Shafi Na Biyar
by @sanazty
A CIKIN IDO...
Ake tsawurya
Wattpad @SaNazdeeyah_
Heart touching love story🥰
KARAMCI WRITERS ASSOCIATION
[karamci tushen mu'amula tagari]
Na sadaukar da littafin nam gaba ɗayanshi ga BEEBAH LUV Allah yayi mata rahama ya kuma kai haske kabarinta Amin🙏
Shafi Na Biyar
______________Cigaba ya yi da cewa "Kamal shine zai riƙe ki da gaskiya, kuma no matter what ba zai taɓa goranta miki akan komai ba. Kamar yadda muka alƙawarantawa juna cewa ko wanne a cikinmu shi zai zaɓo wa ɗan uwansa abokin rayuwa nagari, to ni na sauke nawa nauyin."
Ɗago idanunta tayi ta kalli Maheer taga ita yake kallo. Ajiyar zuciya kawai ta sauke tana mayar da ƙwalla bata son a gane damuwarta.
"Abokina, bari na ɗan barku ku gana, zan je office ɗin accountant na dawo."
"Baka da matsala mutumina. Ina godiya matuƙa."
Da ido take bin Maheer har ya fita daga office ɗin sannan ta dawo da kallonta ga Kamal.
Ɗan gyaran murya ya yi sannan ya fara da faɗin "Kusan duk abinda zan faɗa abokina ya riga da ya faɗa, sai dai ina son na ƙara jaddada soyayyata a gareki, kuma bana son mu ɗauki lokaci mai tsayi ba muyi aure ba"
Bakinta ya yi nauyi sosai, ta kasa cewa komai.
"Amma ina son ki faɗa min ra'ayinki a kaina"
Da ƙyar ta iya cewa "Bani da abinda zance sai dai fatan alkhairi, domin na san Beauty ba zai taɓa min zaɓen da bai dace dani ba"
"Naji da daɗin haka sosai, gaskiya na lura kina ji dashi kamar yadda yake ji dake."
Murmushin ƙarfin hali kawai tayi.
Yana ta zuba surutu ita kuma tana binsa da um ko um-um sam hankalinta baya jikinta sosai, har zuwa lokacin daya shigo office ɗin, Noor na biye dashi.
"Ana ta hira kenan" ya faɗa tare da zama kan kujerarsa.
Itama Noor kujera ta samu ta zauna tana kallonshi.
"Ai na lura Sahibar tawa akwai kunya"
Sai lokacin Noor ta kalleshi ta ce "Ko ita ce Amal?"
"Itace" Ya bata amsa a taƙaice.
Ai da sauri ta tashi taje tayi hugging ɗinta "You are welcome Amal, tun ɗazu nake ta zuba ido ashe kinzo"
Murmushi Amal tayi, suka gaisa cikin sakin fuska.
Suna ta hira da Amal a ƙarshe ma tashi sukayi suka koma office ɗin Noor saboda shi Maheer a lokacin ayyuka sun masa yawa.
"Amma mene kike wa Maheer har kuka shaƙu haka? Kuma dan Allah ki faɗa min gaskiya mene tsakaninku, dan ni kam sai nake ganin kamar kuna soyayya"
H
Murmushi Amal tayi sannan ta ce "Maheer shaƙuwata dashi tun daga yarinta ne har zuwa girmanmu, sun fara zama a unguwarmu kafin daga bisani suka tashi, amma still mun shaƙu sosai, kamar Wa da Ƙanwa haka muke da Maheer, kuma babu soyayya wadda kike tunani, sai dai soyayya ta shaƙuwa"
Murmushi Noor tayi tare da goge ƙwalla "Amal ina son Maheer, so mara misaltuwa, tun ina ɓoyewa har na kai ga bayyana masa, amma yaƙi aminta dani, sai dai ya ce shi baya da mata a duniya sai wadda Amal ta zaɓa masa, kullum fatana na haɗu dake, nasha roƙonsa ya bani number ki amma yaƙi ya bani"
Tashi tayi daga kan kujerar da take ta kai gwiwoyinta ƙasa tare da faɗin "Dan Allah ki taimaka ki sa shi ya soni, wallahi son gaskiya nake masa, amma ban san mene laifina a gurinshi ba, ban sani ba ko ina da wani aibu, amma idan ina dashi kamata yayi ya faɗa min, ko kuma ya fara soyayya dani har ya gane halina bani da wani mugun nufi a kansa. Nayi tunanin kuna soyayya dashi ne shiyasa yake kauce min"
Amal ji tayi gabanta ya ƙara faɗuwa, duk da itama tana jin son nashi a ranta, amma ta san Maheer bata ta ta yake ba, da yana sonta da tuni ya faɗa mata, kuma da yana sonta da bai haɗata da wani ba"
Tashi tayi daga kujerar da take ta ƙarasa gaban Noor ta ɗagota. "Indai zan faɗawa Maheer yaji to baya da wata mata sama dake, zaki mallaki Maheer insha Allahu, daga ɓangarena baki da matsala"
Murmushin jindaɗi tayi sannan ta ce "Nagode sosai Amal, in har haka ta faru kece lamba ta ɗaya da ba zan manta a rayuwata ba."
