WAYE SHI?{Behind the mask}

Chapter seventy one: Save me..!

by @autum17

WAYE SHI?( Behind the mask) By Autumn 17 🍁🍁

Chapter seventy one: Save me!....

Over the next few days abubuwa tsakanin Salmah da Amreesh deteriorated ko kaɗan bata zuwa inda yake aduk sanda taga yazo wuri sai tabar wurin jiki na rawa tsoron shi duk ya cika ta ji take kamar the next second sai dai ta farka ta ganta barzahu, Amreesh da yayi noticing hakan ba ƙaramin Abu ya tokare masa maƙoshi ba kenan an samu wani munafikin ya hure mata kunne, kallo guda idan kayi ma Amreesh zaka san baida lafiya he looked much more pale than usual sannan yaɗan rame... Mariya da tayi noticing abinda ke faruwa tsakanin Amreesh da Salmah was more than happy,her motive? Undefined! Musamman ranar da Amreesh ya kira Salmah ta saki ihu harda suma kowa aka zo aka taru wondering what happened, Amreesh bai kalli kowa cikin su ba ya ɗauke ta ya wuce ɗaki da ita, when she opened her eyes and saw him close to her ta sake kurma ihu tana roƙon kada ya cutar da ita...He was hurt,he was pained kawai sai ya tashi ya bar ɗakin... Koda ya dawo bata nan, kwantawa yayi ya ja blanket ya rufe har fuskar shi saboda wani azababben ciwon da yake ji a duk gaɓɓan jikin shi! And it went on every night

Tsakanin Samha da Ahmad kuma ita ma wasan ɓuya take da shi batasan meyasa ba,ada batasan wane irin kallo take masa ba, amma yanzu kallon namiji take masa a fully grown up man Wanda take tsananin so da ƙauna...but there's something..itama kuma batasan mey shi ba but it just doesn't allow her to go close,ko ido bata iya haɗawa dashi and idan suna magana sai ta fara ina ina,she feels so shy around him ada duk bata jin wannan....

Dr Ahmad noticed how distant they have grown..a wani gefen yana jin badaɗi cuz he had looked for her for the past 5yrs and he'd just found her kuma zai so su zauna tare yet they are distant..on the other hand yana ganin hakan daidai cuz yanzu abubuwa aren't the same and she looked shy and uncomfortable around...this means her feelings for him have grown stronger...

****** Hajiya Maleeka***

Zaune take a gefen gado saye da wasu baƙaƙen kaya irin na tsafi ko ina dakin duhu ba haske kokaɗan ta riƙe wani sarƙa silver colored tana juya shi a hannun ta,ɗayan hannun kuma riƙe da wani abun surƙulle, murmushi tayi kafin tayi chanting wasu maganganu ta jefa abun yayi sama kafin ya zama kamar tv... Amreesh ne ya bayyana ya dafe kanshi trying so hard to remember abinda ya faru in the past 25yrs ya dafe kanshi dake sarawa kamar zai tsage sosai,a wannan abun da yakeyi There are only to possibilities ko dai ya tuna abinda ya farun ya shiga coma ko kuma yayi losing ɗin memories ɗinsa gaba ɗaya and he could die.because you can't force yourself to remember what you were made to forget.using hypnosis 😵‍💫.. Murmushin mugunta Hajiya Maleeka tayi ta Kuma taɓe baki tana wani karkatar da kai tace '' Try as hard as you could Emrys...matsawar Ina raye...You won't remember!" Daga haka ta sake chanting ɗin wani surƙullen Muryar ta ta canja da wata ƙatuwar murya ta kira '' EMRYS.....!!!!" Amreesh dake ɗakin shi ya ɗago idon shi yana kallon straight ahead ita kuma a wurin Hajiya Maleeka directly ita yake kallo,sarƙar hannun ta ta ɗago placing it above his eyes ta fara swinging ɗin sarƙar side by side,idanun Amreesh nabin sarƙar idon shi suka juye 😵‍💫, after a while ta fara '' kai ne silar abinda ya faru a wannan daren..daga yau You won't try to remember abinda ya faru kaji!" Gyaɗa kanshi Amreesh yayi don ba a hayyacin shi yake ba,'' Sleep!! '' ta sake bashi order,Jan blanket ɗin Amreesh yayi ya rufe kanshi ya kwanta,at this point yayi kama da mutum mutumi don controlling ɗinsa take kawai.....

