Shafi Na Biyu
by @sanazty
*A CIKIN IDO...*
_Ake tsawurya_
_Wattpad @SaNaz_deeyah_
_Arewapen@sanzty_
_Facebook@Habibtyn Habibi_
*_Heart touching love story🥰_*
*KARAMCI WRITERS ASSOCIATION*
_[karamci tushen mu'amula tagari]_
_Na sadaukar da littafin nan gaba ɗayanshi ga BEEBAH LUV Allah yayi mata rahama ya kuma kai haske kabarinta Amin.🙏_
_Shafi Na Biyu_
_____________Yana driving ita kuma ta kafeshi da idanunta, ko ƙiftawa bata yi.
_Ta ko ina ka haɗu Maheer, kyau, gayu, aji, da kuma kyakykyawar kamala, ina sonka Maheer amma na lura ba ta ni kake ba, zuciyata na sonka amma kai zuciyarka na ga wata, Maheer dan Allah ka fahimci saƙon zuciya, ka kalli ƙwayar idona za ka fahimci saƙonta._ Jin an dafa kafaɗarta ne ya saka tayi saurin dawowa cikin hayyacinta.
"Beautyn-beauty tunanin me kike haka?"
Ɗan ƙirƙiro murmushi tayi sannan ta ce "Ba komai, kawai dai..." Sai kuma tayi shiru.
"Ko dai ya ce zai zo ni kuma na É—aukoki?"
"Wa kenan?" Ta tambaya tana kallonsa.
"Na ƙarfen mana, Allah yasa ba cewa yayi zai zo ba"
"Kaga nifa ban son zolaya" Ta ƙarasa maganar tana turo baki.
"Am so sorry ba zan sake ba, nima ana yi min shagwaɓar nan ina ga..." Sai kuma yayi shiru ya guntse dariya yana fita daga mota.
"Ai da ka ƙarasa ko?"
"Ni a suwa."
Tare suka jera har cikin restaurant É—in, sai da suka samu seat da ya yi musu sannan suka zauna.
Service ne yazo ya tambayi abinda za a kawo musu.
"Coffee and Chips" Maheer ya furta sannan ya kalleta ya ce "And you?"
"Ayi min takeaway na masa ya isa, ba zanci anan ba"
"Oh! Sorry" Ya furta sannan ya kalli Waiter É—in ya ce "Ka kawo mata abinda za ka kawo min, Then ka saka masa ta 2k sannan ka saka 2plates of chips duka takeaway namu kuma ka kawo yanzu."
Yana tafiya ta kalleshi, za tayi magana kenan wayarshi ta fara ringing, kallon wayar ya yi yana murmushi ya kalleta ya ce "Mubina ce..."
Ɗan murmushin yaƙe tayi ba tare da ta ce komai ba, shi kuma ya ɗaga wayar.
"Babe...!" Ya faÉ—a yana murmushi idanunsa akan Amal.
"Oh am so sorry Babe kin ga Beauty ce ta riƙe ni, amma anjima zamuzo da yamma"
"Amal mana." Murmushi ya yi sannan ya ce "Babe rigima, to yanzu dai ayi min afuwa, idan munzo zamu ƙara bayar da haƙuri."
"Okay take care of your self"
"Bye-bye." Bata jin maganar Mubina É—in, sai amsoshin da yake bayarwa.
Yana gama wayar ya kalleta "Ya naga baki fara cin komai ba?" Ya furta yana kai duba da kan table É—in da aka dire abubuwan da sukayi order.
Murmushin yaƙe kawai take, a haka suka fara cin abubuwan ba tare da wani ya sake cewa komai ba.
"Beautyn-Beauty yaushe za ki je gaida Mommy?"
ĆŠan kallonshi tayi sannan ta ce "Duk lokacin da yayi maka"
"Okay yanzu"
Murmushi tayi tare da cewa "Yayi safiya gaskiya, kuma ma..." "Baza kije yau ba"
"Ba haka nake nufi ba"
"To ni dai yau nake so"
"Amma ba kace yau zamuje gidan su Mubina ba?"
"Oh hakane fa, okay to gobe sai kije ko?"
"Allah ya kaimu"
"Amin."
Yana ta cin abinci ita kuma tana kallonshi, bata wani ci da yawa ba, shima bai wani damu ba, a haka har suka gama suka tafi ya sauke ta a gida.
Tana shiga tsakar gidan ta ci karo da mutane gidan ana ta kiciniya, wasu na wanki, wasu na wanke-wanke yayinda wasu sun É—ora sanwar rana.
"Amal...!" Baba Baraka ta kira sunanta. A hankali ta juya ta kalleta. Ita kuma ta tsame hannayenta daga cikin ruwan wanki tana mai gogesu jikin zani.
Har inda take Amal ta ƙarasa tare da faɗin "Baba gani" Kallon ledojin hannunta tayi sannan ta ce "Wannan fa?"
