“SANADIN ƘADDARATA”

Page-40

by @zahratulqalam51

*FASAHA WRITER'S ASSOCIATION*
     (*F.W.A)*©✍️
     ⭐⭐⭐

Ƙungiya masu aiki cikin salon hikima da fasaha gurin juya tunanin al-umma, kaifin alƙalumansu ya zarta takobi ©✍
___________________________________________________



بسم الله الرحمن الرحيم.
اللهم صلي وسلم على نبينا محمد. 




❁ 𝐒𝐀𝐍𝐀𝐃𝐈𝐍 Ƙ𝐀𝐃𝐃𝐀𝐑𝐀𝐓𝐀 ❁ 




Free book📓



By: _*🌹𝑍𝑎ℎ𝑟𝑎-𝑡𝑢𝑙-𝑄𝑎𝑙𝑎𝑚🖋️*_




Page4️⃣0️⃣





Iska ya fara kaɗawa à hankali, wanda yanayin ke ratsa zuciyata gami da fargaba, kamar abun da na ke nema yana bayana, hakan yasa na fara juyawa don inga abun da ya ke faruwa?.

"Keh kuɗin ruwan ki ka zo kawowa ko me?" Na ji maganar mai shagon ɗazu, wanda hakan ya hanani juyawa na maida kallona kansa, sauke numfashi na yi, amma wannan mai shagon akwai masifaffe, nufan gurinsa na yi don na basa kuɗinsa.....

Halima ta yi sa'a ta samu mai mashin ɗin da zai kaita zuwa tasha, don haka ta shiga tana cigaba da hawaye, da sanya hannu a cikinta da ta ke jinsa kamar ƙurji mai ciwo...

Buɗe jaka na yi na ɗau kuɗi na bashi, sannan ya maida min canji da agogona, na gode masa sannan na juya ina tafiya. Sunusi wanda Asma'u za ta aura na kuma hanga, babu tazara sosai a tsakaninmu, murmushi ta yi a zuciyata na ce bari na je na sanar da shi tare na ke da Asma'u.

Turus na ja birki na tsaya, fiskata ya wanzar da mamaki. Ba komai ba ne ya haifar min da hakan sai ganin da na yi wata budurwa ta zo kusa da shi, suka rungumi juna cikin nishaɗi abunsu, raba jikinsa da na ta ya yi haɗi da ɗaga ledar da ke hannunsa yana nuna mata tare da yin maganar da ba jinsu na ke ba.

Gaba na ne ya faɗi sosai, har zan tafi in ƙyalesu, sai kuma wani tunani ya zo min, kada kuma ya zamana rashin fahimta na yi musu, ko ƙila 'yar uwarsa ce, duk da ba abun da ya dace ba ne su rungumi juna haka, amma ya kamata na tabbatar, to ta ya ya?.

Na fara nufar inda su ke, amma ta bayansu yadda ba za su ganni ba, har na kusa isa na ga Sunusi na shirin juyowa ta inda na ke, da sauri na bada baya ina sauke ajiyar numfashi, a hankali na kuma waigowa sai dai ban gansu ba, "to ina su ka yi? Suna nan fa yanzu? Ina su ka shige?" Na jerawa kaina tambayar ina dubawa ko zan gansu.

Na kasa haƙura ya kamata na nemi inda su ke, ko Allah zai sa na fiskanci wani abu, don haka na isa inda su ka baro zuwa gaba ina cilla idanaina nemansu. Can kuwa ma hangesu tsaye a kusa da wata mota, a saɗaɗe na isa haɗi da laɓewa à kusa da su, ta gefe yadda ba za su gane ba, ban san lokacin da na zare ido ba zuciyata na harbawa, na ji kamar ƙafafuna sun manne da ƙasa, sakamakon abun da na ji suna cewa.

"Sweetheart to fushin me ki ke yi haka kuma?" Faɗin Sunusi wa budurwar da ta ba shi baya, juyowa ta yi tana kallonsa fiskarta a haɗe ta ce, "ba komai ba ne ya sani fushi ba, sai abun da ka ke shirin aikatawa, na kasa gane kalamanka Sunusi, ƙwaƙwalwata ta kasa fahimta, yanzu kenan za ka iya yin rayuwa da wata ba ni ba? Da ba don na ji labarin ba da kenan har a gama komai ban sani ba? Me ka mayar da ni ne Sunusi?".

