Pagem-39
*FASAHA WRITER'S ASSOCIATION*
(*F.W.A)*©✍️
⭐⭐⭐
Ƙungiya masu aiki cikin salon hikima da fasaha gurin juya tunanin al-umma, kaifin alƙalumansu ya zarta takobi ©✍
___________________________________________________
بسم الله الرحمن الرحيم.
اللهم صلي وسلم على نبينا محمد.
❁ 𝐒𝐀𝐍𝐀𝐃𝐈𝐍 Ƙ𝐀𝐃𝐃𝐀𝐑𝐀𝐓𝐀 ❁
Free book📓
By: _*🌹𝑍𝑎ℎ𝑟𝑎-𝑡𝑢𝑙-𝑄𝑎𝑙𝑎𝑚🖋️*_
Page3️⃣9️⃣
HALIMA.
Tun bayan da ta suma ba ta farka ba sai can kusan asuba, shi ɗin ma ciwon da ya fi na jiya ne ya ta da ta, sosai cikinta ya ke murɗawa, hatta gaɓɓan jikinta ji ta ke yi yana amsawa, gashi babu kowa bare ta samu mai taimakonta, kwantawa ta yi tana ta juyi da ihu tana faɗin, "wayyo Allahna! Wayyo Allahna, cikina! bayana, jikina!" iya abun da ta iya furtawa kenan, tun tana fitar da ihu har ta kasa fitarwa, sosai ta ke jin ciwon da take da tabbacin maganin da S man ya ce ya sanya mata ne. Anan Halima ta kuma wani sumewan ba tare da ta san ina kanta ya ke ba.
Can ta fara jin ana watsa mata ruwa, sannan saman fiskarta ana ta surutu, nannauyun idanuwanta da su ka kuma zama na wahala ta samu damar buɗesu, sauke su ta yi akan mutanen da ke tsaye kanta, suna furta, ta farka, da ƙyar Halima ta samu damar zama tana kallonsu bibbiyu saboda idanuwanta ba sa tsayawa daidai, wani daga cikin mutanen ya ce, "baiwar Allah daga ina? Me ya ke damunki?".
"Yunwa, ku taimaka min da abinci, ruwa, ƙishi na ke ji" ta faɗi da murya mai fitar da numfashi, daga jiya zuwa yau ta rame sosai, kamanninta har ya fara sauyawa, kallonta kawai mutane ke yi, daga cikinsu wani mai tausayi ya je ya kawo mata abinci cikin mintuna da ruwa, babu ɓata lokaci ta fara afawa cikinta da gaggawa.
Mutane dai tafiya su ka yi su ka ƙyaleta, kafin Halima ta ƙarashe ci cikinta ya fara juyawa, a dole ta ijje abincin ta ɗaura hannunta akai ta fara kuka kamar ƙaramar yarinya, akwatinta ma ba ta san ina ya yi ba, ƙila ansamu mara tausayi ya yi mata wuff da su. Haka Halima ta yi ta bulayi akan titi wasu har su nai mata kallon mara hankali, ta sake ramewa ta gama fita hayyacinta, ga cikinta idan ya tashin mata ciwo ji ta ke kamar za ta mutu.
Kuma baya tashin mata sai lokacin da babu mutane kusa da ita bare su taimaka mata, ba ta da kuɗi bare ta koma Adamawa gurin Innarta, haka ta ke ta gallafiri babu mafaka, duk wanda ta roƙa kuɗi sai su koreta a tuninsu mahaukaciya ce, gwara abinci takan samu.
Halima na zaune gefen hanya, ɗazu cikinta ya gama murɗa mata wanda ta ke da tabbacin kila wannan gubar da S man ya sanya mata shine ajalinta, haƙiƙa S man ya cuceta, ya ha'inceta, ko da a mafarki ba ta taɓa tsammatan S man zai yi mata haka ba, amma sai gashi a zahiriyya komai ya faru da ita, "kaico na, kaico na ni Halima, wace iriyar mutum ce ni, na yi dana sanin duk abun da na yi a rayuwa, ya Allah ka yafe min, kasa kafin na mutu in haɗu da wa'yanda na ma laifi, ya ubangina na tuba, wallahi na yi nadama, ya Allah ka kawo min sauƙi"
Ta faɗi da muryar da ke rauni tare da fitar da zafafan hawaye masu tsuma zuciya, saboda à yanzu ba ma ta da ƙarfin kukan, ta kuma cewa, "dubi rayuwar da na ke ciki a yanzu, kenan haka Nuriyyah ma ta sha wahala bayan mun koreta? Ina ki ke Nuriyyah?" Ta faɗi tana ɗago hoton da ke hannunta duk ya ji jiki shima, amma har a yanzu bai ɓata fiskar ba, kallon hoton ta ke yi tana sake zubar da hawaye.
