A CIKIN IDO...

Shafi Na Sha Uku

by @sanazty

A CIKIN IDO...

Ake tsawurya

Wattpad @SaNazdeeyah_

Heart touching love story🥰

KARAMCI WRITERS ASSOCIATION

[karamci tushen mu'amula tagari]

Wannan littafin na kuɗi ne ₦300 regular group ₦500 V.I.P group.

*Zaku tura kuÉ—i ta wannan account 0088814969 Adamu Halima Salahu, Access bank. Ko ku tura katin waya ko VTU ta wannan number *** sannan ku tura shaidar biyan kuÉ—in ta wannan number ****

Ƴan Niger kuma zaku tura katin Airtel ko Orange ga wannan number +227 86 33 10 00 kada ku manta V.I.P 750f Regular kuma 500fcfa, sannan zaku tura shaidar biya ga wannan number +227 86 33 10 00

```Free Page```

Shafi Na Sha Uku

_______________Ta fi seconds biyar kanta a ƙasa, hannunta riƙe da kuncinta, dan marin da ya yi mata ba ƙaramin shigarta ya yi ba, taji shi sosai, taji zafi da raɗaɗinsa.

Ɗagowa tayi, ranta a ɓace idanunta cike da ƙwalla ta kalleshi. "Meheer marina kayi akan gaskiya ta?"

"Har gaskiya kike da ita Noor? Na aureki bisa amincewar Amal da kuma umarnin Mama, ashe ni ban ma sani ba guntun wani na aura. Dama ko lokacin da Amal ta zaɓa min ke a matsayin wacce zan aura nayi tantama kuma nayi mamaki, saboda a ranar Amal ta fara ganinki bata san halinki ba, sannan kuma ni na san ke kika faɗa mata kina sona, kika fito mata a fuskar mutanen kirki.

Noor ni dai kawai na aureki ne saboda Amal da Mommy, kuma Amal ma tafi ƙarfi akai, dan da Amal bata sonki ko Mommy ta dage wallahi ba zan aureki ba.

Noor ki sani babu wata rufa-rufar da zaki wa É—a namiji wayayye da ya yi zurfi a ilmi, ni ina namiji na gujewa zina na gujewa bin matan banza amma in auri matar da take haka?

Ki sani ba matsi ba, ko mai matsin zaki haɗiye muddin namiji ya taɓa shigarki gurin ba zai taɓa haɗewa ba kamar virgin, ki sani in har kin taɓa saduwa da wani namijin to babu matsin da zai matseki sai dai ya yi wani abin, like ƙara ni'ima da sauransu, amma sai dai namiji ya zauna dake a haka ya yi haƙuri, wani kuma har sai ya faɗa miki, wani kuwa ba zai faɗa miki ba sai dai kuyi ta rashin zaman lafiya, a times har da zargi, to ki sani ni ba zan taɓa zama dake, ba zan taɓa zama da macen da bata da ɗa'a"

A fili ta fashe da kuka, shi kukan nata ma ban da ɓacin rai ba abinda ya saka masa. "Maheer ina sonka, wallahi har cikin raina, dan Allah kayi haƙuri in maka bayani"

"Bayani? Na me? Wanda zan gamsu ne? To yi bayanin ina sauraronki" Ya furta cikin zafin rai.

Hawaye ta goge duk da a lokacin wasu basu daina zubo ba.

"Fyaɗe aka yi min tun ina ƙarama" Tayi maganar cikin dakakkiyar murya.

"FyaÉ—e...!" Ya maimaita.

"Amma meyasa baki faÉ—a min ba?"

"Saboda ina tsoron wannan rana"

"Tun kina shekara nawa aka yi miki fyaÉ—en?"

"Ba zan iya tunawa ba, amma dai ban kai 10years ba a lokacin haka Mameeyna ta faÉ—a min" Ta furta tana sharar hawaye.

