MADUBI

Chapter 1: MAFARI

by @salmaahmadisah

*MADUBI...🪞 *

“The persona effect: A story of hidden identities and betrayal”

*©Salma Ahmad Isah🦋*

*SADAUKARWA*

Wannan littafin sadaukarwa ne zuwa ga Rabi’atu Abubakar (Pinky) A small token of appreciation filled with love from your Lilly, thanks for your support and prayers

~Gaisuwa~

Gaisuwa ta musamman zuwa ga Khadeeja Abubakar Alkali (Khadeeja Candy) a.k.a Oum Namra, Zainab A Baba (Abokiyar Hira), Fatima Ahmad Isah, Amina I. Ibrahim (Nanameera), Jamila Umar (Janafty). Allah ya bar tare.

^°^SHIMFIƊA^°^

Koren maciji ne a ƙarƙashin koriyar ciyawa. Hauwasa suka ce mugu ɗan masara, ana goyonka kana gemu. An ce da ɗan gari akan ci gari! Shin kun yarda da hakan? Idan ka kalli fuskarka a saman ruwan kogin dake gudana, za ka ji tamkar kana kallon MADUBI ne, domin shi MUDUBI kan bayyanar da zahirin abin da ido ka iya gani... Tunanin nazarin suffarka a saman ruwan zai sa ka ɗauka cewa kai ne da kanka a kan ruwan. Kuma hakan ba shi ke nuna cewa babu wasu abubuwa ɓoyayyu a ƙasan ruwan ba. MADUBI na nuna mana zahirin abin da muka yarda da shi ne, zuciya ita ce ma'ajin sirrin kowani bawa. A nan aka samu tangarɗa! Domin kuwa a duniya babu MADUBIn da zai iya haska zuciyar wani bawa. Da ace za a samu, da sharrika da dama ba su wanzu ba, da ace za a samu, da kullika da yawa sun warware, domin MADUBI ba ya ƙarya, ɗan Adam kaɗai ke yaudarar kansa idan ya so. Ta wani wurin abu guda ɗaya ne ya haɗa su, wato kaddarar mahaifi! A wani ɓangaren kuma abubuwa da dama sun bambantasu, duk da maƙasudin kasancewarsu a halin da suke ciki abu ɗaya ne, hakan ba shike nuna cewa idan suka tsaya suka kalli juna a MADUBI ta ko wani gefe kammaninsu za su zamto ɗaya ba. Rikicin cikin gida, wani babban gida da ya ɓoye tarin sirrika masu ban tsoro, waɗan da idan aka bayyanasu ga mai karatu dole ya jijjiga. Murmushin mutanen dake kewayensa shi ne makaminsu. Mahaifinsu ya tarwatsa rayuwarsu da hannayensa, son zuciya da son kai su ne ke kai mutum ga halaka. Ƙawar dake duniya ita ke ruɗar mutane da dama, sukan yarda da abin da idanuwansu ke gani, ba tare da sanin cewa komai da suke gani gaibu ba ne, duk abin da ka samu, wata rana dole ya ƙare. Abu ɗaya ne da ba zai taɓa sauyawa ba, cewa MADUBI ba ya ƙarya...

Page | 1

•°{MAFARI}°•

Haihuwa ita ce silar zuwan ko wani bawa duniya, mutuwa ita ce ƙarshen duk wani abu mai rai... Dalilin mafarin labarin ko wani bawa tana da banbanci da ta saura. Shin! Kun taɓa tambayar kanku ta ina? Yaushe? Tayaya? A wani lokaci labarinku ya fara? Garesu wannan ce amsa, ranar da ƙaddarar naiman magani ta kai kakkaninsu ga yanke hukuncin da sai sun yi nadama a nan gaba...

*Ƙauyen Tulo-Tulo, Yusfari Local government, Yobe state.

*Shekara ta 1989...*

Tun daga saman tilin saharar dake ƙarshen shiga ƙauyen na tulo-tulo, za ka hangi tarin dandazon jama'a a kofar wani babban gida ginin kasa. Kallo daya za ka yi wa tarin jama'ar ka musu kudin goro ka basu sunan masu naiman magani. Ba wai majinyata ne kadai a wurin ba, har da 'yan uwan majinyatan da kowanne a cikinsu ya zo da fatan samun maganin cutar dake damun majinyatansu.

Malam Usman da matarsa Iya Saude, na daya daga cikin tarin mutanen da suka yi wani dogon layi a kofar gidan, wanda idan ka gan shi ba ka ce zai kare nan da gobe ba. Kamar dai sauran jama'ar dake wurin, idanuwansu bude suke kan mutanen da suke fitowa daga gidan ƙasar bayan an sallamesu. Fuska ɗauke da murmushin nasara, domin ko abin da aka zo naima an dace.

Hakan shi ke karawa zukatansu fatan cewa lallai su ma zasu dace, kamar yanda yake ne a kan ko wani majinyaci, duk wurin maganin da zai je gani yake kamar a nan warakar take. Babbar 'yarsu cikin 'ya'yansu mata biyu da Allah ya azurtasu da su dake rike a hannun Iya Saude ce ta yi luuu zata fadi, lamarin da ya ja hankalinta zuwa kan 'yar tasu mai suna Zainab, wadda akewa laƙabi da Jebu. Da sauri ta tarota tare da gyara mata zaman hijabin dake jikinta, kasancewar su ne a layi.

"Me ya faru?"

Malam Usman ya tambaya ganin yanda Iya ke ta kokawa da Jebu.

"Ina ga abin ne ya motsa"

Ta fadi cikin halin damuwa. Malam Usman ya mika hannu ya tallafa mata suka gyara mata tsayuwa suna ta jera mata sannu, duk kuwa da sun san cewa ba a cikin hayyacinta take ba. Yau a ƙalla an kwashe sama da shekara uku ke nan tana kwance tana jinya, irin jinyar dake fitar da mutun a hayyacinsa, ba ta san wanda ke kanta ba, ba ta iya magana, sai dai a kwantar sai dai a tayar.

Magani kuwa babu kalar wanda ba su gwada ba, kuma har kawo yau ba su zauna ba, a na haka suka samu labarin Bogaji Sarkin Mayu. Wanda yake zaune a ƙauyen Tulo-Tulo. Irin labarin da suka samu a kansa na cewar idan an je gare shi ana dacewa yasa ba su yi sanya ba wurin yin takakkiya tun daga garin Kanon Dabo zuwa ƙauyen na Tulo-tulo, zuciyoyinsu cike da fatan dacewa a wannan wuri.

"Na gaba ya shiga!"

