WAYE SHI?{Behind the mask}

Chapter seventy five:The pool side

by @autum17

WAYE SHI?( Behind the mask) By Autumn 🍁🍁

Chapter seventy five: The pool side....

Bayan sun Ƙaraso gaban gadon Ra'esah ta kasa kallon Amreesh duk da yaɗan saki fuska, Samha biye da su... kallo guda itada Amreesh sukayi ma juna kowa ya ɗauke ido,zaunar da ita Salmah tayi kusa da ita she made sure Ra'esah was comfortable sannan suka Hau hira mostly game da makaranta and about Samha, Ra'esah batayi suɓutar bakin gaya ma salmah encounter ɗinsu da dark flames ba or anything they'd been through

Amreesh daga gefe ya cika ya batse sai '' humph '' yake yi, shifa ne mara lafiya yet sun wani zauna sun cika shi da surutu and worst of all he can't send them out saboda Salmah,ƙwafa yayi daidai nan Ahmad ya shigo gaidashi sukayi Samha taƙi yarda ta kalli inda yake,ga wani uban marathon da zuciyar ta ta ɗauka

'' My lady'' ya kira yanda ita kaɗai zata ji, Lumshe idon ta samha tayi without turning back

Idon Ahmad yakai ga Ra'esah murmushi tayi mashi which he returned '' yayan mu ina yini?" Ra'esah ta gaidar dashi, sai lokacin Ahmad ya gane ta, and sai hirar ta ɗau sabon page

Amreesh dake jira yaga karshe yaga abin banayi bane ya ƙara ɗaure fuska '' we were breaking plates...hakan yasa suka kore mu daga kitchen ɗin,it was Samha's idea!" Suka kwashe da dariya Samha was blushing,shi ko Amreesh haushi kamar ya gama da rayuwar sa '' yanzu Ni kuka zo gani ko hira kuka zoyi?" Yayi Maganar glaring at them musamman Samha da Ahmad '' kaji sauƙi ai!" Samha replied da sauri, Ahmad ya kalli Amreesh,they needed to talk Amma yanzu akwai mutane '' Bara inzo in tafi, zaki zo sleep over Samha?" Ra'esah ta tambaya hopefully ta gaji da rayuwa fiye da zaton mai zato amma ganin Samha she felt hopeful again,ganin yanayin ta like she's pleading yasa Samha yarda da sauri ta ɗan kalli Salmah '' just kwanaki kaɗan zan dawo pls Mahma!" Salmah ta rufe bakin ta she didn't know what to say Amreesh yace '' let her go kinji?" Yayi maganar yana jawo Salmah kusa dashi ko kunyar su bai jiba

Gyaɗa kanta Salmah tayi '' b careful pls Banda Jan magana '' Excitedly Samha ta gyaɗa kanta kafin idon ta ya shige cikin na Ahmad mistakenly,his sleepy eyes held something in them,cire idon ta tayi

Itada Ra'esah suna ta godiya kafin suka fita daga ward ɗin Salmah tabi bayan su

'' What was that EMRYS?" Ahmad ya faɗa trying so hard kada ya kai ma Amreesh naushi looking straight at him yace '' What was what?" Matsawa kusa da Amreesh Ahmad yayi ya riƙe kwalar hospital gown ɗin Amreesh cike da fushi yace '' ji nake kamar in kai maka naushi a kyakkyawar fuskar nan taka meyasa bakaji? Na ɗauka komai ya wuce meyasa kake ƙoƙarin kashe kanka? Don't you care? How would I carry on without you?" Cike da fushi Ahmad ke maganar,he was hurt da abunda Amreesh yayi he was reckless '' Babu abinda ya wuce SEB!'' Ya ture hannun sa daga colar rigarsa

'' Oh... you're still obsessed?with the past koda hakan will cost your present and future? Are you darn crazy? You psycho!!!!" Yayi maganar tare da ture kafaɗar Amreesh '' You make too much noise it's not attractive!" Amreesh ya faɗa tiredly, miƙewa Ahmad yayi yana girgiza kanshi walking towards the door yakama handle ɗin ya juyo yana kallon Amreesh daya kishingiɗa tare da lumshe ido '' I hope...I really hope you don't end up hurting yourself EMRYS... You're not alone kayi tunanin matar ka pls!" Daga haka ya fice,dogon numfashi Amreesh yaja kafin ya kwanta yana kallon ceiling

Bayan Salmah ta rakasu komawa tayi ciki, Samha da Ra'esah na tsaka da magana '' K! '' da sauri Ra'esah ta juyo har tana shirin faɗuwa gaba ɗaya annurin fuskar ta ya ɓace ta shiga tashin hankali, juyowa Samha tayi taga waye wannan

Wani matashin saurayi tagani da wata yar iskar shiga harda tattoo yayi wani shegen aski gashi a tsakiyar kai

'' Yaya I.B'' wani banzan kallo ya watsa mata coldly yace '' wuce mutafi!" Cike da bada umarni yayi maganar sannan yayi gaba batareda yayi noticing Samha ba,riƙo hannun Samha tayi suka bi bayan shi Samha was stunned a bit jin yanda yay maganar, bayan sun iso har ya shiga ya fito yana kallon Samha from head to toe'' wannan fa?'' yayi maganar a ɗaɗdage Ra'esah ta fara ina ina '' ƙawata ce zatayi kwana ki ''...

