BLOOD CROWN (THE HEIRS APPARENT)

PAGE _______18 & 19

by @swrites22




Ƙarfe biyu daidai ya tashi daga gaban system ɗin sa, daga shi sai short nicker, zuge curtain ɗin yayi glass wall din ya Bayyana wanda hakan ya bashi daman ƙarewa ko Ina kallo garin yayi shuru sosai baka jin motsin komai sai ƙaran kukan wolf daga nesa kaɗan kaɗan, maida curtain ɗin yayi ya rufe tare da yin miqa ya koma gaban system ɗin ya kashe, sannan ya wuce gaban wardrobe ɗin ya ɗauko kayan da zaisa, tsabar yauqi irin nasa saida yaja 30 minutes kafin ya gama shiryawa cikin Biker jeans dark brown tare da t shirt dark brown sannan ya ɗaura light brown trench coat, ƙafarsa sanye da Boot shi ma dark brown. wucewa yayi zuwa wurin bedside drawer ya buɗe ya zaro wata ƙaramar bottle kamar ta Syrup, buɗewa yayi tare da ɗage kansa ya kurɓe shi duka sannan ya cilla kwalbar cikin dust Bin, Jim yayi a tsaye na tsawon 4 minutes sannan ya wuce kan gadon ya ɗauki neck gaiter ya sa sannan ya daura fedoras a kansa, bug ya ɗauka ya maqala a kunnuwansa, wani file dake kan mirrorn sa ya wuce ya ɗauka ya sanya cikin trench coat din sannan ya fita ya kullo ƙofar ya sanya key a aljihun sa. 

Tafiya yake yana waiwaye wanda hakan yasa kallo ɗaya zaka masa kasan bashi da gaskiya, wata kwana ya yanka wadda tayi daidai da connecting ɗin bug ɗin kunnen nasa, dafe kunnen yayi yana sauraran maganar da ake masa ta ciki, duk kwana da zai shiga in yazo sai a faɗa masa,  yana zuwa kan wani layi muryar dake fita ta ciki ta fara rawa, sake dafe kunnen yayi saidai baikai ga jin komai ba ya yi disconnecting gabaɗaya. "Sh**t "........... Ya furta yana datse haƙwaransa tare da jujjuyawa yana bin layin da kallo, shuru yayi na wasu second sai Kuma ya ɗaga Kai ya kalli wani gida duk da a duhu ne amma yana iya hango mutanen dake tsaye suna shanya a balcony ɗin kasancewar ba ƙofa sai stairs kawai shi ma kamar na kasa ce, matakalar ya bi har ya hau wurin su, yana shirin yin magana, ɗayan cikin su ya garo bucket gabansa wanda ya gangara har ƙasan stairs ɗin ta other side, wurin yabi da kallo juyowar da zaiyi ba mutanan, da sauri yabi stairs ɗin yana kalle kalle, haka ya cigaba da tafiya ba tare da yasan inda hanyar zata kaishi ba amma kallo ɗaya zaka masa ka tabbatar ba wata damuwa a tare dashi saboda tafiya yake cike da nutsuwa kamar ko yaushe. 

A gaban wasu mutanen ya bayyana su huɗu ne kan kujera suna shan shisha, ɗaya daga cikin su ne ya taso yana faɗin. " Sai yanzu kake zuwa?".

Saida ya kalla sauran ukun da suke harkar gaban su kafin ya ce, "Duba agogon hannun ka"............"3am ne yanzu".........Ya amsa .

"Shi ne time ɗin da aka bani. Waye wanda zan gani?"........... Ya tambaya yana kare masa kallo cikin dan hasken dake wurin. 

Juyawa yayi wurin sauran da faɗin, "Jam ga baqon fa ya ƙaraso".......... Tashi jam yayi yana faɗin, " Ina zuwa".