Garjejen gardin dake bakin kofar shiga gidan ya faɗi yana duban Malam Usman, wanda ya saki baki yana kallon matar da ta fito tana takawa kan kafafunta ras, sabanin lokacin da ta shiga tana jan kafartata. Cikin hanzari ya tallafawa Iya suka shiga da 'yar tasu, a babban soron dake farkon kofar shiga suka iske wani farin tsoho, zaune kan tabarma, gefe, da dama da hauninsa dika tarkace ne na kayan magunguna. Daga jikin bangwayen dakin kuma ko ina an sakale fatu na dabbobi iri-iri. A dan karamin muhallin da aka bari a gabansa suka zube su ukun, Iya na ta kokarin gyara tsayuwar kan Jebu da ke a langare.

"Alagafarta Malam barka da rana, wannan ita ce diyar tamu da muka kawo, wadda ta gamu da wani ciwo da ba mu san kansa ba tsawon shekaru biyu!"

Malam Bogaji ya ɗaga kai ya kalli Jebu dake jikin Iya, sannan ya miƙa hannu ya dauki tawada ya fara rubutu bisa allon dake gabansa.

"Nawa ne lissafin taurarin haihuwarta?"

Malam Bogaji ya tambaya hankalinsa bisa kan allon da yake riƙe da shi. Malam Usman ya kalli Iya da ita kanta rudani ya cikata, domin wannan abu ne da ba su sani ba, jin sun yi shiru yasa ya dube su.

"Ba-ba mu sani ba Alagafarta!"

"A wace shekara kuma a wani wata, sannan wata rana aka haifeta!"

Wannan kam cikin hanzari Malam ya zayyana masa, shi kuma ya yi amfani da su wurin lissafa taurarin haihuwar tata da yake bukata, sannan ya ci gaba da rubutu bisa allonsa. Hannunsa dake rike da alkalami ya janye daga kan allon, sannan ya kai kan bakinsa yana nazarin abin da yake rubuce kan allon, yayin da Malam da Iya suka zuba masa ido suna jiran jin abin da zai fito daga bakinsa.

Bayan shudewar wasu sakkani Malam Bogaji ya bude idanuwansa a kan allon, saboda shi kadai ya san abin da ya gani, kansa ya daga ya kalli Jebu, sannan ya sake kallon allon, irin kallon da yay wa Jebu yasa Malam da Iya suka dubi juna, domin abu daya ne ya zo cikin tunaninsu cewar ya gano wani babban lamari dangane da jinyar Jebun.

Gyaran murya ya yi sannan ya gyara zama ya dubesu da kyau yana aje allon hannunsa.

"Zainab sunanta ko?"

Da sauri suka gyada kai, cike da mamakin yanda aka yi sunanta na yanka ya bayyana gare shi ba tare da sun furta masa ba.

"Mayu ne suka kamata. Ku godewa Allah, domin yau saura kwana uku a cinye kurwarta..."

"La haula wala ƙuwwata illa billah! Yanzu Malam ina mafita?"

"Akwai mafita, sannan zan iya mata magani, amma akwai sharadi!"

Malam ya gyara zama, cikin sauri yace.

"Ko nawa ne zan biya domin ka mata magani Malam, zan biya ko nawa ne!"

A karo na farko, Malam Bogaji yay murmushi yana girgiza kansa.

"Bana bukatar ko da ƙwandala daga gareku!"

Batun ya kara saka Malam da Iya cikin mamaki, hakan yasa suka dubi juna, kafin suka sake kallon Malam.

"Me... Kake buƙata mu yi Malam?"

"Ina da mata huɗu, 'ya'yana goma sha uku, gaba ɗaya cikin 'ya'yana goma sha uku biyu ne kacal maza, dika sauran mata ne, babban dana shi ne Auwalu, wanda ya kasance direban babbar mota, abin da nake so a nan shi ne ku bawa ɗana aurenta, ta haka ne kaɗai za ku iya biyana ladan maganin da zan mata!"

A lokacin hukuncin wanzuwar kaddararsu ya sauka a doron duniya, wanda yake rubuce cikin lamhil Mahfouz, wanda aka kirkire shi tun kafin a samar da su. Halin da maganar Malam Bogaji ta cilla Iya da Malam Usman, da kuma tunanin wahalar da suka sha ta naiman magani na tsawon shekaru biyu, yasa nan take suka yanke shawara ba tare da sun yi duba ko la'akari da abin da ka iya zuwa ya dawo ba... A lokacin ba abin da suke tunani face lafiyar 'yarsu, ba su bukaci amincewarta ba, domin sun san halinta, sun kuma san yanda take musu biyayya ba za ta taɓa bujirewa ko wanne umarni nasu ba, musamman idan ta ji cewa dalilin naima mata magani yasa suka yanke wannan hukunci.

Nadamarsu ɗaya ce a wannan lokacin, da suka tuna da matashin saurayi Muhammad Sani, wanda maganar aure ta shiga tsakaninsa da Jebu, domin ba dan wannan jinyar da ta kwantar da ita ba, da tuni an daɗe da yin aurensu, sai dai da suka duba suka gani, sai suka gane cewa wata kila Allah ya ƙadarta hakan ne saboda Jebu ba rabon Muhammad Sani ba ce. Dan haka suke kyautata zaton shi kansa Muhammad Sani zai fahimci inda suka dosa a matsayinsu na iyaye.

Abin da suke hange ke nan a nasu bangaren, ba tare da sanin abin da Malam Bogaji yake hasashe ya sha banban da nasu ba Ya yi duba game da taurarin yarinyar, yaga cewa yarinya ce da za ta kai arziki ga duk wanda za ta raɓa, hakan tasa ya yanke shawarar aurawa dansa ita domin ya zamana su za su amfana da wannan arziki.

A halin yanzu Auwalu yana da mata daya da yaransu biyu, kuma ya san halin mafisa irin ta matar Auwalun, wanda ba za ta bar shi ya zauna da wata mace ba bayan ita, sannan shi kansa Auwalun ba zai taba lamunta da batun auren ba. Amma ya tari aradu da ka, domin da zarar ya nuna masa dalilinsa na yin wannan abu tabbas Auwalun zai yi farin ciki da hakan.

A nan aka kulla wannan aure mai cike da tarin rikici, wanda zai haifar da tarin birkitattun lamuran da kai ba zai iya ganesu ba. Wani irin aure na ban mamaki, wanda zai yi albarka, albarkarsa tai yi girma ta samar da inuwar da ko makiyi zai so ya raɓa.

