8
'''DA KAMAR WUYA...!'''
*HAUWA A USMAN*
~JIDDARH~
'''Wattpad:- HauwaAUsmanjiddarh'''
*ArewaPen:- Hauwaausmanjiddarh*
8️⃣
Ranar Monday aka saka Nadeem a babbar makarantar dake garin Lagos inda acan Nadeer yake, ranar kam anga d'oki da rawar kai wajen Nadeer,
yaron da kullum in zaije makaranta sai rayuka sun b'aci shine yau ya tashi yake shiri da wuri, da kanshi ya shirya Nadeem,
yau kam a makarantar kowa yasan k'anin Nadeer El-Yaqoub yazo, dan babu inda ba'a shiga da Nadeem an gabatar dashi ba, nan fa gaba d'aya makarantar ta d'auka k'anin Nadeer yazo...
Haka ma a Islamiyya abun yake, dan aji-aji Nadeer ya shigar da Nadeem ya gabatar dashi, tsananin soyayyar dake tsakanin Nadeem da Nadeer abin ba'a cewa komai sai dai mutum yayi shiru,
dan duk duniya babu mahaluk'in daya isa ya tab'a Nadeem a gaban Nadeer,
kai ko kallan banza baka isa kayi mishi ba, ko malaman su sun shafawa kansu lafiya akan Nadeem, gashi bayaji yaro ne shi me k'iriniya, ya damu kowa ba Malaman kad'ai ba,
har 'yan ajin ya addabe su, dole tasa kowa yayi shiru saboda tsabar tsoran Nadeer da ake ji..
A gida ma haka abun yake yanzu ne zai sallami ma'aikaci akan Nadeem, ko alamu yagani na kana yiwa Nadeem d'inshi kallan banza aikinka a gidan ya kare,
Mima da Nadeer sun d'auki so da k'aunar duniya sun d'ora mishi, yayinda shima Nadeem d'in duk duniya baya san kowa sama dasu,
duk hutu Nadeem ne ke zab'ar musu k'asar da zasu je hutu, Papa yana ji yana gani Nadeem na neman sangarcewa amma babu yadda zayyi abun yafi k'arfinshi,
uwa da 'ya'yanta sunfi k'arfinshi dole ya zubawa sarautar Allah ido, wani lokacin ma a tsakiyarsu Nadeem yake kwana idan yaso rigimarshi dan gimamme ne Nadeem na ajin farko.
Haka a b'angaren abinci ma yaro ne me tsurfar tsiya baya cin wannan baya cin wancan, sai a jere mishi abinci sama da guda goma, amma idan yaga dama yana iya cewa dukkansu basu yi mishi ba,
haka dole za'a sake dafo sabo wanda yake so, dan haka ma Mima tasa dokar kafin ayi girki a fara tambayar Nadeem abinda yake so, abinda ya bada umarnin a dafa shi ake dafawa...
Suna zaune a babban falon gidan suna kallan film d'in Snow White and the Seven Dwarfs, yayinda Nadeem ke lafe jikin yayanshi Nadeer, yana bashi ice cream a baki,
wayar Papa tayi k'ara kamar ya share sai kuma ya d'aga, a fili yace " innalillahi wa'inna ilaihir raji'un yaushe ya rasu?
" Yau d'in nan ne ma?
" Ubangiji yayi mishi rahama in sha Allah zan zo ta'aziyya cikin satin nan..
Cike da jimami ya kalli Mima yana fad'in " kinji IG ya rasu...
"Wanne IG d'in?
"Badai wanda yayi amana adopting Nadeem ba?
"Shi fa..
Papa ya fad'a kamar zayyi kuka..
"Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un garin yaya?
"Wai jiya aka bishi har gida akayi mishi yankan rago, al'amarin k'asar nan abun yayi yawa fa, kullum abun sai k'ara ta'azzara yake yi,
kuma komai kan mu 'yan Arewa yake k'arewa, da anga wani babba adali dayake san kawo cigaba a Arewa sai an san yadda akayi aka kawar dashi, maimakon manyan mu su magantu amma duk sunyi shiru..
"Kai ma dai Alhaji kamar baka san harkar ba, ya za'ayi suyi magana bayan an cika musu bakunansu da daloli?
"Allah ya kyau!.
"Papa meye rasuwa..?
