KUNCIN ZUCI

Kuncin zuci

by @bintuuu

Tsayawa kallon kallo sukayi na sakanni sai hawayen da Na'ima take riqewa suka zubo a fuskanta, da sauri Ahmad ya taho gareta cikin rada yace "Oh My Na'eemahh" hakan sai yasa ta fashe da kukan da take riqewa, isowarsa ya riqo duka hannayenta biyu da suke jiqe da ruwa, yana kallonta shima cikin karyewan zuciya yace "I'm sorryy" sai ya fara share mata hawayen still yana kallonta zuciyarsa na melting akanta, itama dagowa tayi tana kallonsa, ahankali tace "I'm sorry" yayi saurin cewa "Sshhh..it's alright Babe, I'm sorry too, i should've stayed with you yesterday" sai ta girgiza kai suna kallon juna, sanin ya taba mata nata zuciyan yasashi kwantar da murya yace "Babu komai tsakanina da Laila kinji, bansan da zuwan ta ba" sai ta damqe hannunsa dake cikin nata ta gyada kai kawai, shiru sukayi sai can ya kai hannu yana shafa kumatun ta tareda murmushi yace "The fact that i still love you after all this...scares me, don't be the end of me Na'eemah" da sauri ta girgizai kai wani hawayen na kawowa idonta, kallonta ya rinqa yi baya ko kifta ido, ganin haka Na'ima ta sauqar da idonta qasa sai ya sake dago habanta da yatsansa yana kallon idonta yace "Kibari in kalli idon naki, tunda shi kadai kika amince in kalla" sai ta kauda kai tana murmushi, yana murmushin shima yake kallonta, ji yake duk nauyin da ya kwana dashi a zuciya yana sauqa yanzu da ya ganta, shiru sukayi sai murmushi suke, can ya juya yana kallon aikin da takeyi a kitchen din sai yace "You need help Babe" tace "Ta ina zaka fara iya girki ma" ya dan yi dariya yace "Zan baki mamaki kuwa" sai ya fara tattare hannun rigansa, ai da sauri ta fara tura gefen hannunsa tana fadin "Ka rufamin asiri ka fita, su Mami da Abba na gidan fa" bai dena dariya qasa qasa ba Na'ima ta rinqa turasa har sai da suka kai mafitan kitchen din yana kallonta yace "Zan baki mamaki watarana ko ba yau ba" tana dariya tace "Naji, nidai kaje" da haka ya jijjaga kai yana murmushi sannan ya juya ya nufi bangaren Abba tana binsa da kallo fuskanta dauke da murmushi itama, ji tayi komai ya sauqa aranta a wannan lokacin, sai ta juya ta koma dan ta cigaba da wanke wanken nata..
Ahmad na isa falon Abba ya samesa tareda Mami da Nafisa, sai Nafisa ta tashi daga inda take zaune ta bashi gurin nan qasan carpet kusada Abban ya zauna, sai da ya gaishe dasu sannan Mami tace da Nafisa "Baby dan bamu guri" ta amsa da toh ta miqe, saida ta dauki kayan da Abba yaci abincin dasu sannan ta fice dasu a hannu, sai sannan Abba yace "Ahmad Ina baka hakuri da abunda ya faru jiya" kan Ahmad na qasa yace "Kuyi hakuri da abunda nayi, hakan bazai sake faruwa ba" Abba yace "Bazan ga laifin ka ba Ahmad, nasani ba halinka bane, yaron ba mai hankali bane, he's in to drugs so ko ka bisa a hankali ma ba fahimta zeyi ba, in Sha Allah zan dau mataki akansa" Ahmad yace "Kayi hakuri Abba amma bazan iya barinsa hakanan ba nima, har gidansu na Oxford yaje ya daketa" da sauri Mami takai hannu baki tana ware idanu