Namiji Ƙanin Ajali (Book 01)

Chapter -- 04

by @amdeeytejjdunique587

*******Namiji Kanin Ajali******

=Page 04

Bismillahir Rahmanir Rahim...

Haka dai muka cigaba da tafiya ba abinda ke shiga tsakaninmu sai gaisuwa,watarana ya amsa watarana yaki amsawa,nidai ko a jikina,ya amsa ko kar ya amsa ya rage nashi,abinci kuwa tun daga ranar dai dai ledan magi be sake ɗauka ya bamu ba,nima ban tambaya ba,to me zaisa in tambya ai ya sani tunda haƙƙinsa ne kuma yaga ba zai iya saukewa ba, nidai ban yafe ba ,kuma ban damu ba tunda ina ƙodago ina samun abinda zanci nida ƴaƴana,yaje ya rage nashi,fatana allah ya sanyawa yarana tausayina a cikin zukatansu....

Haka mu cigaba da tafiya,ta ɗaya bangaren na cigaba da sana'ata na ƙwadigo duk wanda na samu zanyi a biyani ,a gidan kuwa ba wanda yasan halin da nake ciki idan ka cire inna Lami da take yar uwata , dan ni ba shiga harkar kowa nakeyi ba a gidan ba wacca mukayi sabon da zan faɗa mata sirrin aurena a cikinsu....

Kamar dai yau ina zaune a bakin kofa na,ina busan shinkafar da zan dafa bayan na gama wankin wani maƙocinmu,sadaka aka kawo min daga gidan Alhaji Madu na azumi duk da ko watan azumin bamu shiga ba,a watan azumin tsoffi muke saidai ya fara nisa dan ankai goma sha ɗaya, amma shi haka yake sau biyu yakeyi yanxu idan aka zo Ramadan zai sake raba gyaro da sugar kai wani lokaci ma harda kudi....

karaɗin hassana ne ya katsemin tunani jin tana faɗin "oh arziki gashin hanci, kai nagode allah ya bani miji abin nunawa na fita kunya" inajin su Rabi suna tambayar me ya faru "shehu ne ya siyo min atampa turmi uku daga nace ya siya min na anko yarinyar yaya uwani shine ya kara min da wasu guda biyu wai dan nafita daban a wurin bikin"

Duk wannan maganar take, tanayi ne tana dan kallon bakin kofana muna haɗa ido da ita ta wani ɗauke kai sai ta ƙara ƙaimi wajen yabon mijinta da zuzuta shi,nidai na kau da kaina ina murmushin takaici dan nasan za'a rina ansaci zanin mahaukaciya,na rasa dalilin da yasa hassana take kishi dani, iya tunani kuma na duba naga babu dalilin da zaisa tayi kishi dani, na farko ita ba kishiyata ba,ba facala ta ba,ba ƴar'uwata ba, babu wata alaqa tsakanina da ita bayan na zama gida ɗaya, amma tun zuwanta gidannan take kishi dani tun ban fahimta har nagane dan ko nama take soyawa ta dingayi suya tana habaicin da bana gane inda ya dosa, gashi Nidai dana duba naga babu dalilin da zaisa ayi kishin sai na tattarata na watsar da ita na kama damuwar gabana, hassana bayan halinta na munafurci da gulmace-gulmace, akwai fariya da son nuna ita watace ,ita ta tafi kowa,matan gidan sune basu san yanda aka samo zanin ba, shekaran jiya ina wanki ta wurin azara da yake hanyar bayan ɗakina ina jinta ita da mai kayan suna magana da alama ta manta da wurin bayan ɗakina ne, mai kayan tace..

"Hassana kiyi 'ko'kari ki hada min
kudina kika kawo min dan wancan karon kinga akwai saura, wancan leshinma har yanzu baki gama biyana ba, wancan takalminma har yau baki dawo da shi ba, wallahi hassana kinsan halina, ba wani abu bane a wajena in kwance miki zani a kasuwa, dan na rabu da mutane da yawa akan wannan kasuwanci saboda irin wannan halin,ke kinsani kuma kinsan ba mutnci nake dashi ba, inba kadafiri da feleke irin naki ba, baki da ko sisi amma sai son nuna ke watace, miji bai tara ba,bai ba wani ajiya ba, amma ke sai son nuna ke ta gaban goshi ce" tana maganar ne da sigar izgilanci..

Hassana ta katse ta da faɗin,

"ya isa haka malama da'allah dakata, kada ki gaya min magana mana dan kina bina kudi, kedai ba kuɗinki kika sani ba,Ina ruwanki da rayuwata, ke idan ba iyayi ba, idan ba irinmu ya ta ina zakiyi sana'ar har ki dinga yiwa mutane fi'ili, ni ki tafi zanzo gidanki ma ƙarasa a can kada wani ya fito ya jimu".Ta ƙarashe maganar kamar mai raɗa..

Mai kayan tace"To ai gsky na fad'a,ke hassana ko y'ammata da muke harka dasu kinfi kauɗi, kuma ay wannan harkar ta ƴammata ne da zaurawa masu neman shiga daga ciki ba ke ba,da duk ma shehun ya gaji dake kema nasan kingaji dashi....."

"Dan Allah ya isa haka kije zanzo in sameki", hassana ta katseta a hassale.

"To ay gaskiya ne,koda yake gara kam kiyi,ki wanke wannan ƙauyancin naki,dan idan leƙa ya hango wata yar shawalwala sai dai kiji ana yiriri guɗa,dan wallahi har yanzu kanki yana tukunya ni wani kwalabonma idan kika haɗa dariya kike bani,sai dai tunda ni kuɗi na sani ba ruwana"ta ƙarashe wanda dagaji kasan na cin fuska ne

"Koda yake ma ance shima ɗin bai san zafin abin duniya ba ɗan bautan ciki ne"

"Ya isa haka malama,waima wani munafikine ya gaya miki wannan maganar?"

