HAWAYEN MARAICI

5

by @asmybaliyu

HAWAYEN MARAICI 5

By

Asmy b Aliyu

Karfe 7 na safe Dr .fatyma zahra tayi parking din motar ta a dai-dai part  din AY waya ta Ciro ta kirasa minti biyar ya sauko ya sameta tare suka shigo gidan suna tafe suna taba hira,Dr.fatyma zahra ma'akaciya ce kwararriyar wacce ke  aiki a karkashin (MAI KEKE  HOSPITAL) haka tana daya daga cikin family dectors din mai keke  shekarunta baxasu wuce 27 years ba a dunia bata da aure ,shiyasa Allah ya dora mata son AbdulHakeem amma sai dai baima San tana yiba.

"Ango kardai baka bi Amaryar mu a hankali ba?? Murmushin sa mai kyau ya saki kinji ki da wani xance zahra aiku  dama mata kun fiye raki  sai idan Abu bai sameku bane."

Daria tayi lokacin da suka iso falon bissimillah xauna bara na dubata."

Anan Dr. Faty tayi masauqi daya daga cikin kujoron da suka kawata falon,bin koina da kallo  take ,gidan yayi mata kyau Allah sarki ko wacece wannan mai sa'ar auren Mr.kai keke  ko wacece ita din Mai sa'ace.

Fitowar ta kenan daga wanka

Aka turo kofar dakin nata saurin dauke kanta tayi akansa shima fuska babu walwala ,Dan yaga alamar yarinyar nan naso ta raina sa kiyi sauri ki shirya ki fito ga Dr.nan taxo ta dubaki yana fadin haka bai jira Mai xatace ba yabar dakin.

dan karamin tsaki taja ji yadda yake mata magana a dage  anya kuwa asirin nan nasu zaiyi wani tasiri akan sa?

sai da tabata kusan minti Ashirin kafin ta fito cikin wata ya'r bingilar Riga  ta shan iska wacce da kadan ta wuce cinyoyinta

Haka rigar   Mai hannun taliya CE, Tayi parking gashinta a tsakiyar kai  simple make up tayi  akan fuskarta ,sai ya tsine fuska takeyi Dr.Faty ta daga kai tana kallonta tana mamakin ina Abdul ya samo wannan matar Dan ta tabbatar da badan fari ba da sai bolaaa.

Kunya sosai AY Yaji yanxu Dan rashin tarbiya haka xata fito da wannan shigar da namiji ne a haka xata fito kusa ga  Ay ta xauna sai dai Dr.zahra ce tayi mata sannu da gida.

A nan ta shiga  aikinta Dan taga matar ta AY.na tsananin ji da kanta tambayoyi ta shiga yi mata a ya'nga ce ta dinga bata amsa ,Dan wani irin haushinta  take ji Wanda tarasa ko na minene Dr.Faty tayi rubutu akan wata takarda ta kalli AY. Murmushi dauke a fuskarta Mr

Mai keke ga drug's nata  da xata bukata nan AY ya amshi takardar yana dubawa godia yayiwa Dr.Faty tareda damka mata 50k Har bakin motarta ya rakata.

Itama jawaheer bangarenta ta koma tana ta kumbure kumbure musamman yadda taga Abdulhakeem din ya sake da likitar da tazo dubata,Koda ta koma dakinta

Ta tarar da miss calls din maminta,

Zama tayi a bakin gado ta kirata

Mami na dauka ta fara yimata korafi,

Dariyar jin dadi Mami tayi cike da so da rarrashi take fadin"ai ni haka nakeso naji

Hakuri Zakiyi da kin Saba shikenan babu wahala,Mami kina bangaren mum ne Nazo?"nifa ba gidan jummai na kwana ba,

A hotel na kwana nida murja,

Muna ma tunanin barin bauchi a yau,

Cikin shawagaba da sangarta take fadin"Amman Mami Zaku zo ku dubani ko?"wallahi bakiga yadda yaji mun ciwo ba."dariyar bariki Mami tayi tana fadin"zamu zo mu dubaki my baby,Sai munzo kwanta kawai ki huta

Amman Dan Allah karki kuskura ki sha komai na maye kinga yanzu amarci kike kibari Sai an kwana biyu,shiru kawai tayiwa Mami,Dan ita kadai tasan dauriyar da take.

