10
'''DA KAMAR WUYA...!'''
*HAUWA A USMAN*
~JIDDARH~
'''Wattpad:- HauwaAUsmanjiddarh'''
*ArewaPen:- Hauwaausmanjiddarh*
🔟
Tsaye yayi yana bin bayansu da kallo deep down yana juya maganganunta cikin ranshi me take nufi da cewa sun fito ta k'azantacciyar hanya?
Me take nufi da ta datti aka samar dasu?
"Mu kan mu datti ne, me hakan ke nufi?
" Dattin dake cud'anye da tushensu, wani irin datti ke cud'anye da tushensu?
Nadeem yayiwa kanshi tambayar while yana tsaye a wajen bai motsa ba yana binsu da kallo har suka b'ace mishi,
jiki a sanyaye ya shiga mota ya koma gida a falo ya samu Mima ta dasa Nadeer gaba tana mishi fad'an aure...
Rolling Lulu eyes d'inshi yayi, saboda ya gaji da rigimar nan ta Mima da Nadeer ba'a sati saita titsiye shi da maganar aure, wai yak'i aure harya kusa tsofa...
"Shekarunka 36 fa, fisabilillahi idan bakayi aure yanzu ba sai yaushe?
"Ko sai ka ida tsufewa?
"Tsufa kuma Mima?
Nadeem ya fad'a yana zama kusa da yayanshi, a fili Nadeer ya sauke ajiyar zuciya dan yasan kub'utarshi tazo, tun d'azu yake ta Allah Allah Nadeem yazo,
har ya fara tunanin kiranshi a waya, " ina kaje?
"Rashinka yasa ana yi min maganar aure, Nadeem yayi maganar cikin rad'a dan kar Mima taji..
"Tsufa mana ace mutum ya doshi arba'in gadan-gadan amma ko niyyar auren babu?
"A'a fa Mima ki dena cewa babu niyya, akwai niyya mana, ya fad'a yana komawa kusa da ita ya zauna had'i da dafa ta..
"Ina fa niyyar Nadeem?
"Mutumin dako budurwa bashi da ita, a tarihinshi ko sau d'aya bai tab'a cewa yana san mace ba, ko irin na k'uruciyar nan bayyi ba,
gaskiya na gaji nasan da Alhaji yana nan ai da tuni kayi, kaima saboda bayyi ba gaka nan zaune, kana neman tasarwa 30, zagada-zagadan samari ace ko zo kiji basu da ita..
D'an shiru tayi kafin tace " wai tsaya ma ku fad'a min gaskiya kodai baku da lafiya ne?
Tayi maganar tana nunasu da d'an yatsa while tana binsu da kallo, murmushi me kama da dariya Nadeer yayi daya sa dimples d'inshi lotsawa..
Shi kam Nadeem kwashewa yayi da dariya harda buga k'afa yasa hannu ya rufe bakinshi, sosai maganar Mima ta bashi dariya..
"Ku fad'a min da wuri in san abun yi kar azo aji kunya, idan har ba baku da lafiya ba babu abinda zaisa ace baku da 'yan mata, kai daga gida sai gida,
kai kuma agogo sarkin aiki, daga office sai gida..
"Zancen rashin lafiya ma ki barshi dan dukkanmu idan kikayi mana aure wata 9 kin d'au jika..
Duka takai mishi tana fad'in " marar kunya, to idan ba rashin lafiya ce ta hanaku kula mata ba meye?
Hannayenta ya rik'o cikin nashi had'i da cewa " lokaci Mima, lokaci ne bai zo ba har yanzu, idan yazo za'ayi, aure, mutuwa da haihuwa duk lokaci ne, idan lokacin su yazo duk duniya babu wanda ya isa ya dakatar,
koka shirya ko baka shirya ba, shi lokaci bak'one baya jira Mima, iska ta furzar daga bakinta cikin sanyi tace " to yaushe ne lokacin shi zayyi?