Shigewa yayi gaba sannan wanda ya fara tarar Amjad yabi bayansa, shi ma Amjad ɗin ya rufa musu baya, gaban wata ƙatuwar ƙofa suka tsaya makulli Jam ya ciro daga aljihun sa tare da buɗe ƙaton ƙwadon dake jikin ƙofar, wani babban falo ne ya bayyana a gabansu tafiya suka cigaba dayi har sai da suka ƙure ƙarshen falon, hannunsa ya ɗaura akai tare da faɗin, "Gamu munzo!"........wata murya ce da basu san daga inda ta fito ba ta ce, "Na ganku ai".

Tiles ɗin dake gabansu ne ya fara buɗewa slowly, wasu stairs zuwa ƙasa ne ya bayyana a gaban su. ( aiki ja, Mamaki ne ya sake kasheni, saboda daga waje in kaga gidan baza ka taɓa tunanin zai dauki wanna Wuraren ba, dan kallo ɗaya zakayi masa kace in akayi wata iska me ƙarfi tsab zatayi gaba da gidan).

Shiga yayi suka bishi a baya suna gama shiga tiles ɗin ya koma ya rufe wani shiryayyen falo ne cike da mata da maza kamar wani ƙaramin club, wani slow music ne ke tashi speakers kawai kakeji suna dukan kiɗa, wasu na rawa, wasu na zaune kujerun dake cikin falon suna hira haɗe da ciye ciye, wasu Kuma suna yan kurɓe kurɓen su, hayaqi ne kawai ke tashi sai ka zata wani abun ake babbakawa.

Dakatar dasu wani mutum yayi, baka ganin komai nasa sai idanunsa kawai Kai kace irin ninja ɗin nan ne. Wanda ya fara tarar Amjad ne ya ce, "Wurin BB LALO"........... baice komai ba ya wuce can ciki wurin wata doguwar kujera wanda wani mutum ke zaune ya ware hannuwansa kan headrest ɗin kujerar, ƙafarsa ɗaya Kan ɗaya, hannun sa riqe da tumbler na wine, gefen sa wata mace ce sanye da yar ƙaramar riga da wando Wanda dasu da babu duk ɗaya, ta ɗaya gefen ya matsa tare da raɗa masa wani abu a kunne, da hannu ya masa alama da yaje ya shigo dasu.

Zuwa yayi ya faɗa musu su ƙaraso sannan ya shige gaba suka bi bayansa zuwa wurin BB LALOn, Sai da ya Ƙare masa kallo sannan ya masa nuni da wurin zama da hannu, tare da duban matar dake gefensa tun kafin ma yayi magana ta miqe tabar wurin, zama Amjad yayi, yayinda BB LALO ya buɗi baki cikin murya irin ta uban daba ya ce, "AMJAD HASHIM DARWIN?"..........gyada masa Kai yayi alamar eh.

Bubbuga dantsen hannunsa yayi sannan ya ce, "buɗe!"......... janye dogon hannun trench coat ɗin tasa yayi bai ƙarasa ba yaji wani irin radaɗi a dantsen hannun nasa kafin ya gama dawowa nutsuwar sa har jam ya zare abun dake hannun sa me kama da syringe, da ido BB LALO yayi masu alamar suna iya tafiya, juyawa yayi ya bar wurin da sauri yayinda shi Kuma mutumin da ya fara taryan Amjad ɗin ya gyara tsayuwa da alama bai gane me BB LALO ya faɗa da ido ba.

Gyara zama BB LALOn yayi da faɗin, "Ina P I file din ka?"........... Zaro file ɗin Amjad yayi a cikin rigarsa ya miqa masa, mutumin nan da ya masu iso ne ya ƙarɓa sannan ya miqa masa, duddubawa yayi sannan ya ɗaga Kai ya kalli mutumin da sauri ya bar wurin, bai fi two minutes ba ya dawo da faɗin, "Gashi sir".......... Da Kai ya masa alamar ya miqawa Amjad ɗin.

Karɓar files ɗin guda biyu Amjad yayi tare da buɗe na farkon, saida ya gama karantawa sannan ya ɗago ya kalleshi da faɗin, "Kai ne shadow din k........."

