Chapter 6
by @zmchubado
*BAFULATANA*
Zm~Chubaɗo
06
Zame glass ɗin da ke fuskarta ta yi ta raka motar Abie da kallo zuciyarta na aiyana mata abubuwa masu yawa akan burinta, sam ba haka Fadilah taso ba taso ace Abie ya yi magana da ƴan jaridar a lokacin da take tsaye a gefansa, ko ba komai ita ma ta samu sunanta ya ɗagu a duniya kamar na Yayanta Muzaffar, tsaki taja sakamakon rushewar plan ɗin data jima tama shiryawa, sai kawai ta bar gurin zuwa inda ta yi parking motar ta shiga ta zauna sannan ta bi bayan Abie.
A cikin watanni biyar ɗin da suka shuɗe da ɓatan MUZAFFAR ABDULWAHAB ABDULLAH C.E.O of Zafar Enterprise ba ƙaramin girgiza Al'uma abin ya yi ba, abinka da masu hannu da shuni duk wata kafar sada zumunta da mutum zai leƙa sai ya ci karo da da sanarwar ɓatan Muzaffar, amma har yau ba bu wani cigaba da aka samu ko wani labari da zai nuna cewar yana raye.
A bangaren jami'an tsaro suma a nasu ɓangaren suna gudanar da binkice akan case ɗin cikin ƙwarewa da sanin makamar aiki, mu samman da ya kasance ƙwararren jami'i aka ɗora akan case ɗin wanda ya cimma nasarorin aiki tareda lambar yabo mai girma. Amma duk ƙoƙarin da bin diddigi irina Acp Galadanci har yau babu wata tartibiyar makama da aka samu.
*** *** *** ***
MAITAMA WUSE II ABUJA.
Unguwace da ta haɗa manyan Ginaginen alfarma ma su tafiya da zamani, duk wani ƙusa da ya amsa sunansa a cikin ƙasar najeriya ya na da property a wannan unguwar, wannan dalilin ya sa masu hannu da shuni su kai mata ƙawanya ta ko wani angle.
Wasu manyan haɗaɗɗun prado's ne baƙaƙe suka danno kai cikin jerin gwano, gabaɗaya motoci shidan ko wacce ɗauke take da Sunan Alhaji Abdulwahab Abdullah, a gaban wani tangamemen gida na alfarma su ka tsaya.
Na gaban ne ya fara matsa horn sannan Get ɗin ya buɗe kansa motocin su ka shiga zuwa cikin babbar harabar gidan wadda aka ƙawata da shukokin zamani.
Da hanzari Guard ɗinsa ya buɗe motar farko ya fita, sannan sauran suma suka futo a tare sika tsaya kamar gumaka, ɗaya da ga cikin Guards ɗinne ya buɗewa me gidan nasu ƙofa ya fito, Direct ƙofar da zata sadashi da maine Perlour ɗin dake gidan ya nufa still fuskarsa da wannan damuwa bata gushe ba.
Hajiya Sakinah ce zaune kan ɗaya daga cikin luntsuma-luntsuman Royal chairs ɗin dake falon hannunta ɗauke da Rumote tana kallon abinda ke faruwa a duniya, kallo ɗaya za kayi mata ka fahimci tana cikin babban tashin hankali mara misali, amma hakan bai hana ƙwalisarta futowa fili ba, ƴar gayu ce ta gani a bada labari wannan ya sa ko ba tai kwalliya ba idan ka kalleta sai ka rantse da Allah shigar alfarma tayi don ta nuna wadatar da take da ita, Hajiya Sakinah irin matan nan ne waƴanda su ka maida kwalliya ta zama tamkar jinin jikinsu wannan ya sa take da matsayi na musamman a zuciyar mijinta dukda tarin fitinarta a wasu lokutan.
Da sauri ta nufeshi cikin maɗaukakin tashin hankali da koɗaɗɗun idanunta waƴanda ke baiyana tsantsar gaskiyar dake ranta ta ce,"Abie har yanzu babu wani labari akansa ko?"