Tayi maganar tana kallan Nadeer, " zai zo karki damu, da zarar lokacin yazo ke da kanki zaki fahimci hakan..
"Ubangiji ya kawo shi da gaggawa, Allah ya gajarce min lokacin aurenku ya matso min dashi kusa-kusa...
"Amin ya Rabbi! addu'a ita ya kamata Mima..
Nadeer na kallan Nadeem yana mamakin yadda yake iya magana me tsaho haka, indan tashi ne sai dai taita fad'an yana bata hakuri amma bazai iya fahimtar da ita da magana mai yawa haka ba...
Hannun Nadeem sak'ale a kafad'ar Nadeer suna tsaye bakin k'aton Swimming pool kifaye sai link'aya suke yi, Nadeer ya zubawa wani jan kifi ido yana tunanin..
"Kifin da Papa yafi so ko?
" Uhuun! Nadeer yace yana sauke numfashi..
" Idan ban manta ba daga Ice Land ya kawo shi ko?
"Eh!
Sake zubawa kifin Ido sukayi na tsayin lokaci a tare..
"Abbaah..!
Nadeem ya kira shi a hankali, bai amsa ba illa Ido daya zuba mishi da alama maganar da Nadeem yake son yi yake jira yayi..
"Abbaah meyasa bazaka yi auren ba kodan farin cikin Mima?
" Zanyi *NAWA!* sunan da Nadeer yake kiran Nadeem dashi..
"Sai yaushe zakayi Abbaah?
D'an shiru Nadeer yayi yana nazari kafin yace " lokacina nake jira, idan yazo zanyi..
"Kai! Abbaah wato amfani zakayi da kalmar da nayiwa Mima wayo, nima kayi min ko?
"Magana ta zaka dawo min da ita.
" Da gaske zanyi Nawa!..
Agogon hannunshi ya kalla had'i da cewa " 5 tayi zanje wani waje..
"Nima Gym nake son zuwa..
Yana fitowa daga Gym around 6 ya gansu zaune kan kujerun shan iska a Garden, har yasa kai zai wuce ya fasa ganin Nadeeyah na hawaye..
Yaje zai zauna Faidah tasa k'afa ta ture kujerar, ya afka kan table, sob'on dake gaban Nadeeyah ya wanke mata fuska da jiki gaba d'aya,
baki suka bud'e gaba d'ayansu ido Nadeeyah da Nadeem suka runtse, ya cije leb'enshi yana fad'in " not again!
A tare suka bud'e idanuwansu ta kalleshi na 'yan sakanni, kanta ta kawar gefe tare mik'ewa tana fad'in " mu tafi!
Yabi bayansu da sauri " kiyi hak'uri please ban san ya akayi hakan ta faru ba amma bada gayya nayi ba..
"Na sani kaje bakomai..
"Ba wani nan wallahi kana sane, ka ci sa'a wallahi kana samun mu a yanayi me kyau...
" A yanayi me kyau?
Ya fad'a yana tushe baki dan kar dariyar dake cinshi ta kwace..
Ido Diyah ta runtse tare da tsayawa cak tana fad'in " me kake nufi da dariyar da kake k'unshewa da kuma cewa yanayi me kyau?
" Gani nayi wannan kullum tana cikin k'unci da damuwa ko sau d'aya ban tab'a ganin annuri a fuskarta ba, amma kina kiran yanayi me kyau,
kallanshi Nadeeyah tayi kamar zatayi magana sai kuma ta fasa, ta rik'e hannun Faidah da Diyah suka cigaba da tafiya...
"Wai meyasa ke baki magana ne?
"Wane bak'in ciki ne a rayuwarki daya hana maki walwala...?
"Sai kace mareniya ko wacce bata da iyaye ai kowacce bata san asalinta ba iyaka kenan...
