Part 8
by @chefmuaysh
RAYUWAR MARYAMA*
_*By Aisha Hamza (MUAYSHGRAPHICS)*_
*BOOK 1*
Ina miki magana kin min shuru kinsan banason rainin hankali koh idan kuma baki sona saiki gayamin duk da ma ko kinaso ko bakiso sai anyi auren nan
Batasan sanda wani kuka ya kufce mata ba saedae kawai itama taji tana yinsa wannan wane irin tashin hankali ne na shiga Ni Maryama wace irin Rayuwa nakeyi ne hakanan wani lokacin sai taji ta tsani kanta ma
Ina miki magana kina kuka kuma sai kace wani abu namiki wallahi karki kuskura ki kaini ƙarshe in miki dukan tsiya anan
Shuru tayi ta koma yin hawaye kawai suma tana ɓoye fuskar ta domin tasan Kabiru zai aikata abinda yafi haka ma domin bata manta shekaranjiya marin da yayi mata ba
Data koma gida kuma mahaifinta yasata a gaba yayi mata faɗa akan wai tanuna masa bai isa da'ita ba shiyasa take nunawa Kabiru halayen banza
Tsaki Kabiru yaja sana yace ke wuce gida gobe zandawo kuma karki sake inzo ki kara sani a gaba kinamin kuka banaso idan kuma bahaka ba jikinki zai gaya miki gaskiya
Bai jira amsarta ba yawuce itama yana wucewa ta shige gida gaba ɗaya idan Kabiru yazo Kofar gidan nasu daƙyar take iya numfashi saboda warin kayan mayen da Kabiru yake sha suna damunta sosai
A zaune take a kofar ɗakinsu domin kwana biyu an hanata fita ko ina tanaso taje taga Antynta Indo hakanan takeson taje ta ganta saboda ko zata bata wata shawarar da zata kwantar mata da hankali
Balaraba ce tafito daga ban ɗaki tashiga kitchen Maryama na kallonta tana so ta tambaye ta amma tanajin tsoron amsar da zata bata
Hakanan tayi ƙarfin hali tace maman Hafizu Balaraba ta juyo tana kallon ta domin jin abinda zatace batare da ta amsa kiran da tayi mata ba
Don Allah inaso inje in gaishe da Anty tsaki taja sai kindawo kamar saukar aradu haka Maryama taji batun sam batayi tunanin abin zaizo mata da sauƙi haka ba
Zaune take saman tabarma tana ɓare gyaɗa zatayi taushe Maryama da gudu tafaɗa jikinta don murna
Kai Maryama zaki ballani wannan murna haka kamar an biya miki hajji Maryama tayi murmushi tace hada ummara ma Anty tunda nasamu yau naganki haka nakeji
Komawa tayi gefe ta zauna tana niyar tayata ɓarar gyaɗa tace ko bakomai Anty yau na rage radaɗin Auren dolen da za,amin tunda naganki
Cikin tausayi Indo tace karki damu Maryama inshaa Allah bazaki wulakanta ba kinji ki sanyawa ranki Aure ibada ne kuma shi zakije yi a gidan Kabiru
Tunda haka Allah ya hukunta miki idan kuma Allah baiyi ba to sai kiga Allah yakawo abinda zaisa a fasa auren nan
Maryama tace dama za,a fasa auren nan Anty ni abinda yake damuna guda ɗaya ne Anty Kabiru baya wanka idan yazo ma daƙyar nake numfashi Anty kenan haka za,ayi Auren 🥺
Tafaɗa a marairaice alamar abun yana damunta batason kazanta bare kuma abu ya haɗa da wari bata iya jurewa zama kusa dashi
Karki damu Maryama inshaa Allah zai daina ai bakiji ana cewa namiji kamar yaro yake ba duk yadda kika koya masa haka zai dingayi a gidan ki
Kunya takama Maryama haka kuwa akayi abinda take so tasamu dama shawarar da zata kwantar mata da hankali take so indo tabata
