Shafi Na HuÉ—u
by @sanazty
A CIKIN IDO...
Ake tsawurya
Wattpad @SaNazdeeyah_
Heart touching love story🥰
KARAMCI WRITERS ASSOCIATION
[karamci tushen mu'amula tagari]
Assalamu Alaikum, mun É—auki mutane a group 1 paid group, yanzu still akwai group 2, ki biya kuÉ—i a sakaki domin ki kwashi darussa da nishaÉ—in dake cikin wannan book, saura 1page free pages ya qare, bayan free page su qare babu wanda zai cigaba da karatu ba tare da ya biya ba.
Ga ɗumbin mutanen da suka sayi littafin nan nagode sosai da nuna ƙaunarku a gareni, wanda basu saya ba ƙofa a buɗe take, akwai details a ƙasan wannan shafin nagode sosai masoya makaranta littattafaina ina alfahari daku🥰🌸
```Free Page```
Shafi Na Sha HuÉ—u
_______________Yana zaune ta fito ta ƙaraso har inda yake ta dire masa letter akan cinya.
"Ka karanta ka gani" "Mommy..." "Ka ga Maheer ka fara karantawa sai muyi magana."
A hankali ya buÉ—e jikinsa a sanyaye ya fara karatun.
Assalamu Alaikum! Maheer kayi haƙuri na tafi ne ba kuma zan dawo ba har sai bayan kayi aure, na lura Mommynka na son haɗa mu sai dai ni kuma gaskiya ba zan iya aurenka ba ka mutu ka barni da yaro in ta fama, a gaskiya ban iyawa kayi haƙuri, ita dai Noor da bata sani ba zata iya jurar hakan kuma naga tana matuƙar ƙaunarka ni kuma tsakaninmu abota ce kawai, dan Allah ka manta dani kar kuma ka nemeni daga Amal.
Ƙara ƙurawa takardar ido ya yi, ya sauke ajiyar zuciya a ransa ya ce Duk wanda ya rubuta wannan to tabbas yaso ya kwafi hand writing ɗin Amal. Amma ni na san Amal ba zata taɓa yin haka ba, kenan Mommy ce ta saka aka rubuta? Amma meyes...
"Ka daina wani tunani, Amal bata ƙaunarka Maheer, nina ɓoye takardar dan kar ka gani, amma yanzu na fahimci cewa ganin shine mafi a'ala"
Ya tsinkayi muryar Mommy na faÉ—in haka.
Idanunsa ya É—an lumshe sannan ya É—ago ya É—ora akan Mommy "Mommy naji wannan na Amal ne, amma meyasa kika tsani ahalinta gaba É—aya?"
"Saboda ba su da hali mai kyau, ubansu tun fil azal kowa a unguwar ya san shi mutum ne mai kwaɗayi da leƙen abin wasu, ga auri saki, sannan gidan nan kowa shi yake bawa kanshi tarbiyya, basu zuwa islamiyya ko kaɗan."
"Mommy ki cire Amal a ciki, domin ita da ƙanwarta har sauka sunyi, sannan Mommy babu wanda ya taɓa zuwa yace Amal tayi ba dai-dai ba."
"To ai ita tafi kowa tabo a gidan, domin ita shegiya ce bata da uba"
Runtse ido Maheer yayi yana jin ƙuna a ransa.
"Saboda an taɓo Amal dole zaka runtse ido, an taɓo tsohuwarka ko? To ka sani ba zan taɓa aura maka marar asali ba a hakan ma kana ganin abinda ta rubuto"
Miƙewa ya yi, ya kalli Mommy ya ce "Ba zan iya cigaba da zama da Noor ba, dan haka na turata gidansu, kuma zan aika mata takarda daga baya, dama na jinkirta sakin ne dan in sanar miki"
"Akan wane dalili?"
"Bata da ɗa'a kuma bata riƙe mutuncinta na ƴa mace ba, ni dai na makara a office dan haka zan tafi" Da sauri ya wuce bai jira jin ta bakinta ba.
Yana fita daga gidan kai tsaye ma'aikata ya wuce, sai daya fara sanarwa da secretary ɗinshi cewa duk wanda yazo ace baya nan, sannan ya shiga yayi locking ƙofar, kan three seater ya nufa sannan ya zauna gami da buɗe wasiƙar.