Kasa ce mata komai ya yi saboda bai san abinda zai gaya mata ba, ko da ace ya gaya mata ɗin ma ba zata fahimceshi ba saboda yanda idanunta su ka rufe akan ɓatan ɗansu. Shi kansa ya kasa nutsuwa akan lamarin balle ita mace wadda take da rauni amma ba shi da wani zaɓi wanda ya wuce ya gaya mata gaskiyar da baya son gaya mata ɗin. A hankali ya kama hannunta cikin nasa in a very low voice wadda ke cike da alhini ya ce,"har yanzu ba wani labari sabo akan case ɗin, amma in sha Allahu ina kyautatawa Allah zato akan wannan jarrabawar da ya yi mana."
Kuka Hajiya Sakinah ta fara sannan ta zame hannunta da ga cikin na Abie ta ce,"wllh inaji a jikina tamkar wani babban al'amari ya faru da yarona! Kullum bana iya bacci saboda tunanin halin da yake ciki, jiya naje gidan Kwamishina da kaina mun zauna akan lamarin yace zasu ƙara tsaurara bincke akai, kullum abu ɗaya akai maimaita min tsahon wata biyar babu wata kyakkyawar makama, wllh Abie nima kuna dabda ku Rasani muddin Ba'aga Muzaffar ba!" ta firta hakan tana ƙara sautin kukanta.
Kansa ne ya yi wata irin sarawa saboda yanda kalamanta suka yiwa zuciyarsa wani irin fami, lumshe idanunsa ya yi sannan ya ce,"Haba Sakinah ke fa musulma ce wadda ta yarda da Allah da kuma manzonsa, ya kamata kiyi imani akan dukkan abinda Allah ya aiko miki mai daɗi ko mara daɗi, muzaffar fa ba ɗanki bane ke kaɗai nima ɗana ne wanda nake ƙauna fiye da duk ƴaƴan da ki ka haifa mini, meyasa kikeso ki ƙara ɗaga min hankali ne saboda Allah?"
Kasa cewa komai tayi har Fadilah ta shigo falon, tsayawa ta yi tana karantar yanayin dake fuskokinsu sannan ta isa tsakiyar falon kanta tsaye ta zauna a gefan Abie ba tareda tace dasu ƙala ba. Wata uwar Harara Hajiya Sakinah ta watsa mata Sannan ta ce," wai Fadilah me ya ke damun tunaninki ne?
wannan wace irin shiga ce sai kace ɗiyar Kafurai? Har zuwa wani lokaci zaki ɗauka a haka kafin kiyiwa kanki faɗa a Rayuwarki?"
"Mom what is wrong with this outfit for God’s sake?"
"Uwarki ce aibun. na ce Uwarki ce aibun Fadilah." Momy ta katseta ta hanyar faɗar hakan sannan ta ƙara da cewa "ba zance komai a kanki ba tunda Allah sheda ne akan irin tarbiyar dana baki, yanzu ke don Allah ko kunya ba kiji ba Ace ɗan uwanki namiji an nemeshi an rasa tsahon wata biyar kenan amma ke kina nan kina yawo a gari da shigar ƴan iska anya kuwa kina tsoron Allahkuwa?"
Miƙewa Fadilah tayi tana tura baki tabar Falon tana faɗin,"aini dama an daɗe da tsanata a gidan nan kowa yafi fifita Yaya Muzaffar akan kowa, da ace nice ma na ɓata I'm sure babu wanda ze damu irin haka daga ke har Abie ɗin." Ta faɗa tana jan ƙofar glass ɗin dake falon da ƙarfi.
Da ido kawai suka bita aka rasa wanda zai ce komai.
**** **** **** ****
RUGAR ARƊO
A kwana a tashi ba wuya a gurin Allah yau Matashin ya cika watanni biyar tareda iyalan Baffah, zuwa yanzu ya samu sauƙi sosai sai dai taɓon ciwukan kawai, a ɗan watannin da ya shafe tare dasu ya koyi abubuwa masu yawa a tareda su sannan shima ya koyar dasu wani abu da ga cikin ɗabi'unsa na yau da kullum.