tace "Hasbunallahu wa ni'imal wakil, kuma basu fada mana ba" Ahmad yace "He has been following her Mami" tace "Ni Fatima, me yake nufi da rayuwan yarinyar nan ne" sai ta kalli Abba tace "Ni ko sai ya kashetan zasuji dadi ne"  ta kalli Ahmad ma tace "Ahmad ka illatamin yaron nan tukunna" sai Abba yace "Baza akai har gandun nan ba, I'll take matters into my hands, karku manta mahaifinsa yayi riqo da Na'ima a lokacin da ta rasa gatan ta a rayuwa, kar mu zamo masu manta alkhairy Fatima, yaron nan duk lalacewar sa dan'uwanta ne" Ahmad yayi shiru, sai ya sake duqar da kai yace "Abba ina neman alfarman kubani auren Na'ima dan Allah" dan stiff sukayi dukansu jin abunda yace, sai Abba ya sauqe numfashi yace "Son inda inada cikakken iko da Na'ima kasani ko anan gurin zan iya baka auren ta, amma bani ke da al'hakin wannan ba, it is high time mun kaita gurin uban riqonta ya san me yake faruwa, rashin maidata garesun dama muna buqatan tadawo cikin hankalinta ne saboda yanda sukayi depressing dinta a lokacin da tazo garemu" Ahmad har sannan kansa na qasa ya gyada kai cikin ladabi, sai Abba ya cigaba "Ka dan bani lokaci kadan son, in sha Allah in har komai ya daidaita, nikuma na maka alkawarin zan nema maka aurenta da kaina" Ahmad ya amsa da "Nagode Abba, Allah ya qara girma" Mami dake jin farin ciki na cikata tace "Allah ya shige mana gaba" suka amsa da Amin..

Na'ima na tsaye a dining area tana jera flasks din da ta zuba abincin aciki while Nafisa na ajiye plates itama tace "Wai daman a kitchen din da na fada masan ya sameki sis" Na'ima ta gyada kai hankalinta da na kan abunda takeyi, sai Nafisa ta sake cewa "Ya fa san be kyauta ba shima, ai ni da saurayina ne nagansa da mace haka, toh ko ni ko ita, kawai dan be san zafin kishi bane shiyasa" dago kai Na'ima tayi tana kallonta sanin cewa batasan abunda ya faru jiyan ba, sai taji bata kyauta ba da bata fada mata ba, kafin tace komai sai ga su Abban sun fito zasu tafi masallaci shida Ahmad dan maghrib tayi, Mami dake bayansu tace "Sannu Habibti, har kin gama komai" Na'ima tace "Eh Mami" sai ta mata sannu, ficewa su Abban sukayi su Na'iman suka tafi nasu dakin yin sallah suma, sai bayan da Abban ya dawo sai suka shigo tareda Faruk, yace da Nafisa takai musu abincin bangaren Abba shida Ahmad din, sai kawai ta dauka duka ma takai can din, su Abu da suma dawowan su kenan aka hadu duka a falon Abba har Ahmad din, baya Na'ima ta bashi da suka zauna cin abincin anan qasan carpet dan kar su hada ido ma dan tasan zai rinqa kallontan nan ko ajikinsa, ita da Nafisa sukayi serving kowa na falon cikin nasa plate din sannan sukaci nasu tare, ranan har karfe tara Ahmad yakai a gidan shima ana hiran dashi, duk sai Na'ima tayi shiru a falon saboda kunya, dan ita tunaninta kar su Abba sun san alaqar dake tsakaninta da Ahmad while shi hiran sa yake sama sama ko ajikinsa, da Mami ta lura da shirun ta sai tace "ko bacci kikeji Habibti" Na'ima ta amsa da "Eh" tareda yi musu sallama zataje ta kwanta sannan ta fice...
