DA KAMAR WUYA...!

4

by @hauwaausmanjiddarh

'''DA KAMAR WUYA...!'''

*HAUWA A USMAN*
~JIDDARH~

'''Wattpad:- HauwaAUsmanjiddarh'''

*ArewaBooks:- Hauwaausmanjiddarh*

#500 Only
Hauwa Auwal Usman
Gt Bank
0153259310
***, katin MTN banda VTU saboda WhatsApp kawai nake yi da Number, so idan kikayi transfer kati kai tsaye cikin layin ko kikayi VTU kinyi asara domin ba Jiddarh kika turawa ba, ki siyi katin MTN ki turo min numbobinshi ko hotonshi.

4️⃣

Papa yaso yaje Police Station amma saboda rashin tsaron dake damun k'asar yasashi yanke shawarar nufar office d'in shugaban 'yan sanda na k'asa baki d'aya,
wayarshi ya ciro a aljihu yayi dialing number bugun farko yayi picking yana fad'in " Allah ya taimaki masu k'asa...

"Wake da k'asa inba ku ba, ai kune manyan k'asar nan?

Dariya shugaban 'yan sanda yayi yana fad'in " ranka ya dad'e wane mu ga ku?

Murmushi Papa yayi me sauti cike da dattako, kafin yace " to mun godewa Allah...

"Ubangiji ya taimaka ya k'ara sutura ranka ya dad'e, Shugaban 'yan sandan ya fad'a cikin girmamawa..

"Kana office?

Papa ya buk'ata..

"Eh! Ranka ya dad'e, ko inzo ne?

"A'a ba saika zo ba, gani nan a hanya..

"Haba ranka ya dad'e da kanka?

"Maimakon kayi min waya nazo har gida na same ka?

"Bakomai! maganar ce a gida gaban Nadeer da Halimatu bazata yiyu ba, zasu zo maka da rai ne, nasan kai kuma kana iya goya musu baya...

"Ok, badamuwa Allah dai yasa lafiya?

"Lafiya lau, kan wani issue ne, na wani yaro dana tsinta jiya da daddare.

"Ah to ba damuwa Allah ya kawo ka lafiya.

Papa zaune a office d'in shugaban 'yan sanda akan sofa, an ajewa Papa ruwan sanyi da drinks ga green tea agabanshi,
kanshi ya d'ago ya kalli shugaban 'yan sanda yace " jiya ina kan hanyar zuwa Airport zan bar garin nan zan koma gida Lagos, na tsinci wani yaro...

"Tsinta fa kace Alhaji?

Tabbaci Papa ya bashi ta hanyar kallan da yayi mishi..

"Kodan ba abun mamaki bane musamman a irin yanayi da k'angin rayuwar da ake ciki, ga yunwa ga tsadar rayuwa ga rashin kud'i,
zaka ga wasu lokutan 'yan k'auyen nan irin 'yan gudun hijira zaka gansu da 'ya'yan suna biye dasu birjik, yaro yayi wani wajen uwar bata sani ba, wasu lokutan ma da kansu suke zubar da 'ya'yan,
sau da dama zakaga yaro d'an shekaru uku zuwa hud'u yana bara a danja shi kad'ai ba uwa ba uba ba wa ba k'ani, idan dare yayi su nemi gefen titi ko cikin lunguna su kwanta, kai wasu ma a cikin kwalbatin da ba ruwa suke kwana,
kwata-kwata basu san daraja da kirmar 'ya'yan ba, basu san hakkokin dake kansu na yaran ba, abinda suka sani kawai su haifa su yar,
kaga miji bashi da uwar komai bai aje ba, bai bawa wani ajiya ba, bashi da cin yau bare na gobe amma ana yi mishi gasar haihuwar a gida da kishiyarki ta haihu to kema sai kin haihu dan karta fiki yawan 'ya'ya, 
idan akace musu su tsagaita haihuwa ma'ana suyi tsarin iyali sai suce maka Annabi yace suyi aure su hayayyafa saboda yayi alfahari dasu ranar alkiyama.

"Kwata-kwata mutane basu san meye ma'anar Hadith ba, gaba d'aya an jahilci Hadith, shin da wanne irin 'ya'ya Annabi zayyi Alfahari dasu?

"Da irin 'ya'yan da kuke haihuwa bakwa iya d'aukar nauyinsu Annabi zayyi Alfahari daku?