The next day Salmah bata ga Amreesh a dining ba hankalin ta ya tashi cuz over the past few days taga yanda ya rame,he had lost the glow on his face ya zama more isolated and lonely more aloof and cold ɗakin shi ta shiga bata ganshi ba ta fito looking so sad, yaushe ne ma? Ba ita tace zata zauna dashi ba in any condition? Me yasa take gudun shi yanzu? Was her love fake? Cikin garden ta shiga tana kuka kamar ranta zai fita,miƙo mata ruwa yayi daga bayan ta yana faɗin '' Crying isn't the solution...naga yanda kike gudun ZAKEE over the past few days ba daidai bane,ba lallai ya faɗa maki ba but i can see how much he loves you and you suddenly treating him like this isn't fair...kina wahalar dashi knowingly or unknowingly...'' Juyowa tayi tana kallon Dr Ahmad baki buɗe she didn't know what to say..ƙasa tayi da idon ta,ajiye ruwan yayi ya juya yana faɗin '' make it right..don't push him into further isolation..'' daga haka ya fita daga wurin..zama Salmah tayi tana juya maganar Ahmad acikin ranta...what should she do? Abinda aka faɗa mata fa? Should she just... fashewa tayi da kuka tana dafe goshin ta '' ya Allah '' ta furta desperately not knowing what to do,bata tashi daga wurin ba sai da ta yanke hukuncin abinda zatayi next!

01:00am

Saye take da kayan bacci a pink nightgown da hular saƙa,her cleavage exposed, miƙewa tayi tasa slippers ta fara tafiya slowly kamar ɓarauniya ta nufi hanya '' leaving without a good bye?" Samha ta faɗa suddenly juyowa Salma tayi their eyes met,ƙasa tayi da nata tace '' i have to...ban kyauta da abinda nayi ma Amreesh ba,I broke my promise...I said...'' da sauri Samha tazo ta rufe bakin Salmah '' i understand Mahma and I'm honestly proud of you da kika ajiye tsoron ki gefe kika fuskanci reality!" Hawaye suka zubo daga gefen ido Samha ta share tace '' Hey don't cry..I got you okay?" Jinjina kanta Salmah tayi kafin ta rungume Samha then she left a ɗar ɗar Samha closed the door behind...

Tura ƙofar ɗakin Amreesh tayi ta shiga zuciyar tana ɗarɗar..ganin ɗakin take kamar wurin yan mafiya already her imagination was going wild, hawaye na wanke fuskar ta,ta isa gaban gadon tana leƙa fuskar Amreesh,buɗe idon shi yayi suddenly, zuciyar ta tayi wani uban tsalle kamar zata fito ta baki tayi baya baya ta faɗi, fashewa tayi da kuka Ganin Amreesh ya tashi zaune, pausing Amreesh yayi yana kallon ta with his sick eyes yanda take Matsawa da baya jikin tana matuƙar rawa she looked frightened by him kamar shi dodo ne, Salmah kuwa addu'a kawai take cikin ranta tana matsawa baya ganin Amreesh ya miƙe coming close to her... Sunkuyo wa yayi daidai tsawon ta amma akwai space tsakanin su,ta wani takure heart beating at a wild phase... Bayan kusan minti biyar a haka Amreesh yace '' do you think I'm a monster?" His voice deeper and quieter fiye da kullum, Salmah ta ɗago idonta ta kalleshi,duk da duhun ɗakin suna iya ganin juna saboda hasken dake fitowa daga A'c she could see how pale he looked maganar ma daƙyar yayi ta, sauke idon ta tayi tana ƙara takurewa her lips moving but she couldn't find the words '' I'm not what they told you Mahee... I'm not a monster...you're hurting me by being scared of me..'' ya faɗa tare da stretching hannun sa ya taɓa ta,ta saki kuka me ƙarfi pressing ɗin lips ɗinsa yayi together yana cigaba da kallon ta his heart aching '' zan iya sauwaƙe maki..I can divorce you idan baki so ki cigaba da zama dani..'' Amreesh ya faɗa wani irin ɗaci na mamaye zuciyar sa har zuwa bakin sa...the words were so bitter in his mouth.. Salmah ta wani ɗago da sauri jin abinda ya faɗa miƙewa Amreesh yayi yana tafiya slowly his heart burning and itching... Har ya kwanta saman gadon yaja ya rufa da blanket

Salmah tayi shiru kalaman shi na maimaituwa a kunnen ta,if he divorces her...No! Bazata taɓa iya rayuwa ba Amreesh ba! She might be scared of him,but she's unwilling to leave him! Ko da take faɗawa Samha su bar gidan cikin fitar hayyaci ne kawai she can't do that!