Zuwa yazu matsayin da baffah ya ke dashi a zuciyar matashi ya jima da canzawa, sannan ya canza masa suna da ga wanda ya taimaki Rayuwarsa zuwa Maysayin na Uba, tabbas moddibo mutum ne na musamman wanda ya kamata ya bawa muhali mafi daraja da ga zuciyarsa, saboda samun irinsu a wannan lokacin abune mai matiƙar wahala.
A ɗan zaman da ya yi tareda su ya ƙara ilimi akan zamanta kewar Rayuwar duniya musamman ta ɓangaren mu'amala da jama'a.
Rabe ce ta fito da ga bukkar Baffah hannunta ɗauke da babbar Fanteka za taje ɗebo Ruwa a rafi, a zaune ta samu Matashin ya zubawa Shanun dake cikin garke idan, har ta ƙarasa gurin be sani ba saboda nisan da ya yi a cikin duniyar tunani, ganin haka ya sa ta ɗauki wani ƙaramin sanda ta jefa masa.
Miƙewa ya yi da Sauri yana kallonta sannan ya haɗe Rai ya ce"What’s wrong with you?" sai da ya kalleta sama da ƙasa sannan ya ɗan ja tsaki saboda sanin ba gane abida ya faɗa tayi ba, common Hausa ma wani abun se yayi da gaske sannan take Fahimta balle kuma turanci.
Ganin yanda fuskarsa ta sauya sosai ne ya sa tayi dariya har seda beauty point ɗinta suka lotsa sannan ta ce " Amma dai kaɗo anyi ƙaton banza Aradu, yanzu kai saboda Allah wannan abinne ya razanaka haka?"
"That girl is completely crazy, for real." ya firta hakan yana murza goshinsa wanda hakan ya zame masa tamkar ɗabi'a.
"kaɗo karkayi ƙunci don Allah." ta faɗi hakan tana ƙoƙarin laƙa fuskarsa, cikin rashin sa'a fantekar ta faɗa masa a jiki.
Turo baki ya yi sannan ya ture kwanon da ga jikinsa ya ce,"ke kalleni da kyau wai nayi maki kama da shashasham ƙauyene da kike ƙoƙarin mai dani sakarai abokin wasanki?"
Dariya ta yi sannan ta durƙusa ta ɗauki fantekar ta juya a hankali zata bar gurin ya ce,"Ke!"
Tsayawa tayi sannan ta juyo har lokacin bata dena dariyar da take ba, hakanan sai ya ji a ransa bai kyauta ba akan hantarar da yake mata, saboda tunda yazo gidan su itace ke ɗawainiya da duk wani abu da ya shafeshi bata taɓa nuna gajiyawa ba.
Sosai yake kallon innocent face ɗinta wadda ke cike da tarin ƙuruciya, hakanan sai zuciyarsa ta bashi umarnin yayi mata martanin dariyar da take masa, sai kawai ya yi murmushi ya ce,"ni sam ba matsoraci bane." ya yi maganar a sanyaye kamar ba shi ba.
Dariya ta sakeyi sannan ta ɗaga idanunta a hankali tana kallon reshan bishiyar dake saitin kansa, ba tareda tace dashi ƙala ba, jin tayi shiru ne yasa ƙara kallonta ya ce,"me kike kallo haka?"
Ɗaga kafaɗunta ta yi sannan ta ce,"kawai Gizo-gizo nake kallo a saman kanka." ta yi maganar tana nuna masa shi da hannunta.
Ihu ya saka sannan ya daka wani Uban tsalle ya ya faɗa kanta suka faɗi ƙasa a tare still yana ihun bai bari ba, jinsa a jikinta ya sa ya ƙanƙameta yana ƙara shiga da ita cikin jikinsa ya hanata motsi. Ƙoƙarin tureshi take amma ya hanata wannan damar sai da yaji numfashinta yana ƙoƙarin katsewa sannan ya yi saurin janye jikinsa daga ruƙon da ya yi mata.