Cak Nadeeyah ta tsaya had'i da runtse idanuwanta, yayinda da Faidah da Diyah suka kalli juna kafin suka mayar da kallansu kanshi suna girgiza mishi kansu..
Idanuwanta da suka zama asalin jajaye ta bud'e ta watsa su cikin nashi tarr, in banda namijin duniya ne zai iya tsora da yanayin data shiga...
"Kai meka sani akan rayuwa?
"Wacce rayuwa ka sani in banda ka ci kasha ka kwanta iyayenka sun tara maka, wata k'ila ubanka b'arawon gwamnati ne, mahaifiyarka na can zaune shirim sai dai tasa ayi mata komai 'yan aiki na zagaye da ita...
Marin daya kifa mata ne yasata yin shiru dole, yanayinshi gaba d'aya ya canja idanuwanshi sunyi jajir while jikiyoyin kanshi dana kwanjinshi sun fito rud'u-rud'u,
ya nunata da yatsa yana fad'in " kul! karki soma aibata min iyaye nasan daraja da k'imarsu, dani kika tab'a da bazanyi miki komai ba,
amma muddin kika tab'a min mahaifi ko mahaifiya... lips d'inshi ya cije da k'arfi..
Matsowa tayi daf dashi ta yadda kowannensu yana iya jiyo bugun zuciyar junansu, " kasan da hakan kake maganar asali da tsatsan wasu?
"Su iyaye naka shafaffu da mai ne da baza'a...hannu ya d'aga zai sake kifa mata mari, ta rik'e hannun nashi, " karka soma, karka kuskura ka soma, ka kalli wutar dake gabanka, koba yau ba ka sake magana akan asalina saina k'ona ka da ranka,
ta yarfar da hannunshi gefe tare da karkad'a mishi yatsa a fuska alamar gardad'i,
ta dasa hannu ta tura shi baya tana fad'in " ja jiki...
Wata irin tasafa zuciyarshi keyi, lokaci d'aya duk ilahirin jikinshi ya d'auki kerrrrma in banda mace hmm, yau da namiji ne d'an uwanshi yayi mishi wannan haukan daya gane Allah yana da girma..
Bayansu ya nuna da d'an yatsa had'i da cije leb'enshi ya shiga mota ya figeta da wani irin gudu in banda sun matsa daya take su...
Tunda ya shigo gida Mima ta gane yau d'an nata ba lafiya, ya wuce bedroom d'inshi had'i da banko k'ofa, " yau rigimar ta motsa, ko shida wa oho?
Ta fad'a had'i da mik'ewa ta nufi bedroom d'in nashi, yana kwance rufda ciki ta zauna gefen gadon a hankali had'i da d'ago kanshi ta d'ora saman cinyarta,
tana shafa kwantaccen gashin kanshi, a fili ya sauke ajiyar zuciya gami da sanya hannunshi ya sake rungume Mima sosai..
"Fad'a min meya faru, waya b'ata maka rai?
"Kai da wa?
Kwata-kwata bai saba b'oyewa Mima komai ba haka baya yi mata k'arya, dan haka ya kwashe komai tun farkon had'uwarsu ya fad'a mata,
a fili ta fitar da numfashi had'i da cewa " tabbas akwai wani abu, ina zaton cikin maganar daka fad'a mata akwai abinda ya shafi rayuwarta shiyasa daka fad'a abun ya tab'a ta...
"Wacce maganar?
" Imma *MARAINIYA..!* ko "*MARAR ASALI...* cikin biyun nan tabbas akwai d'aya..
Maganganun dayaji ta fad'a ranar daya zuba musu ruwan datti ya tuno, tabbas akwai wani al'amarin...
" Me kake tunani?
" Ko ta tab'a fad'a maka wani abu daya shafi rayuwarta ne?
Haka nan yaji bazai iya sanar da Mima maganganun Nadeeyah ba, karo na farko kenan daya tab'a b'oyewa Mima wani abu...
