A CIKIN IDO...

Shafi Na Takwas

by @sanazty

A CIKIN IDO...

Ake tsawurya

Wattpad @SaNazdeeyah_

Heart touching love story🥰

KARAMCI WRITERS ASSOCIATION

[karamci tushen mu'amula tagari]

Wannan littafin na kuɗi ne ₦300 regular group ₦500 V.I.P group.

*Zaku tura kuÉ—i ta wannan account 0088814969 Adamu Halima Salahu, Access bank. Ko ku tura katin waya ko VTU ta wannan number *** sannan ku tura shaidar biyan kuÉ—in ta wannan number ****

```Free Page```

Shafi Na Takwas

__________"Mene ya faru?" Kamal ya yi tambayar.

"Amal...." Sai kuma ya juya ya É—auki key a side drawer. "Muje dan Allah"

"Nazo da mota ai"

"Okay muje" Ya faÉ—a yana yin gaba.

Yazo fita kenan sai ga ƴar aiki ta shigo da ƙaton tray a hannunta da kayan break fast.

"Ki mayar dashi ba zan samu damar ci ba" Yana gama faÉ—a ya wuce kawai.

Kamal na driving amma Maheer sai ƙara dialing number Amal yake yana jin ta switched off.

"Maheer ka kwantar da hankalinka dan Allah"

"Ta ya ya hankalina zai kwanta."

"Ni fa gani nake ta yuwu tana nan kawai dai bata son ganina ne, may be bata da ra'ayina ne"

"Bana tunanin haka."

***

Tura ƙofar ɗakin Jidda tayi, yayinda Amal ke biye da ita.

Bedroom ne madaidaici ya sha kayan alatu na more rayuwa, ga sanyin AC na ratsa ko ina.

"Wannan shine bedroom É—inki, zuwa jibi mijina zai dawo, so daga nan kuma zamu wuce America, shi mun bar shi a kano cox visa É—inki bata fito ba har yanzu"

Kai kawai Amal ta gyaÉ—a.

"Zan saka a kawo miki abinci yanzu, ga toilet idan kina da buƙata, sanna ki saka kayanki a closet kinji"

"To...!" Shine abinda Amal ta furta a sanyaye tare da zama gefen gado.

"Idan kina da buƙatar wani abu sai ki faɗa min kinji, ɗakin dana nuna miki shine nawa idan kina da wata buƙatar kiyi min knocking idan ina parlour kuma shikenan. Sannan feel free ki shiga kitchen in kina son ki dafa wani abu ko ki ɗauka, haka parlour ma zaki iya zama kiyi kallonki ko wani abu"

"Nagode...!" Shine abinda ta sake furtawa .

Jidda na fita, ta sauke ajiyar zuciya tare da share hawaye Ko wane hali Maheer yake ciki? Na tabbatar a yanzu ya riski saƙona gare shi.

Sai kuma ta kwanta kan gadon a fili ta furta "Ya Allah kana gani kuma ka sani nayi komai ne dan na ceci rayuwar mahaifiyata, Allah ka bata lafiya ka tashi kafaÉ—unta. Ya rabbi ka bawa Maheer lafiya gaba É—ayansu ka basu lafiya mai É—orewa."

***

Suna tsaye jikin mota, Maheer dai ya sauke kanshi ƙasa ya lula duniyar tunani, a cikin ransa addu'a kawai yake Allah yasa Amal dai tana nan, gara ma ace Kamal tayiwa ƙarya dan kar ta fito.

Suna tsaye Rahina ta ƙaraso bakinta ɗauke da sallama. Gaba ɗaya suka kalleta. "Yaya Maheer ina yini" Ta furta a sanyaye.

"Lafiya ƙalau Rahina, Amal fa?"

Ajiyar zuciya ta sauke sannan ta ce "Amal ta gudu"

"Ban fahimta ba?"

"Ban san inda take ba, yau tsawon kwana biyu kenan, na faɗawa Baba shima ya ce kar a ƙara yi masa maganar tunda ita tace kar a nemeta sai a ƙyaleta"

"Kun yi waya da ita ne?"

"A'a amma dai ta bar min wasiƙa ta ce dan Allah kar na nemeta nan da shekara ɗaya zata dawo. Amma bata faɗa min inda ta tafi ba kuma bata faɗa min dalilinta ba"

