Part 9
by @chefmuaysh
BADAƘALA
✍️ A'isha Hamza
Ganin kofar a buɗe ya tabbatar mata da wanine ya shigo dakin saboda ga ledoji nan guda biyu an ajiye an ɗauke na dazu kuma shine aka kunna tv ɗin parlour a ciki ake wani Film ana faɗa hada harbe harbe ga tv ɗin an kure ƙarar ta
Wata nannauyar ajiyar zuciya ayrah ta sauke tare da faɗawa kan kujera tana maida numfashi don ita kanta a tsorace take a fuska ne kaɗai bazaka ga hakan a tattare da'ita ba
Khairiyya data biyo bayanta ta labe daga jikin kofa ganin ta a zaune ya sanya ta fitowa itama tana baza idanu
Dariyar da Ayrah keyi ne ya dawo da'ita ga dubanta tare da kallon inda ayrah ke nuna mata tana dariya subhanallah ta faɗa tana shafa kayan jikinta
Tashin hankali kenan fitsari ta saki da gaske don jike take sharkaf ita batasan ma tayi ba duk cikin tashin hankali ne
Ɓata fuska tayi tareda kallon tv ɗin da keyi yanzu an canja tasha kuma an rage karar da alama daga ta wani waje ake komai ba'a dakin nasu ba
Ayrah tace yanzu ke fisabilillah Khairiyya duk tsoratar ce ta sanyaki sakin fitsari ta faɗa tare da kara bushewa da dariya hada riƙe ciki
Ita kanta Khairiyya data gama bata ran ganin abinda suke tunanin bashi bane ba ya sanya itama tafara ma kanta dariyar
Toilet ta shiga domin gyara jikinta bayan tagama kuma ta ɗan leko tana faɗin Ayrah bamuda kayan sanyawa fa kayan mu ba'a shigo mana dasu ba
Ayrah ta mike tana faɗin kai to bari in leka Inga ko zanga wani sai nayi mashi magana
Khairiyya tace ina zaki tafi ki barni anan wallahi ni tsoro nakeji gashi ta wani leko iya kanta daga cikin toilet tayi tsuru tsuru tana baza na mujiya
Ayrah tace to ki zauna anan a haka tunda tsoro kikeji ko kuma kifito a hakan kawai sai muje tare tsaki Khairiyya taja tana kwabe fuska to kije amma dan Allah karki dade wallahi tsoro nakeji
Ayrah bata tanka mata ba tayi waje handle ɗin taja ta fito dare yayi amma bazaka gane hakan a cikin babban parlour ɗin ba kasancewar ko ina gauraye yake da hasken lantarki
Yan juye juye tafara yi jin babu alamun motsin mutun ya sanya ta kai tsaye ta nufi cikin babban parlour ɗin jimm tadanyi ganin fa babu kowa da zata ma magana
ga abinci nan idan akwai abinda kuke buƙata ga wata abu nan da kun danna za'a zo aji menene ya faɗa yana nuna musu wani dan ƙaramin abu a jikin bango mai madannai
Tunawa da wannan maganar da wanda yakawo musu abinci ya sanya ta juyawa cikin sauri domin ta koma saidai jin karar motoci yasanya ta ɗan dakatawa kaɗan tana kai dubanta izuwa kofar parlour
Kamar ana ingizata ta nufi kofar saidai ganinta a rufe ya sanya ta jan tsoki kofar ta glass ce hakan yasa take iya hango mutanen da suke a waje
Motoci ne jere kusan guda bakwai suka fara fita daga gidan an rubuta SHAUBAN a kowace number mota da number SHAUBAN 4 5 6 7 8 9 10 haka motocin nan guda bakwai sukayi get ana buɗe musu da guda guda kasancewar kuma kowace mota tinted glass ne bazata iya hango kowa na ciki ba
Dan jimm tayi alamar tunanin ko suwaye suka fita a wannan jibga jibgan motoci oho ❓ hakan yasa ta juya tayi ciki domin ta koma daki