Kallanshi Papa yayi har lokacin fuskarshi bata sake ba, cike da damuwar rasuwar IG, yace " mutuwa Nadeem..
"Meye mutuwa Papa?
"Mutuwa tana nufin mutum ya kwanta yayi bacci a hak'a rami a binne shi, kuma bazai sake tashi ba har abada..
"To Dole kuwa sayya mutu?
"Dole ne Nadeem.
"Nidai kowa ya mutu, a d'auke kowa a bar mun Abbaah na, Nadeer kenan, tun daya koma cewa Papa, Papa yake cewa Nadeer Abbaah..
Cike da mamaki Mima da Papa suka kalli juna, kafin Mima tace " meyasa Nadeem?
"Mu duk mu mutu abar maka Abbaanka?
"Eh! Amma.. ina son shi daya sosai fa, idan ya mutu nima mutuwa zanyi, dole sai dashi nima zan zauna a duniya...
Kallanshi Nadeer yayi idanuwanshi cike da hawaye tab!, ya shafa kanshi had'i da cewa " haka kake so na Nadeem?
"Fiye da haka ma Abbaah, ina sanka fiye da kowa...
Hawayen dake idanuwan Nadeer ne suka gangaro saman kuncinshi ya kwantar da kan Nadeem a saman k'irjinshi had'i da lumshe idanuwanshi yana sake jin k'aunar Nadeem na k'ara ratsa ko'ina nashi...
"Papa dama ka fad'a Allah zai bani wanda zai so ni, fiye da komai da kowa, Ubangiji zai bani d'an uwan dazai iya sadaukar min da komai gashi Allah ya bani...
A hankali Papa ya sauke ajiyar zuciya yana d'auke idonshi daga kansu, dan sosai maganganun Nadeem suka bashi mamaki had'i da d'aure mishi kai,
" Ubangiji ya had'e min kanku, Allah yasa wannan k'aunar da kuke yiwa junanku ta kasance har rai da mutuwa, duk abinda zai zame muku matsala Allah ya kawar muku dashi daga duniyarku, haka duk mutumin da zai zame muku fitina Allah karya bashi ikon shigowa rayuwarku,
imma ya shiga ina rok'on Allah ya fitar muku dashi daga duniyarku, Allah yasa ku rayu tare ku mutu tare, Ubangiji ya sake k'ulla soyayya da zumunci mai k'arfi a tsakaninku...
Papa yayi maganar yana k'ok'arin mayar da hawayen dake son zubo mishi, dan haka nan yaji a jikinshi kamar akwai wani al'amari mai girma a rayuwar yaran, jikinshi yana bashi wani abu mai kama da K'addara zai iya faruwa a tsakaninsu...
"Amin ya Allah, suka fad'a gaba d'ayansu har Mima...
Haka rayuwa taita tafiya lokuta na shudewa, zamaninnika da yayi nata zuwa, rayuwa na k'arewa, mutuwa na k'aratowa, yayinda shak'uwa da soyayya me k'arfi take sake shiga tsakaninsu, suna girma k'aunar dake tsakaninsu na girma itama, while Mima da Papa suka karkata hankulansu wajen renon 'ya'yansu....
*Bayan Shekaru Ashirin...!*
Acikin shekaru 20 d'in da suka gabata abubuwa da dama sun faru ciki har da mutuwar Papa El-Yaqoub, daya rasu shekaru goma baya, fad'ar halin da Nadeer da Nadeem da Mima suka shiga b'ata baki ne,
bai wani dad'e yana jinya ba, a tsaitsaye yayi d'an zazzab'i na kwana biyu, ranar juma'a da asuba Ubangiji me kowa mai komai ya amshi ran El-Yaqoub Abubakar Gege...
'Ya'yan Mima sun girma sun zama samari, Nadeer nada shekaru 36 yayinda Nadeem keda 26 dama shekaru goma cif-cif ne a tsakaninsu, while soyayya da tsananin shak'uwa ba'a magana a tsakaninsu...