Duk abinda ya kamata Maryama tasani haka indon tadinga fada mata tana nuna mata wasu abubuwan wasu kuwa idan aka gaya mata kunya ma ake bata
Sosai taji daɗin ziyarar data kaiwa Antyn tata yau ko bakomai tasanya ta nishadi da ɗebe mata kewa sunji daɗin kasancewa da juna Dukansu
da yamma tayi Maryama bataso tafiya gida ba amma haka ta haƙura dole tawuce gidan nasu
Yau da gobe sai Allah watarana malam habu yafita watarana kuma jikin yaƙiya hakanan dai yaketa lallaɓa wa
Balaraba kuwa tanata abinda taga dama a gidan malam habu da dukiyarsa da ƴaƴansa domin ta rabashi da kowa yanzu har makotansu yanzu basa ganin mutuncin sa
Saboda yanda suka ga yazama mijin Hajiya sai yanda Balaraba tayi dashi da kuma ganin yadda suke azabtar da yarinya marainiya duk ana ganin malam habu shi yayi sakaci har gidan nasa yakoma haka
Domin shi dama can ba mutum bane mai faɗa bashida magana sosai saidai akwai mutunta mutane sosai amma yanzu gaba ɗaya ya chanja kamar bashi ba saboda yanxu sai yadda Balaraba tayi dashi
Maryama rayuwa tayi mata ƙunci idan har ba gidan Antyn ta indo tasamu taje ba bata samun wani farinciki kwata kwata
Komai bayayi mata daɗi a gidan ga wancan ɗan giyar da za'a aura mata kabiru idan yazo wataranar ma saidai ya daketa yatafi idan taƙi kulasa ga warin shaye shayen da yake yi suna damunta
Indo ce takan bata shawara akan wasu abubuwan da kuma kara bata haƙuri akan komai zai wuce inshaa Allah
Hakanan Maryama ta haƙura tasaki jikinta tunda tariga tasan cewa aurenta da Kabiru yariga ya zamar mata dole sai anyi batada wani zabin daya wuce haka
Da ace tasan wani ahalin mahaifiyar ta da taji daɗi da can zata gudu wajensu tasan zasuyi mata gata zasu kula da,ita amma bawanda tasani ko kuma ta taɓa jin Labarin sa ma
Tunda safe ta shirya ta tafi gidan malam sani domin a gidan za,ayi mata lalle Rukayya ce take lalle a gidan
Rukayya bata wuce itama tsarar Maryama a shekaru ba ai kuwa can tayini akayi mata lallenta da kitso Antynta ce tazo ta kawo mata Abincin rana ma agidan
Dukda cewa suma sunyi ɗumamen tuwo sun bata amma sai tace musu ta ƙoshi saboda kunya koda Antyn tata tazo ma saida innar su rukayya tace Wato namu abincin ne bazaki ci ba ko Maryama
Kunya takamata tace Ah ah wallahi inna sanda kika zubamin ne banajin yunwa yanzu ma ba yunwa nakeji ba don nasan Anty saita sani naci dole shiyasa ban Musa mata ba tafaɗa tana murmushi
Ah toh ai tanada gaskiya bai kamata abar Amarya da yunwa ba inji innar rukayya tana daukar buta zata shiga ban ɗaki
Wallahi kuwa innar rukayya don ma dai Antyn Amaryar sai a hankali nima yau nayi ranar girkin ne shiyasa
Sai yamma aka cire lallen másha Allah kyau iya kyau ita kanta Maryama tasan tayi kyau tunda take bata taɓa lalle mai kyau irin wannan ba dama sai Sallah sallah ake musu lalle
Indo kuwa tayita yabata tun tanajin kunya har tadaina jin kunyar ma jibi daurin aure Maryama ba wasu gwanayen ƙawaye ba hakan yasa babu inda take zuwa bare aje ayi wani shiri
Gidan indo kawai take zuwa da yake ita take ta kula da,ita kamar uwa ta zamar mata