"Noor! Ki sani Maheer ba ƙaramin yaro bane, idan fyaɗe aka yi miki ko da girmanki ne zaki iya faɗa min ƙaddara na kan kowa, abu na biyu kuma shine da ace fyaɗe ne wanda tun kina ƙarama da tuni kin haɗe. Kin gani zan tafi office kada in dawo in tarar dake a gidana, ki tafi gidanku har sai na nemeki"

Miƙewa ya yi ya fara tafiya tayi saurin tashi tasha gabansa.

"Maheer dan girman Allah kayi haƙuri, wallahi gaskiya na faɗa maka k..."

"Idan ba so kike na tsinka igiyar aurenmu ba to ki matsa ki bani guri na wuce" Yayi maganar ransa a matuƙar ɓace.

Da sauri ta matsa tana kuka, shi kuma ya wuce abinsa.

***

Yana zaune a bedroom É—in Mommy, yafi mintuna biyar da shigowa, kuma lokacin daya shigo É—inma tana wanka amma har yanzu bata fito ba.

Kallon agogon dake ɗaure a tsintsiyar hannunsa ya yi 11:17am ya gani. Miƙewa tsaye ya yi dan ya makara yana so ya samu ya tafi office da wuri.

Zan ɗauke hotunan Noor daga ɗakin Mommy dan kar ta riƙa ganinta tana tunata har jininta ya hau, dan na lura tana matuƙar ƙaunarta. Ya faɗa sannan ya buɗe side drawer.

Photo Album ya É—auko, har zai rufe ya ga letter a ninke an rubuta Maheer. Gabansa ne ya faÉ—i, ya saka hannu ya É—auka.

Letter da Amal ta bani ce wannan. Ya faÉ—a a zuci, mamaki cike da fuskarshi.

Da sauri ya mayar da photo album É—in, bai ma aikata abinda ya yi niyya ba, letter É—in kuma da sauri ya tura cikin pocket É—insa.

Miƙewa yayi da sauri ya fita ya koma parlour.

Zama ya yi jikinsa gaba ɗaya a sanyaye yake. Meyasa Mommy ta ɗauke letter, kuma ina ta nema amma ta nuna bata ma sani ba. Ji yayi ya ƙagu ta fito domin su gaisa ya tafi, dan ba zai taɓa gigin fara karantawa tazo ta sameshi

***

Ajje ɓawon ayabar ya yi bayan ya gama sha, sannan ya ƙara saka hannu ya ɗauki wata ya ɓare, sai daya gutsira sannan ya kalli Rahina.

"Hararata kike?" Ya faÉ—a yana kallonta. ÆŠan turo baki tayi ta ce "Ni ba harararka nake ba"

"To kima harareni ɗin, ai ba kwabonki a cikin wannan ledar, surikina ne ya kawo, kuma bari kiji shi tuwo har abada sunanshi tuwo ba zai taɓa canza suna ba"

Bata ce komai ba. Ya kalli gadon da Mama take ya ce "Gaskiya Balaraba kin bar daÉ—i dama tashi kikayi kika bar kwanciyar nan, domin mu kam mun samu gwarzo mai bajinta yana ta hidinta mana"

"Baba dan girman Allah ka bar maganar nan"

"Ba zan bari ba, ko zaki dakeni ne?"

"A'a" Abinda ta iya furtawa kenan sannan ta mayar da kanta gefe.

"Ina Maheerun?"

"Nima ban sani ba, dan rabona dashi tun jiya"

"Amma ai yau zai zo ko?" "Baba ni bani da masaniya"

Murmushi ya yi tare da cewa "Yaro man kaza, wato ke ana nuna miki annabi kina runtse ido"

Rahina ji tayi baƙin ciki kamar ya kasheta, tayi shiru ta ƙyaleshi kawai.

***

Yana shiga bedroom ya kwantar da Afnan a gado tare da gyara mata kwanciya.

Mommy da take tayi masa magana yaƙi ya amsa sai a lokacin ta shigo "Magana nake maka amma shine ka shareni Ja'afar?"