Nadeem matashin me kud'i cikekken d'an kasuwan da yayi gadon kasuwanci, wanda ya fito daga tsatsan kasuwanci, shine ya maye gurbin Alhaji Abubakar Gege kakanshi da kuma mahaifinshi El-Yaqoub Gege,
Dogo wankan tarwad'a, da fari yana yaro fari ne tas, dan daya taso kamaninshi sak da Mima, kafin daya girma ya juye sak mahaifinshi,
yana da siririyar dogowar fuska mai d'auke da siririn hanci kamar biro dake tsaye carr kamar an kafa shi,
d'an k'aramin bakinshi me d'auke da fararen hak'ora a jere reras kamar an jera su, idanuwanshi kuwa sai dai muce masha Allah,
a shanye suke koyaushe kamar me jin bacci, sai faffad'an k'irjinshi da kowacce mace zata so ta kwanta luf a cikinshi,
kwata-kwata baya san yawan magana, a rana zaka iya irga yawan maganarshi, shiru-shiru ne sosai,
shidai ya karanta jarida koya kalli sports, idan kaji surutun Nadeer to da d'an uwanshi ne Nadeem, ko da Mima bai fiya sakewa yana magana sosai ba,
komai akayi iyakacinshi yayi murmushi, mutum ne shi mai yawan murmushi, yawancin magana da murmushi yake bada amsarta...
Nadeem matashin saurayi me ji da k'uruciya da gayu, ga tsantsar kyau na asali, fari ne fat dogo sai dai bai kai Nadeer tsayi ba,
yana da dogon hanci irin na mazan labarabawa ga d'an k'aramin baki me zagaye da cute pink lips, siririyar wushiyar data raba hak'oranshi ce ta k'arawa bakinshi kyau,
idanuwanshi kam ba'a magana su ake kira da lulu eyes, shanyayyu masu kama dana mashaya,
side dimples d'inshi shike k'arawa dariyarshi kyau...
Nadeem mutum ne mai yawan magana, yana da surutu har da na banza, idan yana gida bakin kowa baya shiru, ga barkwancin da san raha, shi mutum ne na mutane kowa yana sanshi, dan yana da shiga rai sosai...
Shak'uwar dake tsakanin Mima da Nadeem ba'a magana sai dai nabar me karatu ya kintata abun da kanshi...
" Nadeem dakai fa nake magana kana jina kayi shiru ko?
" Mima... Ya fad'a kamar zayyi kuka dan Allah ki barni nayi bacci...
"Zakayi bacci amma ba'a anan ba, ka tashi ka tafi d''akinka wai meye amfanin bedroom d'inka Nadeem?
"Wannan wacce irin rigima ce?
"Mutum ya girma amma bai san ya girma ba, kai kenan kullum cikin neman rigima fisabilillahi?
"Kana baligi kace kullum anan zaka rink'a kwana, wato ma dana d'auke spare foams d'in wasu kaje ka siyo ko?
"Mima idan ban kwana nan ba a ina kike son naje na kwana, so kike na barki ke kad'ai?
" D''akinka zaka kwana..
"Ki kwanta akan gado ni ina k'asa nayi shinfid'a meye laifi anan?
"Ya salam tace tana dafe kanta cike da k'osawa, zaka tashi ko saina kira yayanka?
Murmushi yayi dayasa side dimples d'inshi lotsawa yace " kema kin san bayana zaibi, kira shi kiji..
"Sai ka tashi ka tafi d''akinka, bazai yiyu nida d'akina azo a hanani sakewa ba...
Murmushi Nadeer yayi had'i da tura k'ofar ya shiga bakinshi d'auke da sallama..
Bata amsa sallamar ba, sai cewa tayi " yauwa gwara da Allah ya kawo min kai, ka tab'a ganin inda uwa ke kwana da d'anta kamar wannan fisabilillahi?
"Ko'a garin gab'ab'a kai ko a America cibiyar kafurci baza'ayi haka ba, ka d'auke d'an uwanka ku bani waje..
Fuskarshi d'auke da murmushi ya zauna bakin gado kusa da Mima idan da sabo ya saba da rigimar wajen kwana dan kullum sai sunyi,
kuma kullum sayya kwana a d'akin, idan ma sukayi fad'a yayi yaji da kanta zata nemo abinta..
"Yaya dan Allah ya za'ayi mubar Mima tana kwana ita kad'ai a d'aki ita daba ishashshiyar lafiya ba..?
"Ni lafiyata lau, babu abinda ke damuna, in zaka fita ka fita ma tun wuri...
"A'a gaskiya bai kamata abarta ta kwana ita kad'ai ba, wannan ma ai risk ne..
"Oh! dama yace bayanshi zaka bi, kabi bayan nashi kenan ko?