Bai rufe bakinsa ba yaji harbin bindiga da baisan daga inda ya fito ba, da wani slow move ya Kai kallon sa gefensa inda mutumin nan da ya tarye shi yake tsaya Amma sai ya ganshi zube a kujerar dake gefensa goshin sa na fidda jini alamar shi aka harba, kafin ya gama tantance meke faruwa ya tsinci murya BB LALO in da yake faɗin, "Wannan shi ne hatsarin dake tattare da Shadow, an ma uzuri saboda wanna shi ne zai kasance aikin ka na farko dashi, kuma information da ya samu a kanka yasa ya buqaci yin aiki tare dakai, saboda shi yafi son aiki da wanted criminals irin ka, dan haka Ka kiyaye. Shi ɗin daban yake, inuwa ce da ganin ta sai a haske shi kuma duhu ke lulluɓe dashi, aiki dashi abu ne me matukar hatsari akwai rules a file ɗin dake hannunka, ka karanta sannan kayi signing, Kuma ka sani baka da samar canza ra'ayi tunda har ka zo nan to rayuwa ko mutuwa shine kawai zabin da kake dashi".

Wani shaiɗanin murmushi Amjad yayi Wanda ya sanyashi rikiɗewa ya saje dasu. "Ni da kake gani, zaɓi tsakanin rayuwa da mutuwa bashi bane a gabana, saboda dama ban fito ba saida na shirya tunda kaga har duniya ta shiga rudani a kaina Kuma still ina rayuwana yadda nakeso to ka tabbatar da ni ɗin zaɓi na ba ɗayan biyu bane, zuciyata ta kan kirkiri zaɓi sama da uku, ba buqatar nayi ma dogon bayani dan shi Wanda zanyi wa aiki ya riga da ya san waye ni"..........ya ƙarashe Yana zaro pen a aljihun sa yayi signing.

"Gebriel karɓi Ka haɗa da wannan Ka tabbatar sun isa wurin oga domin sanyasu a record".

Karɓa Gabriel yayi tare da haɗa files ɗin wuri guda. " Ka Kira azo a dauke min gawar nan".......... Faɗin BB LALO Yana sipping wine ɗinsa hankali kwance.

"Okay!"............Gabriel ya Amsa tare da barin wajen.

Gyaran murya yayi yana sake relaxing cikin kujerar ya ce, " A wanna file ɗin dake hannunka akwai paper work na iya adadin mutanen da ake buqata daga wajen ka sannan akwai wani specified person da ake buqata shi ma, akwai sunansa, address da kuma duk wani info ɗin sa a ciki".

"To batun payment fa? Dan ni farashi na per person ne ba wai grouping nake ba".

Girgiza masa kai BB LALO yayi kafin ya ce, "Ba'a tsadance kuɗi dashi dan shi duk wa'anda ke aiki dashi price ɗaya ke garesu, a yanzu za'a baka rabi in aiki ya kammala zaa cika ma."

Ɗan shuru Amjad yayi kafin ya ce, "Inajin kamar ban yadda dakai ba, Anya ba gadar zare aka shiryamin da sunan shadow ba, in ba haka ba ai shi zai ban aiki tsakanin ni da shi ba wai dakai ba" ...........Amjad ya faɗa yanayin sa na ɗan sauyawa haka zalika bugun zuciyar sa Amma a fuska baza ka taɓa iya cewa ga halin da yake ciki ba, Dan masu iya magana nacewa labarin zuciya a tambayi fuska Amma a wurin Amjad ba haka bane duk abunka baza ka iya karantar abinda ke zuciyar sa ba daga yanayin fuskarsa. 

