki. Gefen tsohuwar katifarsu ta zauna, tare da dafe ƙirjinta da hannu, tana maida numfashi. Yanayin hakin da take, yayi kama da wadda tayi gudu na ceton rai.

"Maheer!" Ta furta sunan a fili, cikin wata kasalalliyar murya.

Tashi tsaye tayi, tare da cire dogon hijab ɗinta kalar ƙasa (brown).

Kallo ɗaya zakayi mata kasan cewa ita ɗin Hausa-Fulani ce, fatarta na da ɗan duhu kaɗan(Chocolate) bata da jiki, kuma bata da rama, zamu iya ajjeta a tsaka-tsakiya, tana da matsakaicin tsayi, doguwar fuska gareta mai ɗauke da ƙaramin baki, manyan idanu sai dai hancinta ba wani dogo bane, amma hakan bai saka yayi mata muni ba, tana da kyau dai-dai gwargwado. Abu ɗaya ne ke ɗaukar hankalin mutane a kanta, wato wannan dara-daran idanun nata da shape ɗinsu yake kamar na mage, wanda har ƙwayar idanun nata ma brown ne, sai kuma kwantaccen gashin dake goshinta da gefen kunnuwanta.

"Kin dawo kenan?" Taji anyi maganar daga bayanta, da sauri ta juya ta kalli inda sautin ya fito.

"Na dawo." Ta faÉ—a tana lumshe idanu, bakinta É—auke da murmushi.

Rahina, wadda ita ce ta shigo ɗakin, ƙarasawa gaban Amal tayi, tare da faɗin "An dace?"

Murmushi Amal ta sakeyi, sannan ta ce "Kamar kullum dai."

Itama Rahina tayi murmushi ta ce "Naji daÉ—in hakan." Sai kuma tayi shiru, ta É—anyi jim.

"Lafiya kuwa?" Amal ta tambaya, fuskarta É—auke da damuwa.

"Abu ne mai matuƙar wahala a samu zaman lafiya a gidan nan, ke kin san haka."

Ajiyar zuciya Amal ta sauke, sannan ta ce "Kada mu saka damuwa tayi mana yawa a cikin ranmu, muma muzo mu kwanta jinya, gara mu dage da addu'a da kuma nemowa kanmu farin ciki, ko dan lafiyar mahaifiyarmu"

"Adda yaushe ne zamu samu? Ina tunanin da ace muma muna da yayye maza a ɗakinmu, to da mun samu sassauci a gidan nan" Kallonta ta mayar kan mahaifiyarsu dake kwance kan ƙaramin gadon katakon da babu katifar arziƙi a kanshi, idanunta a rufe suke, alamun bacci take. Kallonta ta mayar kan Amal dake tsaye tana jiran abinda za ta faɗa.

"Na san muna iya ƙoƙarinmu dan ganin mun rufawa kanmu asiri, kuma mun samawa mahaifiyarmu lafiya, amma kuma abinda Baba yakeyi na san da ace muna da namiji a ɗakin nan, da mun samu rangwame, Baba zai iya sayar da ko gona ɗaya ce a kai Mama asibiti, amma saboda bamu da wani gata da ƴanci yayi burus da lamarin, shekara shidda tana kwance a haka." Rahina ta ƙarasa maganar tana kuka.

Amal kamo hannunta tayi, sannan ta zaunar da ita kan tsohuwar katifarsu, wadda da kaÉ—an tafi tabarma.

"Rahina, duk abinda kika ga ya samu bawa, to muƙaddari ne daga Allah, ni ina fatan wannan ciwo na Mama, zai zama kaffara a gareta, kuma ina da yaƙinin zata samu lafiya nan bada daɗewa ba, insha Allahu."

Hannu ta saka tana sharewa Rahina hawaye, tare da faɗin "Zamu cigaba da tara kuɗin insha Allah, a hankali har sai mun kai gejin kuɗin da aka buƙata"

"Adda miliyan É—aya da rabi ba budu É—ari bace, shekara biyu kenan muna tari amma har yau kuÉ—in da muka tara basuyi dubu É—ari biyu ba, saboda mu muke ciyar da kanmu, muyiwa kanmu komai. Da gidan haya, da gidan nan banga bambanci ba"

"Rahina ki sassauta zuciyarki, kada ki damu dan Allah, ni na san ana yi mana wannan abin ne saboda ni, dalilina aka tilastawa mahaifina ya auri mahaifiyata, shiyasa baya sonta, baya sona, kuma kema da kike Æ´ar sunnah abin ya shafeki a dalilinmu."