**Bayan Wasu shekaru**

A ƙalla yanzu an kwashe sama da shekaru ashirin da biyar da auren Zainab da Auwalu, a cikin waɗannnan shekarun da suka wuce, babu rana ɗaya wadda Zainab za ta iya bugar kirji ta ce ta ji dadinta a zamanta da Auwalu, ko da yaushe cikin damuwa, takura da bakin ciki take. Ba a wurin Auwalu kadai ba, hatta kishiyarta wadda ba ta da dadin zama ba ta samun kwanciyar hankali sam, kullum da kalar abin da take bijiro mata da shi, duk kuwa da ba gidansu ɗaya ba. Yaranta tara (9) da Auwalu a wannan lokacin, a cikin yaransu tara biyu ne kaɗai maza, dika sauran mata ne, tun daga kan Asma’u da ta kasance ta farko, Kubura, Haulat, Sajida, Hafsatu sai kuma Usman wanda ya ci sunan Malam Usman mahaifin Zainab, daga shi kuma sai ‘yan biyunta Zulaihat da Hindatu, sai kuma auta da Sagir.

Ba za ta ce ba ta samu wani ci gaba a zamanta a ƙauyen Tulo-tulo ba, domin ko hadin kan ‘ya'yanta, da kuma kalar albarkar da iyayenta ke saka mata a ko da yaushe babban ci gaba ne a gareta, wanda ba za ta iya misalta daɗin da take ji a kansa ba, matsawar za ta tuna, domin hakurin zama da take da Auwalu, da kuma biyayyar da ta yiwa iyayenta na yarda da aurensa, ba ƙaramar sadaukarwa ta yi ba, hakan yasa a ko da yaushe iyayenta ke kara kaunarta suke kuma tausayinta.

Allah ya horewa Auwalu, yana samu iya samu, amma idan yasa kafarsa ya tafi Lagos ba sa sake ganinsa sai bayan wani lokaci. Abinci ma wani lokacin sai ta je wurin mahaifinsa, ko mahaifiyarsa sannan take samun wanda za su ci ita da ‘ya’yanta. Sabanin a sashen kishiyarta abin da suka so shi za su ci ita da yaranta.

Tun yaranta na kawar da kai game da abin da suka taso suka ga ana yi wa mahaifiyarsyu, har ta kai ga sun fara magantuwa, a ko da yaushe nusar da su take cewar maganarsu ba za ta sauya komai ba, su tayata da addu’a, domin Allah ya san da su, kuma hakan na cikin kaddarorinsu ne, idan suka daure tabbas za su cinye kaddararsu. Duk wata irin cusgunawa da bakin ciki da take shaka a zamanta a cikin kauyen nan, bai taba sawa ko da sau daya ta yi kokarin fita daga gidanta da sunan yaji ba, kuma ko sau daya ba ta taba bari zuciya ta kaita ta aikatawa mijinta laifin da zai sa ya saketa ba, hakan tasa igiyar aurenta ta fi ta abokiyar zamanta kwari, domin ko sau daya Auwalu bai taba furta mata saki ba, sabanin ita Delu kishiyarta da ya taba sakinta har sau biyu tana kome, yanzu haka igiya daya ce take zaune da ita a gidan.

Duk yadda Delu, iyayen Jebu da kuma su kansu ‘ya’yan Jebun suke so auren Jebu da Auwalu ya mutu, Allah bai nufi mutuwarsa ba sai a wata ranar Talata. Kamar yanda suka saba kama mata aikin gidan, dika ‘yan matan ‘ya’yan nata na ta aikace-aikace a gidan, ciki har da Zulaihat dake da lalurar rashin magana, wadda ta samu asali tun daga haihuwarta, domin ba ta taso tana magana kamar sauran yara ba, sabanin ‘yar uwarta Hindatu, wadda take magana kamar sauran mutane. Wannan rashin maganar yasa mutane ke iya babance Zulaihat da Hindatu, domin babu abin da ya rabasu a kammani, yau ko ciwon kai ɗaya ta kwanta to ita ma ɗayar za ta kwanta, akwai alaƙa mai ƙarfi a tsakanin su biyun. Saɓanin sauran yaran da Auwalu bai taɓa nuna musu soyayya ba, Allah ya ɗora masa soyayyar Zulaihat, duk cikin ‘ya’yan Jebu su tara Zulaihat ce kadai ta san soyayyar uba ga ‘ya’yansa. Wata kila yana tausayinta ne saboda lalurar rashin maganar da take fama da ita, wata kila kuma kawai Allah ne ya fidda ta zakka cikin ‘yan uwanta, irin soyayyar da yake nunawa ‘ya’yan Delu yake nuna mata.

Jebu ta fito daga ɗakinta, ta tsaya a kofar dakin, murmushi ta yi tana duban Zulaihat da ta aje kwandon kwanikan da ta wanke.

“Ki je ki yi wanka ki fara shiryawa kafin ‘yan uwanki su ƙarasa aikinsu ku tafi islamiyya”

Cewar jebu ga Zulaihat, domin tana ji, magana ce bata iya yi kawai, ta daga kai ta kalli mahaifiyar tasu, sannan ta gyaɗa kai alamun to. Cikin hanzari Zulaihat ta nufi daki domin yin shirin tafiya islamiyya, yayin da ita kuma Jebu da suke kira da Mama ta zauna bisa kujerar dake tsakar gidan. Ta kalli yaranta dake aiki a tsakar gidan ɗaya bayan ɗaya, idan ka ɗauke Usman da dama ba zama yake a gidan ba, sai auta Sagir da shi ma ba zaman yake ba, sai kuma Kubura da ta tafi kasuwa, dika sauran 'yan matan na gidan. Wani tunani ne ya zo ranta, irin wadda ko wacce uwa ke yi a kan 'ya'yanta a wasu lokutan. Duk da a ƙauye ta haifesu, duk da akwai jinin ƙauye a jikinsu, duk da ba su da wani mashahurin kyau ta san Allah ya gama mata kyauta, domin ba yadda za ayi ka kalloy yaranta ka ce 'yan ƙauye ne, hakan ya samo asali ne da taimakawar iyayenta da ba su naɗe hannayensu sun barta ita da 'ya'yanta cikin wahala ba, suna taimaka mata da abinci da kuma tufafi da kuɗib yin wata ɗawainiya har ta kwashe tsawon waɗannan shekarun a gidan aurenta, abin da ya riƙe auren nata ya yi ƙarko har kawo yanzu ke nan, domin ta tabbata ba dan iyayenta na tallafa mata ba ba ta san a wani hali suke ita da yaranta a yanzu ba. Sannan ta sani ba sai an faɗa ba, ita jajirtacciyar uwa ce, wadda ta dage wurin ganin ta haɗa kan 'ya'yanta, tana iya bakin ƙoƙarinta wurin ganin rayuwar 'ya'yanta ta kyautata, duk da ba ta da shi sai abin da Allah ya bata.

