Chapter fifty six : The contact lenses
by @autum17
𝑊𝐴𝑌𝐸 𝑆𝐻𝐼?(𝐵𝑒ℎ𝑖𝑛𝑑 𝑡ℎ𝑒 𝑚𝑎𝑠𝑘)𝐵𝑦 𝐴𝑢𝑡𝑢𝑚𝑛 17
𝐶ℎ𝑎𝑝𝑡𝑒𝑟 𝑓𝑖𝑓𝑡𝑦 𝑠𝑖𝑥: 𝑇ℎ𝑒 𝑐𝑜𝑛𝑡𝑎𝑐𝑡 𝑙𝑒𝑛𝑠𝑒𝑠....
Dr Ahmad ya fara miƙewa bayan ya cire Samha daga jikin shi, Itama tashi tayi tana kakkaɓe jikin ta, batareda ta kalli koma wane ne ba tace '' Gaskiya wannan ƙaton jikin naka yayi min amfani...'' dakatawa tayi kafin ta juyo idanunta suka shige cikin nasa... Slightly foxy eyes ɗinta suka ƙara girma and she looked so temptingly beautiful, Matsawa baya tayi Dr Ahmad yacigaba da kallon ta,damn! Jiyaye fushin sa na ƙaruwa cuz meyasa bata sa hijabi ba? He felt so jealous,tsaki yaja kafin ya ƙara taku biyu ya riƙe kunnen ta yace '' ke meyasa baki ji eh? Ina hijabin ki?" Samha ta ƙwalalo ido tana tsalle tsalle saboda yanda take jin zafi, ɗaura hannunta tayi saman nasa tana faɗin '' Wayyo kunnena yi haƙuri ba zan ƙara ba'' tayi maganar a shagwaɓe tana Turo baki, sakin ta Ahmad yayi yana ja baya,yanda tayi maganar it was making him feel weird ɗan ƙaramin tsaki ya sake ja yana kallon Samha da take murza kunnenta, tana kumbure kumbure, Cire lab coat ɗinsa yayi, ya matsa kusa da Ita, dakatawa tayi daga abinda take her chest hammering lokacin da idon su ya haɗu, Yar harara yayi mata kafin ya sa mata kan coat ɗin ya rufe har gashin ta yana cusa sauran da aya leƙo cikin lab coat ɗin fuska ba walwala,samun kanta tayi da ƙare masa kallo zuciyar tana gaba tana baya, His masculine scent invading her nose ga wani butter flies dake fluttering acikin ta, duk da jikin su bai haɗu ba tana iya jin ɗumin jikin sa and that made her take jin kamar ana mata tafiyar tsutsa a jiki numfashin sa felt ticklish against her skin, ƙasa tayi da idon ta, it fell on his muscular chest dake fitar da wani daddaɗan ƙamshi me tsuma zuciya, she stared at his red lips instantly taji maƙoshin ta ya bushe, tafara kallon shi with dreamy eyes lumshe idon ta tayi tana turo bakin ta gaba,as if asking for a kiss hannayen ta biyu dafe da ƙirjin sa, '' what's wrong my lady?" Dr Ahmad daya ji saukar hannun ta a ƙirjin sa ya faɗa tare da ɗage gira,her eyes flew open ji Samha tayi kamar an watsa mata ruwan sanyi she felt so embarrassed Ashe imagination ne ba dagaske ba, Matsawa baya tayi da sauri fuskar ta kamar zatayi kuka she just embarrassed her self gaban shi! Cije leɓenta na ƙasa tayi feeling so frustrated yaushe ma tafara tunani irin haka? Can taja tsaki, Ahmad ya zuba hannayen sa cikin aljihu yana kallon yanda take behaving weirdly.... His eyes reading her reaction, juyawa yayi ya tafiyar shi with a smirk on his face.... '
'' Ni dai ba yar Iska bace ehe!" Tayi maganar tana murguɗa baki, juyowa Dr Ahmad yayi ya kashe mata ido ɗaya, his mood was elevated duk fushin da ya kwaso har ya tafi. Zaro ido Samha tayi ta ƙara ɓata fuska yaji Abinda ta faɗa and yaga abinda tayi kenan? Ina! Dole taje tayi clearing ɗin komai wallahi it's not what he thinks....