Hira suka cigaba dayi tana faɗa mata ta yadda zata shawo kan Maheer da irin abubuwan da yake so.
***
Yana driving ya juyo ya kalleta ya ce "Ya kika ga ma'aikatar tamu?"
"Tayi kyau sosai, kuma ƴan cikinta suna da karamci"
"Masha Allah, kin ga kuwa Kamal ya dage shi zai kai ki gida, sai dana ce masa gida zamu je ki gaida Mommy, amma ya ce min anjima zai zo, ki riƙe Kamal hannu biyu domin mutum ne mai kirki, har ya so ya fini ma."
Tuni annurin fuskarta ya ɗauke, ta haɗe ranta tamau, bata ce masa komai ba, haka shima bai sake magana ba har suka ƙarasa gidan su Maheer.
Ƙara ƙarewa gidan kallo take, karo na biyu da tazo gidan kenan.
"Ki saki jikinki gidanku ne fa" Ya faɗa lokacin daya fito daga mota.
Murmushin yaƙe tayi, sannan suka ƙarasa cikin main part na gidan.
Tun daga parlour yake ƙwalla kiran Mommy kafin ya kalli Amal dake tsaye ya ce "Beautyn Beauty zauna mana"
Zama tayi kan kujera a ɗarare take sosai.
Momny data sauko daga uptairs kallon shi tayi tana faɗin "My love ai sai ka saka hankalina ya tashi irin wannan kira"
"Mommyna kin san ban san shigowa gidan nan inga baki kusa"
Amal kuwa suke gwiwoyinta ƙasa tayi ta gaida Mommy.
"Tashi ki zauna Amal" Mommy ta faɗa cikin fara'a. Shi kanshi yaji daɗi sosai yadda Mommy bata nunawa Amal komai ba.
Ƙwalawa ƴan aiki kira tayi , su biyu suka shigo suka rissina. "A kawowa Amal kayan motsa baki" "To Hajiya."
Ita dai Amal duk a takure take jinta.
"Daga ina kuke haka?"
"Daga office nan mukayo"
"So ya kamata kayi wanka ka huta sannan kaci abinci, Yayanka anjima ya ce min zai zo"
Ɗan ɓata rai ya yi sannan ya ce "Ni kam ba zan jirashi ba, dan na san da wannan mara kunyar matar tashi za su zo"
"Matar Yayan naka kake kira da mara kunya"
"Mommy wallahi gani nake ita take hana Yaya zaman ƙasar nan"
"To ba sai suyi tayi ba, Allah ya shiryasu"
"Amin ya rabbi."
"Amal ana ta hira kinyi shiru" Cewar Mommy.
Ɗan murmushi tayi tana wasa da yatsun hannunta.
Maheer ne ya kalleta ya ce "Beautyn Beauty nan fa gidanku ne ki saki jikinki" Ya miƙe tsaye tare da cewa "Mommy bara naje na watsa ruwa na fito"
Kallonsa Mommy tayi tana murmushi za tayi magana sai kuma ta tsaya cak tare da miƙewa tsaye.
"Ma...Maheer me nake gani?" Ta furta a kiɗime.
Sai lokacin Amal ta kalleshi, itama miƙewa tsaye tayi a tsorace.
"Jini a hancinka"
Tissue dake kan center table ya zari ɗaya sannan ya gogo ya kalla.
Ɗan murmushi yayi sannan ya ce "Ina tunanin haɓo nayi"
"Ban yarda ba, mu tafi asibiti"
"Haba Mommy ɗan wannan abin ba wata matsala bane"
"Maheer bana son wasa kasan larurarka, ka wuce muje, ka ajje key ɗin motarka zan yi amfani da motar gida.
Larura? Dama Maheer yana da wata larura da ban sani ba? Amal furta a zuciya tare da gyara gyalenta.
Su uku suka ɗinguma zuwa asibiti, Mommy sai sharara gudu take akan titi.
Ta mirrow Maheer ke kallon Amal, wadda kana kallon fuskarta zaka tabbatar tana da damuwa.
Suna shiga asibiti kai tsaye office ɗin likitansu suka ƙarasa, dama tunda suka taho Mommy ta kirashi a waya.
Bayan ya ɗan duba shi ne ya ce "Ko za ka tsaya a waje zamuyi magana da Mamanka"
Bai iya cewa komai ba ya juya ya fita, Amal har ta nufi ƙofa zata bishi Mommy ta dakatar da ita.
Dawowa tayi ta tsaya kusa da Mommy jiki a sanyaye.
"Doctor ya ake ciki?"
"Cutar ce dai ke cin jikinshi"
"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" Ta furta lokacin da wata zuffa ta keto mata.