" Bafa ta magana! yaushe har zata fad'a min wani abu?
Murmushi Mima tayi while tana cigaba da shafa kanshi tace " kodai naka lokacin ne yazo?
Zabura yayi ya tashi zauna yana kallan Mima yace " lokacin me?
" Na sani ko ita ce surukar tawa, ka fad'a tarkon da kai kanka baka sani ba...
" Tur Allah ya kiyaye Mima, Ubangiji ya tsare ni, ke kin ganta kuwa?
" Me zan gani d'in?
" Ba kyan gani, yayi maganar yana tab'e baki kamar yaga kashi...
Murmushi me kama da dariya Mima tayi gami da cewa " karfa wata rana azo ana yiwa Mima kukan so, ana suman kaji..
Dariya ya sanya sosai yace " badai akan wannan ba, ai da bazan tab'a yafewa kaina ba, kai! ai har abada ma, ba'a haifi macen da zan zubar da hawaye na akanta ba Mima, d'anki jarumi me sai dai ayi kuka akanshi..
Dariya Mima tayi tana fad'in " hmm Allah yasa to...
********************
" Please Mima ki barni na kwana anan na yau kad'ai daga yau bazan sake kwana ba nayi alk'awari..
" Kullum haka kake cewa indai akan kwanan d'aki na ne baka martaba alk'awari kwata-kwata..
"Wannan karon zan cika miki alk'awarin ki in sha Allah...
"Dena ma wani marairaicewa kana langwab'ar dakai bazaka kwana ba, magana ta kenan yau..
Jikinshi sanye da riga da wondo na bacci marasa nauyi, while k'afarshi sanye da safa, sai Clogs shoes masu laushi,
yana tsaye bak'in k'ofa yana jinsu, yasan idan ba shiga yayi ba, ba lalle su gama yanzu ba, duk da yana da tabbacin sai Nadeem ya lallab'a Mima ya kwana a d'akin duk dad'ewar da zasuyi,
bakinshi d'auke da sallama ya shiga d'akin " yauwa grantor k'araso dama yanzu zan kira ka...
Bakin gadon ya zauna kusa da ita, fuskarshi d'auke da murmushi kamar yadda ya saba,
cikin nutsuwa ya d'ora hannayenshi saman k'afuwanta yana mammatsawa, " dama wancan lokacin kai kayi mishi grantor ko?
"Eh! yace a nutse, " yauwa to! ja shi ku tafi!.
"Kiyi hak'uri ki barshi ya kwana nayau kad'ai, bakiga yadda d'akinshi yayi k'ura ba, gobe da kaina zan saka a gyara mishi..
Nadeem ya tab'e baki kamar zayyi kuka had'i da langwab'ar da kanshi gefe, Mima ta kalli Nadeem tare cewa " wai haka ne?
Kai ya d'aga mata kana ya kwantar da kanshi saman kafad'arta, Ido ta rufe tare da nuna musu d'an yatsa tace " na yau kad'ai, gobe ka tabbatar an gyara d'akin kun ji ko?
"Naji! ya fad'a a shagwab'e yana sake shigewa jikinta..
Juyawa tayi ga Nadeer tayi mishi kallan tsanaki kafin tace " kai kuma ya maganar mu?
"A ina muka kwana?
Sarai ya gane inda maganar Mima ta dosa amma ya basar had'i nuna bai fahimci maganarta ba, " dakai fa nake Nadeer ko baka jina?
"Nace ya maganar mu, ko har yanzu lokacin ne bayyi ba?
Nadeem yayi caraf yace " Mima na manta ban sanar miki ba, Abbaah fa baya jin dad'i...
Kallan Nadeer d'in tayi tana san gano ko gaskiya Nadeem ya fad'a, tasan zai iyayin k'arya dan ya kub'utar da Nadeer, cikin ranta tace " ta ina ma zan gane shi kullum gashi nan kamar marar lafiya?