*********
Zaune take tana jujjuya littafin tama kasa karantawa, Amreesh take so tagani gaban ta kawai, tashi tayi ta shiga ɗakin Samha ta ɗauko wayar ta tashiga tiktok tana kallo to pass time.
*****Ladies room*****
'' shegun yaran kun gansu kuwa? Kamar wasu masu taɓi hankali!" Azeezah ta faɗa masu Saudat tundaga farkon abinda ya faru a kitchen da yanda su Salmah sukayi faɗa and how Amreesh came. Sultana taja tsaki tana faɗin '' ai in sun san wata basu san wata ba zakuma su gane!" Jinjina kansu sauran sukayi agreeing with sultana, maraƙisiyya dai tayi shiru batacewa komai yet akwai abinda take shiryawa
Miƙewa tayi ta doshi hanyar fita tana faɗin '' da kansu zasu fita daga gidan nan,worry not" daga haka tasa kai ta fice su kuwa sauran suka cigaba da ƙulle ƙullen su
******Dining*****
Yau kowa ya hallara banda Amreesh da Salmah, Amreesh bai dawo ba, Salmah na ɗaki taƙi fitowa, Samha ce kawai a wurin bawai Dan tana jin yunwa ba she was officially here to seek trouble, zaune take kusa da Ahmad tasa wani ƙaramin hijabi rabin guiwa, Ahmad ya sauke ajiyar zuciya ganin ta a hakan, he was relieved khaleel yana zuba ido yaga Salmah amma bai ganta ba, Sultana da Azeezah sai hararar Samha suke yet she didn't care, Maraƙisiyya ta zauna Kamar wata Queen with a smug look on her face jin yanda ake korowa su uncles ɗin su duk abinda ya faru a kitchen,duka laifin aka basu Samha,she was sure korar su za'ayi, Dr Ahmad ya juyo yana kallon Samha be was shocked meyasa bata faɗa masa ba?kallon Samha su Uncle T suke like what the hell? Daga zuwan su har an fara samun matsala? '' they have to leave!" Uncle Naseer ya faɗa da rinqnnun idanunsa yana dukar table ɗin, Matarsa ta goyi bayan sa kafin sauran mutanen wurin suma suka goyi bayan su, Samha was so calm yo ita akwai wani abu dazai tada mata hankali pls?
'' we don't accept tyrants in this house,babu yanda za'ayi mu zura ido azo anay ma yayan mu ta'addanci no way!"
'' ƙwarai kuwa Naseeru, maganar ka haka yake!" Uncle T ya faɗa yana ma Samha wani mugun kallo, Ahmad was a bit tensed su Azeezah ko sai daɗi suke ji, Samha data gama cin abinci ta goge bakin ta ta miƙe with a smile tana kallon Uncle Naseer tace '' pls waye ɗan ta'adda for clearity?" Every body paused suna kallon Samha har da Ahmad,itafa Samha baza'ayi mata baƙa ta yi shiru ba ahto!
'' Ke dan baki da tar..."
