DA KAMAR WUYA...!

6

by @hauwaausmanjiddarh

'''DA KAMAR WUYA...!'''


*HAUWA A USMAN*
~JIDDARH~

'''Wattpad:- HauwaAUsmanjiddarh'''

*ArewaPen:- Hauwaausmanjiddarh*




6️⃣


El-Yaqoub ya taso ne da ra'ayin Boko da Turawa kasancewar a cikinsu yayi rayuwa, sai dai yana da ra'ayin addini amma fa ba mai zurfi ba,
kwata-kwata bashi da ra'ayin kasuwanci summan irin kasuwancin da mahaifin shi keyi,
ba wai ya raina gwangwan bane a'a shi mutum ne mai tsari da ra'ayi, yafi son aikin office na gwamnatin,
a cewarshi babu pressure komai ga albashi duk wata abinka hankali kwance...

Daga b'angare d'aya kuma Alhaji Abubakar Gege jira yake yi, El-Yaqoub ya kammala karatunshi ya karb'i ragamar komai,
duk da ya fuskanci hankalinshi ba'a nan yake ba, yafi karkata ga fannin Boko, bayan El-Yaqoub ya kammala karatunshi ya dawo Alhaji Abubakar yayi mishi maganar aure,
ya tuntub'eshi ko yana da wacce yake so..?

Cike da jin kunya yace " Eh! Baba.!

"Masha Allah wacece..?

" 'Yar inace?

"Ai 'yar gida ce ma, 'yar k'anwar Mama Maryama ce Halimatu...?

Sosai Alhaji Abubakar yaji dad'in hakan, dan yasan Halimatu yarinyar arziki ce, tana da hankali da nutsuwa, ga kamun kai, uwa uba kuma ilimi tana da ilimin addini mai zurfi a Boko kuwa, iyakacinta Diploma,
yaso ta cigaba tad'an k'ara koyaya ne, amma tace " hakan ma Alhamdulillah Baba ya isa...

Alhaji Abubakar Gege ya kira Halimatu ya nemi tabbaci daga gare ta, cike da kunya ta amsa mishi da eh!

Abinku da masu hannu da shuni cikin sati biyu aka gama komai aka d'aura aure, ya lula Honeymoon da amaryarshi...

Halimatu Babarbariya ce usul uwa da uba, fara ce sol kamar ka tab'a jini ya fito, ga kyau da diri kamar ita tayi kanta abin sai dai muce masha Allah....

Shima El-Yaqoub Gege mutum ne mai haiba dogo mai kira irin ta cikukkun mazan da ake so kuma ake sha'awa, sai dai shiba bari bane kuma baza a kira shi da bak'i ba, wankan tarwad'a ne, yalwatacciyar k'asumbar dake fuskarshi ita ta k'ara fito da kyanshi...

Bayan sun dawo daga Honeymoon Alhaji Abubakar ya kira El-Yaqoub falonshi, anan suka karya tare, bayan sun tab'a 'yar hira Alhaji Abubakar yayi gyaran murya tare da kallan El-Yaqoub sosai ya karkata gaba d'aya hankali da nutsuwarshi ya soma magana....

"To ka dai gani, ni yanzu girma ya fara kamani, shekaru sun ja, furfura ta fara yawaita, gab'b'ai da jikiyoyin jiki sun fara yin sanyi, yanzu kuke kan ganiyarku,
kuke da k'uciya kuke tashi, kasan Bahaushe yace mai laya kiyaye me zamani, komai ya fara komawa a zamanance, da ilimi da wayewa, 
kasan duka bani da ko d'aya bani da wayewar zamani, haka bani da ilimin Boko, 
a halin yanzu ko sana'ar kwasar kashi mutum yake yi dole sayya had'a da abu biyun nan, ilimi da wayewa, balle sana'a ta, sana'ar gwangwan ta fara komawa ta zamani ita,
ta juya akalarta wajen matasa irinku masu ilimin Boko, yanzu daku ake damawa bada irin mu ba, ana tafiya damu ne dole dan mune muka san kanta, 
mu muka kafata ita ta gina mu, dan haka nake ganin nima lokacina yayi daya kamata na hak'ura naja baya na koma gida na huta na kwanta,
na jira 'yan jikoki na suzo muyi wasa, dan haka ina so na dank'a maka ragamar komai ka fara ja daga inda na tsaya....

Tunda Baba ya fara magana El-Yaqoub ya fahimci inda ya nufa tun kafin ya dasa aya amma dayake d'an zamani ne sayya cewa yayi " kamar yaya ka kwanta a gida ka huta?

