E.P2️⃣6️⃣⏩2️⃣7️⃣
by @prettys01
***
𝒀𝒂𝒓 𝑵𝒐𝒍𝒍𝒚𝒘𝒐𝒐𝒅
Story and writing✍️
```𝐏𝗿𝗲𝘁𝘁𝘆 𝐒𝐊
```
~SAKINA ABDULLAHI~
> *PRETTYN JAJIRTATTU 💪✍️
✽»≿━༺🌹﷽🌹༻━≾»✽
E.P2️⃣6⃣⏩2️⃣7⃣.
*Adam*
________________Tun bayan shigowarsa Lagos sau biyu ya je shooting dan be da wani scene masu yawa, yana da wani target akan new year, so yake shi da kansa ya ɗau nauyin wani zazzafan Film da za su yi, labarin ya riga ga siya, so yake su kammala *LOVE AT THE FIRST SIGHT* .
Zaune yake kan kujera yana shan drink, a yanzu babu abin da yake yawan tunani sai fuskar yarinyar da ta ce mai sunanta *Inayah* , gaba ɗaya ta hanashi sukuni, babu dare ba rana fuskarta yake gani tana mai murmushi.
A kowani lokaci jiran kiranta kawai yake yi, sai dai har yau ba ta kira ba, kuma a ƙalla da haɗuwarsu sun kai 6days, duk sai ya ji ya damu.
Har Sarah ya rage kulawa, dan kuwa Inayah ta sace zuciyarsa.
Ya na so zuwa gobe ya koma Kaduna dan jiya mahaifiyarsa Ammee, ta kirasa akan akwai matsala, wai Ayan ya fasa auren Ruma, kuma yanzu wani auren zai yi.
Hakan ya ɗaga hankalinsa sosai, so yake ya koma ya ji abinda ke faruwa.
Wayarsa ne ya ɗau ƙara, ganin ƴan uwan aikinsa ya sa ya ɗauka.
“Okay, ganin zuwa.” da haka ya miƙe ya nufa room.
Wow bedroom ya haɗu sosai, be tsaya a ko ina ba sai close-set ɗin sa, buɗe wa ya yi sannan ya zaɓa ƙananun kaya ya sanya.
Cikin ɗan Lokaci ya fito sanye da ƙananan kaya kamar ko yaushe. Fita ya yi ya hau motarsa sannan ya nufa in da suke shooting ɗin.
Motar sa ƙirar Bugatti Veyron black ya shiga, a hankali ya dinga tafiya har ya isa, saura 2 Episode a kammala Film ɗin, so suke su sake shi lokaci ɗaya.
Asibiti ya nufa dan a can ne za'a yi shooting ɗin.
Da isansa bakin asibitin, wasu maza biyu suka nufosa da sauri suna takamai baya. Tun anan ya ga masu aikin Film ɗin.
*Jim Iyke* shine mahaifinsa a shirin, wani ɗan babban kafiri.
Zama suka yi, mai yin makeup wata Angel, ta zauna ta yi ma Jim Iyke, sannan aka ba shi wasu kayan na masu kuɗi sosai dan ya sa.
A.G ma makeup aka mai amma na ciwuka dan kuwa a wancan Episode ya yi accident akan soyayyar wata yarinyar wanda mahaifinsa Jim Iyke ya hanasa aurenta, to hakan ya haifar mai da damuwa, har ya yi accident.
Ana gamawa aka shiga ciki, wani room aka basu, A.G ya kwanta ya lumshe idanunsa.
Sanye yake wanda jeans black da white shirt, ya cire sarƙokin jikinsa da ɗankunne, dan a yaro mai hankali ya fito. Fuskansa kaman ciwon gaske, an dai rufe waje biyu da bandage, amma har launin jini aka sanya musu, sannan an yi kaman ana ƙara mai jini.
“Action." Ya ji an faɗa, yasan an fara kenan, yana kwance Mahaifinsa ya shigo a ruɗe yana kallon yaronsa cikin wani hali.
Har yana tuntuɓe ya isa gaban gadon, take ya fashe da kuka kaman na gaske yana jijjiga gadon da yin magana cikin English.
“My Son.... please wakeup...... my son...... Alexx, wallahi yanzu na amince da ka aura Mercy , na yarda , ka tashi na yarda, ko ma wacece kake so by now na yarda. Ko wacce ba ta da ƙafafu na yarda.........oh Jesus help me........" (Astagafirullah 😓😓) Ya kai nan kukan na fin ƙarfinsa.
Take doctor ya shigo sai ga wata budurwar yarinya wacce suka yi mata shiga na talakawa, riga ce T-shirt sai mini-skirt irin na kanti, a ruɗe ta shigo, amma suna haɗa ido da Mahaifin Alexx sai ta juya, a tsorace za ta fita.
“Me................Mercy, please come back.......na amince da Ya aureki yanzu.” ya faɗa yana miƙa mata hannunsa.
Take director ya ce su sake wajen, haka dai aka sake sannan ya yi, bayan ta isa gaban dagon tana kuka, fuskar A.G take ta shafawa kamar t samu fuskar yaro, tana ce mai da ya tashi ta dawo.
Bayan sun ɗau lokacin da director ya basu umarni.
A hankali ya buɗe idanunsa kaman dama wanda yake a sume ɗin. Ya ɗan ɗau lokaci kafin ya gane suwake akanta.