Har lokacin ƙokarin jan numfashi take bai gama dawowa dedai ba amma haka ta yuunƙura ta tashi, ta fara karkaɗe jikinta ta ce,"Kaɗo amma dai ka iya mugunta kalli yanda duk ka talitse mini nono." ta yi maganar tana ƙoƙarin ɗaga masa rigarta wadda ta suturta ƙirgar dangin da sika fara futowa a ƙirjinta.
da Sauri ya miƙe ya bar mata gurin tun kafin ta aikata abinda tke ƙoƙarin yi saboda ya lura gabuwace ta gaske, tura baki tayi sannan ta ɗauki fantekar ta nufi Hanyar Rafi tana ƙyalkyala masa dariya wai mai tsoron gizo'gizo. Sai da ya tabbatar da ta bar gurin sannan ya dawo ya tsaya a gurin yana murmushin, gwiwar hannunsa ya kalla ya ga jini sai a lokacin ya lura da kujewar da yayi lokacin da suka faɗi ƙasa tare.
Hannunsa zuba cikin aljihun wandonsa sannan ya bi bayanta yana tafiya cikin nutduwa har ya rusketa, suna tafiya tana yi masa hira har suka isa babban kogin, takalmin ƙafarta ta cire sannan ta janye zanin jikinta sama sosai har ana iya ganin fatar gwiwarta, sanɓan ta saka fantekar a ciki ta kamfato ruwan ta fito dashi.
A hankali ya janye idanunsa daga kan kyawawan diga'diganta yana mamakin girman da dantsen ƙafarta ke dashi. Ruwan ta kinkima ta ɗora a kanta sannan ta kalleshi ta ce,"muje kaɗo"
Bai ce komai ba sika kama hanyar gida, tafiya kawai suke bame cewa wani ƙala a tsakaninsu har suka iso hanyar data raba Rugarsu Rabe da Rugar su Bamanga. Har cikin ranta addu'a take Allah ya sa kar su haɗu da mutanan Bamanga a hanya, ba ta gama addu'ar dake ranta ba sika kewayesu.
Ɗaure Fuska Rabe tayi tana kallon Bamanga cikin harshen fulatanci ta ce,"meye haka za ku tare mana hanya kamar wasu ƴan Daba?"
Kallon tsaf Bamanga ya yi mata Sannan ya ce,"yanzu ke har kinada bakin magana akan na tareku? Yau kwa nawa kenan ina zuwa gidanku kullum seki ce min in tafi baki da lfy? Ashe wannan gardin shine ciwon dake hanaki fitowa gurina ko?" Bamanga ya faɗi haka yana nuna Matashin dake gefan Rabe a tsaye yana kallon ikon Allah.
A ƙarshe da abin ya isheshi Fantekar Ruwan ya sa Hannu a kanta ya ɗauka sannan ya kalleta ya ce,"I’ll go now, when you’re done with them let’s just meet at home" ya yi maganar fuskarsa ba yabo ba fallasa ya yi tafiyarsa ba ko waiwaye.
Be jima da barin gurin ba Rabe tabi bayansa da gudu tana kiran sunansa, lokaci guda Su Bamanga suka bita da idanu baki a Sake.
A iya lokacin da matashin ya kwashe a tareda su akwai wata shaƙuwa da Allah ya saka a tsakaninta da shi sai dai kai tsaye ba zamu iya fassara shaƙuwar da sunan syayyah ba, tafi kama da soyayyar ƴan'uwantaka saboda a cikin tsarin matashin babu agender soyayya a lamarin sa.
Wannan shi bahaushe ke kira da sabo tirken wawa, a haka suka shafe watanni masu yawa a muhali guda. Sosai ya ke jin daɗin Rayuwar Rugar amma har cikin Zuciyarsa yana kewar Mahaifinsa da mahaifiyarsa, idan tunanin ya isheshi sai kawai yabi Rabe su tafi kiwo saboda baya so tunanin ya yi nasara a zuciyarsa ya haifar masa da damuwa, wannan dalilin yasa yake binta kiwo duk don ya ragewa kansa damuwa.