Bayan tafiyar Dr .fatyma Zahra Shima AY

Motarsa ya shiga ya nufi pharmacy nemowa Jawaheer magani,

####

Kusan qarfe 9 mum ta shigo apartment dinsu AY taci ado ta saka manyyan gwala gwalai a wuyanta Sai kamshi take zubawa

Bayanta Yan aiki ne kusan mutum biyar

Kowane da katon tray a hannunsa,babu kowa a falon sai karar Ac ta umurci Yan aikin da su Aje komai akan dinning area su fita,bayan Sun Aje Sai Mami ta rasa wane dakin jawaheer din take,ta kira wayar Abdulhakeem har yagama ring bai dauka ba,nan ta kira ta jawaheer Sai da ta kusa katsewa ta dauka, jawaheer an tashi lafia daman breakfast ne na kawo maku

Murya can ciki take fadin."ta tashi tana dakinta,Kai tsaye mum ta nufi dakin na Jawaheer,mum ta tsaya bakin kofa bayan ta tura kofar dakin tana kallon jawaheer

Dake tsakiyar gado zaune da waya a hannunta,mum ta karaso cikin dakin

da murmushi a fuskarta tana karewa jawaheer din kallo dan ta ta tabbatar da komai ya daidaita Sai taga jawaheer din wani iri alamar komai ya kankama

Zama tayi gefen bed ,dakyar jawaheer ta gaisheda mum ganin yadda take binta da kallo kamar wata tsohuwar manya.

Ina Abdulhakeem din yake ?

Mum ta tambaya tana kallon yadda Jawaheer ta mayar da hankalinta kacokam akan wayarta,ya fita tun dazu bai dawo ba.da mamaki mum ke fadin"a Ina zaije a irin wannan lokacin yabarki."tuni surutun mum ya fara damun Jawaheer,ta matsu ta fita tabar mata dakin,ina zan sani nida ke dakina mum,yanzu ma wanka zanyi

Jawaheer ta mike kamar da gaske ta nufi hanyar toilet mum ta bita da kallo

Jawaheer tana shiga ta wani tura kofar da karfi,bayan wasu mintuna mum tabar dakin.

Some hours latter.bayan AY ya dawo daga pharmacy Sai da yayi wanka ya nufi bangaren jawaheer,wannan Karon tayi wanka ta canja kayan jikinta riga da skirt ne ajikinta na atamfa Wanda suka kama koina dakyar take fitar da numfashi ,tun daga sama har kasa yake kallonta tayi kyau babu laifi ,haka ya tuna masa da daren jia.saurin kawar da tunanin yayi aransa,hannunsa nadama ya Mikamata alamar tazo Dan tana zaune ne akan doguwar sofa dake cikin dakin,wani irin ya'r taji tana kallon hannun nasa,

Nan take zuciyarta ta wani narke da sabon sonsa,ita har ga Allah tana son namiji Wanda ya iya soyayya sosai ,hannun tabasa babu musu ya mikar daita tsaye

Ya dan hadata da jikinsa,murya can ciki tamkar mai tsoron magana yake fadamata tayi kyau,narkewa tayi ajikinsa

Tana shakar kamshin dake tashi ajikinsa.

Tare suka nufi dinning area shi yayi serving dinsu ,tare Sukaci abinci ya bata maganinta.ganin yadda Abdulhakeem ya saki jiki Yana kula daita yasa ta Kara narke masa.wuraren qarfe 12 na rana

friends din AY suka shigo Anan sukayi breakfast gabadaya ta tsane su su kuma sai Janta sukeyi da hira a haka sukayi shirin tafia sukayi mata Alkhairi na ban mamaki babu yabo babu fallasa tayi godia ,Abunda yyi bala,in kular da AY kenan.

A  airport Tafeeda  ya kallesa gaskiyya matar nan taka bata da fara'a ko kadan kaga yanda take wani cin magani kodai first night din Kane na jia ya shafe mu??"

Sabida haushi AY ko amsa Tafeeda baeyi ba suna nan tsaye shida sageer jirgin su ya daga xuwa Abuja shi Kuma Nura sai jirgin Karfe 3 na Rana  zaibi xuwa Kano.

