DA KAMAR WUYA...!

5

by @hauwaausmanjiddarh

'''DA KAMAR WUYA...!'''

*HAUWA A USMAN*
~JIDDARH~

'''Wattpad:- HauwaAUsmanjiddarh'''

*ArewaBooks:- Hauwaausmanjiddarh*

#500 Only
Hauwa Auwal Usman
Gt Bank
0153259310
***, katin MTN banda VTU saboda WhatsApp kawai nake yi da Number, so idan kikayi transfer kati kai tsaye cikin layin ko kikayi VTU kinyi asara domin ba Jiddarh kika turawa ba, ki siyi katin MTN ki turo min numbobinshi ko hotonshi

5️⃣

Ba Nadeer da Mima ba, Papa kanshi ji yayi kamar an fisge wani abu daga k'irjinshi, nasu fitowa fili kawai yayi shima yana jin yaron har cikin ranshi....

Kallan kallo aka shiga yi tsakaninsu, aka rasa wanda zayyi magana, sai da aka d'auki lokaci kafin Papa yayi k'arfin halin cewa " matsala wacce iri?

Gyaran murya shugaban 'yan sanda ya sake yi a karo na biyu tare da gyara zamanshi yace " tun ranar da mukayi magana dakai nake bincike akan yaron,
nasa an saka hotanshi a social media da gidajen jaridu da fari ba'a samu wanda yace ya san yaron ko iyayenshi ba,
kafin daga baya wani mutum ya nuna ya sanshi...

"An samu iyayenshi kenan?

Mima ta katse shi batare da tasan tayi hakan ba..

Kallanta Papa yayi da niyyar yin magana sai dai me?

Yanayin daya ganta ba k'aramin d'aga mishi hankali yayi ba, a hankali Papa ya tashi daga inda yake zaune ya koma kusa da Mima tare da rungumo ta jikinshi,
kamar jira take yi ta fashe mishi da kukan daya narkar da zuciyar Papa, 
tana k'ara matse yaron a jikinta tamkar a lokacin za'a rabata dashi...

" Alhaji ban san meye zakayi ba, amma kayi koma menene dan mu mallaki yaron nan...

"Ko mawa ne ka kashe dan yaron nan ya cigaba da zama damu...

Ta fad'a cikin muryar kuka...

Shi kam Nadeer dake zaune kamar an dasa shi, ko wanda ke zaune saman wuta ya kasa magana illa Ido dayake binsu dashi...

Sai da Papa ya had'iye malolon bak'in ciki kafin ya mayar da kallanshi ga Shugaban 'yan sanda tare da furta " ina.... jinka...

Yayi maganar a rarrabe kamar me koyan magana..

Iska ya furzar yana binsu da kallo deep down yana mamakin in banda tsabar sangarta da samun waje mace babba da ita kamar Hajiya Halimatu data isa ta aurar harta d'auki jikoki,
ta tsaya tana yiwa mutane kukan shagwab'a da sangarta, wai dan k'arfin hali ma a kashe ko nawa ne, ita dai a bar mata yaron,
lalle gard'in kud'i na sa sakarcin banza, ji shi kanshi Alhaji yadda yake wani lallab'a ta kamar k'aramar yarinya,
d'an siririn tsaki yaja cikin ranshi cike da takaici yana fad'in rashin duka ne...

Jin yayi shiru yasa Nadeer cewa " an samu ahalinshi ne?

Murmushin dole ya k'ak'aro ya shinfid'awa fuskarshi yace " dayake a social media ne mutumin yace ya sanshi, sai muka nemi ganin mutumin Ido da Ido,
so dayazo ne yake yi mana cikekken bayanin asalin iyayen yaron 'yan Katsina ne, a haramar hukumar Batsari, ba'a cikin garin Batsari suke da zama ba, 
cikin wani d'an k'aramin k'auye ne dake k'ark'ashin k'aramar hukumar Batsarin,
su Fulanin tashi ne, wanda akafi sani da (Fulanin yawo).

Rikici da fitintinu da rashin zaman lafiya da Jahar Katsina ke fuskanta a hannun Kidnappers da Bandit musamman a yankin Batsari,
yasa sukayi gudun hijira zuwa garin Abuja neman kud'i, mutumin yace iyayen yaron suna zaune a unguwar talawa futuk a k'auyen dake gefen Abuja,
ruwan da akayi a ranar daka tsinci yaron shine yayi sanadiyyar mutuwar kowa na yaron har iyayenshi Uwa da Uba, da k'annenshi biyu, duk sun mutu,
dayake mun samu labarin abinda ya faru a k'auyen yasa bamuyi mamaki ba, dan har shugaban k'asa yasa an tura jami'ai na musamman,
shima da kanshi yaje yayiwa ragowar wad'anda suka rage a k'auyen jaje dan ina cikin wad'anda suka raka President wajen..

