BAFULATANA🐄

Chapter 5

by @zmchubado

*BAFULATANA*

ZM~CHUBAƊO

     05

Murmushi moddibo ya yi  sannan ya juwaya ya janyo  ƙatuwar jakar da ya ke zuba magani idan ya ƙulla ya sa hannu ya  ɗaukko wani farin magani ya jiƙashi a wani madaidaicin kwano, sai da maganin ya ɗan ɗauki lokaci a cikin kwanon  sannan ya ɗagota ya fara ƙoƙarin bata. Ba ta yi masa gaddama ba ta karɓa tasha sabda bata ƙin magani kokaɗan. duk  abinda suke idon sa ya na Kansu sai kallon su ya ke a ransa yana mamakin yanda moddibo yake Iya gane duk wani ƙullin maganin dake cikin jakar, shi a tsarinsa be yarda da maganin Gargajiya ba sai na Asbiti saboda a cewarsa wai a maganin Gargajiya ba ya maganin cuta dake damun mutum sai dai ma ya ƙara maka wata cutar da baka da ita.

Amma sai ga shi a yau maganin Gargajiya ya yi masa ranar da ko a mafarki bai taɓa zaton hakan zata faru ba, haƙiƙa duk wata baiwa da ubangiji ya yiwa bawansa ado da ita ba abar rainawa bace, ga shi tun ba'aje ko'ina ba ya samu kansa a ƙarƙashin Abinda ya jima yana  Rainawa.

A hankali zuciyarsa ke motsawa tana karɓar abinda idanunsa suke gani, nan nan sai yaji abin ya fara birgeshi sosai.

Haƙiƙa sanin itace shima Ilimine mai zaman kansa sai wanda Allah ya horewa sani  kaɗai ne ke yin irin abinda Baffah keyi a gabansa. B ata jima da shan maganin ba baccin da ba ta samu tayi a daran jiya ba ya ɗauketa, abin mamaki tana baccin tana haɗa gumi kamar amma kuma hakan bai sa ta farka daga baccin da ya ɗauketa ba, gumin da ya ke kwance saman goshinta Baffah ya kalla shine ya bashi tabbacin cewar zazzaɓin ya sauka.

Matashin ya kalli Baffah cikin alamun na nuna da damuwa a fili ya ce,"ya Kamata kayi wani abu again ka kalli yanda take gumi ko dai zamu kaita asibiti ne?"

Kallon tsaf Baffah ke binsa dashi da mamaki kwance akan fuskarsa ya ce,"hmmm a wannan ƙungurmin Dajin kake tinanin Samun Asibiti?"

Ba tare da tunanin komai ba ya ce,"So because you live in the bush, you won’t be able to take her to the hospital in town just for a check-up?" 

kau da kai Baffah ya yi saboda shi ba fahimtar wannan turancin banzan nasa yake ba. Ya ci gaba da aikin gabansa hakanne ya sa matashin ya murza goshinsa ya ƙara cewa,"Baba saboda kuna rayuwa a daji bai isa ya zama dalilin da zai hanaku zuwa Asibiti idan buƙatar hakan ya taso ba, za ku iya samo abin hawa ko kuma kuyi amfani da dabbobinku kuje Asibiti, amma wannan ba dalili bane da zai sa ku zauna hakanan babu kulawar likita."

Tunda ya fara magana Baffah ke haɗa maganin da zai fita dashi bai katse shi ba har sai da ya kai aya, sannan ya ɗaga kamilallun idanunsa ya yi masu masauki a kyakkyawar fuskar matashin na ɗan wani lokaci, sannan ya sauke idanunsa yanayinsa na canzawa.

Bai yi niyar bashi amsa ba amma jin yanda yaron ya yi maganar ya sa ya ji a ransa ba zai iya shareshi ba dole ya bashi amsar da ya ke nema ya ce,"yaro ka kalleni nan tunda ƙuruciyata har na fara manyanta ba mu taɓa tunanin muyi nisa da wannan dajin ba, tun shekaru talatin da biyar da suka wuce muka zo nan muka yada zango damu da jama'armu, a haka muke rayuwa bamu taɓa neman wani abu mun rasa ba.

Asalin mu 'yan jihar Adamawa ne iyayen mu mazaunan ƙaramar hukumar Numan ne can cikin daji muke a nan rugar mu take, garin mu garin alheri ne wanda ubangiji ya wadata da albarkatun ƙasa masu yawa, duk da kasancewar mu fulani makiyaya amma mu manoma ne wa ƴanda muka dogara da kanmu. Haka muke rayuwar cikin aminci da kwanciyar hankali kwatsam ba zato ba tsammani wani gagarumin iftila'i ya faɗa mana, ba don zuciyar mu naso ba don dole haka mukai hijira mu ka bar nahiyar mu zuwa nan muka fara sabuwar rayuwa har muka saba."