Beauty...! Kayi haƙuri na san zaka zo ka tarar bana nan, sai dai wannan letter tawa, beauty ba zan iya zama in jure ganin ranar aurenka ba. Beauty ban sani ba ko na fara sonka ne daga yarinta ko kuma sai da nayi wayo, amma ni dai abinda zan iya tunawa shine da sonka na tashi na tsinci kaina, a lokuta da dama ina rabaka da ƴammatanka ne domin ni nake sonka kuma ina son nima ka furta min amma sai hakan taƙi yuwuwa, tabbas lokacin da mukaje gurin Mubina na so barinku kuyi soyayya amma sai ka kasa jurar wulaƙancin da tayi min.
Beauty a lokuta da dama na kan zauna nayi kuka domin na san baka sona ban taɓa ganin alamun a tattare da kai ba. Lokacin dana samu labarin kana da blood cancer kuma Mommy na son taga jikanta naso tsatsonka zai fito daga gareni ne amma gaban Likita Mommy ta ce bata son aura maka ni saboda bani da asali kuma ni talaka ce, nayi kuka kamar raina zai fita, ranar ban iya runtsawa ba ko da gyangyaɗi.
Na zaɓa maka Noor saboda ta nuna min tana matuƙar ƙaunarka. Beauty bani na halacci kaina ba, bani nayo kaina a shegiya ba, amma haka ƙaddarata take, dan Allah karka nemeni zan dawo da kaina.
Kuma ina roƙonka da ka sha maganin da za a kawo maka kada kayi sakaci dasu, ina da yaƙinin zaka samu lafiya, ka kulamin da kanka, kada kayi wasa da yunwa, dan Allah. Ina sonka kuma zan cigaba da sonka har ƙarshen rayuwata. Amalul-Islam.
Gaba É—aya ji yayi zuffa ta keto masa, duk da cewa akwai sanyin AC. Cire suit É—in yayi ta saman ya bar ta cikin.
"Innalilahi wa inna ilaihi raji'un Mommy me Amal tayi miki?" Ya furta tamkar zaiyi kuka.
Wayarsa da ta fara ringing ya janyo, ya kalla a hankali, lokacin idanunsa har sun fara canza launi.
"Hello!"
"Meheer"
"Daddy ina kwana" Ya furta a sanyaye.
"Mene ya haÉ—aka da Noor gashi ta dawo mana nan tana kuka.
"Daddy maganar ba ta waya bace, zan zo gidan idan na tashi daga office."
"To sai ka zo."
Few Minutes Later
A hankali ya buɗe idanunsa da suka kaɗa sukayi jajir, jikinsa gaba ɗaya karkarwar zazzaɓi yake.
Da ƙyar ya iya ɗaukar waya ya kira Kamal ya ce ya zo office ɗinsa. Dama tun daya gama karanta letter ɗin ya yi unlocking ƙofar.
"Maheer lafiya?" Kamal ya furta yana ƙarasowa gabansa lokacin daya shigo office ɗin.
"Ka kaini gidan Mommy am sick jikina kamar ana dakashi"
Kamal ne ya ɗagoshi ya riƙe sannan suka fita, aikuwa sauran ma'aikatan aka rirriƙeshi sai da aka sakashi mota sannan Kamal yaja, lokacin kuwa jikinsa kamar garwashi.
"Me yake faruwa?" Mommy ta furta tana ƙarasowa inda suke tare da riƙo shi.
"Yana office É—insa, ya kirani yace baya da lafiya na kai shi gida"
"Maheer...!" Mommy ta faÉ—a tare da fashewa da kuka.
"Kamal kama shi mu kaishi bedroom" Ta faɗa a gigice, tare suka kai shi suna ƙoƙarin kwantar dashi aikuwa ya duƙe a gurin ya fara aman jini.
"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" Shine abinda Mommy ta furta tana zubar hawaye.
"Mommy ko dai asibiti zamu kai shi?" Kamal ya faɗa yana ƙara riƙo Maheer ɗin.
Da ƙyar Maheer ya ce "Mommy ni babu inda zanje dan Allah ku kira min Amal" Ya riƙo hannun Kamal ya kalleshi, idanunsa gaba ɗaya sun zama jajir. "Ka nemo min beautyn-beauty dan Allah, bana so na mutu ban ganta ba, zan faɗa mata ina sonta dan Allah" Lumshe ido ya yi yana sauke numfashi. Mommy cikin tashin hankali ta kira Likita.