"Wane ni Mima, ai ni kullum ina bayanki, yayi maganar yana daddana k'afuwanta, zatayi magana yace " bari nayi shari'a ta adalci, Nadeem ka tsaya idan tayi bacci ka tabbar ka koma bedroom d'inka, ya k'arasa maganar yana kashewa Nadeem Ido..
"Shikenan Abbaah magana ta k'are..
"Ban yarda ba haka kullum kake rena min hankali da wannan shari'ar taka, yanzun zai tashi ya fita..
"Naji kiyi hak'uri na tsaya mishi as grantor daga yau bazai sake kwana ba..
" Ka tabbatar?
"Sosai ma Mima..
Juyawa tayi ga Nadeem tace " ka yarda?
"Na yarda kin san ban tab'a cewa a'a ga hukuncin Abbaah na..
"To shikenan Allah ya tashe mu lafiya ta k'arshe maganar tana kwanciya...
Tun Nadeem yana yaro yawanci a d'akin Mima yake kwana, kafin daga baya daya soma girma sosai ya koma wajen yayanshi duk da kasancewar yana da bedroom nashi na kanshi,
amma bashi da wani amfani kullum yana wajen Abbaah, daga ranar da Papa ya rasu Nadeem ya koma d'akin Mima da kwana, tana kan gado shi kuma ya shinfid'a katifa da barguna ya kwanta a k'asa,
sosai hakan keyiwa Mima dad'i dan ya nuna tsaro da kulawa a gare ta, danta Nadeer babu abinda ya dame shi, shi mutum ne d'an I don't care,
shi kanshi ma bai damu da buk'atun kanshi ba, balle na wani, yawanci Nadeem d'in ke kula da komai na rayuwarshi har abinda zaici da abinda zai saka,
daya girma sosai ne girima ya b'arke tsakaninshi da Mima,
dan rana tsaka ta tada borin sayya dena kwana d'akinta, yayinda shi kuma yayi tsalle ya dire yace nan fa d'aya ai har rai da mutuwa bamai raba shi kwana da Mimanshi,
wannan yasa kullum ake rigima wajen kwanciyar ta tubure bazai kwana ba, shima ya tubure sayya kwana, kafin daga baya Nadeem nazo yayi musu sulhu da sunan daga ranar bazai sake kwana ba,
kullum a haka ake da alk'awarin daga ranar bazai sake kwana ba...
Siraran hawayenta ta goge tana murmushi ta juya tana kallan kyakkyawar fuskarshi cike da soyayyarshi,
zata iya rantsewa tafi son Nadeem fiye da Nadeer dan tafi sabawa da shak'uwa dashi, ita mema ta sani akan Nadeer?
Nadeem d'inta kam tasan komai akanshi, ko fita yayi yaci wani abu sayya rago mata nata koya siyo mata, bai tab'a fita waje yasa wani abu a bakinshi batare daya kawo mata ba,
so da dama tana k'ok'arin hanashi, amma sayya ce mata " Mima ina tuna sanda kike hana kanki ki bani,
ina tuna lokuta da dama sai kin saka abu a baki nasa rigima nace na cikin bakinki zanci kuma ki cire ki bani, akwai sadaukarwar data fi wannan?
"Duk duniya babu sadaukarwar data kai ta uwa balle tafi, duk abinda zanyi miki bazan tab'a biyanki ba Amma na..
Takanyi murmushi tace " Allah yabar min kai, Allah yasa kada matarka ta rabamu.....
"Wallahil azim ba'a haife ta ba Mima, ko Babarta ma ba'a haifa...
Ko sallar asuba bai cika fita masallaci ba, anan d'aki yake jansu jam'i shida Mimanshi, idan tayi mishi magana yace " ina so kema ki samu ladan jam'i Mima...
Tayi k'arya idan tace bai fiye mata kowa da komai a duniya ba, ta sani yana santa ita da Nadeer fiya da kowa da komai a duniya,
itama hakanne tafi sanshi fiye da kowa a duniya..
A hankali cikin sanyin murya tace " fiye da kowa, kuma akan kowa...
Tana kallanshi tana murmushi bacci mai nauyi yayi awon gaba da ita....
Ni kam nace kada Allah ya kawo k'addarar da zata raba kan uwa da 'ya'yanta...
JIDDARH...✍🏻