"Bangane ka dank'a ragamar komai a hannuna ba?

Murmushi yayi irin na dattawan zamani wanda suke a waye karrkarr kamar farar takarda, duk da bashi da ilimin Boko, ai yana dana Mahammadiyya,
sannan akwai hankali da zurfaffan tunani gami da lura irin ta mutanan da, yana kuma da gogewa kan zaman duniya, a Kudu fa ya zauna, a tsakiyar Lagos yayi rayuwa,
ya rayu cikin yarbawa da inyamurai har shi za'ayiwa alaye, murmushi ya sake yi a karo na biyu had'i da girgiza kanshi yace " Babana kenan.. har Allah ya kawo mu lokacin da zaka yi mun alaye kan wani abu?

"Kana ganin shekarunka had'i da wayo da dabararka sun kai kayi min wayo?

" Kodan kana jin ina waita cewa bani da ilimin Boko da wayewar zamani?

Murmushi ya sake yi yana kallan El-Yaqoub yace " wannan ma duk cikin sigar kasuwanci ce yaro, kabar ganin kayi PHD a London, 
wallahi cikin 'yan sakanni dana zagaya layin baya daka zan cefanar dakai, na siyar dakai na amshe kud'inka na zuba a aljihu na dawo gida,
to sannu me yawo, yaran zamani kuna ganin kamar ilimin Boko shine wayo, shine sanin komai na duniya da rayuwa ko?

"Gani kuke yi duk wanda bayyi karatun Boko ba kamar bashi da wayon komai dashi da Dabba ko Mahaukaci duk d'aya?

"Kuna ganin kamar cikin k'iftawa da Bismillah zaku iya kifar da mutum ko ku b'atar dashi ku wuce ko?

Wannan karon dariya yayi marar sauti sosai dake nuna mishi Maza bisa kanka yaro, an riga an fika, " ka shirya gobe mu fita kasuwa idan harka kadani a ilimin rayuwa da sanin halayyar d'an Adam bazan sake yi maka maganar sana'ar gwangwan ba har abada,
amma muddin na kada kai ka sani dolen dole kayi sana'ar ka yarda?

Saida yayi murmushi me kama da dariya har sautin shi ya fito cike da yarda da kai, yace " na yarda Baba, kai Alhaji Abubakar ya jinjina yana murmushi yace " tashi kaje Allah ya kaimu goben,
ya mik'e ya fita Alhaji Abubakar Gege yabi bayanshi da kallo cikin ranshi yana fad'in " yaro gobe za'a nuna maka ilimin Boko da wayewar zamani banza ne ba'a ko'ina suke aiki ba, dole saika had'a da gogewar zamantakewar duniya, sai kayi gwagwarmaya a rayuwarka, 
ka gwafza da Maza a filin daga ka kadasu kayi gaba, ka basu tazarar gaske yaro...

Washe gari k'arfe goma da mintuna ashirin na safe Alhaji Abubakar ya fito sanye cikin kufta riga da wando anyi mata zanen sarauta, k'afarshi sanye da takalmin d'awisu wanda akayi da zallar fatar zaki, ya shafa turaren Hajarul Aswad, 
tsaye ya tadda El-Yaqoub jikin d'aya daga cikin motocin dake fake, agogon hannunshi ya kalla kafin ya kalli Baba yana fad'in " kayi lattin minti ishirin da biyu,
Alhaji Abubakar yayi murmushi mai cike da ma'anoni da dama yace " ayi min afuwa ranka ya dad'e...

Tartanin murmushin shi El-Yaqoub ya mayar mishi had'i da mik'a mishi hannu yana rusunawa yace " ina kwana Baba?

" Lafiya lau, Alhamdulillah, ya kwanan yak'ini da yarda dakai?

K'eyarshi ya shafa yana murmushi yace " Alhamdulillah, muje ko?

Ya fad'a yana bud'ewa Baba bayan motar ya shiga ya zauna, El-Yaqoub ya mayar da murfin motar ya rufe kana ya zagaya zai shiga, 
driver ya taso da sauri jiki yana rawa hannu El-Yaqoub ya d'aya mishi yana fad'in " kabarshi zan ja, ya k'arasa maganar yana shigewa ya zauna a mazaunin driver,
juyawa yayi ya kalli Baba yace " wanne Company zamuje?

"Tushe mafari mana, muje na Agege, bayyi magana ba yaja motar suka tafi....