Wata irin dariya irin ta basawa BB LALO yayi kafin ya ce, "In dai akan shadow ne kar kayi tunanin ganinsa ko haɗuwa dashi har iya tsawon lokacin da zakayi aiki dashi, shin zaka iya yadda in nace ma tsawon shekaru ashirin Ina aiki tare dashi Amma ban taɓa ganin sa ido da ido ba"........... Ɗan dakatawa yayi tare da ɗaukan kwalbar wine ɗin dake gabansa akan table ɗin da ya raba tsakiyarsu tsakanin sa da Amjad ɗin, sake tuttulawa yayi a tumbler ɗin sannan ya cigaba, "Zaifi kyautuwa idan ka kawar da duk wani tunani dake kwakwalwar ka, ka maida hankali Kan aikin dake gabanka ba wai batun ganin Shadow ko wani abu ba. Akwai deadline na aikinsa yana nan a cikin file ɗin dan haka Ka Kula ka Kuma kiyaye dokar sa".......... Ya Ƙarashe yana ɗaukan wayar sa ya tura wani saqo, wani Ninja ɗin ne yazo sanye yake da kaya irin na Gabriel hannun sa ɗauke da wata babbar suitcase, da ido ya masa alamar ya bashi. A gaban Amjad ya ajje sannan ya juya ya bar wurin.

"Wanna shi ne rabin kuɗin aikin ka, kana iya tafiya".........Bai sake cewa komai ba ya ɗauki suitcase ɗin ya tashi.

Kunsan meysa suka harbe wanna mutumin dukda shi ɗin ya kasance Yana aiki a karkashin su ne, to saboda ya kuskure wurin fahimtar alamar da BB LALO yayi musu da ido, haka suke basu da sani ko sabo, kuskure kaɗan kayi a bakin Ranka.

_____________Shi kuwa Amjad Masaukin sa ya koma, bayan yayi locking ɗakin ya Ƙarasa bakin gadon tare da ɗaura suitcase ɗin akai ya buɗe shi, tozali yayi da bundles na wasu miqaqqun pounds masu uban yawa, dan zai iya cewa daga bank sai cikin suitcase ɗin nan saboda yadda suke wani daukan ido"...........wani light smile ya saki tare da lumshe idanun sa ya buɗe, ɗaukan suitcase ɗin yayi ya adana sannan ya faɗa bathroom.

_____________"Anah wato maganar gsky mutanan nan sun gudu, ni daman tun farko nasan basu da gaskiya shirya musu komai akayi".

"Hasbunallahu wani imal wakil, to Juraysh meysa baza a nemo su ba, in aka barsu sunci banza kenan sun ɓatawa yaro na suna Kuma sun gudu".

"Ai Anah ko mu bamu nemo su ba hukuma zata nemo su, inaga mu bar musu komai kawai dan dole za'a nemo su, in Kuma ba'ayi hakan ba mu sai mu dau mataki".

"Shikenan, amma gsky raina yayi matuƙar ɓaci whl wanna ai rainin wayo ne ma, wai dan ALLAH me mutane suke so da yaron nan ne? Me ya tare musu a rayuwa? Kowa bashi da buri da ya wuce su ɓata shi, ka duba fa sanadiyyar haka Alhaji ya kwanta ba baki ba ƙafa ba hannu wanna wani irin tashin hankali ne".

Cikin jimami Juraysh ya ce, "Anah duk wani Wanda ke nasara a kan komai kamar Amjad dama dole yayi maqiya a boye ai harma da filin, shi ɗin fa guguwa ce da in ya taso dole kowa yayi ƙasa da kansa, ALLAH ne kaɗai yasan iya adadin mutanan da Ƙurar Amjad ta shigarwa ido".

"ALLAH ya fisu, cigaban sa Kuma da basa so in Sha ALLAH saidai zuciyar su ta buga, ni gashi ma tunda ya tafi KM ɗin nan ban cika samunsa a waya ba".

"Kai Anah bafa yau Amjad ya saba tafiye tafiyen nan ba, Kuma kinsan dama duk lokacin da yayi tafiya to ayi sallama da samunsa a waya ".

"Amma Kuma yanzu ai a cikin ƙasa yake Bai kamata ace ana rashin samun sa ba kamar da da yake fita abroad. Me ma yaje yi to shi da yanzu ba wani aiki yakeyi ba, ba gwara ya zauna a gida ba Nima Ina ganin sa hankali na ai sai yafi kwanciya".