'' gidan uban ki ne da zaki kawo mana gayyar...'' kafin ya gama a high kick landed on his jaw yayi baya baya ya faɗi tus! Kanshi na wani irin ciwo, Ra'esah ta saki baki tana kallo '' idan ina a wuri ba'a zagi...U get it?'' Samha data rage tsawo tadawo daidai level ɗinshi ta faɗa tana waro ido, zafin da IB keji yasa baiyi magana ba kawai ya gyaɗa kai '' good!" Samha ta faɗa tare da miƙewa ta buɗe ma Ra'esah ƙofa suka shiga suka zauna

Kusan minti biyar kafin IB ya miƙe ya shiga motar ya jasu mamaki ya kasa barin shi, through out the ride was silent....

Zaune Amreesh yake rike da paper, slowly yayi unfolding paper yana karanta abinda ke ciki

“ _The_ _game_ _is_ _still_ _on_ ....!”

*_Yours_* *_Anonymous_*

Naɗe paper yayi, Dr ne ya shigo to examine him Salmah tareda shi, turjewa Amreesh yayi akan sai an sallame shi,he didn't want to stay in the hospital duk yanda Dr yaso yayi convincing ɗinshi yaƙi dole aka sallame su... They didn't have much with them hakan yasa the journey was easy don ko Ahmad bai sani ba

Riƙe da hannun ta ya shigo gidan walking majestically mutanen parlor sukayi musu Chaa da ido,no body spoke...no body said a thing,idon khaleel pinned on her yana haɗiyar yawu at the same time he had a recall of what happened ranar, maraƙisiyya,saudat, Mariya da Azeezah weren't in attendance...

Suna shiga ɗakin su ya rufe ƙofar ya jawo ta suka faɗa saman gado she gasped '' Amreesh ciwon k..." '' shhh!" Ya katse ta kafin ya fara cire hijabin dake jikin ta bata hanashi ba ta dai lumshe idonta, ajiyar zuciya Amreesh ya sauke afterwards ya mayar da ita gefe suna facing juna '' Don't ever try to leave me again... I can't take it!" Tsareta yayi da ido kawai without saying a thing ya jawota ya rungume....

**********

Kwanaki sun cigaba da tafiya, Salmah was taking care of Amreesh with so much love and affection, Samha da Ra'esah suka ƙara kusanci for all the days Samha ta zauna a gidan su... IB ma yasha duka not once wurin Samha,duk da Ra'esah taƙi faɗa mata abinda ke faruwa hakan bai hana Samha koya mata self defense techniques data sani ba,tun bayan tafiyar Samha Ahmad became more and more busy har yanzu Dr Haleema bata haƙura da ƙudurinta ba she's just waiting for a perfect chance... Ranar Christmas Samha ta dawo daga gidan su Ra'esah it remained just few more days kafin new year, Amreesh ba zaune yake ba rather yana zuba ido yaga ta inda anonymous zai yi striking so he counters

On the 26th bayan Amreesh ya tafi wurin aiki, Salmah tana zagayen gidan taking a tour ta kawo wurin wani swimming pool,ruwan ciki were deep blue she was astonished,she was awed... Zuƙunawa tayi daga baki tana wasa da ruwan,ita bata taɓa sanin akwai swimming pool a gidan ba tana wurin har saida akayi sallar azahar before she left, Wurin sallar la'asar ta kira Samha su tafi tare amma Samha taƙi,taɓe baki tayi ta koma abinta while Samha stayed in the room lots of thoughts swirling in her mind...

Wurin ƙarfe shida Amreesh ya dawo though ba lokacin tashi bane..he just missed his wife...

Pool side

Zaune take tasa ƙafafunta cikin ruwan tana gaba da baya dasu loving the atmosphere...dama Amreesh na nan?

'' Shall we?" Sultana ta tambaya tana kallon maraƙisiyya,girgiza kanta maraƙisiyya tayi Azeezah tace '' naso ace wannan banzar ƙanwar Tata itama tazo!" Babu wanda yace komai akan hakan

'' Mutafi!" Maraƙisiyya ta faɗa dukan su suka fara tafiya da mugun ƙuduri a zuciyoyin su, juyowa Salmah tayi jin tsayuwar mutum bayanta kafin ta gama registering abinda ke faruwa su duka suka tura ta cikin pool

Sama da ƙasa ta farayi tana miƙo hannu '' Ki mutu!" Maraƙisiyya ta faɗa kafin batareda ɓata lokaci ba suka bar wurin zuciyoyin su cike da farin ciki

Salmah tayi ƙoƙarin ta kasance daga saman ruwan kada ta nutse har ƙasa amma ta kasa, ruwa sai shiga hanci da baki da idon ta suke

'' Amrrrr...!!!"

"Amreeshhhh!!!!" Ta kira desperately one last time kafin tayi ƙasa

******

Shigowa ɗakin su yayi da tsammanin ya ganta amma bai ganta ba,rigar suit ɗinsa ya cire ya rage daga baƙin wando sai farar rigar ciki,his sleek hair swept back,wanka yake son yi amma yet he felt uneasy

Fita yayi daidai Samha ta fito daga ɗakin ta '' Ina take?"

'' Pool side!" Fita yayi without a word ya tafi wurin swimming pool ɗin Amma baiga kowa ba,har zai bar wurin yagan ta...tayo sama kwance samɓal kamar bata da rai, his heart skipped violently in his chest....!

Comment and share

Littafin WAYE SHI?( Behind the mask) Book 2 paid book ne ga duk wanda ke buƙata ya biya ta wannan account ɗin

9138091955

SALMA ALIYU Monie point shaidar biya ta wannan number***