'' Aish....I hate hearing same thing Banda tarbiyya Banda tarbiyya...come on say something I ain't heard before'' Samha ta faɗa tana wani jujjuya ido, Hajiya Maleeka ta ɗauki kofin shayi tana kurɓa tana kallon Samha something swirling in her eyes '' My Lady '' Ahmad ya kira gently '' wait a second '' Samha ta faɗa sannan ta cigaba da balbale su da masifa duk sai suka nemi bakunan su suka rasa '' we're not so helpless dazu ku taka mu yanda kuka ga dama, If you think you're going to bully us kuma muyi shiru then you're utterly wrong...kuma Ni man da ya zube mata ai bakomai bane tunda her skin didn't peel, Dan wallahi da nice da ko ganuwa bazatayi ba! Kai ni fa a duniyar rabbi to fight is my favorite,idan naga ana jana faɗa wani irin thrill nake ji har cikin ƙahon zuciya ta wallahi..." Samha ta faɗa tana dariya Ahmad was more than surprised da abinda Samha ta faɗa, suko sai zaro ido suke..'' You're sick..'' Azeezah ta faɗa a fusace murmushi mai kyau Samha tayi tana faɗin '' Exactly! Ashe kin gane point ɗin,zan iya illata mutum without a second thought so ku kama kanku Uhm,in kunne yaji jiki ya tsira!" Tana gama faɗar haka ta bar wurin skipping on the stairs tabar su da sakin baki, Shima Ahmad ya tashi ya bar wurin, while su Uncle Naseer felt so speechless da ɗaya bayan ɗaya suka bar dining kowa zuciya cike da ƙunci....
Samha na tsaka da tafiya Ahmad ya finciko ta ta faɗo faffaɗan ƙirjin sa, Idanun ta cikin nasa ,riƙe hannun ta yayi ya jata zuwa ɗakin sa, rufe ƙofar yayi ya juyo yana kallon ta his face expressionless,Ji Samha tayi cikin ta ya bada ƙuuu haka kawai Matsawa baya ta shiga yi shi kuma yana matso ta, fuskar sa ba wasa,'' m..mm..meye haka?'' ta faɗa muryar ta na rawa duk da tayi ƙoƙarin ganin tayi maganar normally...'' What's with the speech in the dining?" Ya faɗa da wani irin husky voice daidai suna Dangane wa da bango, '' ohhh..'' Samha ta faɗa da mamaki,sai kuma tayi dariya ta taɓe baki tare da faɗin '' kawai ina faɗa musu gaskiya ne''
'' cikin rashin kunya?" Ahmad countered, slowly ta ɗago foxy eyes ɗinta staring right at him tace '' Does it hurt here!?" Tayi maganar tana tura ƙirjinsa daidai saitin zuciyar sa da yatsanta tana ɗage gira, lumshe idon sa Ahmad yayi baice komai ba, The atmosphere was a bit tensed yanda suka tsurawa juna ido, it could amount to something dangerous....abunda su biyun basu shirya ma ba, Ɗauke idon ta samha tayi tana faɗin '' forget it'' daga haka tayi nufin barin wurin ƙara jawo ta Ahmad yayi his hand on her waist,She froze!
Idon Ahmad tar akanta,his eyes darkening with a deep voice yace '' Answer me!" Yawu Samha ta haɗiye suddenly taji wani irin sanyi da zafi suna tarammata, She felt apprehensive,motsa bakin ta tafara wanting to answer yet nothing came out... Idanun ta sai yawo suke every where, shima Ahmad he knew he was gambling with something he shouldn't...tun farko ma bai kamata su kasance anan ba,the way they're! Yet he couldn't help it, he knows duk sanda yayi having any form of body contact da Samha it never ends well yet....tana Turo baki tace '' Toh ba su suka fara ba,kuma nidai baza'a dinga cutamin ba ina ji inyi shiru...'' ta ƙarashe maganar tana yi mashi wani irin kallo, Dum! Ji Dr Ahmad yayi yana neman losing control, da sauri ya saki Samha idanun shi na Lumshewa ya matsa baya, He was speechless...like yana da abubuwan da zai faɗa yet it seemed impossible.. he'd rather ya kama kan sa, Samha tayi ƙasa da kanta tana wasa da yatsun