Sai a lokacin Amal ta fashe da kuka, ta saka dogayen hannayenta ta rufe fuska.

Hannu Rahina ta saka ta rungumi Æ´ar uwarta tare da faÉ—in "Dan Allah ki daina faÉ—in haka, ki daina magana akan abinda ya riga ya wuce"

"Abu ne da kowa ya sani, shekarata ashirin da uku a duniya, amma har yanzu bani da tsayayyen masoyi, duk wanda yazo da niyyar aurena sai a tsegunta masa, koda baiyi niyyar rabuwa dani ba, iyayensa zasu tilasta masa, saboda da uba ake ado ni kuma an haifeni ba ta hanyar aure ba."

Ta ƙarasa maganar tana fashewa da kukanta a fili.

"Adda, kina da uba, Baba shine mahaifinki kuma duniya ta shaida hakan, ya yaudari Mama ya saka mata magani a lemo tasha tayi bacci yayi mata fyaɗe, dake da Mama babu mai laifi a cikinku, Allah yayi sai kinzo duniya domin a labarin da Mama ta bamu, ta faɗa mana babu yadda Baba baiyi ba kan zubar da cikin, amma yaƙi fita, saboda Allah ya ƙaddara dole sai kin shaƙi numfashin duniya, kuma zaki zama abin kwatance a gaba, ko yanzu ƴan unguwarnan suna kwatance dake, saboda irin haƙuri da tarbiyyar da kike da ita."

Amal ta goge sauran hawayen dake fuskarta sannan ta ce "Ina da damuwa sosai Rahina, amma ina ɓoye hakan ne saboda in faranta ranki dana Mama, idan har ban kawo farin ciki a cikin rayuwarku ba, to rayuwata bata da amfani, Mama tayi ƙoƙari sosai a kanmu kafin wannan rashin lafiyar ta sameta, shiyasa nima zan jajirce dan ganin na nema mata lafiya"

"Ki duba ki gani Adda, sau É—aya ake bamu abinci a gidannan, sauran sai dai mu nema fa"

"Rahina kada ki damu da wannan, kin manta cewa akwai wanda sai suyi kwana biyu basu saka komai a bakinsu ba, mu kam ai sai dai muyi godiya ga Allah, kin ga, ina so ki kwantar da hankalinki kinji, nima kinga na kwantar da nawa kuma insha Allah Mama za ta samu lafiya"

"Amma Adda meyasa baki faÉ—awa Maheer gaskiya ba?"

"Rahina ba zai yuwu na É—aura masa nauyi ba, kuma ai ba saurayina bane, he's just a friend"

"Amma ai zai iya, tunda suna da wadata"

"Hmmm har yanzu baki san wacece mahaifiyar Maheer ba, amma ni da nake tare dashi ai na sani."

"Na san masifaffiya ce mana, amma ai na san zai iya taimakawa"

"Abin kunya ne in faɗawa Maheer ya taimaka mana, bayan muna da dangi ta ko wane ɓangare, su sun kasa taimakawa sai bare?"

"A lokuta da dama bare sun fi ƴan uwa, lafiyar Mama tafi mana komai a halin yanzu, ki jarraba tambayarsa, ai ba laifi bane dan kinyi roƙo akan lafiyar Mama"

"Hakane, to zan jarraba, dama ya ce min gobe da yamma zan masa rakiya gidan budurwarsa inga yadda take idan tayi ko batayi ba."

"Saura kuma ki ce batayi ba, dan na san ƙaramin aikinki ne"

Murmushi Amal tayi lokacin tana cire socks ɗin ƙafarta. Sai da ta cire ta saka a gefe sannan ta ce "Idan tayi zan faɗi gaskiya ai"

"Wallahi na san halinki Adda, ni fa ina ganin ya kamata ki haƙura da Maheer..."