A harabar Company yayi parking ma'aikata suka taso tarar me gida cike da mamakin ganinshi, dan yafi shekara bai zo ba, isu-isu ne suke badak'alarsu, su tsoma biyar su tsame goma,
tuni cikkunansu ya d'uri ruwa hantar cikinsu ta soma rawa,
dama Alhaji Abubakar Gege yace suzo nan ne dan za'a fi samun matsaloli da yawa, El-Yaqoub na biye da Alhaji Abubakar har suka shiga babban Office d'inshi,
ya zaune kan kujerar office d'in, yana tuno abubuwa da dama cikin ranshi, saida ya nisa kana yace " ina san ganin kowa a nan yanzu, baki na rawa murya na sark'ewa d'aya daga cikinsu yace " ranka ya dad'e har leburori?

Bai d'ago ya kalleshi ba, idonshi kan wani file yana dubawa yace " ai kowa kaji nace ko?

"Ko kaji na ware wasu ne?

"Kayi hak'uri Alhaji..

Ba'afi mintuna biyar da fad'ar ba sama da mutane d'ari suka zube gabanshi, mutum ishirin Shuwagabanin Company ya ware yana kallansu yace " uhummm naji ku shiru bakuce min komai ba tsayin shakara d'aya ni banzo ba ku baku je ba, meye matsalar?

Bai bari sun bashi amsa ba ya d'ora da fad'in " na duba files d'in dake nan banga sabo ba, dukanninsu tsofaffi ne, meke faruwa ne?

Manager ne ya fara magana da fad'in " wallahi Alhaji ina son nazo gudun karna dameka shiyasa banzo ba, kuma nima bana zuwa sosai dan nafi watanni shida bana nan ina India jinya, bani da lafiya, idon Alhaji Abubakar tsaye kanshi yace " meyasa baka sanar dani ba?

"Amm amm dayake rashin lafiyar lokaci d'aya ta kwantar dani, kuma ma ai na fad'awa Jamilu ya sanar dakai, ya juya wajen Jamilun yana fad'in " Jamilu dama baka sanar da Alhaji ba?

Wanda aka kira da Jamilu ya zabura ya mik'e a nutse babu alamun rashin gaskiya a tattare dashi yace " ai kana tafiya aka aiko min mahaifiyata bata da lafiya shine hanzarta tafiya ban dawo sai watan daya wuce....

Alhaji ya juya ga ma'ajin Company yana fad'in " kai fa!?

Shima a nutse cike da kamala ga gemunshi sai k'alli yake yi, wandonshi a k'auri, yace " Assalamu Alaika wato ainahin na tafi Umara ne daga can kuma na tsaya nayi aikin hajji, " yanzu nawa ne a asusun Company?

"Wato ainahin dayake ban dad'e da dawowa ba amma nabar komai a hannun dattijon arziki, nafi yarda da gaskiya da amanarshi, ya juya cikin mutanen dake zaune yana fad'in " Malam Takur taso mana,
wani tsoho tukuf ya taso yana sanye da farar Jallabiya hannunshi rik'e da jarrabi gaba d'aya gashin kanshi da tsayayyan gemunshi dake har k'irji sun zama furfura da gani zayyi shekaru 70 a duniya,
" sannu Baba, tsohon ya amsa da yauwa Akaramallahu, yace " ya maganar asusun Company dana bari a hannunka?

"Kasan har yanzu komai yana hannunka ban karb'a ba tukunna?

"Eye! kace me yaro?

Tsohon ya fad'a yana sake karowa Akaramallahu kunnenshi, ya d'ora da fad'in " kasan kunnen tsufa bana ji sosai..?

Akaramallahu yace " ashsha sannu kaji, kara bakinshi yayi a kunnen tsohon tare da d'an d'aga murya " ya maganar asusun Company dana bari a hannunka?

"Aiyo..!, tsohon yace kafin ya d'ora da " kasan bana ji sosai kuma banyi karatun Boko ba, ga bana gani, ina zan iya lissafinku na 'yan Boko shiya ba barwa Adamu komai, ni ina Kano asibitin Makka na Gadon k'aya naje ana duba idona..

Akaramallahu yayi gyaran murya had'i da kallan Alhaji Abubakar yace " watan jiya Allah yayiwa Adamu rasuwa, murmushi Alhaji Abubakar yayi yana fad'in " Adamu ya rasu kuma babu wanda ya fad'a min ba?

