AMRAH

AMRAH PART 12

by @hussainyusuf

AMRAH

©Hussain Yusuf✍️

<<PART 12>>

Sai da dodannin nan suka yi wa Maigari da Gargaji lilis, suka farfasa musu jiki da bulalai, sannan Amrah ta ce su ƙyale su. Dishi-dishi Maigari ya rinƙa gani. Shi kuwa Gargaji, banda nishi, babu abin da yake yi. Gaba ɗaya ya fita daga cikin hayyacinsa, kamar ba shi ne wanda Maigari yake sakawa yana dukan mutane ba.

Nuni ta yi wa dodannin, take suka ɓace ɓat, kamar ba su taɓa wanzuwa a wajen ba. Ta kalli Maigari da Gargaji da suke kwance cikin wani yanayi, ta daka musu tsawa, ta ce, "Ku ɓace mini daga nan matsiyatan banza!"

Duk da tsananin zafin ciwon da suke ciki, hakan bai hana su tashi sun kwasa da gudu ba. Shi dai Maigari, Allah ne kawai ya kai shi gida, don ya jigata sosai.

Suna tafiya, Amrah ta ɓace ɓat, ba ta bayyana a ko'ina ba sai a ƙofar gidansu.

Tana shiga cikin gidan, ta tarar da Inna Ladidi tana yi wa Malam Buba ruwan ɗumi, yana nishi sama-sama. Inna Ladidi tana ganin Amrah, ta tashi tsaye da sauri, tana kallonta cikin mamaki. "Amrah! Ya aka yi kika kuɓuto daga hannun wancan azzalumin Boka Durwas?"

Amrah ta yi murmushi, ta ce, "Ai Inna bai isa ya iya yi min wani abun ba. Kawai dai na bi shi ne don na samu damar hallaka shi, kamar yadda na hallaka maigidansa Boka Rubbas."

Kallon Amrah Inna take yi, tana jin duk abin da take faɗa, amma sai ta ga bakinta ko motsi ba ya yi. Kuma muryar da take magana da ita, sam ba ta yi kama da muryarta ba.

Da Amrah ta ga Inna tana bin ta da kallon mamaki, sai ta ƙarasa kusa da Baffanta, ta tsugunna, ta riƙo hannayensa, tana kiran sunansa a hankali.

Buɗe idanuwansa ya yi, ya kalle ta. Nan take, murmushin ƙarfin hali ya bayyana a kan fuskarsa. Muryarsa can ƙasa ya ce, "Amratu, dama za ki dawo gare ni? Ya aka yi kika kuɓuta daga hannun azzalumi Boka Durwas?"

Amrah ta yi murmushi, ta ce, "Baffa, yanzu mu ƙyale wannan maganar. Lafiyarka ita ta fi damuna yanzu. Wallahi idan har ka rasa ranka, babu wanda zan ƙyale a garin nan! Sai na hallaka su gaba ɗaya, tun da suka yi maka wannan zaluncin don sun ga bana nan."

Malam Buba ya riƙo hannun Amrah ya riƙe sosai, ya ce, "Amrah, ki zama mai yafiya, kin ji ko?"

Girgiza kai ta yi, ta ce, "Baffa, ba zan iya yafe jininka ba! Ko Maigari da shi da Gargaji da suka yi maka wannan ɗanyen hukuncin, ban ƙyale su ba. Sai da na yi musu hukunci dai-dai da abin da suka yi maka. Don haka, idan har ka rasa ranka a dalilin wannan dukan da suka yi maka, to babu wanda zan bari a cikin garin nan sai na yi wa kowa hukunci dai-dai da abin da suka yi maka."

Baffa ya riƙo kanta, ya kawo saitin bakinsa zai faɗa mata wata magana, amma sai muryarsa ta sarƙe. Daga baya kuma, tari mai tsanani ya sarƙe shi. Nan take, jini ya fara zuba daga bakinsa da hancinsa.

Rungume shi Amrah da Inna suka yi, suna kiran sunansa, amma sai suka ji jikinsa ya yi sanyi ƙalau.

Amrah tana kwance a jikinsa tana kiran sunansa. Inna ta ɗago ta kalle shi. Nan take, ta rushe da kuka. Ta ɗago Amrah daga jikinsa ta ce, "Amrah, Baffanki ya tafi, sai dai haƙuri."

Amrah ba ta gane abin da Inna ta ce sosai ba, sai da ta ga ta ja mayafi ta rufe fuskarsa, sannan ta fahimci abin da yake faruwa. Ta taƙarkare, ta tsandara uban ihu wanda babu wanda bai ji ba a cikin ƙauyen. Mutane da suke cikin gida, kowane cikinsa ya ɗuri ruwa. Ga su dama Musulunci bai ishe su ba. Ƙalilan ne a cikin su suka iya karanto addu'ar neman tsari, ita ma ba irin wacce Allah da Annabi suka koyar da mu ba.

Nan take Amrah ta fice daga gidan da gudu. Inna tana kiranta, amma ko waigowa ba ta yi ba. Tana fitowa, ta fara rikiɗa zuwa wani ƙaton tsuntsu mai ɗauke da manyan fuka-fukai. Ta tashi sama fir, ba ta dira a ko'ina ba sai a kan wani tsauni mai tsayin gaske da ya zagaye ƙauyen. Tsawon shekaru masu yawa, babu mahaluƙin da ya taɓa hawa saman tsaunin sai yau da Amrah ta hau.

Mutanen ƙauyen gaba ɗaya suna hango ta daga cikin gidajensu. Nan take, ta fara magana da kakkausar murya wacce ko ƙarƙashin gado ka shiga, sai ka ji ta raɗau, kamar da loudspeaker take magana.

Gargaɗi ta hau yi wa mutanen ƙauyen a kan mutuwar Baffanta. Ba za ta bari ta tafi a banza ba, sai ta hallaka kowa na cikin ƙauyen, babu wanda za ta bari. Daga ƙarshe ta ce, tana umartar kowa yaro da babba, su fito wajen jana'izar Baffanta. Duk wanda bai zo ba, sai ta hukunta shi, ko waye.

Hussain Yusuf✍️