"Amma Anah abun zai masa yawa idan akace za'a takurashi sosai, sai ya zama rana zafi inuwa quna, kawai dai mu cigaba da addu'a har ALLAH ya bayyana gsky ".

Sallamar Nuhail ta katse musu zancen nasu, Juraysh ne ya amsa, bayan ya ƙaraso ya miƙa masa hannu suka gaisa sannan ya zauna yana faɗin, "Anah barka da rana".

"Barka Nuhail ashe ka shigo, ya gida ya yaran?".

"Duk sunan nan lpy, ai ƙawar taki ma saida na mata wayo na fito dan in dai taji nan zanzo an dinga rigima da ita kenan saita biyoni".

"Allah sarki, Kai Kuma baka son kawo su ba".

"Ba haka bane Anah, Ina cewa zan taho da ita su ma sauran zasu ce sai sunzo ni kuwa bazan iya yawo dasu duka ba saisa sai nace su bari sai maman tasu zatazo saisu biyota".

"Allah sarki, ALLAH ya albarkace su gabaɗaya ".

"Ameen ya ALLAH!, ya wurin Amjad kuwa, kwana biyu bana ganin sa kuma bana samun wayar sa, dama akwai wata maganar da zamuyi ne?".

"Eh tou nima gsky ba kasafai nake samunsa ba tunda yayi tafiyar nan".

Ta tabbata dai yayi tafiyar kenan ya faɗa a zuciyar sa, ba tare da yasan zancen zucin da yake ya fito fili ba.

"Naam magana kake ne".........Anah ta tambaya.

Da sauri ya ce, "Ah ah bakomai cewa nayi mu bamu ma san yayi tafiyar ba ina yaje ne?".

"Khor maksar"..........Juraysh ya bashi amsa a daƙile Yana hararar sa ta ƙasan ido.

"Au ashe ma Yana ƙasar ai na ɗauka ko ya samu fita ne dukda har yanzu bamuji abinda ƙasashen suka yanke ba a Kan sa, kuma gashi abun yana son shafar yanayin aikin mu dan a yanzu babu zancen fitar da Kaya daga refinery's ɗin Dada haka kuma kasuwar ƙasashe masu shigowa HD aurum mining yanzu sunja baya, ga batun case ɗin sa da yarinyar nan Kuma naji an fara raɗe raɗin wai an batar da yarinyar da iyayen ta".

Kallon Anah Juraysh yayi kafin ya ce , "kamar ya? an batar dasu ko Kuma sun gudu saboda basu da gaskiya".

"Ei to ni dai abinda naji kenan cewa an batar dasu "..........."A Ina kaji?".

"Zancen duniya ai baya ɓuya malam Juraysh, ni dama abinda yasa nake neman sa mu tattauna kenan saboda wanna Abun qimar gidan mu ce gabaɗaya, batar da yarinyar da iyayen ta bashi bane solution kamata yayi a zauna ayi maslaha".

"Kai cema akayi shi ya ɓatar dasu kenan?"............ Juraysh ya tambaya yana tsare shi da ido.

"Haka mutane suke cewa, Wai saboda gudun tonuwar asirin sa".

"To kai mutane ne? Kai ai ɗan uwansa ne, kai me iya ƙaryata wa ne ma ba wai kazo kana cigaba da yayatawa ba".

"To yanzu wani wuri naje nayi zancen ne? Ina cewa anan wurin daga ni sai Kai sai Anah, waye bare a cikin mu Anah da take mahaifiyar sa ko Kuma Kai da kake cousin ɗin sa".

"Whl ku canza hali, Sam wanna bashi bane abinda ya kamata ku dingayi matsayin ku na yayyun sa, abinda ya shafe shi ai ya shafe ku ne duka".

"Ya isa haka juraysh"......... Anah ta faɗa tana ƙoƙarin tausar zuciyarta dake zafi.

"Ka dai yi min gurguwar fahimta ne kawai Juraysh Amma ba damuwa, Anah ni zan koma".......... ya karashe Yana miqewa ya musu sallama ya fita.

Waya Anah ta ɗauka. "Anah me zakiyi?".......... Juraysh ya katseta.