Jan numfashi ya yi, ya saukar tare da sakin murmushi ya ce, "dama wannan ɗan abun ne ya sa sweetheart ɗina ɓacin rai?" Wani irin kallo Billy ta jefa masa ta ce, "ɗan abu ne ko?" Janyota ya yi ya rugume. 

Ni kuma a wannan lokacin zuciyata ta riga ta tabbatar min, wannan ba rashin fahimta ba ne, wannan ba 'yar uwarsa ba ce kamar yadda na yi tunani ɗazu.

Sunusi ya dubeta ya ce, "na ɗauka mun riga da mun wuce wannan babin. Billy na riga da na sanar da ke dalilin da yasa zan auri Asma'u, ko kin manta da ke mu ka tsara komai masoyiya?".

Itama sai da ta sauke numfashi sannan ta kama hannunsa tana cewa, "ai gani na ke kamar kana son karɓanta da gaske cikin zuciyarka, idan ba haka ba taya har za a sa maka ranar aure da ita ba tare da ni na sani ba?" "No Billy Kada ki yi wannan tunanin ma, ina da ke me zan yi da wata wai Asma'u? Na san na yi kuskure da har aka sa ranar ba ki da masaniya, to albishirinki" Billy ta kmsa da goro.

"Iyayen da na tura ba nawa ba ne, 'yan kuɗaɗe na ba wasu tsofaffin bariki, sannan na aikasu da sunan ahalina, su suka nemar min aurenta, sweetheart trust me, ke ce wacche na ke so, please kada ki sake yin wannan tunanin kin ji?" Sake fiska cikin jin daɗi Billy ta yi ta ce, "shikenan, na yarda da kai masoyina", ta faɗi tana sake rungumarsa, shima hakan ya yi mata, fiskarsa ya fitar da murmushi yana yi mata kallon wawuya daga zuciyarsa, ka na ya kuma cewa, "we can go now?" Ɗaga masa kai ta yi ya kama hannunta su ka shige motar da na budurwar ne.

Da sauri na juya na bada baya gudun kada su ganni, hawayen da suka taru tun da na fara jin maganganun Sunusi da wannan budurwar ne su ka tsiyaya kan fiskata, cikin zuciyata sai ambatan inna lillahi wa inna ilaihi raju'un na ke yi, 'me yasa Sunusi zai yiwa 'yar uwata haka? Wacche babu abun da ya ke cikin ranta sai soyayyarshi?' Na faɗi cikin raina ina sake matse hawaye.

Sai kuma na share hawayen da ke zuba a idona, a fili na ce, "Allah na gode maka da ka nuna min asalin gaskiyar wannan bawan na ka" na faɗi sannan na juya ganin sun bar wurin, "Sunusi! Ɗayar fiskarka ya bayyana a gareni, don haka ba zan taɓa barin burinka ya cika akan Asmee ba! Ita 'yar uwata ce, ba za ka taɓa samun abun da ka ke so daga gareta ba. Tabbas zan je na sanar mata da duk abun da kunnuwana su ka ji anan!".

Na faɗi fiskata babu tsoro, cikin raina na ce, 'ya Allah ka kare min 'yar uwata daga sharrin wannan mutumin'. Sannan na juya don komawa inda su ke, sai dai ko da na isa ban samu su Asma'u ba, kuma banga motarmu ba, na tambayi mai shagon ice cream, ya sanar da ni sun jirani da su ka ga ban dawo ba, sai su ka tafi, ya ji suna cewa ƙila na tafi gida, godiya na yi masa sannan na nufi kan hanya na tari napep na hau. 