Wuraren Karfe 4 na yammacin Ranar friends dinta suka shigo,Suna zaune a falon kasa Sai shewa suke ganin yadda kwana daya kawarsu ta wani canja,

Daman turaren na mugun tane kika bani kikasa nayi amfani dashi billy,gaba dayan  su suka fashe da daria to meya faru?kice komai zamzam,

Harara ta watsa mata ban saniba,

Ihu billy tayi kice jiya kun kwana kuna aikin lada? Dogon tsuka jawaheer taja ke Dan Allah bakida aiki sae wannan maganar  mubarta kun san meye ta kalli sauran friends dinta biyu Feedo da Ummy nop sai kin fada??"

Mota nakeso Abdul ya siyamun?? Gaba dayansu   suka hada baki wurin fadin mooooootah!!

Kwarai kuwa yana ga kowacen Ku ta zaro ido??"....har kuna mamakin irin baxai yuyu ba ma kenan guy's karku damu Ku zuba eyesss naku kusha kallo har school na keso na cigaba anan     ,tunda na baro Legos baxai yuyu kuma nabar karatu na ba nayi bautar aure,Kun San dai a irin wannan gidan ko jirgi na bukata Zaa bani barantana mota,Daria billy tayi ta dora da fadin"hakane kawata Amman fa kema

Sai kin waye naga alamar xaayi fama dake,

"Kamar ya zaayi fama dani,kwarai kuwa

Ummy ta fada tana dorawa da fadin"kema

Sai da iya kissa da sarrafasa a bisa gado,

Jawaheer har ta Bude baki zatayi magana

Sukaji sallamarsu mum,tana ganin maminta tayi wurinta da sauri ta taho tayi hugging dinta,cikin shawagaba take fadin

Mami Sai yanzu?"Mami bata kula jawaheer ba ta kalli su billy dake gaisheda Mami,

Mami ta amsa a dakile ta kalli mum,

da Dan murmushi a fuskarta take fadin."jummai bari naga yarki na minti biyar,da haka Mami taja hannun jawaheer zuwa bangarenta,itama mum bangaren tabari.suna shiga daki Mami ta rufe kofa

ashe bakida hankali Jawaheer?"cike da mamaki jawaheer ke fadin me Kuma nayi Mami?"na dauka tun jiya xaki rabuda way'annan kawayen naki rabuwa na har abada!"cike da shock Jawaheer ke fadin

Kamar ya na rabu dasu har abada Mami,

Me sukayi mun?"Mami tayi wani murmushin takaici ke yarinyya CE bazaki gane mai nake nufi ba ,kin samu Abdulhakeem mai keke cikin sauki

Ina tabbatar maki da cewa idan kikayi wasa Zaki rasa sa acikin sauki.

"Ina son daga yau ki yanke duk wata Alaka keda way'annan kawayen naki,ke baki San acikin su wata na iya kyasa maki miji ba,

Haba Mami meyasa ma Zakiyi wannan tunanin ni friends dina ba haka suke ba wallahi,jiyama billy har turare ta Kawo mun,da sauri Mami ta katseta kikayi me da turarenta?"nayi amfani dashi mana,

Da gaske jawaheer bakida hankali Sai na tashi tsaye akan lamarinki ,ki dauko turaren nan kibani yanzu na tafi dashi,

Kafin nan Mami ta Bude Jakarta ta ciro mata wasu maganin ,ta Mika mata

Tana mata bayanin yadda Zatayi amfani dasu lallai kafin tabar bauchi Sai ta Raba jawaheer da way'annan kawayen Nata

Idan ba haka ba duk wani shirinsu zai rushe.ko mum data hada Auren,

Mami tana son ta koyawa jawaheer yadda Zata zauna daita ,dan tasan mum makirar macce ce,tunda Sun samu anyi Auren

Mallakar Abdulhakeem mai keke bazai masu wahala ba,Sai da Mami tasan yadda tayi tasa su billy gaba sukabar gidan Jawaheer....

#HAYEN MARAICI

#AY MAI KEKE

#JAWAHEER

#ASMY B ALIYU

#***