Chapter fifty: How they met
by @autum17
𝑊𝐴𝑌𝐸 𝑆𝐻𝐼?(𝐵𝑒ℎ𝑖𝑛𝑑 𝑡ℎ𝑒 𝑚𝑎𝑠𝑘)𝐵𝑦 𝐴𝑢𝑡𝑢𝑚𝑛 17
𝐶ℎ𝑎𝑝𝑡𝑒𝑟 𝑓𝑖𝑓𝑡𝑦: 𝐻𝑜𝑤 𝑡ℎ𝑒𝑦 𝑀𝑒𝑡....
AURA PRIVATE HOSPITAL.....
09:00am
Buɗe idanun ta da sukayi luhu luhu tayi tana kallon ceiling ɗin ɗakin, She felt paralyzed for a moment kafin komai ya shiga dawo mata tiryan tiryan,zabura tayi ta sauka daga kan gadon Gashin ta trailing behind her tayi kama da mahaukaciya at the same time aka buɗe ƙofar Dr ne ya shigo wata nurse biye dashi,Wani irin kallon Mahmah yake from head to toe yana lasar baki, especially yanda rigar ta kamata bringing out her shape
Wurin su tayi da gudu,da sauri nurse ɗin ta riƙe ta, sai struggling Mahmah take wanting to break free,'' ki barni in tafi,pa yace mu jira shi zai dawo mutafi gida pls let me go he must be waiting '' Mahma ta faɗa tana ƙoƙarin ƙwace kanta daga nurse ɗin'' kiyi haƙuri ki zauna pls " inji nurse ɗin helplessly,kuka Mahma ta fashe dashi tana turjewa, zuciyar tana mata wani irin raɗaɗi
Perhaps duk abinda ya faru mafalki ne kawai, maybe idan ta koma can wurin zata ga cewa komai wasa ne, komai mafalki ne, maybe zata ga pa smiling at her and he will hug her yet again....
Dr Nan ne ya ƙaraso wurin su ya riƙe Mahma yana ƙoƙarin sata jikin shi,ture shi tayi with tremendous force sai da ya faɗi, waro ido yayi jin yanda ɗuwawan shi suka daki ƙasa,itako nurse ɗinnan sai calming Mahmah take '' rungumeta Mahmah tayi tana Cigaba da risgar kuka cikin kuka tace '' Maam, it's all over yanzu mun zama marayu kenan? Pa yace mu jira shi zai dawo why didn't he return?" Sosai Mahmah ta ba nurse ɗinnan tausayi, ''it's okay '' nurse ɗin ta furta idanun ta na cikowa da hawaye ta tausaya musu sosai. Lokaci guda Mahma ta tuna da Samha,raba jikin su dana nurse ɗin tayi looking around '' Ina ƙanwa ta?"tayi maganar tana zaro idon ta da sukayi jaa,'' Tana I. C.U, kiyi sallah sai kizo in Kai ki!" Jinjina kanta Mahma tayi ta miƙe ta shiga toilet ɗin tayi Alwala tazo ta ɗauki hijabin ta da yayi datti tasa ta tada sallah, although in her mind tana tunanin me Samha keyi a Icu?
Drn miƙewa yayi yana dafe ƙugun shi ba karamar buguwa yayi ba,kallon nurse ɗin yayi yana faɗin '' Bring her to my office after wards Nurse habeebah''
'' okay sir'' nurse habeebah ta faɗa. Bayan Mahma tayi sallolin da ake Binta zama tayi wurin tana tuna duk abinda ya faru,kwantawa tayi tana sharɓar kuka kamar ranta zai fita, Nurse habeebah tazo tana yi mata nasiha, zuciyar Mahmah raɗaɗi take mata, ji take ina ma zata iya cire zuciyar ta ajiye a gefe.
