WAYE SHI?{Behind the mask}

Chapter fourty nine: his last hug

by @autum17

𝑊𝐴𝑌𝐸 𝑆𝐻𝐼?(𝐵𝑒ℎ𝑖𝑛𝑑 𝑡ℎ𝑒 𝑚𝑎𝑠𝑘) 𝐵𝑦 𝐴𝑢𝑡𝑢𝑚𝑛 17

𝐶ℎ𝑎𝑝𝑡𝑒𝑟 𝑓𝑜𝑢𝑟𝑡𝑦 𝑛𝑖𝑛𝑒:𝐻𝑖𝑠 𝑙𝑎𝑠𝑡 ℎ𝑢𝑔

Ji Aliyu yayi komai ya tsaya masa cak, the noise was in back ground tuni ruhin sa yayi tafiya,tafiya mai nisa that perhaps ba zai dawo ba cuz it's too much... Me yasa bala'i ke ta afka masa ɗaya after the other? Ba gidan ne damuwarsa ba, memories ɗin dake gidan,his wife's last momento were turned to ashes tare da sauran abubuwan daya mallaka

'' Ya Allah '' Aliyu ya furta slowly yana yin baya baya kamar zai faɗi

Da sauri su Mahma dake rusar kuka sukayi saurin taro shi, mutanen dake ƙoƙarin kashe wutar wasu daga cikin su suka zo su ka ɗauki Aliyu suka zaunar dashi ƙarƙashin bishiyar that was a little away from their home

Su Mahmah zaune gefen sa,sai abun yayi kama da movie sune yan kallo

Dan zama sukayi suna kallon sauran neighbors ɗinsu da suma gidan su ya ƙone suna birgima suna ihu

Sai kuma gidajen su da suka ƙone ƙurmus,ga fire service sai aikin bada ruwa suke amma a banza, it turned out fuse ɗin ɗaya daga cikin gidajen ne yayi sparking, shine wuta ta kama, kasancewar unguwar masu kuɗi babu mutane da yawa ba'a ankara ba sai da abu yayi nisa,

Aliyu was more than heartbroken,he was shattered ji yake kamar wutar ba'a ginin take ci ba,but on his heart.

Mutane sai kai komo suke wasu sun taru a gefe suna kallo.

Babu abinda suka tsira dashi dukan su in Banda kayan jikin su. Jin yanda suke ta rera kuka especially Mahmah yasa Aliyu rungume su yana lallashin su duk da shima dai yana buƙatar hakan, daga ƙarshe bayan komai yaci ya cinye sai gani yayi ana kwasar neighbors ɗin nasa especially matan zuwa asibiti,sauke kansa Aliyu yayi, he didn't know what to do.....

Wasu daga cikin mutanen dake tsaye wurin ne suka iso inda Aliyu yake suna bashi haƙuri,Aliyu dai ya kasa cewa komai sai gyaɗa kai yake that's all he could do

'' toh yanzu ina zaka Mallam Aliyu?" Ɗaya daga cikin mutanen ya tambaya,Aliyu ya kalli su Mahma kafin ya kalli mutanen,bai san inda zai je '' Bansa niba nima'' inji Aliyu he's mind wandering,wani can daban yace '' Toh ko kana da gida a wannan unguwar?" Girgiza kansa Aliyu yayi sai kuma Yace '' Nawa ake renting gida a unguwar nan?" Kallon juna mutanen biyu sukayi kafin wanda ya fara magana da farko yace '' duk da ba anan nake da zama ba, aƙalla sai ka tanadi sama da miliyan goma Mallam Aliyu ko ba haka ba Mallam Sani?"

''Hakane Mallam halilu!" Inji Mallam Sani, Share fuskar sa Aliyu yayi, kuɗin dake hannun shi basu kai yawan abinda sukayi mentioning ba,what should he do? Aliyu ya shiga tsananin tashin hankali '' Amma akwai unguwar talakawa daidai idan kana so Mallam Aliyu '' Inji Mallam halilu, da sauri Aliyu ya jinjina kanshi yana zuba musu idanunsa da suka yi uban ja,'' Toh muje a nuna ma, dare na ƙara yi ''Slowly Aliyu ya miƙe,su Samha ma suka miƙe suna biye da mutanen Nan as they led the way, Abin hawa suka hau suka bar anguwar

Bayan tafiya mai ɗan karin nisa suka iso Kado kuchi, unguwar talakawa talak talak kallon ko ina su Mahmah suke they honestly don't like this place, Especially yanda ko ina yake so cramped Babu buɗaɗɗen filin da mutum zaibi ya wuce sai kanayi kana faɗawa gidan mutane wai kuma duk hanya ce.