"In haƙura fa?" Amal tayi saurin tarar numfashinta.

"Eh mana, tunda baya sonki, sai dai yayi ta faɗa wa soyayyar wasu. Ke kuma kina rabawa, a ƙawa ya ɗauke ki, kawai na lura yana baki matsayine ta yadda duk wadda kika ce kar ya yi soyayya da ita to yana haƙura, amma a zahirin gaskiya baya sonki."

Ajiyar zuciya Amal ta sauke sannan ta ce "Ina son Maheer sosai, tun muna yara mun taso tare, tun suna talakawa har suka zama masu kuÉ—i, amma nima na daÉ—e da gane cewa Maheer baya sona, ni ce nake haukan son shi, nayi tunanin idan ina rabashi da duk macen da yake so, to zai gane feelings É—ina a kanshi, amma sam ya kasa ganewa"

"Ba zai taɓa ganewa ba, tunda baya sonki, a matsayin friend ya ke kallonki, dan haka kawai ki haƙura, Allah ya baki kema wanda zai soki da gaskiya"

"Idan Maheer yayi aure, na san shikenan zai fara mantawa dani."

"Dole kema ki ɗaga ƙafa, domin kin san mata da kishi, da kuma zargi"

"Shikenan, na ɗauki shawararki, amma ni na san ina son Maheer, kuma har abada ba zan daina sonshi ba, amma kuma dole zan haƙura dashi tunda ba tani yake ba, kuma mahaifiyarsa ta damu yayi aure."

Girgiza kai kawai Rahina tayi, cike da tausayawa, sannan ta ce "Na san da ciwo, ni nayi tunanin ma an dace, dan naga kin shigo cikin fara'a, am....." Bata ƙarasa maganar ba ta ga Baba ya buɗe labulen ɗakin ya shigo.

Dukkansu suka durƙusa har ƙasa gami da faɗin "Barka da shigowa Baba."

Kallonsu kawai yake, kafin ya ce "Ke Amal waye wan can wanda ya ajje ki a mota?"

Kanta a ƙasa ta ce "Maheer ne Baba"

"Wannan Maheer É—in dai dana sani É—an gidan Alhaji Muhammad Salis?"

"Eh shine"

"To mene tsakaninku? Dan na lura motarsa na yawan zuwa layin nan"

"Ba komai, ya ganni a hanya ne sai ya rage min hanya, kuma dama mun san juna tun muna yara"

"Wane irin sani?"

Kallon juna sukayi ita da Rahina sannan ta ce "Ina nufin munyi wasa tare"

"Yanzu ke ko kunyar faÉ—a bakya yi, shekara ashirin da biyar amma baki da mashinshini, ki kalli wancan saurayin amma wai sa'anki ne"

"A'a Baba, ko da muna yara ai ya girmeni"

"Rufa min baki shashasha kawai, ga ƙanwarki nan shekara uku kika bata amma har an saka mata rana kina nan zaune, ko dan ai kya zauna ki cigaba da jinyar uwarki." Yana kaiwa nan ya juya ya bar ɗakin.

Kuka Amal ta fashe dashi, tare da kai kanta ƙasa. Rahina ta riƙota tana mai bata haƙuri.

******

Magana yake mata amma sam taƙi kulashi. Ta wuce bedroom ɗinta kai tsaye, ranta a matuƙar ɓace. Tana shiga ta haye gado tare da yin rub-da-ciki.

Shigowa É—akin ya yi, ya zauna daga gefen inda take a kwance ya ce "Please darling, ki tashi muyi magana"

"Ni ba zan tashi ba, na gaji da abubuwan da danginka suke min, musamman ƙannenka, gaba ɗaya sun rainani basu ganin girmana, Yayyanka kuwa duk sun tsaneni, haba dan Allah ai bani nayi kaina ba"

"Kukan da kike, ba shine mafita ba Jidda"

Sai lokacin ta tashi hawaye kwance a fuskarta ta ce "To ya kake so nayi, munje asibiti fa, kuma ga abinda doctor ya ce, amma kai sam kaƙi yarda."

"Idan na yarda shikenan kin daina fushin?"