Bayan ta tsagaita da kukan ta share hawayen ta duk da she didn't think zasu tsaya, '' Ina Samha?" Tashi Itama nurse habeebah tayi ta nufi ƙofa Mahma biye da ita,ICU suka tafi,tun kafin su shiga ta window ta hango Samha kwance saman gado ansa mata oxygen,mutumin da ya kawo sune ya biya kuɗin. Kallon nurse habeebah tayi tana neman ƙarin bayani as they stepped in, nurse habeebah bata ce komai ba,sai fita da tayi. Mahma ta ƙarasa kusa da Samha dake kwance rai hannun Allah wani Gwauron numfashi Mahmah tana, suddenly feeling kamar oxygen ɗin wurin wasn't enough, what is happening? Taya rayuwar su turned upside down in a moment? Slowly ta Isa bakin gadon Samha hannu na rawa ta kai ta riƙo na Samha that felt cold, itama Samha tawani irin zama pale kamar bata da jini
Ga life supporting machine ɗin da aka laƙa mata, hankalin Mahmah ya tashi '' Meya same ki Samha?" Ta faɗa in a barely audible voice. '' why are you like this? Samha kada ki barni pls,my heart can't bear it, wake up for me Samha '' Mahmah ta faɗa wani kuka na ƙwace mata yet again idanun ta har wani zafi zafi suke mata.
Tana nan sai ga wata nurse different from nurse habeebah tazo tayi leading ɗinta zuwa office ɗin likitan ɗazu
Izinin shigowa yayi musu kafin bayan wannan nurse ɗin tayi knocking, Shiga Mahmah tayi,wuri ya nuna mata a gaban table ɗin sa yace ya zauna,zama Mahmah tayi tana share Hawaye ɗauke idon shi yayi daga kallon ta yana lasar baki yace '' baku da wani elder family member ?" Girgiza kanta mahma tayi kafin tace '' We have lost our father,Ni da ita kaɗai ne'' gyaɗa kanshi yayi a ran shi yana faɗin ta kwana gidan sauƙi kenan '' I'm sorry for your loss M.s...?Slowly with a cracked voice mahma tace '' Aliyu '' jinjina kanshi Dr yayi yana jin daɗin Muryar ta. '' Me yake damun kan wata?" Ta tambaya without looking at him,shafa gemun sa yayi kafin slowly yace '' Condition ɗinta yayi worse sakamakon hayaƙin da ta shaƙa,da ace ta ƙara mintuna ba tare da ankawo ta asibiti ba she could have lost her life" duk wannan bayanin da yake mahma wasn't getting it,Meya ke damun samha ne? Dama tana da wani ciwo ne? Murya na rawa tace '' Me yake damun tane?" Yana kallon confusion ɗin dake fuskar ta,miƙewa yayi yazo ya tsaya bayan ta ya ɗan ranƙwafo yana faɗin ''Tana da lung cancer final stage, I'm sorry da baki sani ba and it got to this stage,tana buƙatar surgery da gaggawa '' yayi maganar yana ɗaura hannayen sa kan kafaɗar ta ya wani ƙwalalo ido yana lasar baki, just like a typical ɗan iska....
Mahma ko wani jiri taji yana kwasar ta, yaushe? Sheshsheƙar kuka ta fara hakan yasa ya fara bubbuga shoulders ɗinta his hands roaming on her shoulders da wani fake tausayi a fuskar sa '' How did this come to be?" Ya faɗa in a whisper, Gabaki ɗaya hankalin ta baya tare da ita. Tana kuka tace '' Nawa ne kuɗin surgery?" Ƙara tausar kafaɗar ta yayi yana faɗin '' 2 million '' wani irin zabura tayi ta mike daga saman kujerar in the process ta buge masa hanci Da baki da kanta, baya baya yayi yana dafe bakin shi Dammn shit!!! It hurts
It's bata ma sani ba,cuz a ruɗe take '' Ina zan samu wannan kuɗin....? WHO will help us...? Ya Allah...'' on and on she went.