Ai kuwa tana tura kofa Khairiyya ta watsa da gudu cikin toilet Ayrah tace lafiya, wai taji shuru shine ta leko tagani
Wannan abun kamar yanda aka musu bayani ayrah ta danna ai kuwa ba'a fi 3 minute ba saiga shi ana musu knocking Ayrah ce ta duba sai taga wannan saurayin ne daya kawo musu abincin rana
Me kuke buƙata ya faɗa a takaice Ayrah tace dama kayan mune da mukazo dasu munaso zamuyi amfani dasu okey kawai yace ya fita
Khairiyya dai tagaji da zaman toilet tacewa Ayrah gaskiya tabata hijab ɗin jikinta ita dai ta fito don tagaji wallahi
Dole ayrah ta bata saboda tasan halin rigimar ta idan taki bata karshe haka zata fito ko ba kayan
Wajen 30 min kuwa saiga shi ya dawo da wata trolley mai shegen kyau ya shigo da'ita Ayrah tace masa bashi bane kayan nasu murmushi yayi sai yace shine oga Sameer ne yace a kawo musu wannan ɗin jin an ambaci Sameer yasa suka karba
Sakin baki sukayi a lokacin da suka buɗe akwatin sukaga abinda ke ciki dogayen riguna ne kusan kala goma duk biyu iri ɗaya haka duka suke kowace da ɗan ƙaramin dankwalinta
Su Hajiya Khairiyya fa an saki baki itace ma tafara faɗin wow Ayrah gaskiya kayan nan sunyi kyau nan tafara fito dasu hada takalma kala hudu biyu kamar silifas masu shegen kyau sai biyu flat iri ɗaya
A ciki akwai Black Abaya biyu sai Brown biyu sai purple biyu sai sauran biyun materials ne shima dogayen riguna kowa biyu duk iri ɗaya dai
Murna kamar Khairiyya zatayi hauka nan tafara canki cankar kayan da zata sanya ita dai Ayrah ta zuba mata idanu tana kallon ikon Allah 🤔
Saida ta gama shirya wa kafin tace kowa yanada kala biyar kenan sai takalman su da tun a dakin ta fara sanya nata tana kaiwa tana kawowa wai tazama yar gayu Ayrah dai Murmushi tayi ta kwashe kayan ta shiga dasu daki kafin tadawo
Saida suka idar da Sallah isha'i kafin suka jawo ledojin da aka kawo musu yanzu din ma hada kaza sai fried spaghetti da cowsulow da faro da lemu Saida suka ci suka koshi kafin Ayrah itama tace xatayi wanka
Wajen tara da wani abu bacci yafara cin ƙarfin su suka koma daki suka kwanta Ayrah dai wajen karfe uku ta farka saboda sabon da sukayi na yin sallar dare haka tayi sallolin ta tayi addu'a kafin takoma ta kwanta
Basu tashi ba saida akayi knocking Innalillahi wa'inna'ilaihirajiun Ayrah tafada yayin da taga gari fa yayi tangaram alamar ya waye
Fitowa tayi parlour tare da bada izinin shigowa matar jiya ce yauma sanye da kayan chefs a jikinta wadda aka kira da Hayrana
Morning ta faɗa tana sakin Murmushi itama ayrah saita maida mata da ina kwana lafiya lau ta amsa tana faɗin nazo na faɗa muku oga Sameer yace ku shirya daya shigo zaku fita shopping
To Ayrah tace har zata juya tace mata don Allah karfe nawa nuni hayrana tayi mata da agogon bangon da take manne a ɗakin tana faɗin ga agogo nan a ɗakin
Ayrah ta daga kai kafin takara dubanta tace ban iya irin wannan ba naga bata da numbers murmushi hayrana tayi kafin tace yanzu ƙarfe goma da rabi ta juya tana ƙara faɗin ku shirya da wuri fa don yace yanzu zaizo inajin a waje ma zaku karya