Shiru ne ya ratsa gurin na ɗan lokaci sannan Baffah ya sauke ajiyar zuciya yaci gaba da cewa,"Mu uku kacal iyayenmu suka Haifa, mu biyu ne maza sai ƙaramar ƙanwar mu BAƊƊO wadda a halin yanzu ban san inda take ba ta na raye  ko ta mutu Allah shine masani."  Ya faɗi hakan hawaye na zubowa da ga idanunsa.

Duk yanda ya so ya danne kukan karya fito haka abin yafi ƙarfinsa sai kawai ya fashe da kuka, wani irin kuka ya keyi wanda ya daɗe beyi irin sa ba a wannan lokacin, sai dai ko da wasa Matashin beyi yinƙurin ya dakatar dashi ba saboda ya lura kukan da ya keyi da ga ƙasan zuciyarsa ya ke tahowa, wannan ya sa ya barshi ya yi mai isarsa har zuciyarsa ta yi Sanyi. 

Sai da yayi me isarsa sannan ya dedaita nutsuwarsa ya cigaba da cewa"tun da ga ranar da muka nemi ƙanwata Baɗɗo muka rasata muka shiga tashin hankali mara misali bayan wanda muka samu kanmu a ciki kafin ɓatanta, wannan dalilin ne yasa muka tattara ƙwanmu da ƙwar-kwatan mu mukabar NUMAN muka dawo nan da zama sakamakon ƴan fashin da suka sa mu a gaba ba dare ba Rana, babban takaicin ma shine ba Iya fashin da suke mana bane matsalar har yaran mu mata ƙanana suke yiwa Fyɗe a gaban idanun mu ba tareda imani ko tausayi ba. Wannan Shine dalilin da yasa muka bar jaharmu ta asali muka dawo wannan dajin, dik kan mu da kake gani duk ƴan uwan juna ne, shiyasa muke zaune lfy lau a nan ɗin ba tareda mun leƙa cikin gari ba kai ko hanyar titi bama bi tunda ɗan Uwana Zakariya ya gamuda Haɗarin mota a lokacin da zai tsallaka titi tareda shanun mu, a wannan lokacin munyi ƙoƙarin ganin mun kaishi Asibiti saboda munin da haɗarin ya yi, da babur ɗin malm Iro muka tafi saboda wanda ya kaɗeshi da motar ya gudu, mu uku muka nufi Babban Asibitin Gwamnati dake cikin garin gyambu Amma sam suka ƙi taimaka mana wai sai munzo da ɗan'sanda, munaji muna gani a gaban idon mu Zakariya ya rasa Rayuwarsa, a wannan lokacin munyi kuka har mun gode Allah sannan muka sake ɗakko gawar muka dawo da ita gida, tun daga lokacin zuwa Asbiti akan wata lalura ya ficemin a rai wllh ko sunansa bana son ji, saboda mutanan mu na wannan lokacin a cike suke da son zuciya da Rashin tausayin talaka."

Sosai jikin matashin ya yi sanyi da labarin Moddibo wanda yay matiƙar taɓa masa zuciya sannan ya ce "A zaman da nayi a tareda kai na fahimci kai mutumin ƙwarai ne kuma mai baiwa ta musamman a cikin mutane, Baba kana da wata ɓoyayyiyar baiwaa wadda kai kanka baka san iyakarta ba, da ace Hukumar lfy zasu samu labarinka tabbas da sun Amfana da kai."

"Hmmm kai dai ai sha'ani kawai yaro amma lamarin mutanan dake cikin wannan duniyar tsoro yake bani, wata rana da yamma bana mantawa wasu mutane suka shigo mana Nan da sunan Su jami'an hukumar lafiya ne, kuma sunzo ne don su kafana mana Sansanin kiwon lfy a nan sbda muma mu samu cigaba. Ba tareda tunanin komai ba muka karbe su hannu biyu Ashe abinda bamu sani ba cutarmu sukazo suyi, wasu da ga cikin mu kasuwanci shanu sukeyi wanda ya zame mana tamkar Sana'ar Gado, saida suka bari kowa ya dawo daga kasuwancin sa yaxo da kuɗaɗe masu yawa sannan suka far make mu cikin Dare suka ƙwace komai sannan suka kashe na kashewa, 
Tun daga lokacin muka daina karɓar baƙi gabaɗaya.

Shiyasa da naji ka ambaci sunan Asibiti kaga yanayina ya canza wllhi ko sunan Asibitin banason ji, yanzu zancen da nake maka da mutanan Rugar nan zasu samu labarin zuwanka tabbas da se sun koreka kokuma ma su kashe ka.

A firgice Matashin ya zaro manyan idanunsa yana Baffah jin kalmarsa ta ƙarshe wato kisa sannan yace "to Baba meyasa lokacin da abin ya faru Baku nemi tai makon jami'an tsaro ba?"