Itama Amal sai da ta kalla sannan ta ce "Maheer ne ya kawo min"
"Yanzu ke Amal ba zakiyi wa kanki faÉ—a ba, mahaifiyarki na kwance amma ke kina naman lalata rayuwarki "
Umma Hadiza dake iza wuta ta ɗago idanunta da suke ta faman ruwa saboda hayaƙi ta ce "Dama kin daina wahalar da kanki a kan wannan kilakin"
Da sauri Amal ta juya ta kalleta "Kurwata kur, mai idon mayu" Ajiyar zuciya Amal É—in ta sauke.
"Kina ganin abubuwan da muke miki kamar tsana ce, amma ba haka bane, kina gani a gidan nan babu abinda ba'a sayarwa, tun daga kan kayan miya har zuwa su kayan cefane, sannan kuma ni kin ga bayan itace da nake sayarwa ga sana'ar wankau ina yi tare da ƴaƴana, amma ke Amal sai dai namiji ya ɗauke ki a mota kawai ya fita dake ya dawo dake da kaya niƙi-niƙi"
"Baba na rantse miki da Allah, Maheer bai taɓa riƙe hannuna da sunan iskanci ba"
"To amma wane namiji ne zai riƙa kashe miki kuɗi haka ba tare da wani abu ya shiga tsakaninku ba, kince kuma ba soyayya kuke ba, to mene amfanin zamanku tare, Amal ki riƙe mutuncinki ki kuma yi tunani, ƴan unguwa fa surutu suke tayi a kanki, kuma ɗazu Sule ya shigo nemanki, da ya sameki sai kin ɗanɗana kuɗarki."
Shiru Amal tayi ba tare da ta ce komai ba.
"Shikenan kije kawai" Baba Baraka ta faɗa tana ƙara kallon Amal.
A sanyaye Amal ta wuce, Umma Hadiza ta ƙara da faɗin "Bawa Amal shawara ai ɓata lokaci ne, kwanaki har sun fara sana'ar wankau suka daina, saboda son abin duniya."
Tana shiga É—aki kuwa bata tarar da kowa ba sai Mama dake kwance kan gado, tana bacci.
Cire mayafin jikinta tayi, tare da ajje ledojin hannunta, a sanyaye ta zauna gefen yaloluwar katifarsu.
_Maganar Baba Baraka gaskiya ce, dole mutane za su riƙa zargar wani abu a kanmu, ni na san ko ban faɗawa Maheer cewar ina son shi ba, to ya fuskanci hakan kawai dai baya sona ne shiyasa ya nuna kamar bai sani ba. Sannan Mama na kwance na jinya tsawon shekaru amma Maheer bai taɓa yunƙurin cewa zai kaita asibiti ba, sai dai dubiya da siyayyar kayan ciye-ciye._
Ta ɗaga wayar hannunta ta kalla sannan ta sake furta _Maheer ya san cewa ƙaramar waya ce a hannuna kuma duk taji jiki amma bai taɓa cewa zai sake min ba, wai shin mene matsayina a gurinshi? Ko dan ina talaka shiyasa baya taimaka mana, amma kuma akwai samari da dama da suke kyautatawa ƴan matansu ko dan ni ai ba budurwarsa bace._
Ajiyar zuciya ta sauke tare da faÉ—in "Na lura Maheer na daga cikin mazan da sai an tambayesu sannan suke yin alkhairi, ni kuma ina ganin hakan a matsayin zubar da mutumci"
Hannu ta saka ta goge guntun hawaye sannan ta É—aga hannuwanta sama.
"Ya ubangiji ka kawo mana ɗauki, ka bamu ikon samun kuɗin da zamu nemawa mahaifiyarmu lafiya ba tare da mun wulaƙanta ba."
"Amin ya rabbil alamin."
Juyawa tayi dan ganin mai maganar.
Rahina ce ta shigo É—akin tare da samun guri ta zauna.
"Daga ina haka?"
"Bayan kin fita sai ga É—an Aunty Murja yazo kiranki, shine naje na ce mata kin É—an fita ne, ta ce dama kitso take so zakiyi mata."
"Okay, bara anjima sai naje kafin yamma dai"
"Me aka kawo mana?" Rahina ta faÉ—a tana jan ledojin.
"Wow amma Yayana ya gano ni" Ta faÉ—a tana É—aukar masa tare da kaiwa baki.
Amal kallonta kawai take ba tare da ta ce komai ba.
"Ya naga kamar kina cikin damuwa ke da kika dawo daga gurin masoyinki"
Ɗan murmushin yaƙe tayi sannan ta ce "Rahina ya kamata na daina yaudarar kaina akan Maheer"
"Ban gane ba?"
"Rahina ni na gane cewa Maheer baya sona, meyasa bai taɓa cewa akai Mama asibiti ba? Kuma bai taɓa tambayana wane magunguna Mama take sha, ni na gane cewa shi ba mutum bane mai damuwa da damuwar wani kanshi kawai ya sani."
Tashi Rahina tayi ta cire hijab É—in jikinta sannan ta sake zama a gaban Amal ta ce "Na fahimci hakan nima, domin sai yayi sati yana zuwa gidan nan amma ba zai shigo ya duba Mama ba, sannan ya kamata ace ya taimaka mana da wani abu bawai yayi ta sayan kayan ciye-ciye ba.