Bayan na isa ƙofar gida na sallami mai mashin sannan na tura gate na shiga, gaba ɗaya hankalina ya gaza kwanciya, ina isa cikin falo Momy ta hau tambayata ina na tsaya? Yanzu ta gama yiwa su Asma'u masifa akan me za su dawo su barni? Kwantar mata da hankali na yi ina tambayarta ina Asma'un ta ke? Ta ce da ni yanzu ta fita ƙila tana ɓangaren Hajiya Kaka.

Da sauri na yi ɗakinmu na ijje jakata, ban tsaya jira ba na fice nufan sashin Hajiya Kaka. Ko da na isa samunta na yi a zaune kan kujera ta yi tagumi, ban lura da Ayusha da ke zaune can gefe ba, da ya ke ba na cikin nutsuwata, kiran sunanta da na yi ne yasa da hanzari ta miƙe tana kallona ta ce, "Nuriyyah ina ki ka shiga ne? Mun yi ta jiranki ba ki dawo ba, mun yi tunanin kin dawo gida amma kuma bakya nan, Momy sai faɗa ta ke yi mana, wai akan...".

Ba ta ƙarasa maganar ba saboda rungumarta da na yi idona na tsatso ƙwallah, ɗagowa na yi ina kallonta yayin da ita kuma ta ke bina da kallon rashin fahimta, "me ya same ki?" Ta faɗi tana dafa ni ganin yanayina wani kala, ni dai na kasa magana, bansan ta ina zan fara sanar da ita abun da na ji ba, na san Asma'u tana matuƙar son Sunusi, to ta ina kuwa zan sanar da ita wannan lamari? Na san za ta ji zafi sosai cikin ranta.

Asma'u ta girgizani ta ƙara cewa, "me ya faru ne don Allah Nuriyyah? Just tell me what happened to you?" Sai da na haɗiyi miyau ka na na ce, "zan sanar da ke, amma mu je ɗakinmu za mu fi jin daɗin maganar" na faɗi sannan na janyo hannunta mu ka bar sashin.

Ayusha kuwa da ta ke kallonmu, sai ta miƙe domin kuwa ya kamata itama ta ji me zan sanarwa Asma'u.  
Zama na yi a gefen gado bayan mun shiga ɗakinmu, na ma rasa ta ina zan fara yin wannan zance haka? "Yi maga mana, mun shigo ɗakin amma kin yi shiru, a ƙarshe ma zama ki ka yi kin kasa cewa komai, kin kullar min da kai wallahi" faɗin Asma'u.

Daurewa na yi na ɗago ina dubanta na ce, "Asmee wani babban al'amari na ji, kuma na gani Asmee" zama kusa da ni Asma'u ta yi cikin damuwa ta ce, "mene shi al'amarin? Komai lafiya kuwa?" ''Yar uwata akwai matsala, ina jin nauyin sanar da ke don na san za ki cutu, amma kuma ba ni da zaɓi saboda ba zan iya zuba ido wani ya illata min ke ba", na yi maganar cikin sanyin jiki.

Asma'u ta ce, "dan Allah Nuriyyah ki gaggauta sanar da ni abun da ke faruwa, kimin bayani kai tsaye kin fara razanar da ni", sauke ajiyar zuciya na yi, na rintse ido sannan na buɗe ina faɗin, "Asmee... abin da zan faɗa miki zai girgiza zuciyarki" kallona kawai Asma'u ta ke yi cike da tsoron abun da zance, na ɗaura da cewa, "akan saurayinki wanda ki ke son ya zama mijinki ne wato Sunusi" Asma'u ta miƙe da sauri zuciyartana harbawa, "me ya samu Sunusin? Me ya same shi?!".

Nima tashi na yi na sake cewa, "babu abun da ya same shi, hasalima shine ke son cutar da ke" "cutar da ni?! Kuma Sunusin? I don't understand", ta faɗi cikin rashin gane inda na dosa. Kama hannunta na yi na kuma zaunar da ita saman gadon na fara cewa, "ƙwarai kuwa Sunusi na son cutar da ke, yau na ga asalin halinsa, ba son tsakani da Allah ya ke miki ba, yana da wache ya ke so, ba ma wannan ne abun damuwar ba, shiri ya yi ya zo gurinki don cinma wani manufarsa".