Sai kuma ta fashe da kuka "Adda bata sonmu bata damu da halin da zata barmu ba, bata damu da larurar da Mama ke fama da ita ba amma haka ta ɗauki ƙafa ta bar ni da tashin hankli. Yaya Maheer ka san gidanmu gidan yawa ne, kullum haka nake fama da gori"

"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, Ya jikin Mama yake yanzu?" Ya faɗa cikin ƙarfin hali.

"Da sauƙi zan ce, amma tunda Amal ta gudu haka Mama ke ta faman kuka."

Lumshe ido yayi, yana jin ƙunar zuciya amma kawai dauriya yake.

Sai daya shiga ya duba Mama, idanunta biyu, tana dai zaune kan gadon, sai dai koda Maheer É—in ma ya shiga tana ta zubar hawaye.

"Rahina...! Ya kira sunanta a sanyaye.

Kallonshi tayi ba tare da ta ce komai ba. Shi kuma ya cigaba da faɗin "Tun kusan sati uku da suka wuce muna ta fafutukar Visa saboda akai Mama Egypt a duba lafiyarta. To kuma an samu taki amma ta Amal ce ba a samu ba, shiyasa ma naƙi sanar daku, domin an tabbatar min za a iya samun tata a wannan wata. Ranar dana zo na karɓi passport da bayananku abinda nayi kenan, domin na biya har kuɗin asibiti.

Sauke gwiwoyinta ƙasa tayi, ta saka hannu ta rufe idanunta tana hawaye. Ashe ma Maheer yana ta ƙoƙari a kansu suna ganin aibunshi.

"Baba fa?" Ya tambaya yana kallonta. "Naji ya shigo tun É—azu"

"To dan Allah kiyi min iso gurinshi."

Kai kawai ta gyaɗa, sannan ta miƙe ta fita.

"Sakarai mara wayo" Shine abinda taji Hannatu ƙaramar ƙanwarsu ta faɗa.

Ɗagowa tayi ta kalleta, sai kuma taga ta cigaba da wanke-wanke bama ta kallon inda take, dan haka ta ƙyaleta ta wuce.

Da sallama ta shiga ɗakin Baba, a ɗarare take, yana ta buga tsohuwar radio ɗinsa taƙi saituwa.

"To to sarkin ƙorafi menene kuma?"

Har ƙasa ta tsugunna sannan ta ce "Dama Yaya Maheer ne ya ce yana son magana da kai?"

Washe baki ya yi, domin a rayuwarsa ba abinda yafi ƙauna irin yaji ance wani mai kuɗi na nemansa, dan ko ranar da ya yi masa faɗa dan a gaban Sule ne.

"Ina shi Maheerun?" "Yana É—akin Mama"

"Muje to"

"Baba da ka zauna sai yazo nan"

"Ƙaniyarki, ke zaki faɗa min abinda zanyi, ance fa in kaji kira samu ne" Ya ƙarasa yana ajiye radio tare da miƙewa tsaye.

Yana gaba tana biye dashi, Matan gidan kusan duk suna tskar gida suna ta aikace-aikace kasancewar hantsine, a haka ya fito yana baza tsohuwar babbar rigarsa da ta yamushe ta gaji da duniya.

Suna shiga ɗakin Maheer da Kamal suka duƙa har ƙasa suka gaidashi.

Amsawa ya yi yana washe baki tare da cewa "Maheeru yaron arziƙi, ka ga ita waccan da yake ba ƴar sunnah bace ta gudu, ai dama kamata ya yi a cikin yaran nan nawa ka zaɓi nutsatstsiya na aura maka amma ka zauna kana biyewa waccan mara ɗa'ar"

Maheer har cikin ransa yake jin zafin abinda Baba ke faÉ—a. Amma dai ya daure ya ce "Baba dama munzo ne akan rashin lafiyar Mama"

"To inajinka"

"Dama na samo ma Rahina Visa zasu tafi can ƙasar Egypt domin akwai ƙwararrun likitoci da zasu iya treating ɗin ta har ta samu lafiya"

"Kuma yanzu kai Maheer sai ka samowa uwar da Æ´ar kaÉ—ai, meyasa ba zaka haÉ—a dani ba?"

"Baba naga kai kana da iyali, bai kamata ka tafi ka bar su ba"

"Su kuma ka turasu can wata ƙasar suji daɗinsu, ni kuma ka barni anan, idan sun warke ma ba dawowa zasu yi in suka ji daɗin can"