a gidan su kuwa Balaraba tafi bada ƙarfi a gidan dan uwanta domin suma sunacan sunata shirin biki
Bata damu da Maryama ba sosai dukda kwana biyu saboda Shirin bikin yasa bata wahalar da,ita har sakar mata fuska take tana tsokanarta wai kar taje gidan danta a hanata ruwa
Maryama saidai tayi shuru tana jinta domin batasan ma amsar da zata bata ba hakanan gidan ƙunci yake mata sai ƴan shige da fice ake daga gidansu Balaraba
Akawo wannan a fita da wannan bata samu zuwa gidan Antyn ba kwana domin ance da daddare za,a kawo lefenta kuma dama kwana biyun nan tana kwana acan din saboda hidimar bikin da Balaraba takeyi bata dawowa gidan daga ita har yaranta sai dare
Akwati uku ce sai ƴar jaka da yake auren gata za,a yiwa kabirun hada wata ledar daban inda aka sako takalma balaifi Maryama kayan lefenta sunyi kyau
Mahaifiyarsa tanason auren sosai domin shine babba saboda shaye shayensa yasanya baiyi auren da wuri ba saidai ƙaninsa ma ya riga shi makwabta masu murna da masu zuwa ganin me aka kawo sunzo domin ganewa idonsu
Saidai lefen ba yabo ba fallasa baka isa ka kushe ba Balaraba kuwa baki har kunne wai ita zata hada ƴaƴanta auren zumunci kamar yadda take cewa
Saida kowa ya watse da daren nan sana Balaraba ta kira Maryama domin tazo taga lefen nata ita kunya takeji ma ga wani baƙinciki daya tokare mata zuciya
Ta rasa meyake mata daɗi a wannan Lokacin ma bata iya daga komai taduba yadda ya kamata ba tace tagani tamike ta nufi ɗakinsu
Kukanta tasha hakan ya haddasa mata ciwon kai sosai domin da safe ma kowa ya ganta sai ya tanka ganin yadda idanunta suka kumbura
Hakan bai yiwa Balaraba daɗi ba domin ita lallai so take ace Maryama tana farinciki da auren nata saboda mutane kar sugane tilasta mata akayi
Da wuri tabar gidan ganin jama,a sunfara taruwa sakamakon gobe ake daura aure wai zasuje jeren kayan ƴan gidansu Balaraba su sukayi ruwa sukayi tsaki domin sunce da Amaryar da angon duka ƴaƴansu ne
Sunata rawarsu suna kuma kiɗinsu saida Indo tayiwa Maryama faɗa sosai sana tasaki jikinta tadanci abinci shima kaɗan tayi wanka kwance take a falon Antyn nata kawai tanata tunane tunane
Kamar an tsunkule ta tamike da sauri tacewa Antyn nata tana zuwa ina zakije Maryama yanzu fa kikasha magani kince kanki yana ciwo
Yanzu zandawo Anty tafaɗa a hanzarce tana fita gidansu ta shiga tana sauri zata shiga ɗakinsu kamar daga sama taji ance ah ah ga Amarya ga Amarya kokarin shigewa take dakin domin batason yawan jama'a
Ke Maryama aka ambata da sauri ta juyo taɗan saki murmushi taƙaraso wajen ina yini Anty fauziyya
Wadda aka kira da fauziyyan tace aida bazakizo ba kenan ina ga Amarya ga Amarya ah ah Anty banjiki bane Maryama ta faɗa tana sunkuyar da kanta ƙasa
Toh shikenan jeki kar dai muzo gidan dan namu a dinga sharemu irin haka kamar bata jiba tayi sauri tawuce
Fauziyya kanwwace ga Balaraba itace autar su basu shiri da Maryama dama can kuma ita tafi Balaraba masifa don ko Angon Kabiru kenan basu zama inuwa ɗaya da'ita domin karamar uwace a garesa