Duk da haka hankalina bai kwanta ba saida na saka wasu daga cikin jami'an mu suka sake komawa sukayi mana bincike dan samun tabbaci,
har can Batsarin saida na aika jami'ai aka binciko min k'auyen nasu, amma an shafe k'auyen ya zama tarihi yadda kasan Allah bai tab'a halittar d'an Adam a wajen ba balle gari....

A hankali Nadeer ya zame k'asa yayi Sujudul Shukru, dan nuna tsantsar godiyarshi ga Allah, ya dad'e kafin ya d'ago fuskarshi cike da hawaye,
itama Mima murmushi take yi while hawayen farin ciki nabin kuncinta..

"Alhamdulillah Alhamdulillah Alhamdulillah ya Rabbi, Allah na gode maka, Papa ya fad'a cikin bayyanan farin ciki marar musultuwa,
fad'ar farin cikin da Nadeer da Mima ke ciki b'ata lokaci ne dan bazai tab'a bayyanuwa ba..

Yadda yaga suna hawaye cike da farin ciki ya kashewa shugaban 'yan sanda jiki, zuciyarshi ta tsinke da al-amarin Ubangiji,
wato mutum kullum cikin jarawa yake Ubangiji baya barin mutum ba aiki, yana iya jarrabar bawa ta fannoni da dama, a idon duniya El-Yaqoub Gege bashi da wata damuwa ko matsalar komai,
wasu ma gani suke me zai rok'i Ubangiji kuma, bayan ya bashi komai, an sallame shi tuni an gama mishi komai,
abinda basu sani ba Allah baya tab'a barin d'an Adam babu aiki kullum cikin aiki da Jarabawa muke,
daga wannan ya wuce wani ne zai b'ullo, wasu suna can 'ya'yan sunyi musu yawa, wasu ma ji suke kamar su zubar da yaran su gudu,
wasu kam zubarwar ma suke yi su gudu, wasu yanzu haka adai-dai wannan lokacin suna can sun shan maganin zubar da ciki,
yayinda wasu ke cikin matsanancin k'unci da damuwa na samun cikin ko d'an, ga wasu na farin ciki da annashuwa kan kyautar d'an da Allah yayi musu wanda bama nasu bane,
basu suka haifeshi da cikin su ba, ba gudan jininsu bane, asalima basu had'a komai dashi ba, Allah kenan gwanin hikima, kai dai godewa Allah a duk yanayin daka tsinci kanka...

Katse shi Papa yayi ta hanyar cewa " ina so nayi Adopting nashi ta ina zan fara?

Sai da ya goge siririn hawayen daya zubo mishi deep down yana tunanin kyakkyawar zuciya irin ta ahalin El-Yaqoub kana yace " I think Adoption letter zaka cike ban dai sani ba,
bari zan bincika komai na yadda ake yin adopting a Nigeria da hanyoyin da ake bi, in sha Allah I will let you know...

"Okay nagode sosai da k'ok'arin ka, sai naji daga gare ka...

Tsalle Nadeer ya soma yana fad'in " Allah nagode maka, ya fad'a jikin Papa yana dariya cike da matsanancin farin ciki yana fad'in " Papa kayi gaskiya,
dama kace idan har Allah ne ya aiko min shi dan ya zame min d'an uwa, Ubangiji zai zaunar dashi a tare dani, ga tabbacin Allah ne ya aiko min dashi Papa....

Hannu Papa yasa a gadon bayan Nadeer yana bubbugawa while fuskarshi d'auke da yalwataccen murmushin dake nuni da tsananin farin cikin dayake ciki,
Mima na zaune rungume da yaron tana murmushi babu abinda take furtawa sai Alhamdulillah ya Rabbi...

Washe gari Papa yayiwa yaron hud'uba da sunan da Yayashi ya zab'a mishi Nadeem El-Yaqoub Gege, aka yanka shanu da raguna, akayi babbar walima, aka ci aka sha aka hantse...

Bayan kwanaki uku Papa na zaune rungume da Nadeem a jikinshi yana ta zuba mishi surutu irin na yara, Papa na biye shi, 
while Mima na zaune kusa dasu ta cake d'aurin d'an kwallin atampa,
wayar Papa ta soma rori kamar bazai d'auka ba, saboda yana jin dad'in yanayin kasancewarshi da Nadeem...