Ya ɗauki lokaci wurin nayi masa zoge kafin ya sai ta kanshi ya miƙe yana jawo mahma wanting to take advantage of the situation, hannayen ta biyu ya riƙe suna facing juna, Slowly ta zuba almond eyes ɗinta cikin Kananan idanun sa da sukayi ja, and what a very set of ugly eyes he had... Mahma natsuwa tayi tana kallon shi, da wata yar iskar murya yace '' zan iya taimaka miki da kuɗin surgery in kin bani haɗin kai!" Yayi maganar yana lasar baki yana mata kallo from head to toe,Tuni ƙwaƙwalwar ta tafara taro mata abinda ya faru a China, shaking jikin ta ya fara ganin yanda yake ƙara kusanto da fuskar shi dab da Tata,girgiza kanta ta fara yi Hawaye nabin fuskar ta,he wasn't listening '' No'' ta furta in a whisper tana ƙoƙarin ƙwace kanta,ƙara riƙe ta yayi gam, her trauma kicked in her her adrenaline high and survival instincts?"No!!!!!" Ta faɗa da ƙarfi kafin da duk strength ɗinta ya ture shi faɗawa yayi saman table ɗin sa duk abubuwan dake saman table ɗin suka faɗi ƙasa... Rufe kunnuwanta tayi da hannayen ta,tana numfashi kamar zata shiɗe
Dr ɗin nan kuwa kasa tashi yayi dama akwai wata Allura saman table ɗin nashi and his butt landed on it..🤣
'' Damn shiiit!!! '' ya faɗa yana sauka daga saman table ɗin,yar ƙara yayi kafin ya miƙa hannu ya cire allurar da ta laƙe masa, it was painful..wurin mahma da ta gama ruɗewa ya ƙaraso a fusace yace '' Ke dan uwar ki matsiya ciyar dan kin samu za'a taima keki shine zaku yi ma mutane hauka ko? To Bari in gaya maki your sister if she doesn't get treated today mutuw...'' kafin ya idasa sentence ɗin da, mahma da ta rufe kunnuwanta ta miƙe idanun ta sunyi wani arnen ja,kamar zakanya tayi tsalle ta cafko wuyan shi, tazaro ido tana faɗin'' Idan ka ƙara faɗin ƙanwata zata mutu,i will cut your tongue and feed it to the dogs I swear'' tayi maganar tana ƙara damƙe masa wuya ta haɗa shi da table ɗin sa,idanun sa waje,har ya fara shinshino mutuwa when suddenly wasu nurses mata biyu suka shigo office ɗin,zubar da Files ɗin hannayen su sukayi suka iso suna ɓanɓare mahma that seemed to be out of her senses,da ƙyar suka cirota daga jikin Dr ɗinnan in the process suka yaga mata hijabi ya rabe gida biyu. Tana sakin shi ya faɗi wurin gasping for air yana matsawa baya, yana tari,ƙwace kanta tayi tafita daga office ɗin looking completely insane
Kan doctor sukayi suka tayashi miƙewa,kallon office ɗin sukayi it looked scattered ruwa ɗaya daga cikin nurses ɗin ta bashi ya karɓa gulping it down completely har yanzu bai dawo daidai ba dan ba ƙaramar shaƙa yaji ba.
Bayan ta fita daga office ɗin ward ɗin Samha ta koma looking at her for the last time,she can't imagine life without her she had lost more than enough. Share hawayen ta tayi ta nufi kofar baya ta asibitin ta fita, nan ta samu wani baƙin hijabi daya ga ruwa yaga duniya tasa,a little away ta hangi slippers sun ci sun cinye suma tasa sannan ta fita daga asibitin.
Tafiya take bata san inda zata ba,ta faɗi nan,ta tashi can, ta zauna nan tayi kuka,ta miƙe can ta cigaba da tafiya she wasn't sure ta ina zata fara neman miliyan biyu in one day ba,idan ta ga masallaci zata tsaya tayi Sallah before she carries on, bayan tayi sallar la'asar unknowingly ta ɗauki hanyar asokoro, tsohon gidan su ta tsaya tana kallo,har yanzu ba'a gina wurin ba,har yanzu the ruins were still there except yan gwan gwan sun kwashe roofs ɗin. Hawaye na Shatata kan fuskarta tabar wurin,inda Aliyu ya zauna ranar taje ta zauna,wani kuka ne ya ƙwace mata remembering how he hugged them ranar,"Papa!! Mama!!" Ta kira da ƙarfi and helplessly,ta daɗe tana kuka awurin kafin ta miƙe ta bar wurin ta cigaba da tafiya without knowing inda take sa ƙafa ba, kallon setting sun ɗin tayi zuciyar ta na mata wani irin zafi sai kuma ta kalli tall buildings ɗin anguwar there wasn't a single soul waje, cigaba da tafiya tayi.. ashe har ta hau kan titi ita bata sani ba ƙiiiii!! Kake ji saura kaɗan mota ta buge ta,it was Dr Ahmad
**""End of flash back""**
'' And that's how I met him,who in turn brought me into your life Amreesh " Salmah ta faɗa tana riƙe fuskar Amreesh that had an unreadable expression, duk wannan labarin da ta bashi,she made sure ta cire part ɗin da akayi abusing ɗin su to her it's not something Worth saying,wani irin tausayi yaji ta bashi tausayin da bai taɓa jin shi akan kowa ba, rungumeta yayi sosai ajikin sa, Slowly tace '' I can't lose you Amreesh, losing you will be an even bigger blow to me than all I have been through,kada ka barni ''tayi maganar hawaye wasu na bin wasu,'' I won't Mahee '' Amreesh ya faɗa kissing her hair,shima he had been through a lot but ba kamar su ba.