Kamar zararriya take haɗa kayan yayyen nata a wata jaka cikin sauri duk abinda yazama nasu ne mallakinsa saeda ta kammalashi waje ɗaya a cikin jakar da yake tanada girma
Ƴar tsanar ta taɗauko takurawa ido har saida ƙwalla suka fara zubar mata ta tuna da faɗan da Indo tayi mata akan zata illata kanta da hawaye bayan addu'a ya kamata ace tanayi
Share hawayen nata tayi ta sunkuci jakar daƙyar tafice da,ita tayi sa,a ba wanda ya kula da fitar tata dama fargaban ta kenan a tambayeta ina zata da jakar
Indo kanta saida tayi kuka ganin Maryama tasa kayan gaba tana tunanin inda zata iya adana su domin tana ganin kayan kaɗai sun isa su rage mata radaɗin wani abin da yake damunta
Sosai indo ta fahimtar da,ita akan ajiyar kayan basuda wata fa,ida domin duk yau da gobe lalacewa zasuyi tunda yadidikan sanyawar su ne wasu ma dama sun tsufa
Indo tace zaifi kyau ki bayarda su ga mabukata dukda bata so ba amma taɗauki shawarar tata domin ta nuna mata muhimmancin yin hakan sana tace taɗauki wasu riguna masu kyau a ciki saita dinga sanyawa masu kamar na kwallo
Maryama ta dubi Indo tace Anty kinsan idan na kalli wannan ƴar tsanar sai inji kamar ina tareda yaya najibu domin itace kyautar sa ta ƙarshe a gareni kawai saita fashe da kuka mai tsuma zuciya
Kai Maryama ki rage kukan nan mana kinji Maryama ta dubeta da jajayen idanunta tace Anty tayaya zan rage tayaya bayan ni banida wani gata a yanzu inaji ina gani an rabani da farin cikina inaji ina gani za,a min auren da bana so Anty wannan kukan bansan ranar daina shi ba
Haka indo tasha rarrashi domin tariga tasaba ma ita kanta wani lokacin sai Maryama tasanyata tayi kuka idan tafaɗi wani abun
Sosai tayi bacci yau ita kanta batasan ya akayi ba hakan ta kasance da,ita ko maganin da Anty tabata ne haka tafara tunani tamiƙe jin ana kiran sunanta
Rukayya ce wadda ta mata lalle au Amarya har yanzu baki tashi ba kenan ko ita tamanta ma da yau ake daura mata Aure saida taji rukayya ta faɗa
Rukayya kece ya gida rukayya tayi murmushi tace ke zanyiwa ya gida ai Maryama kece da gida yanzu ai murmushi itama Maryama tayi domin tunda taje lalle Rukayya take ta Binta duk inda taje tanajin daɗin hakan domin dama ita batada wata kawa a layin nasu ma bare kuma a nesa
Tab ɗijam ana wata ga wata fa masu karatu ku tayani ji Maryama zatayi aure to ya zata kasance kuma a gidan kabiru ku biyoni don jin irin sinƙi sinƙin ƙalubalen da Maryama zata fuskanta kuma a gaba muje zuwa ina yinku masoyana masu karatu❤️❤️👍👍
Karki bari karku bari kar mu bari abamu labari top 3 Na A'ishatu Hamza wadda kuka fi sani da Muaysh graphics 🤟 🤗 basai na faɗa muku ba littafaine wanda daga jin sunayen su zaka gane cewa na musamman ne
(UMMU OR SALMA) UMMU kO SALMA
(ORPHANAGE HOME) GIDAN MARAYU
(MARYAM’S LIFE) RAYUWAR MARYAMA
Wannan shine account details din mu 👇
3201868037 A'isha Hamza First bank
Ko kuma 9131096058 A'isha Hamza Opay bank
RAYUWAR MARYAMA akan 400 kacal GIDAN MARAYU akan 400 sai kuma UMMU KO SALMA akan 400 ga wanda yake buqatar duka zai biya 1000 instead of 1200 sana zaka tura receipt after payment a wannan number *** ta whatsapp