"Sai haƙuri, Allah haka ya ƙaddara masa, ba yanda muka iya"
"Amma kana ganin ba zai kai kwanakin da kuka faɗa ba?"
"Mun ƙiyasta ne, wata ƙila ya wuce haka, amma koda ya wuce watanni shidda a duniya to ba zai ƙara sati sama da ɗaya zuwa biyu ba"
Amal dake tsaye gaba ɗaya idanunta sun firfito, ta zare ido ta dafe ƙirji, hankalinta gaba ɗaya a tashe yake. Bata san lokacin da hawaye masu zafi suka zubo daga idanunta.
Ƙarasawa tayi gaban kujerar Likita ta kalleshi da idanunta wanda sun ɗan fara canza launi a lokacin. "Doctor me kuke nufi da wata shidda ban fahimta ba?."
Mommy ce ta goge hawaye sannan ta ce "Amal zauna" Ta nuna mata kujera.
A sanyaye ta zauna lokacin da wasu zafafan hawaye suka ƙara fitowa daga kogon idanunta.
"Bana son rasa Maheer..." Ta furta a sanyaye.
"Nima mahaifiyarsa dashi kansa mun ɗauki wannan ƙaddara" Ta furta sannan ta kalli Doctor
"Ina son Maheer ya yi aure, saboda ko bayan ranshi zan riƙa ganin abinda ya bari a matsayin shi, amma sam yaƙi kawo min mata har yanzu, tun lokacin da aka tabbatar min yana da blood cancer kuma ba zai wuce shekara ɗaya a duniya ba, tun a lokacin nake bin kanshi, gashi abin har ya dawo wata shidda ma'ana anci rabin shekara."
"Amma Hajiya ita wannan ba budurwarsa bace? Me zai hana ku haɗa aurensu?"
"Doctor ina son Maheer ya auri mace mai asali, wannan abokiyar shi ce, babu alaƙa ta soyayya, kuma ba irin ta nake son ɗana ya aura ba, saboda jikana ina so ya fito daga tsatso mai asali" Sai kuma ta kalli Amal wadda a lokacin ta rufe fuskarta da tafukan hannunta.
"Amal na fahimci Maheer yana jin maganarki fiye da tawa ma, dan Allah Amal ki saka shi ya fiddo min mata, na san kema zaki so ki riƙa ganin jininsa a doron ƙasa." Tana gama faɗa ta tashi da sauri ta bar office ɗin.
Sai da Amal taji fitarta sannan ta cire hannunta daga fuska, hawaye gaba ɗaya ya wanke mata fuskar.
"Kiyi haƙuri kinji" Doctor ya faɗa, ita kuwa ba ƙwari ta miƙe ta nufi hanyar fita.
"Mommy me Doctor ɗin ya ce?" Maheer ya tambaya yana riƙe hannuwan Mommy.
Shiru tayi ta saka hanky tana goge hawaye.
"Mommy wai kukan me kike? Ina Amal?" Yana faɗa idanunsa akan office ɗin Likitan, dai-dai lokacin Amal ta fito ta tsaya ta jingina jikinta da bango tana ƙara sharar hawaye.
Da sauri ya saki hannun Mommy ya ƙarasa gurin Amal. "Beautyn-Beauty mene yake faruwa?" Ya furta muryarsa tamkar zai yi kuka. Ita kuwa Mommy wucewa tayi ta bar gurin.
Amal ji tayi ƙafafuwanta gaba ɗaya sun mata nauyi, bama zasu iya ɗaukarta ba, dan haka ta tsugunna a gurin. Inda Allah ya taimaka ba giccin mutane sosai a gurin.
Ajiyar zuciya ya sauke ya durƙusa gabanta, ya ɗan sauke kanshi ƙasa yana sauke ajiyar zuciya, tsawon seconds talatin kafin ya ɗago kai ya kalleta.
"Kukan da kukeyi na san dalilinsa" Ɗagowa tayi ta kalleshi idanunta har lokacin cike suke da wasu hawayen.
"Mommy na kuka saboda an jaddada mata kwanakin da suka rage min a duniya, ke kuma kina kuka ne saboda yau kin san abinda baki sani ba"
"Me..mene..ya..ya..saka..kak...ka ɓoyemin?" Da ƙyar ta iya furtawa.
"Bana so ki shiga damuwa, bayan a yanzu ma kina cikinta, Mama ba lafiya kuma sannan in ƙara faɗin abinda zai ɗaga miki hankali ai bai kamata ba."
"Kenan bani da muhimmanci a gurinka?"
Kai ya girgiza tare da faɗin "Ka da kiyi min fahimtar bai-bai"
Miƙewa tayi cikin tsawa ta ce "Maheer ni baka ɗaukeni a yadda na ɗauke ka ba, bani da wata daraja a idonka, sai yau na tabbatar da bani da wani matsayi a gurinka. Saboda ni talaka ce ko? Mara asali" Tana gama faɗa tayi saurin wucewa tana kuka.
Har zai bita sai ga Doctor ya fito daga office tare da dakatar dashi.