Khairiyya ce ta fito dai-dai hayrana najan kofar dakin tana mika tafara yan kalle kalle kafin ta tsaida idanunta kan Ayrah tana yamutse fuska tace na ɗauka abinci aka kawo mana
Ayrah tace to acici bashi bane uncle Sameer yace mu shirya zamu fita ne wai shopping
Gwalalo idanuwa Khairiyya tayi tana faɗin don Allah fa wayyo daɗi bari inyi sauri inyi wanka ai ba shiri ta afka toilet
Ayrah dai sakin baki ma tayi tana kallonta
Wajen sha ɗaya da rabi sun shirya tsaf suna jiran kira kowa tasha doguwar rigarta Khairiyya dai brown Abaya ta sanya ta yafa dan kwalin ta takau kurama mirror ido wai a lallai itafa yau kyawunta kaɗai take gani irin wanda bata taɓa yi ba
Ayrah kuwa Saida ta wanke kanta tass data shiga wanka ta fito a saman mirror taga dryer da karambani ta karanta yar takardar dake cikin kwalin yanda ake amfani da'ita aikuwa sai gashi tadanyi ƙoƙarin busar da kanta nan Khairiyya ganin gashin Ayrah yayi masifar kyau tasa rigima wai itama sai ta wanke Ayrah tace to ai saita bari sai sun dawo Koh
Materials Ayrah ta sanya peach color 🍑 mai green flowers 🌻 da yellow sai madaidaicin mayafin tayi rolling Masha Allah ta furta yayinda ta kalla kanta a jikin madubin dakin saida ta danyi murmushi don ita kanta batasan tanada wannan kyawun ba don zata iya cewa ita ɗin ba ma'abociyar kallon madubi bace ko a gida bare kuma basu da irin wannan
Khairiyya data dawo parlour tun ɗazu ta kurawa tv ido da keta faman aiki tana zaune akan lallausan carpet ɗin dakin saiga Ayrah ta fito wow ta furta tana mikewa hada wani kamo hannunta tana jujjuya ta kinganki kuwa Ayrah wannan kyau haka karfa mu haɗa go slow a garin nan
Sosai tabawa Ayrah dariya wai karsu haɗa go slow suna cikin magana akayi knocking Khairiyya har sauri take wajen budewa don tace ta kagara yazo dama don ita yunwa takeji
Hayrana ce yanzu ma tace su biyota takalmin da aka kawo musu suka sanya suka fito har zuwa parlour ɗin bakowa sun dauka anan zasu ga uncle Sameer din sai sukaga tayi hanyar waje basu ce komai ba dai suka cigaba da binta har suka fito gaba ɗaya daga parlour ɗin
Parking space ta wuce dasu wajen wata mota arsh color sai kyalli takeyi alamar ma kamar sabuwa ce ta buɗe musu bakowa a ciki hakan yasa sukayi tsaye suna baza idanu
Hayrana ta dubi Ayrah tace ku shiga wajen sa za'a kaiku don shi ya kira waya yace bazai samu shigowa ba nan ɗin
Ba musu Ayrah ta danna kai Khairiyya ta biyo bayanta basuyi tunanin da mutum ba saida suka zauna sukaji ana ƙoƙarin tashin motar kafin suka san ashe driver yana ciki
Tafiyar Minti sha biyu suka tsaya dai-dai wani ɗan ƙaramin Restaurant a bakin hanya driver ya fita yana waya bayan ya gama kuma saiga wannan matashin da yake kawo musu abinci a gida yazo yace su biyo shi
Aikuwa tunda suka fito kallo ya koma sama don ganin mutanen wajen duk kamar su suke kallo ya sanya suma duk suka tsargu Khairiyya ana tafiya ana hade hanya
