Shafi Na Sha Biyar
by @sanazty
A CIKIN IDO...
Ake tsawurya
Wattpad @SaNazdeeyah_
Heart touching love story🥰
KARAMCI WRITERS ASSOCIATION
[karamci tushen mu'amula tagari]
Wannan littafin na kuɗi ne ₦300 regular group ₦500 V.I.P group.
*Zaku tura kuÉ—i ta wannan account 0088814969 Adamu Halima Salahu, Access bank. Ko ku tura katin waya ko VTU ta wannan number *** sannan ku tura shaidar biyan kuÉ—in ta wannan number ****
Ƴan Niger kuma zaku tura katin Airtel ko Orange ga wannan number +227 86 33 10 00 kada ku manta V.I.P 750f Regular kuma 500fcfa, sannan zaku tura shaidar biya ga wannan number +227 86 33 10 00
```Na sadaukar da shafin nan ga makaranta wannan littafi na A CIKIN IDO...```
*Last Free Page*
Shafi Na Sha Biyar
_______________Firgigit ta miƙe zaune, tare da dafe ƙirjinta da taji yana mugun buga mata.
Turo ƙofar da akayi aka shigo ya saka tabi ƙofar da ido duk da dai ta san wacece saboda ita kaɗai take shigowa ɗakin, dan ko masu aikin bata ganinsu haka nan a parlour sai da dalili bare bedroom.
"Amal ya dai?" Jidda ta faɗa lokacin da ta zauna gefen gado tare da ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya.
Amal dai sauke hannunta tayi daga dafen da tayi masa a ƙirji, sannan ta kalli Jidda ta ce "Ba komai Aunty"
"Kar fa ki ɓoye min wani abu, idan kina da damuwa ki faɗa min"
Girgiza kai tayi tare da cewa "A"a ba komai"
"Yauwa to dama na zo in tambayeki bayan Amal da wane suna ake kiranki?"
Da mamaki Amal take bin ta kafin ta girgiza kai ta ce "Sunana Amal dashi ake kirana, bani da wani sunan bayan shi"
"Amalul Islam ko?" Ta tambaya tana kallonta.
"Eh..."
"Okay zan riƙa kiranki da Islam, amma a Visa da Passport ɗinki da Jamila Muhammad aka yi amfani, kin san cuwa-cuwa ta Nigeria, dan mijina ba shine ya yi ba, wani ne ya yi shi kawai shi zai karɓa ne. Amal idan na kiraki da Jamila zaki shiga confused amma idan na ce Islam fa?"
Shiru Amal tayi dan ta rasa abin faÉ—a.
"Tambayarki nake idan nace Islam zaki fahimta ko?"
Kai ta gyaÉ—a alamar eh.
"To zan faɗawa mijina hakane sunanki saboda tsaro. Amal ina da zafin kishi fiye da tunaninki, zan iya komai akan mijina dan haka ki kiyaye, ba ruwanki da rayuwarsa in yana parlour to ki haƙura da zaman parlour, iya abinda ya kawo ki, ki tabbata shi kika yi, idan baki raɓi mijina ba to nima baki da matsala dani amma idan kika raɓe shi gaskiya zamu iya samun gagarumar matsala"
A tsorace Amal ke gyaɗa kai kamar ƙadangare, a haka Jidda ta fita ta barta da zulumi.
Tana fita ta miƙe tare da sauka daga kan gadon. Da bango ta jingina tare da fashewa da kuka mara sauti.
Beautynah...! Ina matuƙar ƙaunarka, dan Allah ka kasance a raye har zuwa lokacin da zan dawo, ganinka a cikin wannan duniya ma kaɗai ya wadatar dani ko da ba a aura min kai ba. Ina sonka Maheer amma na san kayi min nisa. Mommy ba zata taɓa yarda mu zauna a inuwa ɗaya ba. Ajiyar zuciya ta sauke sannan ta zauna a dan-dan tiles "Beauty gabana faɗuwa yake ina fatan kana lafiya."