Jiyowa ya yi ya kalleta ya ce "Mommy dan Allah, dan darajar annabi da al-qur'ani kada ki cigaba da jifana da mummunan kalaman da bani da wani masaniya akai"

"Ja'afar kenan, to mene yasa baka so ayi maka maganar da ta zama dole, ai gaskiya muke son sani, ko kafi son muyi ta zama a cikin wannan masifar?"

"Duk wata cuta maganinta dole sai an haÉ—a da ayoyin Allah, kuma na gayyato malamai za su zo suyi addu'a, za ayi saukar al-qur'ani"

"Sauka har ta nawa za'ayi kenan, zuwan mu gidan nan anyi suka yafi a ƙirga"

"Addu'a ba ta taɓa tafiya a banza, Allah yana tare da mai tawakkali"

"Shikenan, nagode wannan shine ladar haihuwarka da nayi ko Ja'afar? Ba komai insha Allahu na fita sabgarka da kai da ƴarka, domin ba zan riƙa zama ina faɗa kan musa min ba"

"Allah ya huci zuciyarki"

Bata bashi amsa ba ta wuce rai a ɓace.

***

Yana latsa wayarshi sai gata ta fito parlour'n. "Maheer kaine da safe haka?"

Har ƙasa ya tsugunna ya gaidata sannan ya koma ya zauna, itama ta zauna. "Mommy..." Sai kuma ya yi shiru, idanunsa a lokacin har sun kawo ruwa, dan shi haka yake, baya iya jure hawaye.

"Lafiya, me kuma ya faru?" Ta furta idanunta a kansa.

"Mommy ina son Amal, bana jin akwai macen da zata iya jure zama dani kamar ita, Mommy wallahi zuciyata har zafi take idan na tuna Amal"

Tuni annurin fuskarta ya disashe, ta kalleshi ta ce "Maheer ka farka daga nannauyan baccin da kake, domin dalilin wannan yarinyar naji na tsani talaka na tsanesu sosai, kuma ban da wannan ma, ai ita Amal ɗin dan mugunta bata ce tana sonka ba, sai ta haɗaka da Noor kuma Noor mutuniyar kirki ce, kai ko da ma ace bata haɗaka da Noor ba, ni ba zan taɓa aura maka Amal ba domin abin hannunka take so ba kai ba, haka ahalinta gaba ɗaya"

Kallon Mommy yake, da idanunsa da suka gama rinewa ya ce "Mommy meyasa kika faÉ—i haka?"

"Saboda ina da hujja, kuma yanzu zan kawo ka gani" Miƙewa tayi ta nufi upstairs shi kuma ya bita da kallo.

***

A hankali take sauke takunta har ta ƙarasa cikin parlour.

Jidda na zaune tana kallo, hannunta É—auke da glass cup da lemo a ciki.

"Aunty barka da hutawa" Amal ta faÉ—a tare da zama kan É—aya daga cikin kujerun.

"Yauwa Amal ya kike?" Ta faÉ—a fuskarta ba yabo ba fallasa.

"Ina lafiya...?" Sai kuma tayi shiru, kafin ta É—ago ta kalleta ta ce "Aunty dama akwai wani Friend É—ina baya da lafiya, to da...da..d..dama..ina..so..na kirashi na duba jikinsa"

Cak ta tsaya tana kallon Amal kafin ta ce "Amal dama wani ya san za kiyi wannan abin?"

"A'a babu wanda ya sani, ko ƙanwata da muke ciki ɗaya, domin ban taɓa ɗaukar alƙawari kuma nazo na saɓa"

"To kiyi haƙuri, kamar yau ne, abinda ya saka ma bamu tafi ba, abubuwan naki ne da yawa, sai da yayi miki passport ga kuma visa, amma ya faɗa min jibi zai shigo Abuja"

"Tam Allah ya kaimu"

"Amin dan Allah ki riƙe alƙawari please" Kai kawai ta gyaɗa bata sake cewa komai ba.

*Ku riƙa Following da Vote tare da comment a Wattpad*