"Juraysh so nake naji ko da gaske da sa hannun sa a ɓatan yarinyar da iyayen ta, hankali na gabaɗaya ya kasa kwanciya, zuciyata ta rasa sukuni". 

Girgiza kansa yayi da faɗin, "Haba Anah Kar ya zama kema ana influencing ɗinki mana, Anah idan har Amjad zaisa a batar dasu kenan bashi da gaskiya kuma ya aikata laifin da ake zargin nasa dashi"........... Shuru tayi ya sake faɗin, "kiyi tunani sosai fa Anah, ni whl ko wa'annan Yan uwan nasa ba wai na yarda dasu bane, ki duba fa yadda yake Ƙara wani sussunkuyar dakai, shi fa munafiki baya zuciya duk abinda zaka masa zai shanye ne".

Shuru Anah tayi tana tunanin maganganun Juraysh ɗin Kuma da alama suna tasiri a tattare da ita.


_____________Zaune suke a wani madaidaicin falo su biyu ne sanye da ƙananun kaya polo t shirt da sweet pant irin na sport, t shirt ɗin ta bayyana ƙwaryar tumbin nan nasu ras dashi. "Dalilin da yasa na buqaci ganin ka Alhaji Huzaif daga ni sai Kai ba tare da ko su Abid sun sani ba shi ne nasa an dauke yarinyar nan da iyayen ta"............Saurin kallon sa Alhaji Huzaif yayi kafin ya ce, " Mai sa zakasa a ɗauke su, yanzu in kotu ta zauna aka nemi ganin su fa, ai sai mutane suce dama ƙazafi suka masa".

"Eh ai gudun tonuwar asirin sa ne yasa ya ɓatar dasu"......... Kallon sa yake cike da Neman Ƙarin bayani.

"Saboda a wannan zaman zasu bayyana shaidun da kotu ta buqata mana sunan sa zai ida baci ".

Shuru Alhaji Huzaif yayi kafin ya ce, "To naji, amma ai tare ake komai dasu Alhaji Abid mesa yau Kuma kace mu haɗu mu kaɗai daga ni sai Kai?".

Gyara zama yayi da faɗin, "Abinda ya tara mu anan daban ne, bana so mu bawa Ahuoyzah haɗin Kai ya samu wanna karɓuwa a majalisar man fetir ta duniya, domin fa mu yan kallo zamu dawo".

"Ehhhh Kuma haka ne, amma Kuma ai zai biyamu sannan yanzu in mun masa haka miye namu"......... Ɗaura ƙafarsa yayi ɗaya kan ɗaya yana murmushi ya ce, "Zamu barwa Ramphant Juwaira filin domin shi ya dace ya samu wanna karramawar ta wanna shekarar".

"Canza hanya zamuyi dasu kenan?"....... Alhaji Huzaif ya tambaya yana gyara zama .

"Ko ɗaya muna daga nan ɗin zamuyi komai Amma bana so su Hammoud su sani, na janyo ka ne saboda Kai ma ka samu alheri a tare dashi, saboda shi babu wanda yafi mu shiga gabansa kuma kasan bai taɓa samun ko da star ɗaya ba so yana cikin ɗokin samu, zai sakar mana ragamar komai ne".

Cikin jin dadi Alhaji Huzaif ya ce, "Dama ai munafukai ne, ni dama tun can na lura sun ɗaukemu kamar wasu yaran su, Kuma mu zamu bisu ta ƙarƙashin ƙasa saidai su gansu kasat wanwar"...........Dariya sukayi tare da tafawa Hajj zawaad ya ce, "kanka na ja Mutumi na".

"Amma fa wani hanzari ba gudu ba".........."Ehh wanne kenan?".

"Batun yaran HD".

"Ina sane da su barsu, dama nake basu kawai suyi nasu tunda yara ne kuma kasan ai su basu san Kan harkar ba, wancan yaron ne ya sani yanzu kuma sun tsige shi gefe, so ba abinda zasu samu wahalar banza zasuyi karshe zasu bace a kasuwar duniya gabaɗaya".