A matsayinta na uwar 'ya'ya mata, dole ta dage wurin ganin 'ya'yanta sun fito kamar sauran 'ya'ya, renon 'ya mace akwai wahala, ko da ace akwai dafawar uba, ballantana ita da ita kaɗai take kiɗanta take rawarta, ga shi dai rayuwarsu a gidan iyayensu taƙaitacciya ce, amma tarbiyyar da suka samu a wannan lokacin ita ce za ta ja ragamar rayuwarsu har zuwa ƙarshenta, Allah yana gani, kuma ya sani, tana yin bakin iyawarta, domin ganin yaranta sun samu kyakkyawar gobe, me haske, wadda za ta haska maƙiyansu da nata, ta amfanar da wanda yake kallon ba su da amfani, tuni ta daɗe da yayewa kanta damuwar Auwalu da Delu, domin yau aurenta shekara 25 amma babu wani sauyi, sai yaushe za a samu sauyin ke nan? Dan haka ta jingine su a gefe ta tsaya ta fuskanci rayuwa a yadda take. Tun bayan sanda ta amince za ta auri Auwalu bisa biyayyar iyaye ta hango tarin ƙalubale a zamanta da shi, wanda har yau ba su ƙare ba, amma ta sa a ranta cewar jarrabawa ce Allah yake mata ta rayuwa, kuma da taimakonsa za ta cinye...

Yayin da take wannan tunani, wani na gefe yana tsara yanda rayuwar 'ya'yanta zata kasance, domin dalilin da yasa aka aureta ke nan. Don ba ta gama tunanin da take ba, ta ji an rangaɗa kuɗa tun daga zauren farko na gidan, kafin hayaniyar mata ta biyo baya, mamaki yasa dika 'yan matan suka dakata da aikin da suke suka tsaya jiran ganin abin da ake tafe da shi. Jebu ta miƙe tsaye tana faɗin innalillahi wa inna ilaihi raji'un, domin sai da gabanta ya faɗi.

"Mama su waye?"

Sajida ta tambaya.

"Ya za ayi na sani Sajida?"

Mama ta bata amsawa.

"Bari na ga me..."

Asma'u ba ta gama haɗiye maganar ba matan da ke ta rangaɗa guɗa suka fara shigowa gidan ɗauke da kayan "Na gani ina so". A yanda al'adar ƙauyen take, Kayan na gani ina so shi ne abu na farko da saurayi yake fara kaiwa gidansu yarinya idan ya fara ganinta, a matsayin iyayenta sun san cewa yana ciki. Abin mamakin a nan shi ne, duk cikin 'ya'yanta babu wadda take da takamemen saurayi, ba za a rasa ba sai dai ba masu aure ba, duk yadda suke da sutura, kamar matan birni da diri irin na 'ya'yan fulani kuma duk yadda suke isa shekarun auren babu ɗaya da aka taɓa maganar aurenta a cikinsu, kuma hakan ya faru sakamakon Kankansu da ake ikirarin maye ne, shi yasa ba'a auren jikokinsa ko wani daga tsatsonsa. To yanzu wannan kuma daga ina? Sannan babbar ayar tambayar ita ce 'yan uwan mahaifinsu ne matan da suka shigo da kayan.

An ce wai baƙonka annabinka, dan haka ba tare da sun yi ko wace tambaya ba Jebu ta umarci 'yan matan da su samawa bakin wurin zama. Tun da aka zauna, Jebu ban da kallon kayan kawai take, tunani ɗaya ne ya ɗarsu a ranta, wanda bai tabbata ba sai da ɗaya daga cikin matan da suka shigo ta buɗi baki ta zayyana mata shi. Cewar kayan Na gani ina so na Haladu suka kawowa Kubura!.

••Hanyar Kasuwa••

'Yan Mata uku ne suke tafe, kowaccensu riƙe da ledojin dake nuna cewa daga wurin siyayya suke. Hirarsu suke irin ta ƙawaye, kamar daga sama wani mashin, ya faka a gabansu, a tsorace suka dakata, wadda ke tsakiyarsu ce ta sauya fuska ganin Haladu ne ɗaya daga cikin yaran ƙanwar mahaifinta Altine. A fusace ya sauƙa daga kan mashin ɗin, sannan ya nufeta, irin kallon da yake mata yasa ƙawayen nata suka tsorata suka dare suka barta tsaye, yana isa inda take ya finciki hannunta ya soma janta.

Ita ma ba ta tsaya haka nan ba, ƙoƙarin kokawa da shi ta soma kan ya sakar mata hannu, amma ya ƙi, bai saketa ba sai da ya jata har bayan wani gini, ya makata da jikin bango, tana ƙoƙarin yin magana ya zaro wuƙa, take ta haɗiye kukanta haɗe da tsoron da take ciki ta hanyar toshe bakinta, kara wuƙar ya yi a saitin wuyanta, sannan cikin fushi matsananci yana huci yace.

"Idan har kika bari aka ɗaura aure tsakanina da ke sai na kasheki, idan kuma ba ki yarda ba ki gwada ki gani, zan shayar da ke mamaki!"

Kallonsa kawai take da manyan idanuwanta da suka cika taf da hawaye, sun firfito waje kamar za su yi magana, amma ita ta kasa maganar, domin ba ta gane inda kalamansa suka dosa ba. Saƙon da ya zo isar mata ke nan, dan haka yana kammala isar da shi ya janye wuƙar daga wuyanta, ya barta a nan tsaye jikinta na rawar tsoro. Da ƙyar ta ƙarasa gida, Allah kaɗai ya bata ƙarfin halin yin sallama, tana shiga gidan ta ja birki tana kallon mahaifiyarta da 'yan uwanta da suka yi jigim-jigum ga kuma wasu kaya kan tabarma.

Ganin kayan ya tunatar da ita maganar da Haladu, sai a lokacin ta ɗora maganar a mizanin hankali, ta aunata, sannan ta tantance abin da uake nufi, wani sabon kuka ne ya ƙwace mata, kuma sakin kukan da ta yi ya ankarar da su wanzuwarta a wurin silalewa ta yi a ƙasa, kan ka ce me duk 'yan uwanta sun yi kanta suna tayata. Ba ta yi ƙasa a gwuiwa ba wurin sanar da Mama abin da ya wakana tsakaninta da Haladu, sannan ta ƙara da.