Washegari Mami ta tafi unguwa har yamma bata dawo ba, bayan su Na'ima sun gama ayyukan da sukayi agidan sai Nafisa ta shirya fita gidan wata qawarta da take birthday ranan tace da da Na'ima ta rakata, sai tace "Nafee kaina na ciwo" kamo hannunta Nafisan tayi tana cewa "Da'alla ki tashi muje, minti goma tayi yawa zamu dawo" haka sukayi ta ja'inja da maganan nasu dan ita Na'ima tasan in Mami na nan bazata barta ta fita ba kuma, gashi Nafisan batasan me ya faru ba balle ta fahimci dalilin qin zuwanta, sai tace "ki zauna muyi magana Nafee" Nafisa na tsammanin duk acikin rashin son zuwan ne yasa Na'ima ke fadin hakan, hade fuska tayi tace "Na'ima meye haka wai, i was thinking mu biya ta site dinda akemin aikin can ki gani ma fa" shiru Na'ima tayi sai kuma tace "Toh kiyi hakuri muje din toh..amma kince 10 minutes, u promise" Nafisa ta gyada kai sannan Na'ima ta hau shiri suka tafin, da suka isa gidansu qawar Nafisan sai taga ashe a cikin gidansu yarinyar ake party din ma, sai sannan ta samu nutsuwa sosai, tun da sukaje kuwa tana zaune a guest table har suka tashi tafiya Nafisa ta zo suka tafin, hanyar site din suka nufa ahanya kiran Ahmad ya shigo wayan Na'iman ta dauka sai taji muryansa yayi low, tace "Meya sameka?" ahankali yace "Ina kan hanyar komawa gida, gajiya ne Babe" tayi murmushi tace "Yau kuma, kaine da gajiya?" Yace "Laa yarinyar nan me kika dauke ni" jin sunan da ya kirata dashi yasa ta yin dariya, dan bai taba ce mata yarinya ba, sai tace "Workaholic" yace "Kudin auren mu nake nema Babe, inason tara dayawa dan ki huta kinji" tana murmushi tace "Duk bayan wanda ka tara?" yana dan dariya yace "Wa ya fada miki, talaka ne ni Na'eemah, so i had to work hard" sai tayi murmushi tace "Allah yayi jagora to" yace "Amin Babe, yanzu kina Ina?" tace "Mun tafi ganin gurin aikin shagon Nafisa" sai ya tambayeta address din ta fada masa yace "Bari nazo mu gaisa" tace "Kai da ka gaji" yace "Gajiyan zai tafi in na ganki" sai tayi dariya tace "What kind of line is this?" cikin kwantar da murya yace "Na son Na'eemah" kawai ta sake dariya tace "You're too much" bai dena dariya ba har sukayi sallama sannan ya cigaba da tuqin motansa yana kallon titi...
Da Na'ima ta gama wayan sai taga har sun kusa isa ma, Nafisa na driving tace "Bobo baki bani labarin interview dinki ba dai" Na'ima ta juyo tace "I thought munyi maganan ma fa" Nafisa tace "Ranan baki da lafiya" tayi turning kan motan zasu shiga gate din premises din, Na'ima tace "Anyi haka..na manta ne sis" da suka shiga uncompleted building din Na'ima was surprised to see that aikin yayi nisa ma, tace "Nafee yaushe duk akayi aikin nan?" ta amsa da "Ginin na wani ne daman yakeson siyarwa sai Abba ya siya" Na'ima na fadin Ma Sha Allah tana bin building din da kallo wanda ya kasance hawa biyu, bayan sungama gani zasu tafi to their suprise ma ranan sai ga Bilal ya faka mota acikin compound din gurin, Na'ima dake bakin matattakalan qaramin stairs din varenda ta tsaya kallonsa ranta na baci, Nafisa na kulle gurin ba ta ma juyo ba sai Bilal din ya qaraso gurin amma bai hau ba yana facing Na'iman yace "I'm sorry Na'ima ranan bacin rai ne yasa nayi komai, ki saurareni please.." Nafisa ta daga murya daga inda take tsayen tace "Wai kai wane irin maye ne Bilal" sai ta qaraso ta tsaya a gefen Na'iman, adaidai lokacin kuma motan Ahmad ta kunno kai cikin gurin, ta cikin