NURIYYAH.
Kafin na baro kallon titi maganaina su ka hango min wata mata daga nesa, yadda ta ke tafiya yasa zuciyata ta sanar da ni ba lafiya ba, ina iya hangan yadda yanayinta ya ke, babbar mata ce domin kuwa za ta kai Maman Wasila à shekaru, da ƙyar ta ke tafiya sannan ga shi tana dosan kan titi, kamar dai ba ta san ina ta ke takawa ba.
Da sauri na miƙe zuciyata na tsinkewa, daidai lokacin da mai ice cream ya miƙowa, su Asma'u su ka sa hannu. "Asmee ina zuwa!" Na faɗi cikin gaggawa hankali a tashe na nufi wannan matar da gudu domin na ga kusantar titin ta ke ƙara yi. Su Asma'u da mamaki su ka bini da kallo yadda na ke gudu, da tunanin ina zani?......
Halima ɗaga idonta da za ta yi ta hango wasu 'yan mata tsaye gurin wani shago, ga hannunsu riƙe da abu mai kama da ice cream, da sauri ta miƙe saboda tunanin da ya zo mata na ƙila idan ta roƙesu kuɗi su ba ta, girinsu ta nufa tana tafiya da ƙyar, domin kuwa gaba ɗaya jikinta ba ƙarfi.....
A cikin wannan gudun da na ke yi ban ankara ba kasancewar burina kawai inje intaimaki matar nan, kawai na yi karo da wata wacche ban san ko wace ba, faɗi ta yi ƙasa tana sakin ƙara wanda muryarta ba fitowa sosai ya yi ba, wani abu da ke hannunta mai kama da hoto ya faɗi ƙasa, da sauri na juya ina kallonta sai dai kanta a ƙasa ya ke ban ga fiskarta ba, "don Allah ki yi haƙuri", na faɗi ina ƙoƙarin sa hannu don in ɗagata, duk da na ga alamunta kamar ba mai cikakken hankali ba, kasancewar yadda kayan jikinta ya ke, duk ƙura da kuma datti......
Halima bayan bangajeta da aka yi ta faɗi da ƙarfi ta saki ƙara, muryar haƙurin da aka ba ta sai da ya sa gabanta ya faɗi, ta shiga fitar da numfashi sosai, duk da ba ta gama gane mai muryar ba,a hankali ta ke juyowa bayanta, amma ko da ta juyo ba ta samu wacche ta bangaje tan ba, samu damar tashi ta yi ta hau waige-waige amma ba ta iya gane komai ba.
Ɗaukar hoton da ya faɗi kawai ta yi tana kallon Nuriyyah da ke jiki, sannan ta cigaba da tafiya zuwa gurin 'yan matan nan.........
Kafin na ƙarasa kai hannuna jikinta na juya sai na ga wancan matar har yanzu tafiya ta ke yi yayinda ababen hawa sai wuceta su ke yi, wani har yana ɗaga mata hannu da masifa, sai dai da alamu ba ta ma san yana yi ba. Hakan da na kuma gani ne ya hanani ɗaga wacche na ture na kuma sa gudu lokacin wani babban mota ya yo ta kan matar. Hankalina ya tashi sosai!.
Cikin ikon Allah na samu damar janyeta da matsanancin sauri, saura kaɗan mu faɗi ƙasa hankalin mutane ya dawo kanmu, take su ka fara maganganu da godewa Allah don ba a rasa rai ba.......
Asma'u da Wasila da su ka miƙe har Asma'u na cewa su bi don ganin me yasa ni gudun nan haka? amma sai Wasila ta ce ta san ba abanza na yi hakan ba, mu jira kaɗan zan dawo, inyaso sai su ji me dalili?.
Suna a haka sai ga Halima ta iso dama su ɗin ne ta gani. Ji su ka yi kawai wata ta durƙusa a gabansu ta fara jero musu roƙo, maganarta da ƙyar ya ke fita, Halima ta dubesu idanuwanta na zubar da ruwa ta ce, "bayin Allah wallahi ni ba mahaukaciya ba ce, na san za ku yi tunanin haka, don Allah ina roƙonku ku taimaka min da kuɗin mota don in koma garinmu, tuntuni na ke ta roƙan mutane amma kallon mara hankali su ke min, don Allah ku taimaka min, ba na neman abinci a gareki kawai kuɗin mota na ke nema".