Shima dai Aliyu unguwar batayi masa ba but yana da wani zaɓi? Sun yi tafiya mai tsawo,suna tafiya Su Mallam halilu na musu bayanin anguwar '' Akwai ɓarayi daya wa da yahoo boys a unguwar nan dole kubi a hankali musamman dakake da wa'yannan kyawawan yaran haka'' Shidai Aliyu jin su yake kawai,sai kuma ya ƙara damƙe hannun Mahmah da Samha cikin nashi jin abinta aka faɗa

Wani one room apartment suka iso luckily wannan gidan ya bambanta da sauran,wannan yana da tsakar gida, sannan zagaye yake da katanga unlike sauran gidajen da suke open spaces,mutum baida wani privacy 🔏

Duba cikin wurin Aliyu yayi, daki guda spacious enough to contain them su uku,duk da ba haka yaso ba, sai akwai wardrobe da gado shike nan, sai tsakar gida akwai toilet da kitchen shikenan

Gidan yayi ma Aliyu hakan yasa yayi payment Wa Mallam halilu dan dama gidan sane, it's a rent gidan kamar sabo

Sallama sukayi ma Aliyu suka tafi.

Dawowa cikin gidan Aliyu yayi ya same su tsaye jigum jigum, Suna ganin shi suka yo wurin shi da sauri,riƙe hannuwansu yayi leading them to seat on the bed

'' Kuyi haƙuri,abinda zan iya yi kenan we have to navigate I know it will be hard Amma insha Allah komai zai daidai ta,idan na samu kuɗi masu yawa zan ƙara gina muna babban gida'' said Aliyu,duk yanda yake ƙoƙarin kada hawaye su zubar masa sai da suka zubo,share masa hawayen sukayi hugging him ,They were all so miserable 😖

****"""

It took a while kafin suka saba da sabuwar rayuwar su,oh they learned to cope, cikin sauran kuɗin da suka rage ma Aliyu ya siya musu kayan sawa,dana abinci dana shafawa sannan yasa su islamiyya he can't play with that...

Daƙyar da suɗin goshi yasamu aka bashi hayar taxi so he became a taxi driver,sai yayi buga buga yake samun costumers

Aliyu ya canja ya zama wani abin tausayi kamar ba shi ba. Bala'in tausayi yake basu, amma alhamdulillah duk da bai samun da yawa they were at peace and contented ga shaƙuwa tsakanin su cuz Aliyu was very much taking care of them yana kaunar su baya son abinda zai taɓa su, suma kuma suna matuƙar ƙaunar baban nasu

Trouble Came knocking lokacin da Samha ta fara yan ciwuka,yau lafiya gobe ba lafiya ciwon ciki ciwon kai,da farko Aliyu ya ɗauka saboda sabon environment ne,cuz akwai sauro So maybe malaria ke damun ta hakan yasa yake siyo mata magani daga chemist, and it suppresses the illness na ɗan wani lokaci sai dai idan rashin lafiyar ya tashi dawo wa it comes back with ful swing,ganin Abu yaƙi ci yaƙi cinye wa gashi idan tayi tari sai ya dinga zuwa da jini yasa Aliyu ya kai ta wani private hospital Dan yasan government hospital ba dole su ɗauki abin serious ba,kuɗin test were very expensive a private hospital ɗin amma haka Aliyu ya biya, Test na farko aka gano tana da lung cancer final stage

Ji Aliyu yayi duniyar tana wani juya masa, lung cancer final stage? How ? Kuma babu wani symptoms daya nuna hakan in Banda tarin da tayi mai jini was it possible?

Dafe kanshi Aliyu yayi '' Hasbun Allah wani'imal wakeel'' Ina zai samu wa'yannan maƙodan kuɗin?