"Wallahi ni ma bana son aurensa Mama! Dan Allah ki yi wani abu, kar ya kasheni!"

Shiru kawai Jebu ta yi a sa'ilin, ta bawa ƙwaƙwalwarta aikin gano mafita. Ba ta bari sai safiya ba, a daren ranar ta ɗauki dika kayan da suka kawo ta maida gidan kakansu domin ta san shi ne ya haɗa wannan aure, sun yi mamakin abin da ta aikata, domin a gaban Bogaji ta buɗe baki tace tana so a soke maganar wannan aure, domin ba ta fatan ya ɗauru, tun da yaran basa so, bugu da ƙari shi Haladu ya yi ikirarin kashe Kubura, yanzu idan ya kasheta ɗin, wa gari ya waya? Ita ce da asara, dan ta san ubansu ko a kwalar rigarsa. Abin da ta aikata ba ƙaramin hassala Bogaji ya yi ba, domin ko a cikin 'ya'yansa ba a taɓa samun wanda ya masa hakan ba, hatta mahaifiyar Haladu ba son auren take ba, amma da yake shi be ya yi magana ba ta iya musa masa ba, domin hatta matansa na tsoron ja da maganarsa ko da ba a kan dai-dai take ba. Sannan shi ya san miye dalilinsa na haɗa wannan aure ba, idan ba ta sani ba ya sa an aureta ne domin yana so ta haifa masa jikoki masu irin sa'arta, kuma ta haifa ɗin, dan haka ba ya jin zai iya bari wani da ban ya auri ko da ɗaya daga cikin 'ya'yanta matsawar ba jininsa ne ba. A daren ranar wasu micizai suka baƙunci gidan Jebu, suka hana kowa fita a ranar, har wayewar gari, amma haka suka tafi ba tare da sun cutar da kowa ba, domin da ma ya turasu ne domin su tsoratasu. Ranar da ta gabata da ta yau Jebu ba ta taɓa fuskantar irinsu ba, ita da 'ya'yanta sun ga tashin hankalin da ba su taɓa ganinsa irinsa ba. Haka suka kasance cikin tsoro har zuwa ranar da Auwalu ya dawo daga doguwar tafiyar fa ya yi zuwa Lagos. Da ma abin da Jebu take jira ke nan, ganin ya kwashe kwana biyu ba tare da ya leƙo gidanta ba yasa ta yi takakkiya ta bi shi har gidan Delu, ta sanar da shi abin da Bogaji ya musu ita da 'ya'yanta. Maimakon ya nuna mata cewar zai ɗauki mataki ko ta hanyar zama ya yi magana da mahaifinsa ne, sai ya ƙara mata da cin mutunci, ya kuma koreta daga gidan, ita kuma ta ƙi tafiya, ta durƙusa har ƙasa tana roƙonsa kan ya taimaketa ita da 'ya'yanta, amma ba tausayawa haka bawan Allahn nan ya mata korar kare, sannan ya haɗa mata da saki, duk kuwa da ba ta yi laifin da ta cancanci sakin ba, ya kuma ce ta ɗauke dika yaranta ta tafi garinsu da su, baya buƙatar ko da guda bayan Zulaihat, kuma ta gwammaci ta bar masa sauran da ta bar Zulaihat ɗin da yake so ta bari, domin ita ce kaɗai mai buƙatar taimako a cikinsu, me take da za ta tafi ta barta cikin wannan wahalar, ɗa ɗaya ba ta bar masa ba haka ta haɗa ta tafi da su dika tara. MAFARIN labarin ke nan... *Bayan Shekaru goma sha ɗaya (11)* *Present Day... 4/September/2025* Ƙarfe 04:45 na yamma A gefen titin babban masallacin juma'a, almajirai ne jere, akasarinsu mata ne, wasu nakasassu ne, wasu ma lafiyarsu ƙalau, mutuwar zuciya ce kawai ta sa suke bara. Idanuwan dikkaninsu na kan traffic light ɗin da suke da tabbacin na gaf da tare ababen hawan dake wucewa a kan titin. Daga ɗan can gefe da inda suke a tare, jikin wata bishiya, wata matashiyar budurwa ce zaune kan buhu, ta jingina bayanta da bishiyar, duk da tana sanye da baƙin gilashi za ka iya gane cewa bacci take, yanda kanta ya langare zuwa gefe, ga kuma nannauyan nunfashi tana sauƙewa a-kai-a-kai, bacci take hankali kwance kamar tsumma a cikin randa, yanayin tufafin jijinta kaɗai zai ankarar da me kallo cewar a cikin talauci take rayuwa, tun daga kan doguwar rigar atamfar dake jikinta har zuwa kan hijabin jikinta da kuma takalmanta. Yayin da take shan bacci hani'an a gefe guda kuma traffic light ne ya dakatar da masu ababen, ai take mabaratan nan suka ruga da gudu, haka suke kurɗawa tsakiyar ababen hawan da wasu ma ba su gama gyara tsaiwarsu ba, wasu na tura wasu duk san su samu na kaiwa baka. A ɗari wani yaro da bai haura kimanin shekaru 13 ba ya rugu wurin da matashiyar budurwar ban ke bacci, yana zuwa ya durƙusa gabanta ya soma jijjigata a ƙoƙarin na son ya tasheta a baccin, domin ya san halinta da nauyin bacci kamar Kasa. "Zulai! Zulai! Ke Zulai ki tashi kar ayi ba ke!" Hannunsa da yake jijjigata da shi ta ture tana juya masa baya, ta gyara zamanta a jikin bishiyar tana gyara baki, saboda daɗin baccin take ji. "Zulai! Zulai!..." Yaron ya ci gaba da ƙiranta, amma ko a jikinta an mintsini kakkausa. Ganin ba za ta tashi ba yasa ya nufi wurin da sauran mabaratan ke zama, ya rarumo wata ruba cike da ruwa, wadda bai na san me ita ba, amma san wadda ta tsaye masa, gara ya tasheta, in yaso idan ta tashi ta samu abin da ta samu duk wacce za ayi sai ayi, ba kallon kowa take da gashi ba. Yana zuwa kanta ya buɗe robar ya kwara mata ruwan a fuskarta. Kamar wadda aka ari numfashinta na wucin gadi sannan aka dawo mata shi haka ta ja numfashi ta zabura tana gwale manyan idanuwanta a bayan baƙin gilashin da take sanye da shi. Haki ta soma kamar ta yi gudun fanfalaƙi ta cire gilashin idonta ta goge fuskarta, sannan ta maida gilashin tana ci gaba da hakin dan a tsorace ta