HAWAYEN MARAICI

6

by @asmybaliyu

HAWAYEN MARAICI 6

By

Asmy b Aliyu

Mahaifiyar jawaheer bata bar garin bauchi ba Sai data tabbatar jawaheer,tagama Shan duk wani magani da boka yace suyi amfani dashi haka sunga canji sosai

Dan a wannan lokacin soyayya Abdulhakeem din yake nunawa Jawaheer,tamkar babu gobe itama sosai ta saki jiki dashi,motar da ta fadamasa tana so tuni ta zabi kalar da takeso Wanda satin sama motocisu da sukayi order zasu iso.haka ya mata Alkawarin duk kasar da takeso zasuje suyi honeymoon dinsu nan da wata daya,ta kira Mami tana gayamata,itama sosai mamin taji dadi,Dan da mamin Zata koma lagos

Ticket ya siya masu haka ya saka Mata 500k a account dinta.

2 Weeks latter.

Yana cikin shigar bakaken suit wandda suka yi balain karbarsa yana rike da briefcase dinsa ya nufi bedroom din jawaheer ,daidai lokacin da agogon bangon dakin ya nuna karfe Tara na safe da sallama ya shiga dakin nata hango ta yayi tsakiyar gado tana barci abunta wani irin abu yake ji akansa wuyansa yakeji sam jawaheer,bata San yadda xata kula da miji ba,wurin kwanciya Zata zage ta basa hadin Kai ,Amman abincinsa kula dashi bata San yadda zata kula dashi ba saboda son jiki kullum cikin bacci take

Ya Rasa wane irin baccine wannan.

Tashin ta ya shiga yi ahankali ta shiga motsi gamida doguwar mika kafin ta bude idonta akansa wani sanyayyen kamshi taji ya daki hancinta.

Har kayi shirin fita office ne ??"ta fada da murya can ciki tamkar mai mura,

Ya kalli gashin kanta dake a hargitsa,

Ehhh xan fita

Break fast fa?? Auhh Peter bai gama hada break fast din bane?" Ina justina batayi serving dinka bane?"

Lokaci daya ta shiga jero masa tambayoyi wani irin mugun kallo ya shiga aika mata dashi ,waye ne xai cimaki abincin ya'n Aiki, ya'n Aikin ma Arna, acikin tsarina bana cin Abincin waje kona ya'n Aiki ya kamata ki canja!

kallonsa tayi gamida turo masa bakinta cike da shagwaba ,amma kasan aikin gidan nan baxan iya shi ni daya ba ko?"

Duka hidimar nawa guda nawa ne?

Zaman aure fa kika zoyi bautar Aure kike, Kar Dan aikin da ya Kara shiga part dina. Juyawa yayi yabar Mata dakin rai a bace,

anan ya tarar da ya'n aiki sai kai da kawo sukeyi duk inda ya wuce ,sai kaji ana fadin good morning sir."

Gidan hajja ya nufa acan yayi breakfast hajja ta tsaresa da tambayar ya kamata matarsa ta fara yimasa girki xuwa wannan lokacin " shidai bai ce komai ba yana gamawa yyi mata sallama ,Tsattsaye ya gaisa da mum.

Body guard nasa suka amshi jakar hannunsa xuwa mota.

Drivern sa na ajesa a company dinsa ,body guard dinsa suka take masa baya xuwa katafaren offishinsa Wanda ma'aikatan gurin sai russunawa suke suna kwasar gaisuwa.

Zaman sa keda wuya ..akayi knocking ,shuru yayi yana duba tarin files din dake xube a katon table dinsa.

Haka aka cigaba da kwankwasa kofar murya can ciki yake fadin "yes come in ..da sallamar sa ya shiga ya kwashi gaisuwa gamida mika masa wani fale ,Zubair hassan kenan wato P.A din AY.

Anan ya shiga dudduba file ya sauke ajiyar xuciya ya ya dago dara -daran idanunsa gamida saukesu akan zubair.

Yaushe ne presentation din?" Jibi ne sir .ohkey zubair ka shiryamin meeting dasu xuwa 2 na rana ohkey sir .