" IG ne fa, ka d'aga kaji ko kan maganar Nadeem ne, tayi maganar idonta kan screen d'in wayar...

" A'a bani na d'aga, ya k'arasa maganar yana d'aga wayar had'i da karawa a kunne yana sallama..

" Ranka ya dad'e na duba maka yadda ake yin Child's Adopting a Nigeria..

"Yauwa nagode sosai da kulawa..

Karka damu ranka ya dad'e ai duk yiwa kai ne, sai dai akwai abubuwan da ake buk'ata a dokance a k'asa, guda 12...

"Ai dole in bi doka, bin dokar ne ma yasa tun farko nace maka zanyi adopting nashi, so karka damu zan bi duk wasu dokoki da tsarin da k'asa ta shinfid'a dan nayi adopting nashi, dame-dame ake buk'atar ayi?

" Ranka ya dad'e akwai :-
1. Service Provider 
2. Apply to be found eligible to adopt 
3. Be matched with a child 
4. Adopt ( or gain custody of) the child in Nigeria 
5. Apply for the child to be found eligible for orphan child status 
6. Pre-approval from the State welfare agency 
7. Application to the Court 
8. Court directed investigation by state government welfare agency 
9. Recommendations by welfare officer 
10. Court order 
11. Final documentation
12. Bring your Child home...

" Kotun k'asa ta yarda da mutum cikekken d'an asalin k'asa ne kad'ai zai iya adopting a Nigeria,
sannan sai wanda yake da aure ne aka yarda yayi adopting yaro wanda bai wuce shekaru daga d'aya zuwa biyar ba, 
hukumar k'asa bata yarda abawa mace ko namiji marar aure yaro ko yarinya ba, ko wanda yake da ciwon hauka ko matsalar kwakwalwa...

Cikin halin ko in kula Papa yace " ah dan wannan ai da sauk'i ma tunda ina da duk wani abunda ake buk'ata, haka bana da abinda ake k'i d'in shima, 
in sha zuwa gobe zan turo lauyoyi na, a gama komai, idan akwai buk'atar lalle nima sai na zo sai ka sanar min,
in kuma ana buk'atar sa hannuna shima ba matsala...

"Okay Sir, already na gama shirya duk abubuwan da ake buk'ata, gobe idan ka turo Lauyoyin naka zan basu, 
idan an gama cikewa sai a dawo min dasu, so bama sai kazo ba, zasu kawo maka saika saka hannu a inda ya kamata ka saka d'in...

"Thank you so much, and kafin komai ya zama ready ana kaiwa kamar kwana nawa...?

"Saboda ina san komawa Lagos ban san tafiya sai an gama komai yadda zan tafi batare dana raba hankali na gida biyu ba, as you know am very busy Man...

"Eh! To! a k'aidance zai iya kaiwa daga shekara 1 zuwa biyu fa...

"Kai! har shekara 1 ma?

"Ai na d'auka abun is very easy fa, ashe is not.

"Ai bama lalle ne ya zama ready a shekara 1 ba, yana iya kaiwa har biyu, amma dayake kai ne masu k'asa da kansu in sha Allah nan da kwana biyar komai an gama..

"Allah yasa! nagode sosai.

Tun a ranar Papa yayiwa Barristers d'inshi waya ya sanar dasu komai, sannan ya fad'a musu suje wajen IG su karb'o takardun su kawo mishi,
washe gari k'arfe goma sha d'aya na safe d'aya daga cikin Barristers d'in ya cike takardun,
ya saka sunan Nadeem a inda ake buk'ata ya mik'awa Papa ya saka hannu, k'arfe sha biyu na safe aka yiwa IG summiting komai, 
har hotunan Papa dana Mima da aka buk'ata, tare da Marriage certificate d'insu...

Kamar yadda IG yayi alk'awari bayan kwanaki biyar komai ya zama ready, da kanshi ya kawowa Papa, 
farin ciki wajensu ba'a magana, 
Papa bai bar Abuja ba, saida yayiwa Nadeem National I'D Card da International Passport saboda kar buk'atar su ta taso babu su,
kafin jirginsu ya d'aga zuwa birnin Lagos...