Girgiza Kai Alhaji Huzaif yayi Yana Dariya ya ce, "Baka da daɗi Hajj Zawaad".

_____________Tsaye yake a ɗakin mahaifin nasu
Yana Kai da kawowa waya ce maqale a kunnen sa yana faɗin, "Awais karka min wasa mana kai ma da nake gani me ƙwaƙwalwa, kasan Amjad yana da basira sosai, yana iya bincikosu in ka ajje su a kusa, san samu a fitar dasu daga ƙasar gabaɗaya, ni fa duk wanna shirun da yayi akan komai hankali na bai kwanta saboda na tabbatar akwai abinda yake shiryawa ta ƙarƙashin ƙasa".

Daga ɗaya bangaren Awais ya ce, "Julaybin fitar da wa'annan mutanan ba ƙaramin aiki bane a yanzu kai ma ka sani al'ummah sun san fuskar su hakan kamar tonuwar asirin mu ne ai".

Shuru yayi can Kuma ya ce, "ka shirya su ka sasu a mota su tsallake iyaka mana a baɗɗa musu kammani kawai"..........Awais zai sake magana ya ce, "ka ga karka kuskura ka sake kirana in ba wanna labarin zaka bani ba"...........Yana kaiwa nan ya katse Kiran yana sauke naunauyan numfashi tare da duban mahaifin nasu dake binsa da kallo idanunsa taf da hawaye. Dariya yayi cike da rashin Imani ya ce, "Ohhh I'm so sorry daada an taba na gaban goshi ko? Whl karka ga laifin mu shi yake shiga gaban mu. Amma kasan wani Abu Dada na ɗauka ma alqawarin tozarta Amjad a gaban idonka da idon duniya sai ya wulakantu irin ƙasƙantacciyar wulakantar da Kare ma bazai shinshina ba, sai mu gani ko soyayyar da kake masa zata iya ceton sa"...........Ya ƙarashe da sautin dake bayyana tsananin wutar gabar dake zuciyar sa sannan ya juya ya fice a fusace.


_____________shigowa masaukin nasa yayi wanda baisan wa ya kama ba ma daga airport kawai aka bashi Address card da key ko fuskar wanda ya bashi bai gani ba. Zubewa yayi kan gadon Yana sauke numfashi dawowar sa kenan daga yawon zaga garin da ya fita, sosai yake sake jin son yin aiki tare da Shadow dan daga gani kamar yadda yake hasashe akwai riba a tare dashi, to amma tsarin su fa, ta ya zaiyiwa Wanda bai sani ba aiki, ya daɗe Yana lissafe lissafe kafin ya tashi ya rage kayan jikinsa ya janyo system ɗin sa, jadawalin aikin dake gabansa ya shiga tare da dudduba abinda ya kamata, saboda so yake ya koma gida a satin nan dan can ma akwai abubuwan dake gabansa. Saida ya gama duk wasu abubuwa masu mahinmanci sannan ya kashe komai ya wuce bathroom ya watsa ruwa ya fito ya fada gado don gobe da yamma zai bar kasar Denmark .

TO JAMA'A NASAN KUN DASA AYOYIN TAMBAYA A WANNA PAGE ƊIN, TO NIMA DAI HAKAN TAKE A WURI NA ALQALAMI NA NE KAWAI ZAI BAYYANA MANA AMSOSHIN MU.



-------------------------√



Tun bayan lokacin da ya kira ya shaida Mata kuɗi ya shiga bai ƙara kira ba saida akayi sallar la'asar sannan kiransa ya shigo wayarta, tsame hannunta tayi daga cikin ruwan da suke ƙarasa wanke kayayyakinsu tare da karɓar wayar da Shazeen ta kawo Mata, amsawa tayi inda ta tsinkayo Muryar sa na faɗin, " Hello".

"Hello Baba ilerika ya ake ciki?"............." yauwa hajiya gashi na ɗauko motar ɗaukan kayan ki turomin addreshin gidan".