motan ya hango Bilal din tsaye gaban Na'ima dake tsaye itama a saman varenda suna facing juna, dakata wa Ahmad yayi yana kallon Bilal din ransa na baci, wani irin zafi ne ya fara taso masa tun daga zuciya dalilin tuna maganganun da Bilal ya fada masa ranan, a wannan lokacin Ahmad ji yayi har jikinsa na dan rawa, kawai sai ya taka motan ya nufi kan Bilal direct, Bilal daya juyo yana ganin tahowar motan sai shock ya tsayar dashi ya kasa motsawa ma kawai yaji an tureshi ya fadi qasa, wani birki Ahmad yaci yana kallon Na'ima dake tsaye gaban motan tana kallonsa jikinta na rawa, cikin ido suka tsaya kallon juna kowannensu zuciyarsa na kadawa, sai kawai ya bude motan ya fito ransa a bace ya nufi Bilal yana nuna sa da yatsa yace "People don't test me and go scot free, but Yoouuu..you keep testing me" duk tsaurin idon Bilal sai da yaji shakkan Ahmad a wannan lokacin ganin yanda jijiyoyin fuskansa suka tashi, Na'ima ce ta matso gurin Ahmad gudun kar su sakeyin wani fadan sai ya juyo yana kallonta rai a bace yace "Shiga motaa" da sauri ta gyada kai ta nufi motan nasa, Nafisa ma da tasha jinin jikinta ganin yanayinsa sai tayi saurin nufan nata motan ta shiga, Ahmad na tsayen ya dago wayansa dake hannunsa yayi typing text sannan ya juya ransa a bacen ya shiga motansa ya tada, sai da ya fara gaba sannan Nafisa tabi bayansa da nata motan suka fice da cikin premises din. Tun da Ahmad ya shigo motan Na'ima ta kasa ce masa kala ganin bacin ransa da bata taba gani ba ko da wasa, aikuwa sunyi nisa da tafiya yayi parking a gefen titi, Nafisa dake bayansu sai tasha gabansu ta wucesu, bai kalli Na'iman ba har sannan sai ya daki sitiyarin motan da dan qarfi yana fadin "Damn itttt, Damn it Na'eemah" da sauri ta dan damqe idanunta sannan ta budesu tana fadin "Kayi hakuri ka saurareni ple.." bata qarasa ba Ahmad ya juyo yana kallonta yace "Do you love him?" sai ta danyi stiff jin tamabayan da yake mata, ya sake cewa "Answer me" cikin sanyin murya tace "Me kake cewa haka?" rai abace yace "Meyasa kika karesa, do you love him Na'eemah?" muryan ta na rawa tace "Ahmad tayaya zan bari kayi kisa, kisa fa zaka yi" yace "Da kin barni na kasheshin, Billahi kashesa zanyi har lahira, sai ya mutu a gabana Na'eemah" ganin yanda ya birkice kamar ba Ahmad din da tasani ba yasa ta kai hannunta ta kamo kansa ta kwanto dashi bisa kafadanta tana fadin "Ahmad listen to me, listen to me Dan Allah, I can't let you do this" ta dago kansa suna kallon juna, hawaye na kawowa idonta tace "Son ka nake, wallahi Ina sonka ne yasa bazan bari kayi abunda zakayi dana sani ba" kallonta yake da idanunsa da sukayi jaa, ta sake kwantar da murya tace "Kai nakeso Ahmad, kai kadaii" sai ya duqar da kai yace "Ina matuqar kishinki Na'eemah, addu'a ce take sauqaqamin hakan, every night i go to bed thinking that wani ya rigani yin rayuwan aure dake, Na'eemah that alone is a torture to me, nazata zan iya daurewa Na'eemah, but i can't....I really can't" Na'ima na hawaye tace "He wasn't there with me, bana tare dashi na tsawon shekara uku Ahmad, ban taba son sa ba, ban taba jin komai na dangane da so akanshi ba" sai yayi shiru yana kallonta, ta sake kwantar da murya tace "Ka yarda dani" sai ya juya yana kallon titi, Na'ima na kallonsa tana mamakin kishinsa, daman kishinsa ya kai haka? , sai ta goge hawayen ta tayi murmushi tace "Bamuyi gaisuwan da kace zakazo muyin