"Kuzo kuna haifarwa mutane da k'asa bala'i da masifa, ku haifi 'ya'yan da bazaku iya d'aukar responsibilities d'insu ba, bazaku basu ilimi both sides, Boko da Arabi ba, ba sutura, ba cin yau bana gobe, ba wajen kwana daga k'arshe su zamewa Al-Umma fitina, 
su bazama suna kashe mutane sun d'auki ran mutum kamar ran kiyashi, su zama 'yan daba 'yan shaye-shaye, Kidnappers, makasa, marasa Imani,
saboda tun suna yara an cire musu jin kai da tausayi, yaro ya taso da bushewar zuciya, babu d'igon tausayi, sanda zai girma zuciyarshi ta gama k'ekashewa, 
ga zafin jahilci, duk d'an da yasan tun yana shakara uku ya fita ya nemo abinda zai ci kaima kasan da matsala a gaba...

"Last week mun samu wani case wai anje kamen 'yan shaye-shaye aka had'o da yara 'yan 8yrs, da muke yi musu tambayoyi sai cewa sukayi su 'yan aikinsu ne, 
su suke aike siyan abinci, da wiwi, su suke suyo musu kwayoyi da sauran kayan maye, wasu lokutan ma suke k'ulla wiwin su siyar, iyayensu na gani akan idonsu amma saboda tsabar jahilci da dod'ewar kai bazasu iya hanasu ba saboda d'an abinda ake bawa yaran suna kawo musu kuma dama rayuwar yaran bata gabansu, sun dai haifa sun zubar ne kawai...

Babban abun takaicin zakaga har a wannan lokacin da muke cikin masifa basu dena haihuwa ba, kullum cikin haihuwa suke, 
kaga mace da tsohon ciki koda d'anyen goyo akan titi tana bara, tasan ta kwanta ta yayewa namiji zani ya hauta yayi mata ciki, mijin da bai san ya sauke hakkokinta dake kanshi ba, mijin da bai san ya sauke hakkokin 'ya'yan da suka haifa ba, ba ci ba sha ba suturar arziki,
ko gishiri wani bai san ya siyo ya kawo mata ba, ba ruwanshi da 'ya'yan da suka haifa, amma ita tasan ta sauke hakkokinshi dake kanta, 
tasan ta kwanta ya hauta yayi mata ciki, abinda yake damunmu kenan, kuma Majority 99% irin wad'annan abubuwan suna faruwa ne a b'angaren mu, a yankenmu, kuma a cikin Al-Ummar mu, Arewa Hausa Fulani, duk bala'i da masifar data shigo Nigeria a gindinmu yake k'arewa 'yan Arewa saboda bamu san ciwon kanmu ba, 
bamu da kishin kanmu, sai hassada da ganin kyashi, dajin haushin junanmu, ba gaira ba dalili an cusa mana k'iyayyar juna, bama tausayin junanmu, bamu k'i kowa ya mutu ba,
babu abinda matasan mu suka iya sai TikTok, da Instagram da Facebook sai Twitter, in anyi posting ayi bad comments, ba'a san a fito a had'a kai a taimaki juna ba,
sai zagin Shuwagabanin da mune muke d'ora su, mun bar k'asarmu a hannun tsufaffin da suka kusa mutuwa, maimakon matasan mu su fito su karb'i k'asar,
su da kansu ya waye suke da ilimi da gogewa ta rayuwa, su fito a had'a kai a zama tsintsiya mad'aurinki d'aya, a zab'i zakwak'urin matashi d'aya mai ilimi both sides a tsaya mishi, a had'a kudi a sai mishi foam,
tunda foam d'in takara ne ke gagararmu, sun sakashi da tsada yadda su kad'ai ne zasu iya siya,
amma ina sai zaman benci a cikin lungunan unguwa, idan wancan ta wuce a zage ta, ace mata karuwa, aikin kenan.

Numfasawa Papa yayi tare da sauke ajiyar zuciya yace " Allah ya kyauta, maimakon su tashi su nemarwa k'asarsu da Arewa 'yanci ko basu amfana ba, 'ya'yansu da 'yan uwansu sa amfana, imba haka ba a haka za'a k'are, an haife su a wahala, sun girma a wahala, su haifi 'ya'yansu a wahala suma, Allah yasa mu dace dai...

"Amin ya Allah, to yanzu Alhaji ya kake son ayi kan maganar yaron?

"To gashi nan dai, Hajiya da Nadeer sun matsa sai an bar musu yaron wai suna sanshi, daga nan Papa ya kwashe duk abinda ya faru tun daga farkon tsintar yaron da rigimar da Hajiya da Nadeer keyi...

"Uhmmm to meye laifin hakan?

"Ina ganin a bar musu shi d'in kawai ai ko?