'' likita za'a iya suppressing ɗin rashin lafiyar further na ɗan wani lokaci har insamu kuɗin da za'a yi mata aiki?"Aliyu yayi tambayar his voice breaking,Jinjina kanshi likitan yayi yana kallon Aliyu da ya rame ya ƙanjame cike da tausayi sannan yace '' za'a iya amma it's very risky,sai dai idan tana shan maganin da za'a bata Insha Allah if she sticks to it hakan zai yi suppressing ɗin rashin lafiyar '' share hawayen shi Aliyu yayi yace '' nawane kuɗin maganin?" Kallon Aliyu Dr yayi kafin yace '' i will give it to you for free Dan gaskiya maganin akwai tsada, dubu ɗari biyar ne magungunan'' gumin da yaketoma Aliyu ya share ya zube akan guiwowin shi yana yima Dr godiya miƙar dashi Dr yayi leading him out of the office suka tafi ward ɗin Samha, she looked pale idon ta biyu tana kallon ceiling, tsayawa bakin window Aliyu yayi yana kallon ta, he felt weak '' kayi haƙuri' inji likitan,gyaɗa kanshi Aliyu yayi,in this life they have suffered enough. Barin shi wurin Dr yayi yaje ya kawo masa magungunan Samha yayi masa bayanin yanda zata sha.yana faɗin '' remember na ɗan wani lokaci ne kawai,kuma ko na rana guda kada ta tsallake maganin uhm?"

'' insha Allah '' Aliyu ya faɗa yana ƙara yima Dr godiya, shiga wurin Aliyu da Dr suka yi,kallon ƙofar Samha tayi ganin Aliyu ta miƙe zaune da ɗan ƙaramin murmushi a fuskar ta,her hair scattered over,tace '' mu tafi gida Pa, ban son wannan wurin it stinks'' Dariya Aliyu yayi dan baison taga hawayen shi ya zauna kusa da ita holding her close yace '' idan kina cewa asibitin Dr na wari zai maki Allura '' Turo baki Samha tayi ta kalli Dr da yake murmushi,yar hararar shi tayi tace '' Toh ai gaskiya ne ''ƙarasowa ciki de yayi da murmushi a fuskar shi,the girl is just so cute, batareda yace komai ba yayi examining ɗin ta,ya tambaye ta how she was feeling '' naji sauƙi pa, mutafi gida Mahmah na jira fa!" Tayi maganar tana sauka daga saman gadon,tayi inda hijabin ta,ta ɗauka tasa, Aliyu yabi ta da kallon tausayi, dawowa tayi ta riƙe hannun Aliyu trying to stand him up miƙewa Aliyu yayi,ya kalli Dr tare da faɗin '' a gafarce mu Dr '' jinjina kanshi Dr yayi fuskar shi ɗauke da murmushi Haryanzu yana cigaba da kallon Samha dake jan Aliyu har suka fita daga ward ɗin

Taji sauƙi sosai saboda Allurar da akayi mata when they arrived.

'' Pa,me yake damun Samha?" Mahma ta tambaya bayan sun gama cin abincin rana,ɗan pausing Aliyu yayi cuz he couldn't tell them what was wrong could he? Ya ƙirƙiri murmushin ƙarya yace '' malaria da typhoid'' tunani Mahmah ta shiga yi, is it possible to cough blood saboda mutum na da typhoid? Ko dai...

Aliyu ya katse tunanin ta ta hanyar faɗin '' zan tafi aikin sai na dawo "

''Allah ya kiyaye ya bada Sa'a,kazo mana da agwaluma" inji su biyun, involuntarily murmushi ya suɓuce ma Aliyu,a genuine one,fita yayi yana dariya...

Bayan tafiyar Aliyu gyara ko ina sukayi suka kwanta suna hira tsakanin su,ko tv basu da balle suyi kallo, kuma Aliyu ya hana su zuwa gidan maƙwabta. Kuma baza su je islamiyya ba cuz Samha bata da lafiya she needs a breathing space

*******

Rayuwar su ta cigaba da tafiya da daɗi da babu, Samha na cigaba da shan magungunan ta,duk in tayi tare sai hankalin Aliyu ya tashi,ga ko rabin kuɗin surgery ɗinta Bai samu ba,farin cikin shi ragagge ne due to this ga hawan jini da depression da yake battling silently. Allah ya taimakisa yana ɗan samun cinikin taxi ɗinsa

Their last moment together shine ranar da birthday ɗin su ya zagayo, Samha ta cika shekaru sha biyar,Mahma kuma sha takwas dan dama birthday ɗinsu ɗaya, Aliyu yana da kuɗi da yawa hakan yasa he decided to take them out suyi celebrating shima kuma ya samu ya ɗan declutter his mind.