ba ma" sai sannan ya juyo fuska a sake yace "Bari dai kiga zance zan fara zuwa daga yanzu ma" bata bar murmushin ba tace "Zance kuma?" Yace "Yau ma zan fara, ya akeyin abun? da yaushe ake zuwa?" dan dariya tayi tace "Ni ma rabona da yin zance tun ina yarinya, around 13 years" ya dan ware ido yace "What..tun kina yarinya haka, wai like seriously a lokacin in aka bar uncles dinki auren zasu miki a wannan time din?" tace "Har an karbi goro ma" sai yace "Kuma a Ina kika hadu da guy din?" nan suka fara hiran tana bashi labarin lawan kamar ba tashin hankali sukayi ba just a moment ago, kamar ba'a gefen titi suke fake ba, kamar basu suka samu sabani ba.....Da Ahmad ya maida ta gida bai shiga ba, anan qofar gidan sukayi sallama ta shiga gidan, tana shiga falo ta tadda Nafisa na tsaye tana jiranta ko zama ta kasa ta nufo ta rai abace tace "Na'ima meyasa zaki ture dan akuyar can?" tace "Ayya Nafisa meyasa bakwa ganin abunda nake gani ne? tayaya zan barsa yayi kisa, ze dau jinin Bilal a wuyansa ne fa har abada" sai Nafisa tace "Inda ya kasheki fa" Na'ima tayi murmushi tace "Ba gashi yayi birki ba" Nafisa tace "Kinyi gambling da naki rayuwan akan Bilal kenan Na'ima, what is wrong with you wai?" ganin bazata fahimce ta ba tace "Kiyi hakuri Nafisa, muje ciki, Mami tadawo?" ta gyada kai ta amsa da "Tana falonta, ni gaskiya kar ki sake shiga fadansu, ki bari Yaya ya koya masa hankali, ke duk abunda Bilal ya miki a rayuwa kin manta ne, shima ai so yayi ya kasheki" sai Na'ima ta kamo hannunta tace "Ayya yunwa ma nakeji dai Nafisa, in munci abinci sai kimin fadan kinji" Nafisa na mita Na'ima ta jata suka wuce sama gurin Mami....
Daren ranan sai wani aiki ya riqe Ahmad din har kusan isha bai gama ba, yana zaune falonsa da laptop bisa kafansa daya miqar akan glass table yana aiki, typing kawai yake amma ransa duk babu dadi, Adam ya sauqo nan falon yana fadin "Har yanzu baka gama ba" idon Ahmad na kan abunda yake typing din ya amsa da "An samu issues cikin report dinnan, the government didn't complied, they haven't accept the permits for the renewals" Adam yace "I thought we've reached the agreement" Ahmad ya girgizai kai yana shafa fuskansa in frustration, abubuwa sun masa yawa a zuciya ranan, babban damuwan ma shine rashin samun wayan Mazzy da yayi, zama Adam yayi a kujera shima sai ya miqa hannu ya dauki daya daga cikin takardun da ke gefen Ahmad din yana karantawa, shiru sukayi kowa da abunda yakeyi, can wayar Ahmad tayi qara sai ya bar rubutun da yakeyi ya dauko wayan, ganin text ne daga Mazzy yasashi janye laptop din daga jikinsa ya miqawa Adam yace "Dan qarasamin, i need to go somewhere now" sai Adam yadan hade gira alamun tambaya, kawai Ahmad ya ajiye laptop din akan kujera ya miqe tareda nufan stairs zaije dakinsa, bai dade ba yadawo sanye cikin wasu qananun kaya da ya chanja har da facing cap, car key ya dauka har sannan Adam na kallonsa yace "Wai ina zakaje ne" sai yace "Saqo aka kawomin" da haka ya fice daga falon Adam na kallonsa...Gudu Ahmad ya rinqa yi a hanya sosai kamar zai bar Abuja ma gaba daya, sai da ya fara idda jeji sannan ya yanki cikin wani layi ya dauki wani hanyan, sai da yayi nisa sosai sannan yayi parking a bakin gate din wani babban gida, da nasa key da ya taho dashi ya bude lock din gate din, madadin ya shiga cikin building din sai ya bi baya ya nusa inda ba'a gama completeling