"Shiyasa dama nace bazaka je gidan ba, dan nasan sai son rai ya shigo, ai ya kamata ayiwa yaron da iyayenshi adalci su ma, ya kamata a bincika idan an gano iyayenshi a basu d'ansu idan kuma ba'a gano ba shikenan, 
kaga mun fita hak'k'in kowa, har iyayenshi da yaron komai zai taso a gaba ina da hujja...

"To shikenan Alhaji ba damuwa yadda kace haka za'ayi, me kake so ayi?

"Bari in tura maka hoton yaron ayi cikiyar iyayenshi ko wanda yasan shi, duk yadda ake ciki saika tab'a ni a waya...

"Okay I will ranka ya dad'e, sukayi sallama Shugaban 'yan sanda ya rako shi har bakin mota...

Papa bai koma gida ba sai yamma, saboda yana da Meeting wanda yayi cancelled d'inshi sakamakon zai koma Lagos, 
yanzu dayaga yana da free time yasa yayi call on na meeting d'in, bai fito ba sai yamma lis, amma Alhamdulillah an cimma abinda ake so,
a falo ya iske Mima rungume da yaron a k'irjinta yana bacci while Nadeer na mammatsa mishi k'afafuwanshi,
har cikin ranshi yaji sun burgeshi sun zama family of 4, Nadeer na nan-nan dashi...

Nadeer na ganin Papa ya taso ya nufe shi jikinshi har 'yar rawa yake yi, " an samu iyayenshi?

Ya fad'a kamar zayyi kuka...

" Haba Nadeer ba sannu da zuwa ba komai?

"Ko bari na, na huta bazakayi ba, kamar wanda ya aike ni?

Yayi maganar yana zama kusa da Mima while yana rik'o hannun Nadeer ya zaunar dashi kusa dashi...

Kallan da Mima keyi mishi yasa shi fahimtar itama a k'age take taji yadda akayi, releasing yayi sosai akan sofa bed d'in ya kwantar da kanshi a jikin sofa d'in had'i da lumshe idanuwanshi yana jin yadda ya gaji sosai,
" sannu da zuwa Papa, muje kayi wanka sai na baka abinci ko?

Ba tare daya bud'e idanuwanshi ba ya d'aga mata kanshi alamar eh!, ta mik'e tare da yaron a jikinta tana fad'in " Nadeer muje na kwantar dashi, saida ya kalli Papa a karo na ba adadi cike da zak'uwar son jin yadda akayi, kafin ya mik'e ya bi bayan Mima,
saman luntsumemen gadon Nadeer aka kwantar dashi, gami da manna mishi kiss a goshi, taja mishi bargo ta fita,
"please Mima kiyiwa Papa maganar idan kun shiga ciki kinji?

Ganin bata bashi amsa ba yasashi sake cewa " kinji Mima?

Still banza tayi dashi...

"Please mana Mima, ki taimaka...

"Amma dai ka bari yayi wanka yaci abinci ya huta ko?

"Inyaso duk maganar da zamuyi sai muyi mishi, idan ya huta a lokacin ya samu nutsuwa zai iya sauraron mu...

"Okay! Okay it's fine, ya fad'a so calm, kallanshi tayi tana murmushi batare data sake magana ba, deep down kuwa tafishi matsuwa taji yadda ta kaya akan yaron...

Light kiss tayi mishi a saman lallausan lips d'inshi, wanda yasashi bud'e rikitattarun idanuwanshi masu cike da bacci da gajiya, "ranka ya dad'e muje ko?

Ta fad'a had'i da d'age mishi gira d'aya, murmushi ya sakar mata batare daya sani ba, ta rik'o hannunshi cikin nata ta jashi zuwa bedroom, Papa na biye da Mima kamar wani k'aramin yaron...

Bayan kwanaki biyu...

Har lokacin Papa bai sake yin maganar yaron da wani ba, ko a gida ko a waje, ko shugaban 'yan sanda bai sake kira ba, ya tsaya yaji daga gareshi yasan komai ake ciki zai nemeshi, 
kuma yana da tabbacin da an samu wani abu da tuni shugaban 'yan sanda ya tuntub'eshi,
duk yadda Nadeer yaso yayi maganar da Papa amma Papan yak'i bashi dama ko fuskar da zai tunkare shi da maganar, 
babu nacin da Nadeer bayyi ba, amma ba fuska, yayinda Mima ma keson tayi mishi magana akan yaron, sai dai tayi alk'awarin bazata sake yi mishi maganar data danganci yaron ba muddin bashi da kanshi yayi mata ba,
daga b'angare d'aya tsanin so da shak'uwa na sake shiga tsakanin yaron da Mima da Nadeer,
ya zamewa Mima kamar cingam, ya lik'e mata, duk inda ta saka k'afa ta cire tashi zai mayar, komai ita keyi mishi, har wanka, da brush, 
gashi rigimamme idan yaso abu, while baya bacci a jikin kowa sai Nadeer, idan baccin dare ne ma sai Nadeer d'in ya rungume sosai, ya shige jikinshi kana yake iya bacci, yayinda hakan ke masifar yiwa Nadeer d'in dad'i, dama shiya sabawa yaron da haka, 
komai Yaya komai Yaya, bai san kowa ba daga Amma sai Yaya, suke mishi komai bai yarda kowa ya tab'a shi, 'yan aikin gidan basu isa suyi mishi komai ba, sai Mima da Nadeer...