Daidai wani table mai mazaunin mutum huɗu ya nuna musu yace su zauna kowa dai ya kasa magana sai rarraba idanu suke ta faman yi basu dade ba kuwa sukaji sallama akan su ko basu duba ba bazasu taɓa mance wannan Muryar ba a rayuwar su
Abin nema ya samu Khairiyya tun kan ta amsa sallama an fara kwabe fuska za'ayi kuka Ayrah ce ta amsa tana gaishe shi kujera yaja ya zauna yana facing Khairiyya tare da hada hannu biyu yana faɗin sorry rigimata nasan nayi laifi
Ayrah dai Murmushi tayi kafin tace Uncle ina kwana lafiya lau Ayrah ya baƙunta nan ma murmushin tayi Tace alhamdulillah uncle, Khairiyya ta katse su da faɗin ai ni uncle duk a tsorace nake wallahi jiya da aka kunna tv a dakin nan har fitsari na saki
Me zaiyi kuwa in ba dariya ba Ayrah ta tayashi tana faɗin kai su Khairiyya manya wato bawani kunya kike fadar kinyi fitsari Koh
Khairiyya tace ai yanda na tsorata ne Ayrah bazaki gane ba daidai nan saiga matashin nan ya dawo tare da wani wanda daga gani maaikacin wajen ne
Nan suka shiga tambayar su me zasu ci kowa aka bashi zaɓi uncle Sameer yace Imran idan ankawo abincin tare dakai zamuje Shopping kaga gobe zasu wuce makarantar
Okey sir kawai yace shima yaja kujerar kusa dashi ya zauna nan suka fara cin abinci itadai Ayrah kaɗan ta tsakura don duk idan ta juya sai ta samu wani yana kallonta ita kuwa goga Khairiyya ai bata kallon kowa bayan plate ɗin gabanta
Saida suka gama tas kafin suka tashi saɓanin motar data kawo su da suka gama basu ganta ba ma sai wata motar ce Imran ke tukin sai Ayrah da uncle Sameer yace ta shiga gaba shi kuma da Khairiyya suka zauna Abaya suna ta fira tana zuba mashi shagwaba
Yauma dai sun sha kallo dai-dai gwargwado don ba karamin shop bane sukaje duk yanda uncle Sameer yaso Ayrah ta dauka abinda take so ta kasa don mamakin da yake cinta ba kaɗan bane don takasa yarda da abinda take ganin a zahiri
Saidai an kwasar musu kayan makulashe da komai da ya kamata a siya ma ɗan makaranta tun daga kan madara milo cornflakes biscuits cabin juice kala kala daga nan basu tsaya ba suka tafi wani wajen aka siya musu trolleys manya biyu ƙanana biyu kuma aka sai musu wasu dogayen rigunan iri iri hada Pakistan
Basu dawo gida ba sai wajen karfe biyu na rana sosai sun gaji don suna dawowa uncle Sameer yace suje suyi sallah shima zaiyi zai dawo yanzu haka kuwa sukayi Saida suka idar da sallah suka kuma fitowa parlour ɗin anan suka iske an shigo da kayan da sukayi siyayya ɗin
Saiga uncle Sameer ya shigo yana waya Saida ya gama kafin ya karaso inda suke zaune kan carpet kujera yasamu ya zauna tare da ɗaukar remote ya kunna tv
Ayrah ce ta dube shi kafin tace Uncle magana nake son muyi kamar bazai amsa ta ba yadanyi jimm sai kuma yace inajinki Ayrah
Saida ta danja numfashi kafin tace dama cewa zanyi mungode sosai Allah ya saka maka da alkhairi akan dawainiyar da kakeyi damu don bamuda kalmar da zata wadatar wajen godiya a gare ka saidai uncle ina ganin wannan dawainiyar ai zatayi yawa sosai kashe kuɗi haka