Da haka ya juya yabar office din fitar sa keda wuya sai ga sageer ya shigo da alamar yanxu ne shigowarsa dama kuma sageer A karkashin mai keke company yake aiki.

Ango !

Ango kasha mai irin wannan kyau haka wai meye sirrin ne?"

bana son iskanci sageer kayi abunda ya kawo ka ."Auh nikake fadawa magana.?" Tukuna dae ina Amaryar mu??

A karo na biyu ya zabga ma sageer harara ka bani ajiyar tane ?"...Wlhi AY.kana da matsala wai daga tambaya ban sani ba sageer!!

"Get out of my office now!

Lokaci daya sageer ya fashe da daria auh harda kora kuma karka manta nifa ne ? " sageer best friend dinka .

Babu shiri AY. Ya jawo laptop dinsa ya shiga aiki dan idan ya biyewa abokin nasa xai iya haukata sa , fisge laptop din sageer yayi ka aje wannan Mln magana xamuyi."

Sageer Dan Allah ka fitar min A office pls Naji xan fita amma ka saurareni first tukuna ina jinka ya fada fuska bbu walwala nan take shima sageer ya xama serious " wani sati xa'ayi order sabbin motoci daga kasar England ina ce kasan da wannan zancen??"

Na san da xuwan su sai kuma meye??

Sai batun presentation ."wandda kai ya kamata ka yisa ,kai na keso kayi sageer sabida jibi ina tunanin zanje Kano.

"Angel xata xo Hutu..woww kace muna da manyan baki a gari nayi shekara biyu banga Mimi ba tom.Allah ya kaimu amma ba tafiar mota xakayi ba ko?"

Ina tunanin ta jirgi xanbi xamu kwana daya sai mu dawo ,ina tunanin ma tareda jawaheer xamu tafi taga gidan Aunty salma."olryt Allah ya kaimu amin ni bara na karasa office.

Ohkey!!

Xuwa 2 dai xamu Shiga meeting olryt allah ya kaimu Amin amin."

4:30pm.ya dawo gidan A babban falo ya tarar da sarauniyar tasa ta hade cikin kana nan kaya Riga da wando wanda gabadaya kayan sun kama jikinta ,tana rike da waya tana dannawa, kayan fruit's ne Agabanta cikin wani kyakkyawn faranti tana dauka daya bayan daya tana ci a hankali

kamshin mijinta kurum taji ta Mai da hankalinta kofar falon cike da kewar mijinta tayi saurin isa gabansa tareda rungumesa tana masa sannu da xuwa.

"rabonsa da ya hada jiki da jawaheer tun anyi kwana biyu, ta karbi briefcase dinsa ta sakala A right shoulder dinta ,tare suka nufi up stairs .

Ita ta fara bude kofar dakin wani sanyayyen kamshi yaji ya daki hancinsa ,dakin ya dinga bi da kallo An gyarasa an canja masa xanin gado.

Kayan jikinsa ya soma ragewa yana kallonta waye ya gyaramin dakina??" Justina mana,ta fada tana masa wani fari da ido,

baki Bude ya saki yana kallonta idan ransa yayi dubu to ya baci mena fada maki daxun da safe??"

Meyasa bakya jin magana ne?"

So nawa xan fada maki bana bukatar wani dan Aiki ya shigo min a part dina ' this iz d first and the last time Jawaheer ,da xan maki gargadi na karshe idan wani dan Aiki ya kara shigowa a part din nan ranki xai baci.

Shike nan na shiga ukku!!

Tunda na aure ka banda kwanciyar hankali wai mekake so ne?"

Tafada cikin shagwaba,

You want to know??

Ya fada yana kallon fuskata kafin yace

"get out jawaheer."

Kallonsa take cike da mamaki, I said get out of my room.!"

Ya sake mai maitawa nan take idonsa ya juye xuwa bacin rai.

A fusace ta juya tabar masa dakin Stupid gal ' ya fada A xuciya anan ya shiga rage kayan jikin ya shige bathroom gamida sakarwa kansa ruwa. Yana fitar da wani irin huci yana tunanin matakin da xai dauka kan jawaheer,ya lura rarrashi da ban baki baya yi mata..