Suna zaune gaba d'ayansu a babban falon Papa suna kallan Tom and Jerry dan shine film d'in da d'an lele ke so, 
yana mak'ale jikin Mima, 
wayar Papa ta soma rori, ganin Shugaban 'yan sanda ne yasashi d'agawa da hanzarinshi, shi kanshi a k'agare yake dayaji matsaya,
saboda zuwan yaron ya kawo mishi sauyi da yalwataccen farin ciki a gidanshi...

Bakin Papa d'auke da sallama ya d'aga wayar, bayan sun gama gaisawa naji Papa yace " eh! ina gida, d'an shiru yayi da alama magana akeyi daga d'aya b'angaren...

"Okay wai kana harabar gidan nan?

"To shigo mana, ka tsaya daga waje kamar wani bak'o?

"Bari na fito...

Mik'ewa Papa yayi jikinshi sanye da Arab Emirates Jallabiya tsadaddiyar gaske, sai kyalli take yi, ya zurar farar k'afarshi cikin Brown Leather Slippers yana fad'in " Shugaban 'yan sanda ne yazo...

A nutse Mima tace " Lafiya..?

Nadeer Ido ya zubawa Papa yana jiran yaji amsar da zai bayar...

"Lafiya lau, akan maganar yaron nan ne...

Fad'uwa gaban Nadeer yayi, kafin suka kalli juna shida Mima, kallo mai cike da ma'anoni da dama, tare suka mik'e suna had'a baki wajen fad'in " an gano iyayenshi ne?

Yadda sukayi maganar yaso bawa Papa dariya dole ya kanne tare da fad'in " ban sani ba yanzu zayyi min bayani...

"Mima mu bisu falon bak'in, muji meke faruwa dan bazan iya hak'uri ba wallahi...

"Fad'i ma b'ata baki Nadeer, in kaji ana raka ni kashi ba zawo bane, Mima ta k'arasa maganar tana ficewa daga falon Papa...

"Rik'e min yaron nan Zeenah ta fad'a tana mik'ewa Zeenah Nadeem, (d'aya daga cikin 'yan aikin gidan) bacci yake yi amma yana jin canjin hannu ya saka kuka yana fad'in " Amma... Yayah...

Fasa bawa Zeenah yaron tayi tana fad'in " bazai yarda ba muje Nadeer, jikinsu har kerrrrma yake yi...

Papa da kanshi ya fita ya shigo da shugaban 'yan sanda falon bak'i, turus yayi ganin Mima da Nadeer zaune, dan abinda bai tab'a gani bane, 
ya saba ko familyn shi ne suka zo Mima waje take basu balle bak'inshi personal, kowaye yazo wajenshi Halimatu bata tab'a zama wajen, koya ce ta zauna bata zama saita fita,
" lalle abun babba ne, ya fad'a cikin ranshi, a zahiri kuma baice komai ba, dan yayi musu uzuri yasan ko yayi maganar ma bata da amfani, rashin yinta yafi alkhairi....

Bayan shugaban 'yan sanda ya zauna, an cika mishi gabanshi da abubuwan motsa baki, Nadeer ya gaida shi, suka gaisa da Mima...

Shiru falon ya d'auka zuciyoyinsu na tsananta bugawa, jinin jikinsu na tsinkewa saboda tashin hankali da fargabar abinda zasu ji,
dan Mima ji take in duniya zata tashi bazata iya rabuwa da yaron ba, tana jinshi har cikin b'argo da kasusuwan jikinta....

Dif-dif Dif-dif zuciyar Nadeer ke bugawa ta yadda wanda ke zaune kusa dashi na iya jiyo bugawar da zuciyarshi keyi da tsananin k'arfi, idanuwanshi sunyi zuru-zuru...

Gyaran murya shugaban 'yan sanda yayi had'i da cewa " da akwai babbar matsala Alhaji....

Ba Nadeer da Mima ba, Papa kanshi ji yayi kamar an fisge wani abu daga k'irjinshi, nasu fitowa fili kawai yayi shima yana jin yaron har cikin ranshi.....

JIDDARH....✍🏻