farka, a fusace ta miƙe za ta zazzage buhun bala'i. "Ub*n waye da wannan aikin?" Tana juyawa ta ga yaron dake tsaye a gabanta yaba riƙe da roba. "Opay kai ne ko?" "Na fi minti nawa ina tashinki amma ko motsi ba ki yi ba, ga shi nan danja ta tsaya gara ki je ki yagi rabonki kin ga tun safe muke yawo amma ba abin da muka samu, idan kuma so kike ki koma gida Yalwa ta jibgi banza ba ruwana!" Take ta haɗiye bala'in da ta kwanta da shi, na rashin samun kuɗi yau, da kuma wanda ta tashi da shi saboda an tasheta tana tsaka da mafarkin ta yi kuɗi, ta tattara hankalinta gu ɗaya ta damƙi sandarta dake gefe, ta miƙawa Opay ya kama suka nufi wurin yana nuna mata hanya kamar makauniyar gaske. Yanda ta shiga wurin sai ka ce bara za ta yi kamar sauran mabaratan, alhalin ita abin da ya kaita wurin da ban, kuma kafin a bawa ababen hawan damar tafiya sai da ta san ta samu abin da yau idan ta koma gida ba ta sha duka a wurin Yalwa ba. Kamar yanda Opay ya sani cewa sai an yi masifa da da Zulaihat kan ruwan da ya ɗauka sai da aka yi, kafin ya jata suka bar wurin. "Nawa kika samu?" Opay ya tambayeta yayin da suka kama hanyar tafiya gida a ƙafa, yana gaba yayin da yake riƙe da sandarta, ita kuma tana bayansa tana riƙe da ƙarshen sandar, wani murmushi ta saki tana faɗin. "Ban sani ba, amma tsaya mu lissafa" Gefen hanya suka koma, ta fito da kuɗaɗen da ta sata a gaba ɗaya ranar yau, domin kuɗin da take samu a barar ba ya wadatar da zalamar Yalwa ta kuɗi, duk sanda za ta kai mata sai ta sha duka ko zagi, ƙarshe ma ce mata ta yi ko da sata ta haɗa ta samo mata kuɗi idan ba haka ba kuma na lahira ma sai ya fita jin daɗi. Za ta iya bawa wani labarin rashin imanin Yalwa, domin a saninta ta rayu da Yalwa na tsawon shekaru 10, kuma a cikin shekarun goma babu kalar halin Yalwa da ba ta sani ba, tun daga zaman da suka yi a Lagos har zuwa yanzu da suka dawo Kano da zama, tsoron rasa rayuwarta a hannun muguwa kamar Yalwa yasa take sata domin ta kai mata kuɗin. "Dubu goma sha tara da ɗari biyar da naira tamanin!" Ta faɗi tana kallon Opay fuska ɗauke da murmushi, ta sauƙe gilashin zuwa kan hancinta, domin da ma tana sakawa ne saboda ta yi bazata, ba wai dan ba ta gani ba. "To ni yanzu miye kasona?" Opay ya tambaya, ta ƙirgo ɗari biyu cikin 'yan canjikan naira biyar-biyar ɗin dake saman kuɗin ta miƙa masa, wani irin kallo ya yi wa kuɗin sannan ya kalleta. "Me zan yi da wannan?" "Ban gane me za ka yi da shi ba, kasonka ne na baka, ko ba ka so na haɗa na riƙe dika?" Ya kawar da kansa gefe alamun ba ya so. "Ka yi da biredi me yanka-yanka" Ta ce tana maida kuɗin cikin sauran, kamar ba zai ce komai ba sai kuma ya yi sauri ya juyo ya warce kuɗin. "Raba arne da makami!" "Da aka ce ba ka ji!" Ta ƙarashe tana hararsa. "Ke kuma nawa za ki ɗauka?" "Ba zan ɗauka ba, saboda idan na ɗauka Yalwa za ta iya cewa kuɗin ya mata kaɗan, gara na kai mata dika" "To kuma da me za ki siyi abinci yau?" Ta yi dariya. "Ba ga naka kuɗin ba!" Sauri ya yi ya cusa kuɗin cikin aljihun wandonsa, sannan ya tashi ya fita a guje, ya san ba ƙaramin aikinta ba ne ta ƙwace kuɗin da ta ba shi, dan dai wasu lokutan tana da imani. "Miye abin gudu bayan gida ɗaya za mu je?" Ta ce tana miƙewa tsaye riƙe sa sandarta. Ta bi bayansa tana faɗin ya tsaya ba za ta ƙwace masa ba, duk duniya Opay shi ne yaron da ya fi kowa kusanci da ita, ta girme shi sosai, amma kamar abokinta take ɗaukansa. Rayuwarta ke nan, rayuwar da ta san tana da ita, za ta iya cewa ba ta da memories ɗin rayuwarta kafin shekaru goma da suka wuce. Bayan rayuwar da ta buɗe ido ta ga sun fara gudanarwa ita da Yalwa a Lagos kawo yau kaɗai ta sani, ta san cewa Yalwa ba mahaifiyarta ba ce, domin Yalwan ta sha faɗa mata hakan lokuta da dama, sai dai ta ƙi sanar da ita iyayenta na gaskiya, kuma ta kasa tunasu, tunanika iri-iri sun sha karakaini a kanta game da iyayenta, ta kan saƙawa a ranta cewar anya kuwa Yalwa ba matar ubanta ba ce ta gudu da ita take bata wahala? Ko kuma tsintarta ta yi a titi? Kokuma... Ko kuma... Ko kuma, tambayoyi da yawa, har gobe babu amsar ko guda ɗaya. Wasu lokutan ta kan hu a ranta yanzu ina ahalinta? Me yasa ba su naimeta ba? Wannan tunanin ke ƙaryata wancan mafarkin wani lokacin har ya kan kai ga ta yi tunani ita marainiya ce ba ta da kowa. Rayuwa a kudu yasa ɗabi'unta suka banbanta da na saura, a iyaka shekarun rayuwarta wanda za ta iya tunawa ba ta taɓa shiga aji da sunan karatu ba, amma tana jin turanci, sannan tana iya magana da shi, ta iya yarbanci da igbo. Ta san halayen mutane iri-iri, tana da basira da saurin koyo, matsalarta ɗaya a duniya, son sanin iyayenta na ainahi, wanda ba ta sani ba ko suna raye ko sun mutu. ```````````````````````` Tass! Sautin gigitaccen marin da hajiya Lawisa ta saukewa Hindatu a kunci ya fidda sautin. Ba Hindatun da aka wankama marin kadai ba, hatta yaran Hajiya Lawisan dake falo sai da suka mike a zabure. Hindatu ta rintse idonta, sannan ta dafe kuncinta da ya yi ja nan take, abin ka da farar fata, tuni idonta