Kallon Halima kawai Asma'u da Wasila su ke yi, tausayinta ya shigesu ƙwarai, da ganinta tana da buƙatar taimako, "na rantse da Allah ni ba mahaukaciya ba ce ku taimakeni" Halima ta kuma faɗi saboda tana gudun kada suma su koreta kamar yadda wasu su ka yi mata. Asma'u ta numfasa ta ce, "kwantar da hankalinki baiwar Allah, mun yarda kina da hankalinki, miƙe to".
Miƙewa Halima ta yi kamar yadda aka ce mata, Wasila ta ce, ",mun ji buƙatarki, amma a gaskiya ba mu da kuɗi a wurinmu ki yi haƙuri" murmushin dole Halima ta samu damar yi, shikenan ba ta samu a wurin wa'yan nan ba, godiya ta yi musu ta juya za ta tafi, Asma'u ta tsaidata, ta juyo ta kalli Wasila ta ce, "ina ga mu ɗau cikin kuɗin sister mu ba ta, na san ko da tana nan za ta yi hakan, kuma za ta yi farin ciki idan mu ka taimaki wani da kuɗinta".
Girgiza kai Wasila ta yi sannan su ka tambayi Halima nawa ne zai isheta, daga ƙarshe dai su ka miƙa mata dubu goma a cikin kuɗin, godiya ta yi musu sosai ta miƙa hannu, ayayin amsan kuɗin hoton Nuriyyah da ke ya zame ƙasa. Har ta kuma juyawa za ta wuce Wasila ta tambayeta ya sunanta? "Sunana Halima" ta faɗi da farin ciki ta bar gurinsu, da a baya ne aka tambayeta, idan ma wanda ya kamata ta amsawa ne ce masa za ta yi Hali sunanta.
NURIYYAH.
Samun gurin zama na yi na ijje matar nan da ta ke ta sauke numfarfashi tana riƙe min hannu, a hankali ta buɗe idonta tana dubana, "sannu Madam, kina lafiya? Sannu kin ji, bari insamo miki ruwa" na faɗi ina yin butik ɗin kusa da gurin, roƙonsa na yi da ya bani ruwan, ina buƙatarsa da gaggawa, amma mai shago ya ce inaa shi fa ba zai ba ni ba sai na miƙa kuɗi, gashi ni kuma na bar jakata a gurinsu Asma'u.
Na rasa ya zan yi kuma matar nan tana da buƙata, agogon hannuna da dubana ya kai kansa na yi saurin cirewa, na miƙa masa na ce ya karɓa ya ijjiye sai ya bani ruwan, inyaso idan na dawo masa da kuɗinsa sai ya mayar min. Sai da ya duba sosai da ya gane agogo ne mai kyau sai ya yarda, ya miƙo min ruwan gora mara sanyi.
Da gudu na koma inda Madam ta ke, na buɗe na ba ta, sai da ta sha sosai sannan ta miƙo min, na amsa na rufe ina sake jera mata sannu cikin kulawa, murmushi ta yi min tana furta, "na gode yarinya, kin ceceni yau da sai dai ake yin wani labarin daban yanzu, na gode sosai" nima murmushi nai mata na ce, "mun gode Allah da ba abun da ya faru Madam, amma me ya ke faruwa da ki ke cikin wannan yanayin haka?".
Kafin ta amsa min sai ga wani mutum yazo da sauri, yana faɗin, "madam ki gafarceni don Allah, cunkoso aka samu agurin abun hawa, ga waya Alhaji ƙarami yana son magana da ke" cewar mutumin wanda da alamu drivernta ne, sa wayar da ta karɓa ta yi a kunne da sallama, daga can gefen muryar saurayi mai sanyi yana faɗin, "Ummi sai da na ce ba na son zuwa saloon ɗin nan, a kawo miki mai yi ta zo har gida ta yi miki, amma ki ka ƙi yarda kuma kin san ba cikakken lafiya gareki ba, me yasa za ki fita ban sani ba? Don Allah ki dawo gida kada wani abu ya sameki, you know I can’t endure it".
"Na san ban yi daidai ba, amma yau Saura kaɗan ka rasani ɗana" faɗin Madam da aka kira da Ummi à waya, cikin tashin hankali daga wayar aka ce, "Ummi me ya faru?!" Ya faɗi da alama ma a zaune ya ke amma jin abun da ta ce sai da ya miƙe. Cikin kwantar da hankali ta ce, "kar ka ɗaga min hankalinka ɗana, wata 'yata anan ta ceceni, ka bari idan na dawo zan sanar da kai abun da ya faru" ba don hankalinsa ya kwanta ba ya ce, "ok Ummi ki kula da kanki".