Karfe goma na dare yana xaune akan soofa yana aiki da laptop dinsa da alamar wani aiki ne mai muhimmanci.

Turo kofar dakin Akayi da sallama amsa sallamar yyi batare da ya kalleta ba gab dashi ta xauna ,tare da Jan karamin center table ta Dora cup tea din akai lokaci daya kamshin turarenta yagama cika wurin,yaji kamshin turaren ta Ya cika wurin ya dago ya kalleta tana cikin wata irin rigar barci light pink wacce Ake hango komai na jikinta.

Rigar barcin ba karamin karbar ta tayi ba ."kayi hakuri idan na bata maka rai tayi maganar gamida kama kunnenta duka biyu kayi hakuri ka yafemun dan Allah .aikinsa ya cigaba da yi batareda ya Kara kallonta ba.

Please mana !

Tayi maganar cike da kissa.

Har lokacin bai kulata ba babu shiri ta daura kanta a kafadarsa haka kuma ta riko hannunsa tana murxawa a hankali saukar hannunsa taji a bayanta da sauri ta dago tana kallonsa kayi hakuri?"

A hankali ya daga mata kai alamar ya hakura.

Nagode!

Ta fada cike da kulawa murmushi dauke a fuskarta ga lipton dinka." Hannu tasa ta dauka ta basa ya amsa a hankali yace ...

" nagode!

Tana gefensa har ya gama shan ruwan lipton dama kuma cikin shirin barci yake .

A nan saman jikinsa ta fara barci xuwa sha daya na dare ya rufe laptop dinsa A wannan lokacin wata irin matsanaciyar sha'awar take Addabarsa yadda ta kanainaye cikin jikinsa ,hannunsa ya saka ya dauketa tamkar wata baby ya nufi kan bed daita.kwantar daita yayi akan bed,

Ya nufi toilet alwalah ya dauro anan ya tada sallah Shafa,i da wutri.

Sai kusan sha biyu yayi shirin barci A hankali yazo ya kwanta gab daita gami da jawota a jikinsa A hankali ya fara Aika mata sakuna masu wuyar misiltawa Wani irin salo ya shiga nuna mata wanda nan take jawaheer ta manta daganan kuma ya dauketa ya kaita wata duniyar.

Washegari...

yau yayi mamakin kyakkyawar tarban da ya samu a gurin jawaheer ,gabaya ta canja da kanta ta hada masa special breakfast haka ta hada masa ruwan wanka ,ita ta taimaka masa ya shirya har suka yi break fast a tare.

Tare suka shiga part din hajja bayan ya gaisa da hajja itama jawaheer,ta gaisheta babu yabo bbu fallasa hajja ta amsa ta maida kallon ta akan Abdulhakeem maganar xuwa kano dauko lailah?

gobe ne hajja,

Amma kasan dani xa'ayi wannan tafiyar ko?

A lokacin AY. Yana tsaye hannayen sa duka xube cikin aljihun wandon sa yana cikin wani tattausan yadi sky blue.

ba karamin karbar sa yyi ba rage tsawonsa yayi haba granny kina haka xakice xaki bimu nan fa da kwana biyu kawai xaki ga Mimi na roke ki grandma kibar wannan tafiyar a jirgi xamu tafi ba'a mota ba nayi maki Alkawari kwana daya Mimi kurum xatayi a kano.

shike nan bbu damuwa yawwa my sweetheart "Dan haka sonki ke dada karuwa kullum a ruhina ina sonki hajja!

nima haka yaro na.

"Allah yayi maka albarka amin hajja ta.

Da haka yayi mata sallama har lokacin jawaheer ,na gefe tana sauraren su wata irin tsanar hajja takeji A ranta yadda taga AY na bata special kulawa hakan bakaramin kona mata zuciya yake ba,

yadda yake kula daita tasan ko rayuwar sa xai iya bata.

Tare suka shiga part din na mum,Wanda kwana biyu bataje wurin mum ba duk Yana cikin khudubar da maminta tayi mata.

#HAWAYEN MARAICI

#JAWAHEER

#AY MAI KEKE

#ASMY B ALIYU

#***