ya fara zubar da ruwan da ba ta sani ba. akwai wani irin marin bazata da idan an maka shi zafin marin ba zai bari ka iya kuka ba, shi yasa ita ma ba ta san hawayen ya fara zuba daga idonta ba. kafin ta gama dawowa hayyacinta bayan marin da ta sha, Hjiya Lawisa ta watsa mata zazzafan ruwan shayin dake cikin kofin hannunta a gaban rigarta fara. Idonta ta sake jimkewa tana jin wata irin kunya, kaskanta da kuma bacin rai lokaci guda na dunkule mata a wuri guda. Ba yau aka fara hakan ba, a tsawon lokacin da ta shafe a gidan tana aiki hakan ya faru ba sau daya ba ba sau biyu ba, ba ma a maganar sabo. “Shegiya matsiyaciya! Har ni za ki munafurta ki ci dunduniyata da kishiyata?” Cewar Hajiya Lawisa a zafafe, har wani huci take, kasancewarta fisattacciyar mace wadda karamin abu ke fusatata, kuma da ta fusata za ta dauki mataki, babu ruwanta da bincike a kan lamari, sai dai daga baya ta zo tana dan da na sani. “Haba Mummy! Me yasa za ki mareta? Bayan ta miki bayani cewar ba abin da kike tunani ya kaita sashin Anti ba, aiki kawai ta je ta mata!” Cewar babbar ‘yar Hajiya Lawisa da ta iso wurin. “Ki rufa mini baki, ba da ke nake ba… har wannan munafukar abar yarda ce? Yau ta fara munafurcin? Sau nawa tana hadani da mahaifinku? Ba dan Allah ya so ni ba kwanaki ba aurena ta so ta kashe mini ba” “Mummy halinki na daukan doka a hannunki yasa kuke fada da Daddy, babu ruwan Hindu a ciki!” Cewar karamar ‘yarta, kallon da ta watsa mata yasa ta ja bakinta ta yi shiru, sai da ta gama watsa mata wani fusataccen kallo kafin ta koma kan Hindatu da har yanzu take ƙame kamar mutum-mutumi. “Daga yau zamanki ya kare a gidan nan, ki tattara naki ya naki ki bar gidan nan, idan kuma kin ki, zan shayar da ke ruwan mamaki!” Ta fadi tana nunata da yatsa. “Haba Mummy! Dan Allah ki yi hakuri, abin duk bai kai haka ba!” “Kin san Allah, kika sake magana sai na kifa miki mari ke ma!” Yarinyar ta ja bakinta ta yi shiru ita ma. Sai a lokacin ta bude idanuwanta da suka sauya kala saboda hawayen da suke zubarwa, har jini ya taru a daya idon nata na barin hagu, ta kalli Hajiya Lawisa. “Allah yasa haka ne ya fi alkairi!” Kawai ta iya furtawa cikin kunar rai da zuciya, sannan ba tare da ta sake kara ko da sakan daya ba ne, ta juya ta fita daga falon. Babu inda zuciyarta ke hasko mata face kawai ta wuce gida, wannan walakancin ya isa haka, yau ko da Hjiya Lawisa ba ta koreta daga aiki ba wannan abin da ta mata ya isa yasa ta hakura da ikin nan har abada, ko nawa ake biyanta kuwa. Kishiyar Hajiya Lawisa wadda duk ihu da masifar da Hajiya Lawisa ke yi yake isa har sashinta ce ta fito ta dakatar da ita ta hanata tafiya, sannan ta bata wasu tufafin ta sauya, kana ta bata kudin abin hawa, ta kuma ba ta hakuri. Da haka ta kamo hanyar komawa gida, gaba daya ranta ba dadi. Babbar damuwarta a duniya ita ce jinyar mahaifiyarsu, wadda ta kwanta jinya tsawon shida, sai dai a kwantar sai dai a tayar. Ba ta amfanuwa sam, magani ba kalar wanda ba ayi ba, karshe sai hakura suka yi suka zubawa sarautar Allah ido. Ta wani bangaren ana alakanta jinyar mahaifiyar tasu da halin da ‘ya’yanta suka shiga na jarrabawar rayuwa, domin a yanzu haka Asma’u tana gida bayan aurenta ya mutu, Haulat da Zulaihat sun bata ba a san inda suke ba. Sajida ta gudu a ranar daurin aurenta da saurayinta da ta fara kawowa a matsayin wanda take so, bayan ta gudu kuma ta je ta auri ɗaya saurayin nata da ta hadu da shi bayan maganar aure ta shiga tsakaninta da saurayinta na farko, tun bayan lokacin da ta gudu ba su sake jin duriyarta ba, Usman wanda a yanzu ya koma Ƙadaggale, yana daya daga cikin marasa jin unguwarsu, ya koma shaye-shaye da sace-sace. Yayin da Kubura ke zaune lafiya a gidan mijinta, yanzu haka yaranta biyu. Sai kuma Hafsatu wadda ta maye wurin Sajida ta hanyar auren Salim, saurayin Sajidan na farko wanda ta ki auransa, ita kuma yaronta daya, sai kuma ita da auta Sagir, wanda duk suke zaune a gidan kakansu Malam Usman, wanda a yanzu tsufa da shekaru suka taba masa idanuwansa ya koma makaho. A halin yanzu suna rayuwa ne ta hanyar dogaro da sana’ar da Ma’u take yi ta ɗinki, da kuma aikatau din da ita Hindatun ke yi, sai dan abin da sauran ‘yan uwanta dake gidajen mazajensu suka tallafa musu da shi, sannan ita ma Iya Saude na yin sana’ar nika, saboda ta mallaki inji wanda ta samu yayin wani rabon tallafi da aka yi a unguwarsu. Duniyarsu ke nan a halin yanzu bayan wadan da take tare da su ba ta da wasu da za ta kira da ahali, domin ba za a bita bashin rantsuwa ba idan tace rabonta da mahaifinta tun ranar da ya saki mahaifiyarsu, shekara goma sha daya baya ke nan, tun bayan da suka dawo Kano ba su kara komawa Tulo-tulo ba, kuma shi ma bai taba zuwa inda suke ba, ba ta sani ba, amma wata kila ya manta cewar yana da wasu iyalan bayan wanda yake da su shi da Delu, ko da yake, ai ba abin mamaki ba ne dan bai naimesu ba, sanda suke gabansa ma ba su da maraba da abokan gabarsa, ballantana yanzu da suka yi nesa da shi, ai sai dai ma