Miƙawa drivernta waya ta yi, sannan ta juyo ta dubeni da fara'a ta ce, "ya sunanki yarinya?" "Nuriyyah ne sunana Madam" na amsa mata, "akaro na biyu ina sake yi miki godiya mara iyaka Nuriyyah, Allah ya albarkaci rayuwarki" da ameen na amsa sannan na taimaka mata zuwa mota, shiga ta yi tana ɗaga min hannu, nima hannun na ɗaga mata motar ta wuce.
Sauke ƙaramar numfashi na yi ina murmusawa sannan na koma inda su Asma'u su ke. Tambayana su ka yi me ya faru na bar wurin cikin gaggawa haka? Shine na sanar da su abun da ya wakana, haɗi da zama akan kujera, mai ice cream ya samun nawa cikin roba kamar dai su Asma'u, ina sha Asma'u ta ke sanar da ni cewa, wata ta zo neman taimako sun ba ta dubu goma cikin kuɗina, murmushi na yi na ce da su, "hakan da ku ka yi ya dace sosai, Allah ya bada lada" na faɗi ina rataya jakata a kafaɗa.
A sannan idona ya kuma kallon wani hoto da ke kife a ƙasa, hannu na sa zan ɗauka don ganin hoton menene? Asma'u ta rigani ɗauka ta ce, ''wannan fa kamar na Halimar nan ne, saboda na ga hoto a hannunta" ta faɗi tana kallonsa, "kai wannan ta so yin kama da ke Nuriyyah" cewar Asma'u, Wasila ma ta gani ta ce, ",Allah kuwa" "ingani?" Na faɗi ina miƙa hannu, sanya hoton Asma'u ta yi akan tafin hannuna, ni kuma da na cika da mamaki jin suna ta cewa wai na yi kama da mai hoton, na ɗaga shi don na tabbatar.
Gabana ya faɗi zuciyata ya yi sauti, da sauri na ijje ice cream ɗin da ke hannuna ina ƙurawa hoton ido, cikin rawar baki na ce, "wannan!... wannan ai hotona ne. Ni ce a kai!" na faɗi ina kallonsu Asma'u da su ma su ka yi mamaki, haɗe ba ki gurin faɗin, "hotonki kuma?!" "Eh... eh ni ce wallahi! Asma'u wacece wacche ta zo ɗin?" Na faɗi da son jin ƙarin bayani.
Wasila ta ce, "dama ba saninta mu ka yi ba ta dai ce sunanta Halima", "Halima?!" Na faɗi ina miƙewa, suma miƙewan su ka yi suna ɗaga min kai, sake tambayarsu na yi wani kalar kaya ne take sanye da su? Sannan ta ina ta bi?. Sake zare ido na yi sosai domin yadda su ka suffanta min ita ta yi kama da wacche na yi karo da ita ɗazu. Kenan Halima ce ban sani ba? "Ku jirani ina zuwa" na kuma faɗi ina wuce. Su kuwa kallon juna su ka mamakin kan fiskarsu bai gushe ba.
Ni kam tafiya na yi ina ta waige-waige kar dai Halimar Inna Jummai, idan ba haka ba waye zai kasance da hotona na shekaru à baya? Zuciyata na ta bugawa sosai ina ta dubawa, har na iso gurin da na tsaya da Madam ɗazu. Dakatawa na yi da tafiyar ina sauke numfashi saboda na gaji, cigaba da rarraba idanu na ke ta yi ko zan ganta, "ina ki ke Halima? Kina ina ne? Me ya faru da ke da har ki ke neman taimako?" Na yi maganar daga cikin raina ina rinte ido.
Ina tsaye a haka sai ga Halima na tahowa ta inda na ke amma ta bayana, idanuwanta na fitar da hawaye da ya zame mata abinci yanzu, ba ta samu mashin ɗin da zai kaita tasha ba, gashi ciwon jikinta na neman dawowa.
Iska ya fara kaɗawa à hankali, wanda yanayin ke ratsa zuciyata gami da fargaba, kamar abun da na ke nema yana bayana, hakan yasa na fara juyawa don inga abun da ya ke faruwa......
Last page
___________________________________________________
Halima dai tana ganin halalar rayuwa, gashi ta samu kuɗin mota, wanda kuma na Nuriyyah ce ba ta sani ba, sun bangaji juna amma ba su ga juna ba. Kuna ganin zasu haɗu? Ga dai Halima bayan Nuriyyah. Wacece matar da Nuriyyah ta ceta?
Mu kasance da ku a next page don jin me zai faru gaba?
_*🌹𝑍𝑎ℎ𝑟𝑎-𝑡𝑢𝑙-𝑄𝑎𝑙𝑎𝑚🖋️*_