*ASALIN EL-YAQOUB GEGE...*

Alhaji Abubakar Gege shine mahaifin El-Yaqoub, asalin d'an Kano ne, a haramar hukumar cikin birni, 
a unguwar sabuwar k'ofa, gidanshi na gefen gidajen 'yan sanda na Kwalli Police Barrack, yana da matan aure uku, sai dai Allah bai bawa biyu daga cikinsu haihuwa ba,
sai amaryar daya auro daga baya ce ta samu haihuwar d'a namiji me kama sak da Alhaji Abubakar Gege, yaro yaci sunan kakanshi wato mahaifin Alhaji Abubakar, 
El-Yaqoub da farko, sauran matan sun fara kishi suka had'ewa mahaifiyar El-Yaqoub kai, 
dan suna ganin tazo ta same su a gida shekara da shekaru amma ko b'atan wata basu tab'a yi ba, sai ita daga zuwa zata haihu,
data tashi haihuwar ma sai ta suntulo mai tsada d'a namiji, ganin ba inda kishin zai kaisu yasa suka tattara suka watsar suka rungume d'an da Aminatu ta haifa, wato mahaifiyar El-Yaqoub...

Hannu bibbiyu tsakani da Allah suke renan d'an tsakaninta dashi shayarwa, dan ko kwana wajenta bai cika yi ba, idan ka shigo gidan baka isa kace ga mahaifiyar El-Yaqoub ta asali ba, 
shi kanshi yaron bai tantance wacece mahaifiyarshi ba, 
Alhaji Abubakar ba wani me kud'i bane ba, yana dai da rufin asirin Allah, yana zaune a gidan kanshi ba haya yake yi ba,
gwangwan itace sana'arshi, da ita yake ci yake sha, yake kuma rik'e da iyalanshi, haihuwar El-Yaqoub tazo mishi da nasibi,
yadda kasan ruwan sama haka arziki da bud'i sukai ta zuwarwa Alhaji Abubakar, harkar gwangwan d'in dayake ta girmi Kano, ya fara haurawa Jahar Lagos,
ganin komai yana tafiyar mishi yadda ya kamata yasa ya siyi gida a Agege ya kwashe matanshi da d'anshi suka koma Lagos,
gidanshi na Kano yabarwa k'aninshi yake zaune ciki da matarshi da yaransu, komawarshi Lagos ya k'ara bunk'asa, sunanshi na asali ya b'ata sai Agege, 
kafin daga baya mutane suka cire harafin A suka koma kiranshi da Gege, duk wani d'an gwangwan dake k'asar nan yasan sunan Gege ya kuma san da zamanshi,
shaharar dayayi ta d'inke k'asar Nigeria da Niger kaf ba wanda bai sanshi ba, wannan yasa akayi mishi muk'amin shugaban 'yan gwangwan na k'asa,
a unguwar Lekki yayiwa iyalanshi gatafaren gidan da yayi girman wani d'an k'aramin k'auyen, El-Yaqoub ya taso cikin gata da wadata had'i da kulawar iyayenshi mata uku,
da kuma mahaifinshi, ga kud'i kamar banza dan babu maganar talauci a zuri'arsu ma baki d'aya dan Alhaji Abubakar Gege ya wadata kaf zuri'arsu,
wasunsuma sun dawo nan gidanshi dake Lagos da zama...

Alhaji Abubakar Gege mutum ne mai taimako da tausayin na k'asa dashi, bashi da girman kai kwata-kwata, haka bai bari giyar kud'i ta rud'e shi ba, 
bai sanka ba bai tab'a ganinka ba, amma muddin kazo ka samu ganinshi an gama, kakarka ta yanke sak'a, shiyasa yawancin zuri'arsu kowa ya zauna da gindinshi daram, 
yakance kud'i bak'i ne sukan zo su tafi, meye amfaninsu idan baka taimaki Al-Umma ba, abinda ka bayar shine rabonka,
shi bayyi karatun Boko ba sam sai na Muhammadiyya shima na Allo, wannan yasashi tsayawa d'anshi El-Yaqoub yayi zurfaffan karatun Boko a Europe a babbar Jami'ar fasaha dake k'asar England, 
haka a fannin Islama El-Yaqoub har Madina da Marocco yaje, ba iya d'anshi kad'ai yake tsayawa ba har 'ya'yan dangi da wanda ma bai san iyayensu ba....

Soyayyar da Zainabu da Maryama kishiyoyin mahaifiyar shi suke nuna mishi yasa ya taso da matsananciyar soyayyar su, ya d'auke su tamkar yadda ya d'auki mahaifiyarshi Aminatu, yakance shi iyayenshi mata uku ne ba d'aya ba....

JIDDARH...✍🏻