Shiryawa sukayi cikin wasu dogayen riguna na Atamfa fitted,Mahma tayi packing gashin ta into a low pony tail,ita Samha ɗan kwalin ta ɗaura akai kawai dan bazata iya wahala ba, ɗan lip gloss suka shafa suka sa fararen hijabbai zuwa guiwa, they looked so breath taking, fitowa sukayi daga gidan suka rufe ƙofar, Aliyu was waiting for them outside cikin motar sa, Fitowa yay daga motar lokacin da ya hango suna zuwa,kafe su yayi da ido har suka iso wurin shi with a wide smile a fuskokinsu, hugging ɗinsu yayi one by one whispering 'ina ƙaunar ku' to which they replied the same.... Shiga sukayi Aliyu ya jasu, suka tafi,yawo yayi dasu sosai sun nishaɗan tu kafin ya kaisu monalisa Park,ya kaisu ShopRite,suka ci suka sha,their happiness knew no bound

But it was short lived,suna tsaka da shan ice cream wayar Aliyu tayi ringing his boss was asking him to return the taxi, Hankalin Aliyu ya tashi miƙewa yayi ya fita daga wurin yana cigaba da amsa kiran,bin bayan shi su Mahmah sukayi,bayan ya ajiye kiran ya kalle su yace '' ku jira Ni yanzu zan dawo'' yayi maganar tare da juyawa zai bar wurin riƙe hannun shi sukayi suna faɗin '' Pa,zamu bika" kyakkyawan murmushi Aliyu yayi, hugging them ɗaya bayan ɗaya one last time ya ƙara faɗin '' Kujirani anan ina zuwa '' badan sun so ba suka barshi ya tafi, bayan ya kusa fita wurin ya juyo yanay musu bye, the rays of the setting sun falling on him, wani irin nauyi ƙirjin su yayi musu, there's a *vague* feeling in there hearts though basu fahimci Meyasa suke jin hakan ba, kamar wuce Aliyu ya dawo.

Motar sa ya shiga yayi reverse ya fita daga wurin,ya tsallaka to the other side zooming off

Kallon juna sukayi,wuri suka samu a harabar wurin suka zauna,zasu jira Aliyu ya dawo su tafi gida kawai

Sunan zaune duk wata motar da ta wuce akan idon su dan dama ShopRite ɗin bakin titi ne, desperately suke jiran Aliyu,amma bai zoba sai wurin ƙarfe biyar da rabi,wani irin farin ciki suka ji ganin dawowarsa, Miƙewa sukayi suka isa bakin gate zasu fita,Aliyu dake ɗaya ɓangaren cikin motar sa yana jiran motoci su wuce kafin yayi crossing over yaji zuciyar sa ta bada Wani duum! Just like that. Shi kaɗai ne a lane ɗin shi, Yar addu'a yayi, shortly after motocin ɗayan side ɗin sunyi clearing Ahankali ya fara tuƙo motar sa, zuciyar sa na tsananin bugawa

Su Mahmah dake tsaye ɗayan ɓangaren nan da nan suka tuna incident ɗin Salamatu,wani irin anxiety buildup with in them,suna kallon motar Aliyu da tayi rabin titi tana tunkaro su,when suddenly wata ƙatuwar trailer tayi wurgi da motar Aliyu, rolling motar Aliyu ta fara har ta cimma sauran motacin causing a huge accident,sai petrol ɗin motar ya fashe at the far end kawai sai motocin suka kama da wuta suka ƙone ƙurmus

''PA NO!!!!" Mahma ta faɗa tana zubewa kan guiwowin ta,Hayaƙi ne ya fara tashi, while sauran motocin sai taka burki suke, kada suma su haɗu da same fate,amma saboda akwai motocin da basu ankara da abinda ke faruwa ba,ko motocin gaba sun taka burki,na bayan su da suka zo at full speed sai su tura su forward making the accident more ugly

Mahma ji tayi ta kasa numfashi Suma tayi a wurin, Samha ko kasa motsi tayi, idanun ta akan accident ɗin har yanzu kafin slowly tafara tari, Tana aman jini.....

Mutanen da suka taru a wurin suka ankara dasu wani mutum ya kwashe su ya wuce dasu Asibiti.

Wurin haɗarin kuwa tsabar hayaƙi the sky looked cloudy,none of the drivers survived harda Aliyu, Fire brigades aka kira suka zo suna ƙoƙarin kashe wutar it felt kamar suna ƙara ma wutar ƙarfi ne instead, mutane especially mata sai kuka suke wasu na video suna azawa a social media....