"Baba nayi maka alƙawarin Mama na warkewa za su dawo"

"To ban amince ba, in banda tsabar rainin wayo in bar ƴata ta tafi wata ƙasar, tana mace, to ko da kake ganinsu da yawa haka duk ina son kayana da dai waccan ƴar titin ce da aka liƙamin aka min sharri aka ce ƴata ce da sai in yarda taje"

"Baba dan girman Allah ko dan lafiyar Mama"

"Kai...! To bari kaji ko qur'ani zaka haɗiya ba zan yarda ba, idan kana son ta tafi to ka bani sadakinta yanzu a hannuna sai in barku ku tafi ko birnin sin ne amma ka ɗauki balagaggiyar budurwa ka turata ƙasar arna ita kaɗai a'a wallahi sam ba zan lamunta ba"

"Baba Egypt ƙasar musulmai ce"

"To ko ƙasar muminai ce ban amince ba, in zaka aureta inji dumus yanzu ma ku tafi, sai shi wanda zata aura na bashi haƙuri, idan kuma ba haka ba wallahi ba zan yarda in bar ta ta tafi ba" Yana gama faɗa ya ɗaga babbar riga ya wuce yana kumfar baki.

Rahina fashewa tayi da kuka. Kamal ne ya fara bata haƙuri, yayinda Maheer ya kasa cewa komai.

Da ƙyar Kamal ya samu tayi shiru, sai a lokacin ya daure ya ce "Rahina karki damu insha Allah Mama zata samu lafiya, zan dawo zuwa gobe dan na ƙara roƙar Daddy.

Kai kawai ta gyaɗa sannan suka miƙe zasu tafi. Kuɗi ya zaro a aljihu bai tsaya ƙirgawa ba ya ajje a gefen gado.

"Yaya Maheer..!" Ta ambaci sunan a sanyaye.

Juyowa yayi ya kalleta "Muna godiya sosai, ban taɓa tunanin kirkinka har ya kai haka ba, Allah ya saka maka da alkhairi"

"Ba komai" Ya faɗa da ƙyar.

Da sauri ta ɗauki ledar da wayar ke ciki ta miƙa masa "Wannan fa?"

"A cikin wasiƙar da Adda tayi, ta ce na baka wannan wayar, da kuma letter a ciki"

Fiddo wayar yayi tare da letter ɗin. Miƙa mata wayar yayi ya ce "Ki riƙe sai kiyi amfani da ita" Ɗan zaro ido tayi sannan ta ce "Kayi haƙuri Yaya Maheer ba zan iya riƙe wannan wayar ba, tayi min girma, kuma Baba ma idan ya gani zai ƙwace, ka barshi kawai nagode, Adda ta bar wayarta anan, zanyi amfani da ita."

"Shikenan idan zan dawo zan taho miki da ƙarama" Kasa cewa komai tayi, har suka fita.

***

Yana shiga É—akin ya zauna gefen gado tare da sauke ajiyar zuciya. Ji yayi an dafa kafaÉ—arsa ya yi saurin É—agowa. Bai ga kowa ba dan haka ya share.

"Ja'afar...!" Yaji an kira sunansa da ƙarfi.

"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" Ya furta tare da runtse idanunsa.

Yana ji ana ta fasa gilasan É—akin amma ya kasa buÉ—e ido.

"Ja'afar dole ka dawo garemu, in ba haka ba zamu salwantar da rayuwar ahalinka"

Buɗe ido yayi a hankali, gani yayi komai an fasa na ɗakin, hatta mirror da kayan dake kansa, wardrobe ɗinsa an watso kayan ƙasa.

Ta window ya ga garin yayi wani irin duhu. Kafin ya ɗauke ido yaga wata mummunar halitta ta taho, ya runtse idanunsa sosai, sai ji yayi an hankaɗeshi ƙasa. Wani razananne ƙara ya saki bai ƙara sanin inda kanshi yake ba.

1 hour Later

A hankali ya buɗe idanunsa, akan Malamin dake zaune yana ta tofeshi ya fara sauke idanunsa. Sai kuma ya miƙe zaune da sauri.

Kallon Mommy yayi da take tsaye, ranta a matuƙar ɓace.

"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" Ya furta tare da dafe goshi.

"Ja'afar mene yake faruwa?"