"To ai shi maganar duniya baya ɓuya, musamman a wannan BBCn anguwar taku,kinma mafi kowa sanin hakan tunda kina ɗaya daga cikin shugabannin magulmat....."

"Naji kije zanzo gida ma ƙarasa"Hassanar ta tareta da cikin sauri. 

Mamaki ya kamani yadda wannan matar take gayawa Hassana Wadannan maganganu amma bata ramawa taɓɓ!

"To naji yaushe zaki zo?, dan Wallahi idan baki zo ba na dawi bazata miki kyau ba tamm''tayi cike da kashedi

"Kidai je zanzo" ta faɗa ƙasa-ƙasa.

"A'a kune anan,sannunku"..

Naji muryar Altine,sai yanzu na fahimci dalilin da yasa hassana ta koma magana ƙasa-ƙasa wato bata son Altine ta jisu, shiyasa ma ta katsewa mai kayan magana kenan, Altine itama matar gidan ce,. Hmmmm wato da akace wanzami baya son jarfa, koda itama altine ay ba baya ce wajen yaɗa magana tasan idan altine taji to kamar kowa yajine, idan naso yanzu sai in kunyatata a gidannan,amma meye ribata idan nayi hakan,kuma bayaga hakama ni damuwatama tafi wannan, da dai halimar Dahh ce,wacca bata ganin zarau saita tsinka,da taga buyagi ganin idonta,haka na saki tunanin hassana na kama tuna rayuwata a baya kafin na shiga kurkukun ƙaddarar auren bature,aikin kawai nakeyi badan hankallina na kan aikinba,bansan lokacinda da suka gama hayagagansu ba,nidai na ɗago ne naga kowacce ta kama gabanta sakamakon sallamar ƙawata Lubna da naji a kaina,da murna na miƙe dan ta daɗe bata zo ba sai yau,..

"Yaushe a gari inji maƙi baƙo?" na faɗi bayan na rungumeta,

"Jiya da daddare ƙarfe (10:30 ) goma da rabi muka iso", cike da murnar ganin juna muka shige ɗaki nikuma na sake fitowa na gyara murhun na ɗora tafasar shinkafa,na fita na nemo yaro ya siyomin lemon kwalba da ruwan leda wato (pure water) bayan na kaimata na fito na yi jajjage, a taƙaice dai sai da na haɗa komai na dafa dukar shinkafa na ɗora har shinkafa na zuba kafin na koma ɗakin, danna san idan muka zauna hirar mu bata ƙare bace,.

Lubna ƙawata ce tun yaranta, tare muka taso dukda cewa ta girmeni dan sa'ar yaya ta Khadijah ce, amma jininmu ya haɗu sosai, dan lokacin da data kaiwa ummanmu cingan ƙawance dani, umma tace ai saidai Khadijah amma tace a'a ni takeso, nima a lokacin ina son ƙawance da ita duk da a farko faɗa ne ya haɗa mu,koda yake yawancin ƙawayena ɗaɗɗaya ne waɗanda ba faɗa ne ya haɗa ƙawancenba, duk yadda umma taƙi ayi ƙawancen dani waini tsaurin idona yayi yawa amma taya zanyi ƙawance da sa'ar yayata inje ina manyance a cikinsu amma ya gagara haka aka barmu,har in aka kwana biyu umma bata ganta ba saita tambaya, ƙawance mukeyi na amana dan bama ɓoye juna damuwarmu abinda bazan faɗawa umma ba, zan faɗawa lubna kuma zata bani shawara mai amfani, a sanda dana auri Bature yaso rabamu amma firrr naƙi har takai yace ta daina zuwa mishi gida, umma ce ta bashi haƙuri tace idan lubna tazo da yake itama a lokacin tayi aure dan tama rigani yin auren,inzo mu dinga haɗuwa acan gidanmu, da auren ta yaƙare kuwa nan yace dama tana shirin kashe auren ta shiyasa ta liƙe min dan ta kashe har da nawa, maganganu dai mara ma'ana,nidai tsabar takaici ma bana iya ce mishi komai, to inba haka ba wazai so kashe aurenshi da gangan harma ya haɗa da na wani, bata daɗe ba ta sake aure a minna zuwan ta na farko muka haɗu a gidan umma daganan muka fita gaishe-gaishe muka yada zango anan,da ya shigo ya same mu ya haɗe rai ta mauuww nidai ban nuna alamar na san me yake nufi ba,inaji.ta gaishe ya amsa a maƙoshi,muka cigaba da hirar mu, nan take ce min

"Ay wlh har naji tsoro,na ɗauka Bature zai yi magana"

na ce mata

"Sai gashi baiyi ba,wai kinje kinga Abbah kuwa?"na faɗa dan kawar zancen kar yayi tsayi

"Bane ba ke zaki rakani ay in zanje''

"To Allah ya kaimu" na faɗa

daganan muka cigaba da hirar mu, a raina ina ayyana cewa tabbas shirun Bature baya nufin ya bar maganar nan ta ƙare, Bature ne fa, mita kuma ai cinikinsa ne.......

Masu karatu adakace ni sai mun sake haɗuwa daku Next  page nagode🙏🙏🙏.......

Bye bye 👋👋👋👋👋

Much love to you❤️❤️💖💖

See you next time👁️👁️👁️👀👀👀