Tafi mintuna goma a zaune a gurin kafin ta tashi ta share hawayenta ta shiga toilet ta É—oro alwallah lokacin sallar la'asar yayi.
***
Da sallama ya turo ƙofar ya shigo ɗakin asibitin inda Maheer ke kwance.
"Mommy ina wuni" Ya faÉ—a gami da tsayuwa gaban gadon.
"Sai yanzu kaga damar zuwa bayan tun É—azu na kiraka"
Kyakykyawan matashi ne fari sol dashi, sajensa a kwance yake luff, ga wani gashi a kanshi tamkar ya yi relaxer, yana da matsakaicin tsayi, sannan yana da ɗan faɗi kaɗan, ya haɗu matuƙa, kana ganinshi ka ga Maheer bambancinsu da Maheer kawai shi Maheer chocolate color ne, sannan kuma Maheer yana da dogon hanci, ƙaramin baki da doguwar fuska, sai dai shi sumarshi bata da yawa kasancewar tana yawan kaɗewa saboda rashin lafiyar da yake fama da ita.
"Yanzu Mahfuz abinda kayi ka kyauta kenan, kana garin nan amma ganinka ya gagaremu, É—an uwanka babu lafiya amma sai yanzu zaka zo?"
"Mommy kiyi haƙuri, wallahi ayyuka ne sun min yawa"
"Yanzu akwai uzurin da yafi namu a gurinka? Maheer fa kana ji na faÉ—a maka aman jini yake, yanzu ko me kake ba zaka ajje kazo ka dubashi ba? Matarka ta fimu a gurinka ko?"
"Mom ban san dalilin da yasa komai ya faru kike zargin matata, Haba Mom wai me tayi miki, tana ƙaunarku fa, kuma wallahi ita bata ma san Maheer baya da lafiya ba, gaskiya bana jindaɗi ko kaɗan"
"Rufeni da faÉ—a kake yi saboda na faÉ—a maka gaskiya"
"Mommy duk zuwan da zanyi sai kin aibata matata, kamar baki so ina zuwa inda kike haba Mommy, amma ba komai ni dai na san ba abinda tayi miki idan kuma ganina ne baki so sai in daina zuwa"
Cikin ɓacin rai Mommy ta kalleshi "Oh haka ma zaka ce Mahfuz to bana son ganin naka ka fita ka bani guri, tunda ka fifita bare a kanmu"
"Shikenan dana san haka zata faru wallahi da banzo ba"
"Yanzun ma ai zaka iya tafiya, ko akwai wanda ya riƙeka?"
Shima cikin ɓacin rai ya kalleta sannan ya kalli Maheer dake kwance idanunsa biyu "Shikenan na tafi kuma zan daɗe baki ganni ba. Bro Allah ya baka lafiya" A fusace ya bar ɗakin.
"Umma ta gaida Assha" Mommy tayi maganar rai a ɓace.
"Mommy...!" Maheer ya faɗa cikin jin jiki, yana miƙo hannu.
Da sauri ta tashi tana goge hawaye ta riƙo hannunsa.
"Mommy bana so na rasaki, ba zan taɓa saɓa umarninki ba, itama Amal naso fitar da ita a raina amma na kasa, Mommy Amal wani ɓangare na jikina ce"
Numfashi Mommy taja, idanunta fal da hawaye, wasu ma har sun samu damar zubowa.
"Maheer na san kana sona kuma ka sadaukar da rayuwarka dan farin cikina, dan Allah ka ƙarfafa jikinka na maka alƙawarin mallaka maka Amal, sam ban san har haka kake sonta ba da banyi koƙarin rabaku ba" Sosai ta riƙe hannunsa da ya ɗau zafi.
****
"Baba sai kiranshi nake bata shiga, nima dama ina so yazo saboda Doctor na nemansa" Rahina ta faÉ—a tana kallon Babansu.