ÆŠago kai ya yi ya kalli Malamin sannan ya ce "Malam mene ke damuna?"

Ƙara kallon ɗakin yake, duk abinda yaga an fasa babu, komai neat kamar yadda ya shigo ɗakin da farko.

"Akwai wani ɓoyayyen sirri wanda babu wanda ya sani sai kai kaɗai, nayi duba na gani"

Kallon ƙasar yayi sannan ya saka hannu yayi wurgi da fai-fain ƙasar ta zube.

Cikin zafin rai Mommy ta wanke shi da mari tare da cewa "Ashe kai mahaukaci ne?"

"Mommy ni ko mene yake damuna na san Allah ne ya saka min kuma addu'a zanyi ya yaye min, idan har na shiga irin wannan yanayi ba zaku kira Malami yayi min iya addu'a ba, to ku barni haka, ba zan lamunci shirka ba, ku bar ni da iya wahalar da nake sha a yanzu, Mommy ko so kike sai na mutu in zo in dawwama a wuta, ba zan taɓa iya tarayya da wani wajen saɓawa Allah ba" Yana gama faɗa ya tashi ya fita daga ɗakin, ransa a ɓace yake sosai.

"Malam dan Allah kayi haƙuri kan abinda ya yi" Mommy ta faɗa tana kallon Malam.

"Hajiya tabbas abinda yaron nan yayi ya tafka babban kuskure, kuma dole aljanu su ɗauki mataki domin ƙasar da suka ɗebo da hannunsu akusa da baitul muƙaddas masallaci na uku mai daraja a duniya, kuma nan ne tsakiyar duniya aljanu ba za su lamunta ba, domin wannan guri ne mai matuƙar daraja, kuma sun sha wuya kafin su ɗebo min"

Yana fita parlour ya tarar da Afnan zaune tana wasa da Teddys É—inta.

Tana hangoshi ta taso da gudu ta rungumeshi.

ÆŠagata sama yayi sannan ya koma suka zauna kan kujera.

"Wasa kike?" Ya tambaya yana kallonta.

Kai ta É—aga tana murmushi.

Ki shirya anjima muje shopping zaki je?"

Kai ta gyaÉ—a alamar eh.

"To shikenan, sai muje ko" Murmushi tayi tana ƙara shigewa jikinsa.

"Malam...Malam dan Allah ka saurareni" Mommy ta faÉ—a muryarta kamar za tayi kuka.

Shi kuwa Malam a fusace ya fita ya bar É—akin.

Mommy ta bi bayanshi.

A parlour ya tsaya suna kallon kallo da Ja'afar, kawai yayi ƙwafa ya wuce.

"Gaskiya Ja'afar na gaji wallahi haba abin ya fara isata"

Bai kalleta ba dan haka bai ce komai ba.

"Gaskiya zan tattara in koma Zaria gidan iyayena, kana gani dangin mahaifinka da duk wani wanda yake tare damu ya fara gudunmu a dalilinka"

"Mommy ba zan hanaki tafiya ba idan har haka shine samun nutsuwarki, amma ni ina nan domin ba zan bar sana'ata ba saboda abinda ke faruwa, kuma ni dai banga wanda ya gujemu ba, domin sai mutum yazo ya zauna damu sannan yake samun matsala, Mommy ni da farko nayi tunanin matsalar tana wancan gidan, amma daga baya sai na gane matsalar tana tattare damu ne, amma na kasa gano mene matsalar"

"Ja'afar kafi kowa sani, ka ɓoyene kawai"

"Idan har na sani da tuni na magance matsalar"

"Kana so kace min baka taɓa shiga ƙungiyar asiri ba?"

Zaro idanunsa yayi yana kallonta cike da mamaki.

"Eh domin Malam ya tabbatar min da cewa ka fita daga ƙungiyar asiri shiyasa su kuma suke bibiyar rayuwarka" Tashi ya yi kawai ya fita daga ɗakin. Sai jin tashin motarsa tayi.

Tashi tayi zata nufi side É—inta Afnan ta taso da sauri. "Ke dakata...!" Ta daka mata tsawa.

"Ki jira ubanki yazo karki sake ki biyoni"

Afnan tsayawa tayi a tsorace tana turo baki kamar za tayi kuka, ita kuma Mommy ta ja tsaki ta wuce.

#Follow, Vote, Comment on wattpad