ginin ba wanda ya kasance kamar warehouse haka amma ba'a amfani dashi, acan bayan ginin ya tadda wani babba shima zuwansa sai ya saka wani key din ya bude, shigansa ya tadda Mazzy zaune da yaransa guda hudu sai zuqar taba suke, Ahmad bai kalli package dinda aka rataya masa tun daga ceiling din dakin ba, sai ya nufi Mazzy daya miqe shima ya miqa hannu sukayi shakes a nutse yace "Thanks Man" Mazzy yace "I'm sorry Boss, mun dauki lokaci" sai ya nuna Bilal yace "Shegen can ya mana zillon kifi" da haka ya ciro wasu takardu ya miqawa Ahmad din ya karba bai bude ba sai Mazzy ya sake bashi wata guda daya yace "This is the final one da muka samu jiya, alluran da yake mata ne" da sauri Ahmad ya karba yana ganin descriptions din, bai qarasa ba ya juya yana qarasawa gurin Bilal dake daure kansa na ganin qasa, sai ya kai takardar fuskansa a nutse yace "Kai aladen ina ne da zaka mata wannan alluran?" Bilal yaqi magana sai Nasir dake gefensa yace "Wai kaidin uban waye?" Ahmad yayi baya yana miqa hannu gurin yaron Mazzy sai ya miqa masa wani murtiqeqen sandan qarfe mai kama dana buga hockey, Nasir yace "Do you know who i a..." Baaaam wutarsa ta dauke bai qarasa maganan ba, Ahmad ya sake saita kansa ya sake buga masa da qarfi har jini na fita a hancinsa, sai ya juya gurin Bilal ya buga masa da qarfi shima shima, sai da yayi hakan sau biyar a cikin Bilal sannan ya tsaya yana huci, sai kalli yaran gurin yace "Kunce min shi" ai kuwa nan suka ware Bilal da tun ba'a je ko ina ba yafara laushi, ya tsugunna gabansa yace "Ka maimaita min abunda kace rannan" Bilal yace "Wanne daga ciki?..na yanda take kuka when i f"cked her?" aikuwa nan Ahmad ya rinqa buga masa sanda, Bilal ya daku iya dakuwa ahannunsa, har kafa Ahmad yasa yana takashi babu wanda ya hanasa adakin, dan Mazzy dake zuqan taba jira yake kawai akashe Bilal din ma, sai yaga Ahmad ya kyalesa bayan ya suma, da hannu Mazzy yayi alamu a yaransa su kawo ruwa, nan aka sheqa akan Bilal ya farka a firgice yana kallon Ahmad dake tsaye a kansa har sannan, anutse Ahmad yace "Sai ka gwammace mutuwarka akan zaman ka a gurina" Bilal ya jijjaga kai yace "Kayi hakuri, wallahi bansan me ya shiga kaina ba" Mazzy yace "Dan uw*rka ba kwaya bace" sai ya karbi wani sandan shima ya hau dukan Bilal yana fadin "Kadauka kai qwaro ne dan ub*nka" Bilal na kururuwa haka Mazzy ya rinqa dukansa sai Ahmad yace "Ku balla min hannunsu daddaya, ku gyara sannan ku sake balla dayan, kuyi masu exact alluran, ku dake su ko suna baccin" da haka ya juya ya fita Bilal da Nasir din na kururuwan basa hakuri, tsayawa yayi a wajen yana duba papers din cikin envelope din, sai ga Mazzy ya fito ya qarasa gurinsa, Ahmad ya nuna masa takardun Stella yace "Wannan fa" Mazzy yace "She went missing in china kwanakin baya and no traces of her, but we are still digging everything" sai yace "Then ku fadada binciken, am adding up the bills" Mazzy yayi murmushi sanin kudin da zai samu, yace "All done, zan aika lesuu, zai dawo da ita i assure you" sai Ahmad ya gyada kai tareda miqa masa hannu sukayi sallama, da haka ya tafi motansa, sai da ya bude wani nook drawer acikin motan ya saka takardun ya kulle sannan ya figi motan ya nufi gida aransa yana tuna beyi sallahn isha ba, kuma again yace wa Na'ima zaije zance...


Karku manta da following Account dina sannan ku danna min Like akan book dinnan please.

Bintu Musa ✍️