Kai ta gyaÉ—a alamar eh.

"To na amince, amma dai ina da sharaÉ—i."

Cikin farin ciki ta ce "Na yarda da ko ma wane sharaÉ—i ne" Ta saka hannu tana goge hawayen fuskarta.

"Ina so ya zama sirri tsakanin ni dake, bana so wani daga cikin danginki ko nawa su sani, saboda ina sonki, bana son wata matsala ta shigo wadda har za ta saka mu rabu."

Rungumeshi tayi, tare dayi masa peck a kumatu "Ba wanda zai sani a cikinsu."

Kanta ya shafa yana murmushi tare da faÉ—in "Sarkin rigima."

******

"Zo nan, munafuka." Umma Hadiza tayi maganar tana yafuto Amal da hannu.

Juyawa Amal tayi ta ƙarasa inda take sannan ta ce "Gani Umma"

Hannu ta saka ta kai mata ranƙwashi, wanda har tsakar kanta taji shi.

"Kece mai ƙarar da ruwan gidan nan bacin ba ɗebowa kike ba, yara tun safe suke fita da mazubai su samo mana ruwa, sai ke da kikayi kwantai a gida zaki ƙarar mana"

Danne zuciyarta tayi sannan ta ce "Umma wallahi É—an kaÉ—an na É—iba, ko rabin buta bai kai ba"

Caraf Baba Baraka wadda itace uwargida a gidan, tayi saurin amshewa da faɗin "Ai ƙarya muke miki ko, ke kam yadda aka haifeki ba ta hanya mai kyau ba, haka kike babu hali mai kyau, gaki da kyau a fuska amma sai zuciyar fir'auna a ƙirji"

Umma Hadiza ta ƙara da faɗin "Dalla ɓace min da gani kar in yi zuciya in hauki da duka, kamar Allah ne ya aikoni."

Amal tana hawaye ta miƙe, ta juya za ta tafi, ƙannenta dake zaune gefe Badi'a da Karimatu suka ƙyalƙyale da dariya.

Juyowa tayi ta kallesu. Umma Hadiza ta ce "Mene kike kallonsu, ai dole suyi dariya, kiyi zuciya ki fiddo miji a gobe."

Bata ce komai ba ta wuce ɗakinsu. Tana shiga taga Rahina tsaye bakin ƙofa.

"Na san kinji komai" Ta furta lokacin da kuka ya kubce mata.

"Adda kiyi haƙuri, wata rana sai labari"

Kasa cewa komai tayi, ta ƙarasa gadon da Mamansu ke kwance. Idanunta a buɗe suke, hawaye na bin gefen idanun Mama.

Zama Amal tayi sannan ta ce "Mama zan jure koma mene ne, zan zauna dake har lokacin da za ki samu lafiya, dama ni na san ba a halicceni dan nayi aure ba, na fidda rai da yin aure."

Hawayenta kawai ta danne, ta kuma saka hannu ta goge wanda ta fara, sannan ta goge na fuskar Mama, tana mai faÉ—in "Ba komai, ni na san babu wani abu dake É—orewa, a wannan duniyar."

Sai lokacin Rahina ta ƙaraso gaban gadon, sannan ta ce "Duk abinda kayi kaima sai an maka, sai sunzo suna baki haƙurin abinda suke miki"

"Ki barsu kawai, ni nafi ganin laifin Baba, domin da ya mayarmu Æ´aÆ´a da duk haka bata faru damu ba."

Haka suka gama jimaminsu, tare da addu'ar Allah ya dai-daita tsakaninsu da mahaifinsu.

Washe Gari

09:30am

Rahina na zaune kan gado ta tanƙwashe ƙafafuwanta, hannunta ɗauke da cup wanda pap ke ciki tana bawa Mama a hankali.

Wayar Amal, ƙirar R.K tana daga gefen Rahina, wayar ta hau ruri. Maheer ta ga sunan akan screen, dan haka ta ɗauka tare da karawa a kunne. Bata kai ga yin magana ba taji ya ce "Ƴammata da yunwa na tashi, kuma na rasa me zanci, ki faɗa min abu mai daɗi da zan iya sakawa a cikina."