Murmushi yayi sosai don yaji daɗin wannan godiyar tata sai kuma yadan kalleta yace bani zaki godewa ba Ayrah shi zaku godewa ya faɗa yana nuna wani hoto dake manne jikin bangon dakin daga sama saidai tunda suka zo ita bata taɓa lura da wajen ba don basu taɓa zaman parlour ɗin ba sai yau
Hoto ne babba na wani saurayi mai cikar izza da kuma kamala a kallo ɗaya bazaka taɓa iya cewa shidin bahaushe bane ba saidai dan duhun fatarsa kaɗan yasa zaka fahimci hakan sanye yake cikin Black suit a tsaye ya riƙe wata yar sanda mai shegen kyau sai kyalli take idonsa manne da baƙin glass sumar nan tasa tasha gyara sai kyalli take kuma tanada ɗan yawa amma daga gani tana bala'in shan gyara da Murmushi a fuskar sa ga wata yar siririyar wushirya tsakanin hakoransa yanada tsawo sai murdadden jiki amma ba irin kiba gareshi ba sosai
Saida ta gama kallesa tsaf kafin tace wani abu Khairiyya da tun dazu hankalin ta yadawo kansu tace wow uncle waye wannan ɗin wallahi yanada kyau ta faɗa hada wani rike kumatunta da hannu biyu tana tsuke baki
Yar harara ya jefa mata kafin yace kina nufin yafini kyau kenan ah ah wallahi uncle ai duk duniya babu mai kyawunka ta faɗa tana dariya shima dariyar ya maida mata
Saɓanin haka suka gani a fuskar Ayrah data kauda kai daga kallon hoton ta kuma daure fuska babu alamar walwala a tattare da'ita Saida Khairiyya ta zunguro ta tace Ayrah don Allah gayen nan bai burgeki ba ta faɗa tare da juyawa tana kallon uncle Sameer tace wai uncle waye wannan ɗin
Saida ya sauke numfashi ganin yanayin Ayrah ɗin kafin yace Yayana ne shine na bashi labarin ku yace to shima ga gudummawarsa ya tura kuɗi akayi muku duk wannan siyayyar
Khairiyya ta mike hada wani dan rausayawa tana faɗin ah gaskiya uncle yayanka yanada kirki sosai wallahi mungode
Hakanan taji zuciyar ta babu daɗi gaba ɗaya zaman parlour ɗin ya gundureta mikewa tayi uncle Sameer gaba ɗaya yana lura da yanayin ta hakan yasa yace Ayrah ina zakije ne dan yamutse fuska tayi kafin tace xanje na dan kwanta ne
Ba inda zakije ya faɗa yana mikewa wa zai shirya muku kayan naku nidai nagaji kuma hayrana ta tafi Imran kuwa yatafi kawo muku abinci yanzu ma zai shigo kibari kuci abinci kafin ki kwanta
Ganin yanda yayi maganar bada wasa ba ya sanyata dawowa ta zauna dole hanyar fita ya nufa sai kawai akwatin ta ta shiga fado mata a rai har zai fice tace Uncle juyowa yayi yana dubanta tace dama wai kayanmu ne akwai abinda nake so na ɗauka a ciki ɗan Murmushin gefen fuska yayi kafin yace okey bari insa a shigo muku dasu ya fice daganan batareda ya waiwayawa ba
Ajiyar zuciya ta sauke kawai saita tsinci kanta da satar kallon hoton matashin saurayin nan masha Allah ta faɗa a zuciyarta tana kauda kai sai kuma ta taɓe baki
Basu jima ba kuwa saiga Imran dauke da ledojin abinci guda uku mai ɗauke da tambarin CHEF MUAYSH a gabansu ya ajiye Khairiyya ba jira kamar zatayi tuntube ta mike ta nufi ledojin ta zari ɗaya tana faɗin dama fa nafara galabaita da yunwa wallahi