Miƙewa tayi zuciya cike da tsananin fargaba ta hau gadon ta kwanta bayan Amreesh hugging his waist...jin hannun ta da kuma ɗumin jikinta a nasa yasa ya buɗe idon sa da suke a lumshe kafin slowly ya juyo suna kallon juna runtse idonta Salmah tayi jin ya juyo her body was shaking incessantly Amreesh ya lura da hakan so he kissed her forehead tareda ɗaura hannun shi a waist ɗin ta pulling her closer cikin Muryar rashin lafiya yace '' Bazan taɓa cutar dake ba Mahee...and as long as I live Bazan bari wani ya cutar dake ba!" Slowly ta fara buɗe idon ta kafin ta kalli fuskar shi their gaze met..she saw sincerity a fuskar shi, ya cigaba da faɗin'' You mean the whole world to me,you staying away from me shattered my heart into pieces Mahee...kada ki ƙarayin hakan...Ni ba mugun mutum bane!" Amreesh ya faɗa sounding so vulnerable so sincere,wasu round of tears suka fara bin fuskar ta cuz ta gane cewa she was wrong to have trusted abinda Mariya ta faɗa mata from the beginning batareda tayi bincike ba she was so foolish!" I'm so sorry Reesh!''she voiced out murya na rawa hannun ta gliding on his face tayi nadama, '' I'm happy you're back to me,never leave me again pls'' Amreesh pleaded, jinjina kanta tayi,ya share mata hawaye his hand feeling softer and warmer... Suna kallon juna eyes burning with flame of passion ƙasa tayi da kanta claiming his lips,a passionate kiss was shared between them...

*****

The next day Salmah da Amreesh suka yi zaunen su ciki, Samha ce ta kawo masu break fast tana yima Amreesh ya jiki tana hararar shi ta gefen ido...tsuke fuska Amreesh yayi tareda faɗin '' nadai ji sauƙi ehe.. ya san ranki?" Samha ta saki baki tana kallon shi,yanda yake magana kamar dama farin ciki take rashin lafiyar shi ƙwafa tayi kafin ta juya ta fita, Salmah dake zaune tana serving ɗin abincin da Samha ta kawo ta girgiza kanta, Matsowa Amreesh yayi ya rungume ta closing his eyes words can't describe how happy and relieved he felt to have her back....

Karo sukaci da Ahmad lokacin da ta buɗe ƙofar zata fita daga part ɗin,da sauri tayi saurin Matsawa baya ido waje suna kallon juna cikin ido,da sauri tayi ƙasa da idon ta her heart begun marathons her stomach fluttered with butter flies Ahmad ya kafeta da ido yana ƙare mata kallo daga sama har ƙasa wai yanzu wannan itace ta ceceshi five years ago kuma yake ta neman ta just to find her under his roof!

Juyawa Samha tayi da sauri ta wuce ɗakin ta without turning back ciki ya ƙarasa wurin su Amreesh when he was giving the permission to enter yashiga

Da rana tareda sauran family members ɗin suka ci abinci, mariya couldn't help but notice sabuwar soyayya da kulawar da Salmah ke ba Amreesh,ba ita kaɗai ba har da sauran mutanen wurin ma suka su da suka san idan tana cin abinci Amreesh comes barin wurin take at 380, maraƙisiyya har takai lomar abinci taji lomar ta laƙe taƙi wucewa saboda tsananin shock itako mariya ko motsi ta kasa wasn't her plan a success? What happened now?

Kallon kallo aka shigayi yet no one spoke, Azeezah ce ta hangi yanda Ahmad ke whispering Abu a kunnen Samha dake zaune kusa dashi and she was blushing har fuskar ta tayi ja,wani irin baƙin ciki taji ya soki zuciyar ta,ƙasa tayi da idon ta abincin ya fita daga ranta gaba ɗaya... Har aka ci aka cinye basu dena mamakin sudden change ɗin da aka samu tsakanin Salmah da Amreesh ba...

Da daddare bayan Salmah ta dawo da plates ɗin da Amreesh ya ci abinci dasu ta wanke zata fita Mariya ta sha gaban ta looking so furious '' me kike yi da Haryanzu baki bar gidan nan ba? Ke ma kina so ki mutune kamar sauran?" Girgiza kanta Salmah tayi looking so innocent tace '' I figured that...we might not really meet the same fate, kowa da tashi ƙaddara Bazan iya barin mijina ba ko da ace zai ke dinga yanka na yana ci everyday!" Wani irin Banzan kallo Mariya kema Salmah tana ji kamar ta shaƙota, Salmah kuwa murmushi ne a fuskar ta,ta wani ƙwalalo ido tana kallon Mariya...'' ke wai ke mayyace eh? Why can't you just leave? Idan kuɗi kike so...''