Nanfa mahaifin ya shaida ya amince, da auren na su. take Mercy ta rungumesa suna kuka kamar da gaske.
Sai da suka tsara wajen sosai yanda zai sanya mutane zubda hawaye dan kuwa duk wanda ya kalla Film ɗin daga farko, dole ya yi hawaye, dan ya na son Mercy duk da talaka ce, sai mahaifinsa Jim Iyke, ya hana saboda yana so ya yi mai auren jari, haka dai aka gama labarin.
Gobe ne shooting na ƙarshe, da haka aka tattara kayan aiki.
A.G ne rike da hannu Mercy suna ɗan hira, shifa dan ta ɓa jikin mace a wajensa ba wani abu bane.
Sai da suka ɗau lokaci suna hira kafin ya yi kissing na ta a kumatu suka rabu.
Gidansa ya koma hankali kwance, yana shiga ya yarda carkey kan kujera ya nufa Kitchen, be jima ba ya fito riƙe da plate wanda ya zuba snacaks a ciki, zama ya yi yana kunna Tv, sai ya fiddo wayarsa, saƙonnine ta kowani App Suka fara antayowa, shi har gajiya yake da amsawa, Saƙonta ko kiranta kawai yake jira, yana so ko sau ɗaya ne ta kirasa sai dai shiru har yanzu.............
*A'isha*
_______Kallon screen ɗin yawarta take yi, ganin wayar ta kuma katsesa ba a ɗauka ba sai ta koma wajen sakon Yaya Ayan wanda ya shigo yanzu, sai ta shiga.
‘yanzu ko hoton ki ba za ki tura min ba.' shine a rubutu ce sai ta mai reply.
‘Ba ka ta ɓa cewa kana so ba.' tana tura mai ta fita, take kiran Shalele ya shigo.
Murmushi ta yi sannan ta ɗauka ta na ajewa akan mirrow dan Video call ne.
A'isha da ke sanye da hijab fari iya ciki sai shuɗin doguwar riga na yadi, murmushi ta kuma yi tana kallon ƙanwarta dake zaune kan kujera, Pjmask ne jikinta pink colour, da band wanda dogon gashinta ya zuba ta baya.
“Ina kika sa wayan ne, 4 missed call na miki fa?.”
“Sorry, earphone yana jikin wayar ne, shi ya sa ban ji ringing ɗin ba.” sai Aisha ta ɗaga min kanta.
“Ya makaranta fatan ana gane karatun ko?."
“Eh Alhamdulillah. Kun fara exam ku ai."
“Eh, mun gama."
“Allah ya taimaka.” take fuskar A'isha ta ɗan bayyana damuwa sannan ta ce.
“An sanya ranar aure na.” murmushi na yi.
“Masha Allah, wata nawa?, Allah ya sa sai ƙarshen shekara, yarda idan na zo na ci uwar ƴar fili, dan rawar da zan yi hmmmmm." Na faɗa ina ɗan mistsike idanuna.
“Hmmm yau yaushe?.”
“Saturday."
“On Friday na satin nan, shine auren.” da sauri na zaro manyan idanuwa ina cewa.
“Dad ya ba da sadakan ki ne?.” harara ta watso min.
“Eh mana, wani irin aure ne za'a sanya sati ɗaya......faɗa min me yasa?.” murmushi ta yi, ita har yanzu a yarinya take kallona shi yasa ta ce.
“Ayan zai yi tafiya ne, so ana ɗaurawa za mu wuce tare." Sai na ɗaga kai.
“Kenan bana gida za'a yi bikinki? Gaskiya ban so ba wallahi." Na faɗa har da turo baki.
“Ina zuwa Sis.” ta faɗa tana katse kiran.
A'isha ji take tun yanzu ta fara na daman ƙaryan da ta yi, gaba ɗaya kwana biyun nan cikin wani irin yanayi take ciki.
‘Ki turomin na ki, da na Shalele, tinda Allah ne haɗa mu ba.’ ta karanta saƙon Ayan, take ta shiga gallery ta tura mai guda uku sannna ta yi offline.
Kan gado ta koma ta kwanta tana tuna abubuwan da suka faru a ɗan kwanakin baya, wanda a dukka a cikin wata ɗaya ne ya faru......................✍️
END.
> Sannu A.G, kana duniya wlh, gaskiya Sarah an cuceki 😓😓.
> Aisha 🥺 bara dai mu ji me ya faru, dan ga dukkan alamu................😬😬😬
> Team of Aisha and Ayan 🧏 ba ruwan Sk.
*📢 Assalamu Alaikum Everyone!*
Muna farin cikin sanar da ku cewa za mu *buɗe Paid Group* na littafin *ƳAR NOLLYWOOD!* 🎬📖
Idan kina son:
✅ Sabbin *updates*
✅ Karantawa cikin jin daɗi da sauƙi
✅ Tare da wasu *garaɓasa na musamman*
To *ki shirya yanzu* cikin farashi mai sauƙi:
💰 *₦300 only* kafin mu gama.
🕒 Bayan an gama: *₦500*
🌟 *V.I.P Access*: *₦1000*
_Zamu kuma ba kowa *Document* da zarar mun kammala, da kuma password_
Kar ku bari a barku a baya, tafiyar na daban ne wannan karan, domin har yanzu wasa muke yi.
```Idan kun shirya, ku tuntuɓi wannan number:
***.```
~SING BY PRETTY SK~