"Yaya Maheer ina kwana? Am... Adda ta shiga wanka"

Daga can ɓangaren a kunyace ya ce "Rahina ya kuka tashi?" "Lafiya lau" "Ya jikin Mama, hope dai da sauƙi" "Alhamdulillah da sauƙi. Yauwa ga Adda ta shigo ma" Rahina ta faɗa tana miƙewa daga gadon.

Amal da take daga ita sai ɗaurin ƙirji, ta tsaya da mamaki tana faɗin "Waye wai?" "To Yaya Maheer ne" Rahina ta faɗa tana miƙa mata wayar.

Hijab ta É—auka ta zura a kanta sannan ta fita daga É—akin wayar manne a kunnenta. "Beauty ya kake?" Ta furta lokacin da ta fita daga É—akin. "Beautyn-beauty gani nan dai sai a hankali"

"Lafiya dai ko?" "Eh to! Amma kafin nan, irinmu guda nawa ne dake har kike tambayar waye ke kira?" "Aini dama bana tsammanin kiran kowa sai naka" "Beautyn-beauty faɗa min gaskiya ko dai na ƙarfen ne?" Murmushi tayi sannan ta ce "Na katakon dai" Dariya yayi, har ta jiyo sautin dariyar tashi, sai kuma ta ce "Yanzu dai ya ka tashi? Ina fatan ka ci abinci ko?" "Banci komai ba, ke na kira ki faɗa min abinda zanci" Shafa cikinta tayi, wanda yake mata ƙugin yunwa, sannan ta ce "Kasha tea ko coffee na san kana son su sosai, sai ka haɗa da irish ko? Ina fatan ya yi" "Yayi, so zan zo na ɗaukeki ki rakani, ki bani 1hour zan shirya nazo" Bai ma jira abinda za ta faɗa ba ya katse kiran.

Murmushi tayi, sannan ta juya ta koma ciki. Sai da ta ƙarasa shirinta tsaf sannan ta kalli Rahina ta ce "Ni fa fita zan yi"

"Zuwa ina kuma?"

"Zan raka Maheer unguwa"

"Amma da safiyar nan"

"Zai je cin abinci, so shine ya ce na raka shi, kin ga na sanu chance na samo mana abinda zamuyi kalaci"

"Eh kuma fa haka ne"

Dukkansu murmushi sukayi.

*****

"Ya ce baya son kowa ya sani shiyasa ma na ƙi faɗawa kowa, kawai kika faɗo min, kuma na san lokacin da nayi aiki dake gaskiya naji daɗi sosai, kuma bayan kin bar aiki a gidan nan yanzu haka wadda kika samo min ina jin daɗinta. Murja ina cikin matsi na dangin miji, shekara bakwai da aurenmu fa"

"Hakane Hajiya dama dole za ki fuskanci wannan ƙalubalen, amma ni gani nake a cikin garin nan ba lallai a samu wadda za ta iya wannan kasadar ba"

"Na san da haka, amma ai dama wanda suke cikin matsala ta kuɗi su za a samo, kin ga ta haka ne idan mun saka musu maƙudan kuɗi ba za su musa ba"

Shiru Murja tayi, na É—an wani lokaci sannan ta ce "Eh to, akwai wanda suke cikin matsala ta neman kuÉ—i, amma dai idan nayi magana da ita zan nemeki"

"Murja ki sanar da koma wacece, aikin da za tayi mana zamu É—auki miliyan biyar mu bata, daga zarar anyi inserting zamu bata miliyan uku idan ta haihu mu cike mata miliyan biyu kin ga ya yi making 5million"

"Miliyan biyar fa hajiya! Ai duk mai hankali ba zai ƙi tayinki ba, ba dan dai kin ce sirri bane, da tuni an cigita miki a cikin dangi"

"Duk wanda za ki faÉ—awa ya zama mutum ne mai sirri, kuma kema da kika yi ai ba zamu barki haka ba."

Murmushi tayi sannan ta ce "Na miki alƙawari ina tashi daga nan gidansu yarinyar nayi, duk yadda mukayi da ita za ki ji"

"To shikenan sai naji ki."

Mu haÉ—u a next page