Jin saukar numfashin ta yayi alamun tayi bacci, kwantar da ita yayi,ya rufa mata blanket ya fita daga ɗakin.
Dr Ahmad ya gani tsaye a balcony hannun shi riƙe da coffee, Ƙarasowa wurin shi Amreesh yayi, sassanyan iskan brushing against his skin tsayawa yayi kusa da Dr Ahmad ya jingina da railing ɗin wurin '' You okay EMRYS?" Dr Ahmad ya faɗa sipping from his coffee,he rarely calls Amreesh da Emrys sai dai zakee,the two men stood in silence for 5 minutes kafin slowly Amreesh yace ''SEB, kana ganin idan tasan koni WAYE will she stay?" Amreesh ya faɗa with a distanced look a fuskar shi, murmushi Dr Ahmad yayi, mainly saboda Amreesh in za'a kaɗa a raya baya kiran sunan shi, neither Ahmad nor Sebastian sai dai yayi maganar shi kai tsaye yet he just called him Seb today? Yar ƙaramar dariya Dr Ahmad yayi,hakan yasa Amreesh ya juyo ya lalle shi ''Sorry'' ya faɗa yana ɗaga hannu sama in a surrender kind of way can yace '' ka damu ne?" Shiru Amreesh yayi yana ƙoƙarin sanin idan ya damu,after a while yace '' I don't know '' jinjina kanshi Ahmad yayi kafin ya juyo fully suna fuskantar juna yana kallon idon Amreesh yace '' Are You afraid of losing her?" Nan ma Wani shiru ya biyo baya kafin Amreesh yace '' taya zan sani?"
'' You love her?" Jinjina kanshi Amreesh yayi, eh yana son ta mana otherwise why would he stay with her?.
Bubbuga kafaɗar shi Ahmad yayi with a grin on his face yace '' Kada ka damu Romeo, Juliet bazata Barka ba"
'' You think so?" Amreesh ya tambaye duk da zuciyar sa doesn't think so, yacigaba da faɗin '' old man Zakee wants me to bring her na tabbatar can wani zai faɗa mata ina the most horrible way possible ''
''Da gaskiyar ka Zakee and that's why it's important kasamu lokaci ku zauna ka faɗa mata da kanka,komai ya biyo baya then You will handle it uhm?" Nodding Amreesh yayi,amma taya zai fara? Bai saba Magana ba taya zai fara? Zata yarda?
'' Go and sleep Zakee '' Dr Ahmad ya faɗa yana tura Amreesh forward, ɗan tsuke fuska Amreesh yayi yace '' stop pushin me Seb'' Dr Ahmad bai ji ba sai da ya kai shi har ƙofar ɗakin shi Sannan yace ''ka wani zo ka tsaya nan,while we are hoping to see babys bouncing,kaje ka rungumi matar ka pls''
'' Ɗan iska '' Amreesh ya faɗa yana shigewa ɗakin shi, dariya Dr Ahmad yayi kafin ya koma ya ɗauki coffee ɗin sa ya shige nasa ɗakin.
Hawa saman gadon Amreesh yayi ya ja blanket ya rufa pulling Mahma close, kallon fuskar ta yayi for seconds kafin slowly yayi pecking ɗin lips ɗinta,in a whisper yace '' I don't know if you will stay with me if you find out Mahee, but I don't want to let go..."