Ayrah dai saidai ta bita da kallo dan gaba ɗaya batajin daɗin komai a yanzu
Saida suka fara cin abincin nasu saiga uncle Sameer tareda wani Babban mutum dauke da kayansu ya shigo
Anan parlour aka ajiye musu kayan mutumin ya fita sai uncle Sameer ya zauna shima ya dauka leda daya ta abincin yaci Saida Suka gama tass kafin ya dubi Ayrah da take ta faman tsakurar abincin yace Ayrah Meyasa bakison cin abinci dukar da kanta tayi tana wasa da yatsun hannunta kafin tadan buɗe baki tace bakomai uncle banajin yunwa ne
Kodai kinfara soyayya ne bamu sani ba ya faɗa yana dariya domin so yake ta sake jikinta buɗe baki tayi tana ware ido sai kuma tasa hannu ta rufe fuskarta tana faɗin ah ah ah wallahi uncle soyayya ina yarinya ta
Khairiyya ce ta amshe da faɗin kai Ayrah kece yarinyar wai kice Ni saidai ace man kwaila kenan me zasuyi inba dariya ba gaba ɗaya suka sake nan suka fara fira sosai kafin yace suzo ya tayasu hada kaya
Shine ma ya raba musu komai kowa Saida aka cika masa akwatin sa manya manyan madaidaitan kuma yace kayan sanyawa su raba tunda komai iri ɗaya ne sai kowa ya ɗauka nashi yace su fito da akwatin da aka kawo musu jiya shima su shirya hada kayan ciki gobe ƙarfe goma na safe zasu wuce makaranta
Baki yaƙi rufuwa su Khairiyya an dage sai haɗa kaya akeyi komai Saida suka shirya tsaf kayan sanyawa kowace Saida ta tashi da kala Sha biyar biyar daga Abaya kuma sai Pakistan kala uku sai materials masu shegen kyau
Ayrah ce tajawo kayanta data taho dasu daga gida nan suma tafara haɗa su hada tsarabar da Inno ta bata duka ta haɗa su Saida taxo kan akwatin ta kafin ta tuna da'ita ma
Ganin tafara fiddo kayan sanyawar data shirya yasa Uncle Sameer dawo da kallon sa gareta lafiya naga Ayrah kin gama shirya kayan kuma kina fito dasu
Murmushi tayi tace Uncle zansaka abu ne daga ƙasa shiyasa okey kawai yace yana kallon dan ƙaramin buhun datake ƙoƙarin turawa kasan trolley ɗin
Sai ya kuma cewa ai gara ki fito da abinda ke ciki saiki saka a ƙasa kinga zaifi zama dakyau
Kin dagowa tayi don bataso yasan meye a ciki shima kuma bai ƙara tanka matan ba suka gama shirya komai daƙyar ta rufe nata trolley ɗin saboda akwatin data sanya mashi
Basu gama komai ba sai wajen karfe huɗu kafin uncle Sameer ya mike yace suje suyi sallah yanzu don akwai abinda zai siyo musu ya manta ne zai dawo bayan maghrib trolleys ɗin kuma yace su bar su anan wajen
Daki suka koma shi kuma ya fita nan sukayi sallah suma sai suka ƙara dawowa babban parlour ɗin gidan wai don suyi kallo saboda tv ɗin da aka bari a kunne
Ƙarfe bakwai da rabi kuwa bayan maghrib saiga uncle Sameer ya shigo tare da Imran yanzu din ma da sukayi sallah nan suka dawo suna kallon
A gaban Ayrah Imran ya sauke wata leda Babba yana murmushi yace gaskiya sir ana matukar ji da yan matan nan tareda juyawa yana duban uncle Sameer dake ƙoƙarin zama saman 2 seater kusa da Khairiyya da take ta faman sakin murmushi kamar zararriya