Moddibo ya kalleshi ya yi murmushi irin na takaici ya ce" yaro da fari munyi ƙoƙarin gwada hakan amma daga baya se muka gane itama hukumar se a hankali, jinin jikin mu kawai suke zuƙa ba matsalar mu bace a gabansu."

Matashin ya yi shiru a zuciyarsa ya ce,"Ashe Dama a kwai mutane masu fiskantar irin wannan rayuwar?"

Bai taɓa zaton a kwai irinsu moddibo dake Rayuwa a cikin wannan halin mai cikeda ƙunci ba,
Haƙika Allah ne ya Ƙaddara zuwansa wannan gurin dan ya ƙara Imani a kan rayuwar duniya, haƙiƙa ba ka sanin Allah ya yi maka wata ni'ima a Rayuwarka har sai ka ga wanda be kaika ba tukunna kake sanin Allah yayi maka Gagarumar Ni'ima.
 
Haka kawai sai ya samu kansa da jin tausayin su tareda ƙudurtawa kansa cewar in sha Allah sai ya temakesu da wani jinjinan Abu daze Amfanesu a rayuwarsu da izinin Allah.

Tunda garin Allah ya waye Jaddah ta fice da ga Gidan saboda bata da wani buri rayuwata da ya wuce Rayuwar Rabe ta lalace, tafi so ta yi Rayuwa a ƙasƙance ta ƙare a tantal baɗeɗe ba wata manufa, shiyasa ta ɗorawa zuciyarta tsanar yarinyar tun bata kai haka ba, duk wani buri na Jaddah a yanzu be wuce taga ta samu haihuwa da Moddibo ba ta hakane kawai zata iya mallake dukiyar sa.


********

*ZAFAR ENTERPRISES*

 Shararren Companyn da ya yi shura a ɓangaren kasuwancin fata a ƙasashen Duniya guda 2 , waƴanda suka haɗa da America da ƙasar Jamus da sauran ƙasashen duniya wanda camfanin yakewa safarar fata daga nan gida najeriya, wannan shahararren company mallaki ne ga babban Ɗan kasuwar nan Alhaji Abdulwahab Abdullah.

Dandazon ƴan Jaridane a harabar Babban Companyn nasu dake birnin taraiyya abuja.

Wani farin Mutumine ya fito daga cikin kamfanin wanda ba zai wuce shekaru Sittin da biyar a duniya (65years) Sanye cikin wata dakakkiyar Suite Baƙa samfurin ƙasar italiya, tafiya ya keyi Fuskarsa babu Annuri ko kaɗan sai bodyguards ɗinsa majiya ƙarfi kimanin Mutum biyar suna take masa baya harya ƙarasa inda ƴan jaridar sikr, sina ganinsa su kai masa caa tamkar ƙudajen da sukai arba da Buhun Sikari, abinka da babban mutum kuma mai wahalar gani.

Kallo ɗaya za kayi masa ka fahimci yana cikin hankalin mai girma wanda ɓatan ɗansa ya sabbaba masa, yau wata huɗu kenan amma babu wata ƙwaƙƙwarar magana akansa. cike da damuwa ya kai hannu ya sauke farin gilashin ƙara ƙarfin ganin dake sagale a idanunsa sannan ya fuskanci ƴan jaridar dake tsaye a gabansa. Zuciyarsa ce tayi rauni a lokacin da ya tuna sallamarsu ta ƙarshe da ɗansa, wani irin takaici ne ya ƙara samun muhalli a zuciyarsa saboda shi bai san abinda ƴan jaridar nan suke nema dashi ba, wannan wace irin masiface?

A halin da yake ciki a yanzu ba yajin zasu iya samun koda kalma ɗaya daga gareshi, Wata matashiyar yarinya ce ta fito daga Companyn itama sanye da Suite Royal blue riga da wando, ƙafarta sanye take cikin wani dogon takalmi me tsinin gaske ta sanya wata irin hula a kanta mai faɗi itin ta mata ƴan ƙwalisa, sannan ta rufe idanunta a cikin wani baƙin glass wanda ya mamaye rabin Fuskarta.

A ƙasaice take tafiya har ta ƙaraso inda ƴan jaridar suke ta tsaya daga gefan Dattijon ta ce"duk wanda ke da burin yiwa Mahaifina tambaya toya dunƙuleta a guri guda ya faɗeta don bamuda lokacin ɓatawa." sannan ta kalli Mahaifin nata tayi murmushi ta ce"Abie ya kamata kayi magana dasu ko da ba mai tsaho bace."

Cikeda ƙosawa ya dubeta yace "Fadilah, there’s nothing I can really discuss with them. Just tell them to leave I’m already dealing with my own problems." ya faɗa yayin da aka buɗe masa mota ya shiga suka bar harabar kamfanin zuciyarsa na zafi akan jarrabawar data sameshi ta ɓatan Ɗansa.



Zmc💋
***