Kansu k'asa sukace kayi hak'uri ranka ya dad'e, to shikenan ba damuwa ku fita ku jira ni a wajen office ina zuwa...

" Kace me?

Inji tsoho yana karo kunnuwanshi, Alhaji Abubakar bayyi magana ba, sai Akaramallahu ne yajashi zuwa waje yana maimaita mishi abinda aka fad'a...

Bayan sun fita Alhaji Abubakar ya kalli El-Yaqoub yace " meka fahimta?

Ajiyar zuciya El-Yaqoub ya sauke yana kallan mahaifinshi yace " ai babu abinda mutum zai iya fuskanta, dan saurin yanke hukunci babu kyau, bincike yakamata ayi me zurfi,
kamar Adamu da sukace ya mutu kace zaka je gaisuwa kaga anan zaka samu tabbacin mutuwarshi, tsoho da Akaramallahu ba sai an bincike su ba dan gaskiya suka fad'a, 
amma duk da haka idan kana san tabbatarwa saika cewa tsoho ya kawo maka takardun asibitin dayaje, shi kuma Akaramallahu kace ya nuna maka hotunanshi na aikin hajji,
tunda a halin yanzu Da Kamar Wuya... mutum yaje aikin hajji da Umara bayyi hotuna ba,
shima Manager kace ya kawo Documents nashi na asibitin India, da visa da ticket,
sai wancan dayace maka yaje jinyar mahaifiyarshi, shima kace ya kawo maka hujja, ina ganin ai shikenan ko?

Tunda El-Yaqoub ya fara magana idon Alhaji Abubakar ke kanshi yana jinjina kai cike da gamsuwa, nisawa yayi tare cewa " to kayi hakan nabar komai a hannunka...

"Okay! El-Yaqoub yace cike da murnar yayi nasara, El-Yaqoub ya fita waje da kanshi ya sanar dasu ranar Monday kowa ya kawo abinda ake buk'ata na hujja, 
babu wanda ya nuna damuwa ko tsoro da firgici balle tashin hankali suka amsa da to...

Har sun juya zasu tafi El-Yaqoub yace " yauwa Akaramallahu ka had'o da visa da hotel reservations, kaima Manager haka, suka sake amsawa da to...

Ranar Monday dukkaninsu babu wanda bai kawo abinda aka ce mishi ba, Akaramallahu ne kad'ai bai kawo hotunanshi ba, amma ya kawo visa da hotel reservations, Alhaji Abubakar da El-Yaqoub suna zaune suka mik'a musu komai, 
Akaramallahu yace " ga Visa da hotel reservations nan na kawo, hotuna ne kawai babu, banyi hotuna ba, saboda bidi'a ce da fariya gami da riya, dan Allah kayi, Ubangiji kayiwa shiya san kayi ba saika sanar da duniya ba,
El-Yaqoub ya karb'a ya dudduba komai, kana ya mik'awa Alhaji Abubakar,
bai amsa ba, sai ma d'agawa El-Yaqoub hannu da yayi yana fad'in aje su nan ba saina gani ba, kai dai ka gani ko?

" Eh!

" Ka gamsu da hujjojin da suka kawo maka?

"Eh! Mana, na duba komai is intact, everything's is completed here, kowa ya bada hujjar da ake da buk'ata meye matsalar?

Idon Alhaji Abubakar kan mutanen yana sake nazartar su, yacewa El-Yaqoub ka sake dubawa ka nazarci komai,
rolling idanuwanshi yayi yana fad'in " babu abinda ban duba na nazarta ba...

"Okay!.. ka tambatar ka gama duk abinda zakayi akansu..?

"Eh mana, yayi maganar cikin rashin fahimtar abinda mahaifin nashi ke nufi....

"Ina baka damar ka ne fa, karka ce ban baka ba, Baba duba fa ka gani komai yayi dai-dai da abinda suka fad'a.

"A'a ba saina duba ba, indai yayi maka shikenan?

"Baba bani kad'ai ba kowa yaga wannan hujjar zai samu gamsuwa..

"Okay tom badamuwa, ya kallesu yace kowa ya fita, a jira ni a waje, kafin ya gama rufe bakinshi duk sun fita,
kallan El-Yaqoub yayi sosai yana fad'in " zan sake baka dama ta k'arshe ka sake nazartar takardun nan sosai fa...

" Meyasa Baba..!?

Saboda dukkaninsu k'arya suke yi babu me gaskiya a cikinsu balle a samu wanda ya fad'i gaskiya...



JIDDARH...!✍🏻