"kaga ba fa wani wuri bane da nisa titin da muka haɗu dazu, wannan dai layin da ya shiga ciki, kuna shigowa ma Ka kirani zan fito saboda ba lalle motar ta iya ƙarasowa ƙofar gida ba".

"To tou shikenan"............Ya faɗa tare da kashewa, Shazeen ta miqawa wayar, "Ungo riqe in ya Kira ki faɗamin bari na fito da kayan, Kai kuma Sahnish kayi Ka haɗa ƙwanukan nan gasunan zuwa da motar ɗaukan kayan"...........Ta ƙarashe tana wucewa ɗaki ta fara fito da kayansu kasancewar ba wasu kayan kirki bane yasa kafin su ƙaraso duk ta firfito dasu suna shigowa bakin layin ya kirata, dankwalin Shazen dake kan igiya ta zara ta rufa a kanta sannan ta zira slippers ɗinta ta fita.

Na gaya muku wani abu? Hushaima sam bata damu da ta wani suturta jiki ba a cikin unguwa Saisa yawanci yan unguwar suke mata kallon karuwa yar iska, ita kawai duk abinda zuciyarta ya raya mata to fa bata tsayawa wani tunani kai tsaye takeyin sa ba ruwanta da kowa kawai rayuwarta take kamar ita kaɗaice a cikin duniyar, tana kuma sane da kallon da yan unguwar suke mata, amma sam hakan bai dameta ba, ba kuma ta damu da gyara tunanin kowa ba tunda har ita ta san kanta. WANNAN KENAN.

A nan farkon layin ta hango su hakan yasa ta Ƙarasa tana faɗin, "Anan kuka tsaya ashe, dama na faɗama ai, motar baza ta samu shiga ciki ba, saidai muje dasu su kwaso kayan ".

"Layin naku ne sai hakuri amma ba damuwa, Kai sauko muje a ɗauko kayan"........ Ya fada Yana wucewa gaba, suna zuwa ta shige gidan, ganin sun tsaya ya sata faɗin, " Ku shigo Ku fita dasu mana ".

"Kuje Ku kwaso, Bari na jiraku anan"............Ya Ƙarashe Yana matsawa jikin wani kango dake opposite da gidan ya kunna lalitar sa yana ja Yana kallon su suna kwaso kayan har suka gama sannan ya kashe ya koma ƙofar gidan inda Hushaima ta fito. "Zaku tafi da Sahnish sai yaga gidan, nawa ne kuɗin motar?".

"5k ne, nama ɗauka tare zamu tafi ai gabaɗaya".

"Ah ah karka damu zamu shirya sai mu taho anjima in sha ALLAH, ga wanna 4k ne anjima zan baka ɗayar in kana dashi Ka ranta min ".

"Ba damuwa hajiya sai kun karaso, muje ko?"...........ya faɗa Yana kallon Sahnish da ya fito Yana dandabe ruwan dake hannunsa a bayan wandon sa. "Bari muje ".......... Sahnish ɗin ya faɗa yana wucewa.

"Tom sai kun dawo"..........Faɗar Hushaima tana me gyara tsayuwa, daga nan bakin Ƙofar take hango su har saida suka shiga motar suka tafi sannan ta koma ciki .

Lokacin da Sahnish ya dawo zaune ya samesu sun gama shiryawa, gefen su ya zauna yana faɗin, " Wai ALLAH gamu gare ka".

"Menene kuma?"..........ta tambaya tun kafin ya kai ga zaman.

Ɗan tsayawa yayi tare da kallonta sannan ya gyara zaman sa yana girgiza kai ya ce, " To ai kya bari na zauna Azagwai. Wai ni dama Hushaima mutumin nan bai kaiki kinga gidan ba kika zuba masa kudi har wurin 70k".

Juyowa tayi gabaɗaya gareshi tare da ragewa manyan idanuwan ta girma ta ce. "Me ya faru? karka cemin tarihi ya maimaita kansa?".

Murmushi yayi me kama dana ƙarfin hali ya ce, "Amma kinyi kuskure babba d........."