30 Minutes Later
Idanunsa a lumshe suke yana sauke numfashi da ƙyar. Doctor ya juyo ya kalli Mommy. "Hajiya, yana amfani da magun-gunansa kuwa?"
"Baya fashi wajen amfani dasu, domin ko bai sha ba ni nake tilasta masa"
"Mommy...Dan Allah ki dawo min da Amal cikin rayuwata ina son zama da ita..!" Ya furta yana daga kwance, yana ta sauke ajiyar zuciya.
"Wacece Amal É—in?" Doctor ya yi tambayar.
"Itace yarinya da muka zo asibiti tare a waccan ranar, kuma sun shaƙu sosai tun suna yara tare suka taso"
"Matarsa fa?"
"Doctor matarsa a yanzu tana gidansu, sun ɗan samu saɓani, kuma ina tunanin hakan ce ta saka ciwonsa ya tashi"
"Ba ita bace, Amal É—in nan ce, ya kamata ku kirata tazo"
"Kamal dan Allah ka kira mana Amal" Mommy ta faÉ—a hankali tashe.
Ajiyar zuciya Kamal ya sauke sannan ya ce "Mommy Amal bata nan, ta gudu fa, kuma bamu san ina take ba"
Miƙewa Maheer ya yi, Aman jini na ƙara zubowa ta baki da hanci.
"Doctor Maheer aman jini yake, shikenan hakan na nufin zan rasa Maheer?" Ta furta tana fashewa da sabon kuka.
Riƙe Maheer ɗin ya yi sannan ya fara danna masa ƙirji. "Ya kamata mu tafi asibiti, wannan aikin ba nawa bane ni kaɗai. Sannan a nemo wannan Amal ɗin koma a ina take.
***
Ya fi mintuna uku a ƙofar gidan su Amal kafin ya samu yaro ya aika a kira masa Rahina.
Badi'a ce ta fito tare da yaron, ganin baƙon mutum ya saka ta fara canza tafiya, ta tsaya jikinsa tana wani rawar kai.
"Ina yini!"
"Lafiya lau. Rahina fa?"
"Ayya ai tana asibiti an kwantar da Mamanta tun jiya"
"Amm...dan Allah ko zan iya sanin wane asibiti ne?"
Tana shirin yin magana sai ga Baba ya fito, aikuwa da sauri ya ƙaraso ganin mutum yazo da jibgegiyar mota.
"Yaro sannu" Ya furta lokacin daya ƙaraso.
Har ƙasa Kamal ya gaishe shi, sannan ya faɗa masa dama yazo neman Rahina ne sai kuma aka ce Mama ce aka kwantar. Yayi masa dubiya ya amsa tare da faɗin "Ya kuke da Rahina?" "Ni abokin Maheer ne nazo ne naji ko anga Amal?"
"Meyasa yaron nan baya ji? Wannan ai ta tafi yawon bariki dawowarta sai Allah"
Shiru Kamal É—in ya yi kafin ya ce "Baba, amma..."
"Kaga dakata samari, kace shi Maheerun yazo da kanshi"
Kamal bai iya cewa komai ba saboda ɓacin rai kawai ya juya ya tafi.
Yana ƙarasawa kuwa Mommy ta tare shi "Kamal ya na ganka ba tare da Amal ɗin ba?"
A sanyaye ya ce "Mommy daga gidansu nake kuma har yanzu bata gida"
Aka Mommy ta É—ora hannu tare da faÉ—in "Na shiga uku, ina yarinyar nan ta shiga?" Kallon Kamal ta yi kafin ta ce "Bana son rasa Maheer ba tare da cikar burinsa ba, zan jingine burina saboda nashi, dan Allah Kamal ka ceci abokinka ka nemo Amal a duk inda take"
"Mommy insha Allah zan yi iya bakin ƙoƙarina" Zama ya yi gefen gadon da Maheer ke kwance yana baccin wahala.
Maheer kana da zurfin ciki, dama ashe har haka kake son Amal ban sani ba, to inda ace na aureta fa? Haba Maheer baka kyauta ba daka ɓoye sirrin dake ranka.
Wannan littafin na kuɗi ne ₦300 regular group ₦500 V.I.P group.
*Zaku tura kuÉ—i ta wannan account 0088814969 Adamu Halima Salahu, Access bank. Ko ku tura katin waya ko VTU ta wannan number *** sannan ku tura shaidar biyan kuÉ—in ta wannan number ****
*Ku riƙa Following da Vote tare da comment a Wattpad*