A zahiri kuma tace " meke damunka?
Nadeem yayi saurin cewa "Kanshi ke ciwo..
Shi kuma Nadeer yace "Zazzab'i....
Kallan juna Nadeer da Nadeem sukayi, while Mima ta tsare su da Ido cike da tuhuma..
"Ai dayake kin san dole idan mutum yana zazzab'i zayyi ciwon kai shine dama..
Kafin ta sake yin magana Nadeem yayi saurin mik'ewa had'i da cewa " muje na kaika d'akin ka, Nadeer ya mik'e yana dafe kanshi kamar gaske..
"Oh! ni Halimatu wai ni yaran dana haifa a cikina zasu yiwa wayo, idan yau kun zame min akwai gobe ai, daga Nadeem har Nadeer babu wanda yayi magana,
suna fita Nadeer ya sauke ajiyar zuciya had'i da cewa " nagode Nawa!
" Dan Allah ka samu kayi auren nan dan ita, kodan farin cikinta, wasu lokutan dole sai mun sadaukar da kanmu dan wad'anda muke tare dasu suyi farin ciki...
"Zanyi in sha, lokaci na nan zuwa, Nadeer ya fad'a a sanyaye...
" Har sai yaushe lokacin zaizo Mima nata jira?
Hannunshi Nadeer ya rik'e cikin nashi had'i da soma tafiya yace " ka sani ma ko lokacin yazo jiran Mima ya k'are, bazata sake dogon jira ba, daga yanzu in sha Allah..
Hannunshi da Nadeer ya rik'e ya zame had'i da tsayawa cak ya dena tafiya cike da mamaki baki bud'e ya juya yana kallan Nadeer Ido cikin Ido gami da ceww " wait wait Abbaah...
"Idan na fahimci maganarka.. dakatawa yayi yana kallan shi still baki bud'e, kai Nadeer ya d'aga mishi alamar eh...
"No! No! it's impossible... Nadeem ya fad'a cike da mamaki..
"It's not.. Nadeer ya bashi amsa fuskarshi d'auke da yalwataccen murmushi..
" Are you kidding me?
"You mean you're in Love..?
"Wow! Wow! Alhamdulillah Alhamdulillah Finally my Abbaah is in Love, yayi maganar yana cusa hannayenshi cikin sumar kanshi har lokacin bai bar mamaki ba...
Shi kam Nadeer baice komai ba illa murmushin dayake yi...
"Who's the luckiest girl in the world?
" Wacce me sa'ar ce?
" Gobe ka shirya zan nuna maka ita in sha Allah..
"Wow! I can't wait longer..
" Get ready shaaa
" And bance ka sanar da kowa ba, I want to surprise Mima..
"Tom ba matsala, bazan iya rik'ewa na lokaci mai tsayi ban sanar da Mima wannan babban albishir d'in ba..
" To Momy Son, ni dai bance a fad'a ba..
Ranar ko baccin kirki Nadeem bayyi ba, kwana yayi yana juyi saboda farin ciki..
K'arfe hud'u na yamma tayi musu a k'ofar Islamiyya, su uku suka jero suka fito kamar yadda ya saba, Nadeem na hango su gabanshi yayi razananniyar fad'uwa...
"Badai cikinsu Nadeeyah Abbaah yake san d'aya ba?
Ya fad'a cikin ranshi...
"Gata can itace Nawa, I love her, I really really love her Nadeem, ji nake kamar zan iya yak'ar duniya akanta, zan iya bada rayuwata da duk abinda na mallaka akanta...
Da k'arfi zuciyar Nadeem ta shiga dokawa da wani irin saurin da zai iya saka zuciyar tashi tsayawa, " har haka kake santa Abbaah...
Nadeem ya fad'a cikin sanyin da bai san yana dashi ba..
"Fiye da haka Nawa.....
JIDDARH...✍🏻