ta, lazily yaje ya zauna bakin gado yace '' sun girme ki respect them for that..'' gyaɗa kanta samha tayi ta ɗan kalleshi,gani tayi ya mata kamar mara lafiya matsowa tayi kusa dashi ta dafa goshin sa '' baka da lafiya?" Sake lumshe sleepy eyes ɗinsa yayi,ya cire hannun ta daga goshin sa '' I'm fine,ki Dena taɓani" yayi maganar agajarce kafin ya kwanta ƙafafunsa ƙasa Hannayen sa bayan kanshi,ya rufe idanun sa, she needs to go... taɓe baki Samha tayi tana ɗan hararar shi, '' bari in kawo maka magani '' tafiya ta farayi,har ta Kawo bakin ƙofa idon ta ya hango wani hoto maƙale a bango, Matsawa tayi wurin tana kallo da kyau, wasu yan mata ne guda biyu turawa kyawawa dasu,daga ganin su yan biyu ne, saye suke da kayan yan Nigeria, Ɗaya da Emerald eyes ɗaya kuma da Ido irin na Amreesh... '' wannan me emerald eyes,is my mom wannan kuma maman Zakee '' Samha taji muryar Dr Ahmad a bayan ta, ɗan juyowa tayi their eyes met,da sauri ta ɗauke idon ta tamayar a hoton tana dariya tace '' suna da kyau Masha Allah,ina suke?'' Samha ta tambaya tana kallon Ahmad,yaɗan ƙara matsowa bayan ta amma akwai distance tsakani slowly yace '' My mom lives in Britain,maman Amreesh ta rasu..." Yayi maganar quietly da wani ciwo a zuciyar sa, '' Allah ya jiƙan ta'' Samha ta faɗa itama tana tuna yanda mota tayi sama da maman su...'' Toh kai meyasa idanun ka ba irin nata bane?" Dawo da idon shi yayi kan Samha dake kallon shi tana jiran Amsar shi, Yawu ya haɗiye yana kame kame yace '' Melanin my lady,Our Melanin differed'' ganin tana gyada kanta meaning she's convinced ya sauke ɓoyayyar ajiyar zuciya..karɓar hoton yayi ya mayar itama sai ta tafi ɗauko maganin.
Bayan fitar Samha Ahmad ya tsaya gaban madubi yana kallon kanshi... musamman idon shi, ƙara waro idon sa yayi before using his hand to take off the brown contact lenses...sai ga ainahin kalar idon sa ta bayyana,it was Emerald Green,kalar idon shi Emerald green ne, ba brown ba!
Yana da contact lenses NE Saboda wani condition dayake dashi da ake kira (vireye syndrome) Wani kalar condition be da idan green colored lights ko haske me yawa in some cases koda hasken wata ne ko globe ya daki idon mutum sai mutum ya zama overwhelmed,ko yaji yana jin amai,ko yana jin jiri or things like that, brown lenses ɗin suna taimaka masa sosai, har yanzu yana yin magani kuma sooner or later zai cire wannan fake lenses ɗin,aduk sanda yake saye da wannan lenses ɗin jinsa yake kamar wani mutum daban da kanshi,he had been trying so hard to navigate...Amma yana so ya zama kanshi...je wants to be him! Da sauri ya mayar da lenses ɗin jin harya fara jin jiri, Ya sauke ajiyar zuciya
Kayan jikin sa ya cire ya ɗaura towel zai shiga bayi yaji jiri na kwasar sa, dage kansa yayi ya kwanta bakin gado kamar ɗazu ƙafafun sa ƙasa hannayen sana tallafo kansa ya lumshe idon sa jin suna masa zogi...
Samha ta shigo hannunta ɗauke da maganin ajiye wa tayi gaban madubi tayo kan Dr Ahmad,sai da ta iso dab dashi taga ashe Babu kaya ajikin sa, ƙwalalo ido tayi her breath caught in her lungs, his madly hot body making her feel tingling sensation all over.. girgiza kanta tayi as if trying to get the thoughts out of her head, Matsawa tayi kusa dashi ta ɗan ranƙwafo ta kanshi ya ɗaura hannunta saman goshin sa, Ahmad da baisan da shigowar taba dan ya ɗauka bazata dawo ba ya buɗe rinannun idonsa ya zube su akanta..faɗuwa gaban Samha tayi,arazane zata matsa baya kafar ta ta zame tayi kansa... They both froze....!