Uncle Sameer yace ba dole ba Imran ai hakkin su ne dole kuma abasu Imran yace haka ne kuma oga nidai xanwuce na kawo muku dinner don nagama aikina daga yau gobe ma bazaku ganni a gidan nan ba
Uncle Sameer yayi murmushi yace ai bakai kaɗai ba Imran kunada yawa sukayi Murmushi suna kallon juna mai ɗauke da wata manufa
Tabe baki Ayrah kawai tayi don yanzu din ma idonta akansu yake ba tareda sun ankara ba
Ledar uncle Sameer ya mike yajawo kusa dashi yana ƙoƙarin buɗewa shikuma Imran yayi waje
Ihun da Khairiyya ta saki tana daka tsalle ya saka Ayrah dubanta wasu hadaddun takalma kuma tsadaddu ne kala goma dukkansu flat shoe ne kowace da nata kala biyar biyar uncle ya mika mata nata shine take ihun murna
Ganin sun ƙura mata ido yasanya ta zubewa saman carpet tana haɗa fuskarta gwuiwa wai kunya taji taga suna kallon ta
Shidai uncle Sameer dariya ma tabashi kafin ya dubi Ayrah yace ga nakinan Ayrah takalma ne sai ku haɗa da naku na jiya wanda aka kawo maku idan kunje makarantar ku kula sosai da kayan ku Kuma ya kare maganar yana girgiza kai alamar tabbatar musu da suyi hakan
Ayrah tace inshaa Allah uncle zamu kula ta ci-gaba da faɗin saidai uncle to naga ancika mu da kayan sanyawa na gida boarding ba'a saka uniform ne
Murmushi yayi kafin yace ana sanya uniform Ayrah acan za'a baku gobe idan kunje saidai don Allah Ayrah ki kulamin da wannan shirmammiyar yarinyar idan kunje makaranta kinji
Jinjina kai tayi kawai tana kunshe dariya ganin Khairiyya ta mike zaune tana zare idanu wai ance mata zararriya hada wani taɓe lips tana faɗin uncle nice zararriya wai
Eh mana ke ɗin zararriya ce ai khairat dina ya faɗa yana dage mata gira yasan yayi tsokana aikuwa nan ta shiga baza mashi shagwaba
Ayrah dai ta mike tabar musu parlour ɗin daki takoma kurya saman gado ta zauna hakanan ta dinga jin zuciyar ta na mata gizon wannan kyakkyawan saurayin na photo sai kuma data tuna shi saita tsinci kanta a cikin bakin ciki tsaki taja kafin ta cigaba da zancen zuci
Oh ya Allah Ni Ayrah nafara tunanin uncle Sameer dinnan Anya akwai gaskiya a tattare dashi tabbas akwai abinda yake boyewa tun a gida na taɓa kamashi a lokacin da mukaji yana waya
(Ohh BADAƘALA ✍️
Ah tabbas anan akwai badakalar kuwa don naga jarumar taku Ayrah tace saita gano badakalar cikin labarinta 😳kuzo mu haɗu mu bata haɗin kai to muma dan muji badakalar nan don kar ayi babu mu wallahi ah to ai inada gaskiya 😲
Karki bari karku bari kar mu bari abamu labari top 3 Na A'ishatu Hamza wadda kuka fi sani da Muaysh graphics 🤟 🤗 basai na faɗa muku ba littafaine wanda daga jin sunayen su zaka gane cewa na musamman ne
(UMMU OR SALMA) UMMU kO SALMA
(ORPHANAGE HOME) GIDAN MARAYU
(MARYAM’S LIFE) RAYUWAR MARYAMA
Wannan shine account details din mu 👇
3201868037 A'isha Hamza First bank
Ko kuma 9131096058 A'isha Hamza Opay bank
RAYUWAR MARYAMA akan 400 kacal GIDAN MARAYU akan 400 sai kuma UMMU KO SALMA akan 400 ga wanda yake buqatar duka zai biya 1000 instead of 1200 sana zaka tura receipt after payment a wannan number *** ta whatsapp