"Hmmm zaki fito ki faÉ—i gaskiya ne, ai ni sam yanzu bana yarda dake, ya zaki ce bai zo tun jiya har yau to yana ina?:
"Wallahi ban sani ba, wataƙila wani aikin ne ya riƙeshi."
"Shikenan, zan tafi amma anjima zan dawo ki cigaba da kira ko za a dace"
Abuja
Tana tsaye daga farfajiyar gidan motarshi ta danno kai ciki. Da sauri ta ƙarasa har yaje ya yi parking a wajen adana motoci.
Yana fitowa tayi hugging É—insa, "My dear you are highly welcome"
A goshi yayi pecking nata sannan ya kama hannunta suka wuce ciki.
"You look so beautiful, extremely extraordinary beautiful"
"Thank you so much my honey, yanzu dai kayi wanka sai kaci abinci ko?"
"Okay babe" Sai da yayi bata kiss a goshi sannan ya wuce bathroom.
Ita tayi serving É—insa yana zaune kan dinning, suna ta hirarsu tana faÉ—a masa yadda tayi kewarsa.
Amal da ta fito daga side É—inta tayo parlour É—an tsayawa tayi turus, ita tama manta cewa maigidan ya dawo. Har zata juya taga ya kalleta.
"Ina yini, barka da dawowa" Shine abinda ta faÉ—a a sanyaye.
"Wannan fa?" Ya furta yana kallon Jidda, É—an haÉ—e rai tayi sannan ta ce "Ita ce Islam da muka É—auka za tayi mana wannan aikin"
"Okay...!" Shine kawai abinda ya faÉ—a.
"Ƙarfe takwas na daren gobe jirginmu zai tashi ina fatan kin gama haɗa komai?"
"We are ready babe, ni fa na fika zaƙuwa da tafiyar nan."
Amal dai juyawa tayi ta nufi É—akinta kawai.
***
Jikinta a sanyaye take jan trolley sam bata son ta tafi, hankalinta gaba É—aya yayi kan Maheer, amma idan ta tuna halin da mahaifiyarta ke ciki sai taji gara ta tafi É—in tunda babu mai taimakonsu.
Ko da suka shiga mota ma ita da Jidda ne a baya, yayinda shi da driver suke gaba. Sam ta lura shi É—in ma ba mutum bane mai sakin fuska, halinsu É—aya da matarsa.
Bayan sun gama komai suna jira time ya ƙarasa a kira jirginsu.
Tana zaune daga can gefensu. Jidda da mijinta wanda har a lokacin bata san sunanshi ba, yana ta hira da matarsa. A haka har aka fara kiran jirginsu sannan suka fara harama.
Tana tafiya kamar wadda ƙwai ya fashewa a ciki. Dama tun fil-azal tana da burin ta hau jirgi taje ƙasa mai tsarki, sai gashi yau zata hau jirgi amma sam bata farin ciki da hakan.
Tana taka steps ɗin taji gabanta ya yi mummunan faɗuwa, wani zazzafan hawaye ne ya zubo mata, ta juyo tana ƙara ƙarewa airport ɗin kallo.
***
Yana zaune daga kan gadon asibitin yana aman jini, yayinda wani ke fito masa ta hanci.
"Na shiga uku, dan Allah Maheer kada ka tafi ka barni."
Ajiyar zuciya yake ta saukewa Idanunsa tuni sun canza launi, ya kalli Mommy "Dan Allah Mommy ki nemo min Amal please Mommy, shine taimakon ta zaki min a yanzu Mommy, ina son na ga Amal kafin na mutu"
Kuka sosai Mommy take, cikin tashin hankali ta fita kiran Doctor.
Har É—an gudu-gudu take, a haka suka shigo ita da Likitan.
Wannan shine ƙarshen FREE PAGE ku biya ku cigaba da karatu. Nagode!
*Amma fa ku sani daga zarar na gama, duk wadda za ta saya complete to ₦1000 ne, ina godiya matuƙa, kuma kiji tsoron Allah in kin saya ke ƙaɗai zaki karanta.
*Ku riƙa Following da Vote tare da comment a Wattpad*