'' ba kuɗi nake so ba!" Salmah ta katse ta,'' Toh me kike so eh? Faɗa min!" Mariya ta faɗa a harzuƙe '' Amreesh nake so!"

'' faɗi farashin soyayyar ki!" Mariya fired,Yar ƙaramar dariya Salmah tayi kafin ta kalli mariya ido cikin ido tace '' You Can't Buy My Love!" Salmah ta faɗa spelling each word and meaning it...'' kuma na gano some useless elements kawai suke son shiga tsakani na da miji na,i can't risk it..'' Salmah ta cigaba with a wink 😉 in the end, mariya tayi sakake tana kallon Salma wai itace useless elements? Tayo kan Salmah a harzuƙe zata mareta kaucewa Salma tayi sai ga mariya tui aƙasa dariya sosai Salmah tayi kafin ta gudu daga kitchen ɗin tabar mariya zaune a wurin

Ɗakin su ta nufa tana Cigaba da dariya but guess what? Khaleel was waiting for her... murmushin gefen baki tayi..she was tired of being the victim.... Approaching ɗinta ya farayi ta tsaya wuri guda...ganin hakan yasa yayi dariya yana jin daɗi don yau yazo da shirin shi,she won't out smart him...wata zalɓeɓiyar bulala ya fito da yana wulwula ta akan Salmah with a smirk on his face idan tayi taurin kai tasha kashi... Salmah kuwa ta cigaba da kallon shi da nutsuwa yana kawo wa Wurin ta ya tsaya yana kallon ta first kafin ya tsuke fuska yana faɗin '' wuce muje..'' kallon hanyar da yake nuna mata tayi kafin slowly ta dawo da idon ta akan fuskar shi '' idan naƙi fa?" Ta tambaya tana ɗage gira, confidence ɗinta ya tsorata shi kawai sai ya shilla bulalar wanting to beat her, kaucewa Salmah tayi,kafin tayi cikin shi giving him a high kick on the jaw ya saki ƙara yana dafe haɓarsa tareda sakin bulalar,sharɓe shi Salmah tayi kanshi ya daki ƙasa,wani ihun ya sake kurma wa,da duk iya ƙarfin ta,ta ishi ishi ta zabga masa bulalar sai ga fitsari shaaa! Yana sakin ihun azaba dariya Salmah tayi crouching down to his height tace '' Too bad...your tricks are just as weak as you...next time kayi ƙoƙarin taɓani or coming in my way...I will break you into pieces inyi packaging and send it to your mom!!" Tayi maganar cike da gargaɗi kafin ta ƙara masa wani round of bulala sai ihu yake yana shille shille saboda zafi salmah na dariya ta bar wurin,jin ihun khaleel yasa mutanen gida zuwa to his rescue Nan suka ganshi kwance cikin fitsari yana risgar kuka every body was confused antamabaye shi me ya faru dashi he refused to say dole suka ɗauke shi suka kai estate clinic...

Dariyar dake fuskar Salmah froze lokacin data ga Amreesh kneeling on the ground hannun shi dafe da zuciyar shi yana aman jini his whole body was shaking fararen kayan jikin shi duk sun ɓaci da jini,abinda ya faru shine bayan Salmah ta tafi kitchen ya zauna shikaɗai kalaman Hajiya maleeka echoing in his head forcing him to believe shine yayi abinda ake tuhumar sa dashi ɗin...but Amreesh ya riga da yasan bai aikata ba so why would he admit daga nan yaji wani ciwon kai ya fara nuƙurƙusar shi,he forced himself to remember, zuciyar sa ta fara ciwo ƙwaƙwalwarsa ta birkice don ya fara ganin abubuwan a buji buji,it wasn't clear,kawai yana ganin pictures ne not clearly..he begun to recall,kaɗan daga cikin abunda ya mantane ya fara tunawa when suddenly ya fara amai..aman jini his head threatening to burst the pressure was too much way too much...idan akayi 😵‍💫 hypnotizing ɗin mutum ya manta Abu any time yayi ƙoƙarin tunawa it will be a bloody fight don zai iya mutuwa ko ya shiga coma ko ya manta komai, Amreesh kept pushing himself yaƙi ya bari, numfashin wahala yake, his eyes utterly red...his teeth clattering jikin shi na rawa jijiyoyin kanshi duk sun miƙe... Salmah was horrified itama jikin ta ya fara rawa

'' AMREESHHHH!!!!!!" Faɗuwa Amreesh yayi kwance a wurin looking lifeless...

Book 2 na WAYE SHI ?(Behind the mask) paid book ne for 1k, ga duk wanda ke buƙata ya biya

Ta wannan account ɗin

9138091955

SALMA ALIYU Monie point

Shaidar biya ta wannan number ***