Bayan sun dawo da ga kiwo a ranar Baffah ya zauna dashi sukayi magana akan ya kamata ya koma gida gurin iyayensa, jikinsa a sanyaye ya ɗaga kai ya kalli Baffah ya ce,"a yanzu bani da niyar komawa gida Baffah, amma idan kace na tafi dole haka zan tafi ɗin."
Shiru Baffah ya yi na ɗan wani lokaci sannan ya ce,"ban faɗi haka saboda na ƙosa da zama da kai ba yaro, kawai abinda ya kamata nake gaya maka saboda suma iyayenka sina da haƙƙi akanka, ina jin tsoron kar rashinka a kusa dasu ya haifar musu da wata damuwar ta daban, idan har zan iya tunawa dedai saura watanni biyu ka cika shekara a tareda mu."
"Eh hakane Baffah Amma don Allah ka ƙara min lokaci kaɗan kafin in tafi." cewar matashin.
Jinjina kai Baffah ya yi sanan ya ce,"Allah ya zaɓa abinda yafi zama alheri a garemu gabaɗaya."
"Amin ya Allah." ya faɗa a sanyaye. A haka hirar ta su ta dasa aya suka kama wata ta daban.
A haka rayuwa ta dinga tafiyar masu cikin Aminci da ƙaunar juna, sun ɗaukeshi ɗaya daga cikinsu ba tareda nuna banbanci ba, wannan yasa shima a tasa zuciyar ya basu matsayin ƴan uwansa na jini.
BAYAN WATA BIYU a tsakani da safe moddibo ya gama haɗa masa komai nasa wanda ya tsinceshi da shi saɓanin Rigarsa wanda jini ya ɓata da kuma yagewar dake jikinta yasa moddibo ya jefar tun a washe garin Ranar da ya tsince shi.
Wata rigar farin Saƙi ya ɗakko ya miƙa masa ya ce "karɓi ka saka wannan a jikin ka, na san idan ka kalli Rigar watarana zaka tuna damu."
karɓa yabyi jikinsa a sanyaye ya saka a jikinsa lokaci guda kuma ya maida kallonsa ga Baffa, sosai Rigar tayi masa kyau sai ya rikiɗe ya zama bafulace zirr.
Bayan ya gama shiryawa Baffa ya zama yana fuskantarsa ya ce," duk abinda aka sakawa lokaci komai nisansa sai yazo, yau dai ga shi ka warke cikin ikon Allah bayan doguwar jinyar da ka sha a tareda mu. Har yanzu bamu san komai a kanka ba tsahon shekara ɗaya, sai nake ganin kamar ya kamata mu san wani abu a kan Rayuwarka ko ba komai ma ƙulla zumunci, Saboda wata rana bamu San a inda zamu sake haduwa da juna ba"
Sosai kalaman Baffah sukai masa wani irin duka a zuciyarsa, alhini da tarin damuwa ne su kai masa rubdugu saboda har cikin zuciyarsa yake jin tsohonsa, haƙiƙa gaskiya ya fada zuwa yanzu ya kamata ya gaya masu shi wanene.
Murmushi yayi sannan ya sunkuyar da kansa ƙasa ya ce," kayi haƙuri Baffah amma nayi maka ƙarya."
Shiru Baffah ya yi yana kallonsa saboda bugawar da zuciyarsa keyi, tsorone ya cika zuciƴarsa jin abinda matashin yace, a hankali ya tattaro sauran jarumtar data rage masa ya ce,"ƙaryar me kayi mini?"
Ka sa kallon idonsa matashi ya yi saboda kunyat abinda ya aikata ya ce,"Baffah nayi maka ƙarya a lokacin daka tambayeni sunana."
"kana nufin ba sunanka Muhammad Kamar yanda ka gaya mana ba?" Baffah ya jefa masa wannan tambayar
ɗaga masa kai ya yi alamar Eh sannan ya buɗe baki ya ce,"Sunana Muzaffar Abdulwahab Abdullah C.EO of zafar Enterprises.....!"
ZMC💋
***