Ta fisge hannuta daga cikin nawa, ta miƙe tana kallona haɗi da girgiza kai cikin rashin amincewa da kalamaina ta ce, "me ki ke cewa? A ah! Waye ya sanar da ke wannan ƙaryar Nuriyyah? Waye ya ke son rabani da Sunusi ya zauna ya tsara miki wannan maganganun? Ba gaskiya ba ne toh, ko kuma ba Sunusin da na ke so ya ke nufi ba, Sunusina ba zai min haka ba, no impossible!".

Miƙewa na yi ina kellonta cikin tausayawa na ce, "Asmee ba wani ne ya sanar da ni ba, ni ce na ji da kunnena kuma agaban idona, Sunusi yaudararki ya ke yi, hatta iyayen da su ka zo neman aurenki gidan nan ba iyayensa na gaskiya ba ne" nan na labartawa Asma'u duk abun da na ji da kuma wanda na gani. Sakin jiki tayi ta zube à ƙasa, hawaye su ka fara galla a kan kumatunta, zuciyarta na bugawa cikin tashin hankali.

"Kenan tsawon lokacin nan ƙarya ya ke sharara min? Dama yaudarata Sunusi ya ke yi? Me yasa zai min haka? Me na aikata masa? Me ya ke nufina da shi?" Cewar Asma'u ta fashi da matsanancin kuka, nima ƙasa na yi na rungumeta ina kuka cike da tausayinta, da ban ji gaskiya ba yau da shikenan rayuwarta ya faɗa cikin matsala, Allah na gode maka.

Ayusha da ke laɓe ta ji komai, jinjina kai ta yi ta juya ta koma falon Hajiya Kaka, ko da ta shiga daidai lokacin da wayar Asma'u da ta bari a falon ya yi ƙara, zuwa ta yi gurin wayar sai ta ga my love ne sunan wanda da ya ke kira, ga numbern kuma a ƙasan sunan, ɗaga wayarta ta yi ta fara ɗaukar numbern, kafin ta gama kiran ya katse, shiga wayar ta fara yi amma kuma akwai pin.

Ta furzar da iska daga baki cikin rashin daɗi, abun da ta ke son yi ba zai yu ba yanzu, kwatsam kuma sai kira ya kuma shiga, ganin wanda ya kira ɗazun ne yasa ta ƙarisa kwashe numbern sannan ta ijje wayar. Zuwa ɗakin da ta sauka ta yi, babu ɓata lokaci Ayusha ta danna dialing numbern, cikin ringing na biyu aka ɗaga, kafin ayi sallama ta ce, "fatan ina magana da Sunusi?".

Daga can Sunusi ya amsa, "eh shine" wani irin murmushi ta sauke sannan ta ce, "Sunusi mai son auren Asma'u saboda wata manufa" "wacece ke!?" Faɗin Sunusi daga wayar da firgicijin kalamanta, "kwantar da hankalinka, ni mai taimakonka ce, ya kamata mu samu lokaci mu tattauna", "zuwa yaushe?" Faɗin Sunusi.

Ayusha ta ce, "zan turo maka da gurin zuwa anjima sai mu haɗu" ta faɗi sannan ta sauke wayar, ta zauna kan gadonta cikin 'yar dariyar mugunta ta ce, "thanks Nuriyyah! Kin kawo min wata hanya da kanki, zan yi amfani da wannan damar don aiwatar da abun da na ke so à kanki!".

YAMMACI.

Tun ɗazu Sunusi ya iso yana jiran wannan wacche ta kira san, da alama kuma ta san sirrinsa, gaba ɗaya ya kasa sukuni sai safa da marwa ya ke yi, ya ma kasa zama yana ta duba lokaci cikin wayarsa. 

Kasancewar ya tura mata da hotonsa hakan yasa Ayusha ta ganesa, musamman ma da ta ga kamar ba a natse ya ke, ta san hankali a tashe ya ke da jin maganganunta. "Sunusi masoyin Asma'u!" Ya ji muryarta ta faɗi hakan, sa sauri ya juyi yana zuba mata ido, Ayusha ta kuma cewa, "mu samu mu zauna mana", ba musu su ka samu guri su ka zauna kan kujerun robar da ke wurin, Ayusha ta ijje jakarta kan table na kujerun da ke tsakiyarsu.