Na kula yadda kika damu da Maheer shi bai damu dake ba, amma kuma daga baya na fuskanci kina sonshi ne sosai ba lallai ki gano aibunsa ba"
Ajiyar zuciya ta sauke tare da cewa "Amma Adda ina so ki masa uzuri kowa da irin halinsa, ta yuwu shi halinsa ne haka, shiyasa kika ji ina cewa ki tambayeshi, sai kuma kika ce ai mahaifiyarsa na da zafi, naga kuma idan ya É—auki abu ya baki ai bai zama lallai ta sani ba"
"Rahina tabbas ina son Maheer kuma ni idan ina da halin in taimakesa zan iya, amma kuma ba zan taɓa iya cewa Maheer ina sonshi ba ko kuma ince ya taimaki Mama, kowa fa ya san dai-dai ni dai ina fatan Allah ya kawo mana hanya, wallahi da ace kamar yadda nake gani ana auren contract a film inda anayi a gaske nima da nayi dan ceto rayuwar Mama"
"Ba damuwa, Allah ne ya saka mu a wannan hali, kuma shi ya yo mu a wannan gida na munafukai, Allah ya kawo mana mafita."
"Amin ya rabbi. Ki ci abincin bari kawai naje nayi mata kitson yanzu"
"Okay to sai kin dawo"
******
ĆŠaga kai ya yi ya kalli Faisal dake tsaye tare da cewa "Ka zauna ga guri"
Zama Faisal ya yi sannan ya kalli Maheer ya ce "Mun samu wannan contract ɗin, har ma Director ya riga ya yi signing, zuwa jibi muke so ka tsayar mana da meeting dan a fitar da ranar da za a fara aiki" Ya ƙarasa maganar yana miƙa masa file.
Karɓa ya yi ya buɗe ya duba tare da cewa "Ka kai Office ɗin Accountant da kuma Marketing manager suyi signing sannan ka dawo min dashi."
"To yallaɓai" Ya karɓa sannan ya fita ya bar office ɗin.
Turo ƙofar da aka yi aka shigo ya saka shi ɗaga ido ya kalli ƙofar.
Kyakykyawar mace, fara siririya ta ƙaraso cikin takun ƙasaita.
"Yallaɓai sannu da aiki" "Yauwa sannu."
Murmushi ta É—anyi, shi kuma ya cigaba da aiki a system dake gabansa.
"Am yallaɓai dama nazo na tayaka hira ne" Ta faɗa tana ɗan juya ido.
Ajiyar zuciya ya sauke tare da kallonta "Noor babu aiki a office É—inki?"
Ɗan haɗe laɓɓanta tayi sannan ta ce "Eh babu, duk aikin da ya kamata ace nayi na riga da har na gama"
"Okay so kin ga yanzu ni aiki nake, and ina so na bar office da wuri, idan ba zaki damu ba zamu iya yin hirar zuwa gobe ko?"
Ɗan ɓata rai tayi sannan ta ce "Okay" Juyawa tayi ta fita ba dan ranta ya so ba.
Sakatariya dake zaune, tana ganin fitowar Noor tayi dariya tare da faÉ—in "Naci bai yi ba."
Kallonta Noor tayi tare da yin ƙwafa ta wuce.
*******
Kallonta tayi a É—an tsorace sannan ta ce "Aunty Murja gaskiya ba zan iya ba"
"Amma banyi tunanin zaki ce ba zaki iya ba Amal, kwanaki fa naji kina faÉ—in kuÉ—in da kuka haÉ—a bai fi dubu É—ari biyu ba"
"Aunty wannan fa tamkar jefa kai a haÉ—ari ne"
"A'a kar kice haka, har kiyi ki gama ba wanda zai san kinyi, domin ba ma a ƙasar nan zaku zauna ba, zaku tafi Egypt acan za ayi komai har sai kin haihu zaki dawo"
Shiru Amal tayi na wani lokacin kafin ta ce "Amma Aunty taya ni da ban taɓa aure ba kuma zan ɗauki ciki?"
"Ba É—auka za kiyi ba, za a saka miki ne, kuma yanayin wata tara kina haihuwa shikenan, Amal million biyar za a baki kada kiyi wasa da damarki, kuÉ—in zaki yi amfani dasu ki nemawa mahaifiyarku lafiya har ma da saura kuja jari"
"Gaskiya zanyi shawara da Rahina"
"Idan kuma kika yi shawara da Rahina ai zance ya ɓaci, na san kin fita hankali shiyasa na nemeki kuma ma su kansu suna son abin ya zama sirri kar wanda ya sani daga ita sai mijinta sai ni, sai kuma ke da nake faɗawa maganar a yanzu"
Kanta ta sauke ƙasa ta lula duniyar tunani.
"Amal akwai mutane da dama da idan na faɗa musu zasu amince amma sai na zaɓeki saboda naga kuna cikin mawuyacin hala, wata tara kamar kwana tara ne kar ma ki tsaya saƙe-saƙe kawai ki amince"
Dafe goshinta tayi da hannu, ta É—ago kai ta kalli Murja.
_SaNaz Ce✌️_