Sannan ta sa hannu ta zare baƙin glass da ke idonta, magananta na kansa ta ce. "Sunusi masoyin ƙarya, mai mummun nufi ga masoyiyarsa mai ƙaunarsa da gaskiya" "wacece ke kuma ya aka yi ki ka san hakan?" "Ba ma ni kaɗai ba, har ita kanta Asma'un da ka ke son aura ta san komai akanka", miƙewa Sunusi ya yi cike da fargaba ya ce, "what!? Ta ya ta sani? ban gane me ki...".

"You want to know, yadda aka yi Asma'u ta sani? To wannan dai Nuriyyahr ce ta sanar da ita komai, domin ɗazu kafin ta dawo makaranta ta ganka kai da wata mace, sannan ta ji duk abun da kuka tattauna, because of that, na san yanzu Asma'u za ta yanke duk wata alaƙar da ke tsakaninta da kai, kuma I'm sure! Aurenka da ita ana gaf da ɓata shi".

Sunusi ya waro idanu yana cewa, "a ah hakan ba zai taɓa faruwa ba! Ta ya Nuriyyah za ta rusa min budget cikin ƙanƙanin lolaci?" Ya ƙarashe cikin ɓacin rai. "Relax relax ɗan saurayi, As I told you earlier, ni mai taimakonka ce, so that, za ka iya zama mu tattauna kaɗan".

Girgiza kai Sunusi ya yi, kamar ya gamsu da zancenta, don haka ya koma ya zauna yana kallonta ya ce, "ta ya za ki taimakeni? Bayan kin sanar da ni Asma'u ta riga da ta ji komai?" Ayusha ta gyara za ma tana faɗin, "ni 'yar uwarsu ce yanzu haka a gidan na ke da zama, hakan yasa na ji duk abun da ya faru. Kar ka damu da don Asma'u ta ji komai akanka, amma ina tabbatar maka idan ka bani haɗin kai to za ka aureta kuma ka cinma muradinka Sunusi".

"Me ki ke so? Menene buƙatarki cikin hanyar? Domin da alama akwai shirinki kema", sai da ta yi masa murmushin gefen baki, sannan ta maida glass ɗinta a idanuwanta, ta ce, "ka canka daidai! Of course nima akwai buƙatata a ciki, shiyasa na ke son mu haɗa hannu a tare, don samun mafita ta ko wace ɓangare".

"Nawa ne kasona à ciki?" Cewar Sunusi da shima fiskarsa ya fito sak asalin halinsa, don ya gane wannan 'yar hannu ce, da mamaki Ayusha ta ce, "Ban gane ba? Wani kaso bayan ko wanne acikinmu burinsa ya ke son cimmawa?" Murmushin rainin wayo Sunusi ya jefa mata ya ce, "maganarki gaskiya ne, amma idan kin lura ke ce ki ka zo gurina, kenan kamar aiki ki kawo min, saboda haka sanar da ni kasona à ciki".

Sakin fiska Ayusha ta yi domin tun da ta samu mafita ba za ta yarda ya kufce mata ba, don haka ta ce da shi, "you have no problem, zan ba ka duk kuɗaɗen da ka ke so" ɗaga kai Sunusi ya yi ya ce, "ok menene shirin yanzu?" Ayusha ta ja numfashi tana kallon Sunusi, sannan ta jingina da kujerar tana dariya......


Last page
___________________________________________________


Toooo ashe Sunusi wani shiri ya ke yi akan Asma'u, Nuriyyah ta gane gaskiya, kuma ta sanar da ita. Ga Ayusha kuma ta samu hanya à dailin haka, to menene shirin da ta ke shiryawa da Sunisin?

Mu kasance da ku à kashi na gaba zuwa gobe idan Allah ya kaimu🥰




_*🌹𝑍𝑎ℎ𝑟𝑎-𝑡𝑢𝑙-𝑄𝑎𝑙𝑎𝑚🖋️*_