hakan ya taimaka masa wurin mantawa da su. Allah ya sani, tun da suka bar Tulo-tulo duk cikin ‘yan uwanta da ma ita kanta babu wanda ya sake tada zancensa ko da a wasa, bayan Zulaihat. Kuma ita ma dan ta yi ba abin mamaki ba ne, tun da ita kadai ce ta san dadinsa a matsayin uba. Saurin ture tunanin ta yi daga kanta, domin tunanin rasa ‘yar uwar tata ba abin da zai kara mata face bakin cikin da kinci… Dakatawa ta yi da tafiya, ta waiga ta kalli bayanta, babu kowa a layin bayan ita, kuma dama da daddare ma ba ganin wulkawar mutane ake a layin ba ballantana yanzu da dare ya yi. Ta sani ba za ta taba samun abin hawa ba a nan kusa, dole sai ta fita babban titi, ga shi tafiyar da nisa, hawayen dakw zuba daga idonta ta share, sannan ta ci gaba da tafiya, tana tunanin yanda za ayi ta sake samun wani aikin, domin zamanta haka ba zai iyu ba, tun da ita ba karatu take ba, kuma ba wani takamemen saurayi gareta ba ballantana tace aure shi ne matsayarta ta gaba, dole ta yi aiki domin tsira da mutuncinta, ba wannan ne gida na farko da ta fara aiki ana korarta ba, ta kasa gane inda matsalar take, da ta fara tuhumar kanta, daga baya sai ta fahimci cewar duniyar ce ta yi karancin mutanen arziki, musamman masu dukiya da suke ganin kamar sun fi ko wani abin hallita daraja a doron duniya… Ba ta kai karshe a tunaninta ba, sanda ta ji karan taka birkin mota a bayanta, kafin ta kai ga waigawa motar da ta taka birkin ta daki wani gini. A razane ta waiga tana dafe kirjinta da yake dukan tara-tara. Domin ta dauka motar kanta ta yo, sakare ta yi tana kallon motar da fitulunta ba su mutu ba, daga nan inda take ba ta iya ganin na cikin motar, saboda babu wani waddataccen haske a layin, kuma ta kasa ci gaba da tafiya, kawai ta tsaya dan ganin fitowar na cikin motar. Amma har bayan shudewar minti guda ba wanda ya fito. To ko dai na cikin motar ya mutu? Ta ji tambayar na yawo a kanta, hakan ya bata kwarin guiwar motsawa dan ta ga abin da yake faruwa. A hankali kamar me tsoron za a kamata ta nufi motar, har ta je gaban motar ta tsaya amma sai ta kasa budewa, saboda tsoron kada fa tarko ne aka hada mata domin a saceta, mugu baya kama. Fadowar tunanin cikin kanta yasa ta yi saurin juyawa danta gudu ta bar wurin. Ba ta yi taku uku ba ta jiyo tari daga cikin motar, hakan yasa ta sake dakawa, ta juyo, wata zuciyar na ce mata ki duba ki gani dai, kila ki zama silar ceton rai, idan kuma kika tafi ya mutu to ke ma kina da kamasho a mutuwarsa. Wata zuciyar kuma ta ce mata ki tafi kawai, dan me ma za ki je ki duba? Wata kila duk shiri ne. Juyawa ta sake yi da niyyar guduwa ta tafi, amma ta kasa, dan har sai da ta tafi din sannan ta sake dawowa a karo na biyu, wannan karon gadan-gadan ta nufi motar, dan ta riga ta yanke cewar komai zai faru ya faru, Allah na gani ai, ba abin da zai samu bawa face yana rubuce cikin kaddararsa. Ta bawa kanta kwarin guiwa da wannan, sanda ta kama murfin motar, zuciyarta daya ta bude kofar, tana budewa wani abu mai nauyi ya biyo kofar. Yaraf mutum ya fado daga cikin motar. Ta kwalla ihun ‘Innalillahi wa inna ilaihi raji’un’ domin ta dauka wani abin cutarwa ne. a tsorace ta kalli kasa, ganin mutum ne yashe a kasa babu alamun rai a jikinsa yasa da sauri ta sunkuya a kansa tana leken fuskarsa. “Bawan Allah!” Ta kira tana leken fuskarsa, amma ba za ta iya cewa ga kammaninsa ba, saboda babu haske sosai. Shahada ta yi, ta yi ta maza ta kama kafadunsa ta zaunar da shi ta hanyar jingina shi a jikin motarsa. “Malam!” Ta kira a karo na biyu tana ta leka fuskarsa, amma ba response. Sai ta rasa ya za ta yi, wani tunani ne ya zo kanta, dan haka ta yunkura za ta mike, bisa ga mamakinta caraf ta ji ya rike tsintsiyar hannunta, hakan yasa ta kara tsorata fiye da da. Ta rikice tana dawo da dubanta kansa, sai yanzu ta fahimci cewa ba wai a sume yake ba, kawai idanuwansa ne a rintse, sannan sai yanzu ta lura da jikinsa ma rawa yake. “Malam kana ji na?” Ta tambaya tana dubansa, cikin rawar baki yace. “Cover my eyes” “Eh?” Ta ce dan ba ta ji me yace ba. “I can’t see, pleace cover my eyes” Ya maimaita. Sai a lokacin ta ji mai ya ce, ta waiga ta kuma waigawa ba ta ga abin da za ta daure masa ido da shi ba. sai kawai ta kama bakin mayafin rigar dake jikinta ta yaga, sannan ta daure masa idon da shi. tana kokarin tambayarsa wayarsa dake cikin motar ta soma kara, ta kalli wayar daga cikin motar, kafin ta mike ta zagaya ta daya bangaren ta dauki wayar. 'Partner' shi ne sunan wanda yake kiran, hakan ya tabbatar mata da makusancinsa ne, ba tare da ta yi shawara ba ta daga ta kara a kunnenta. “Na ce maka kar ka yi tuki da daddare ka bari gobe sai ka tafi…” Abin da aka fara fada ke nan, hakan ke nuna mata cewar ba yanzu aka fara wayar ba. “Am ba shi ba ne” “Wace ce ke?” Na cikin wayar yace. “Ah, motarsa ce ta samu wani karamin hadari a hanya, na same shi a hanya ne” “Yana ina?” “Ga shi nan zaune, kamar ba ya cikin hayyacinsa, dan yace baya gani!” “Ohk yanzu haka kuna ina?” Ta fada masa sunan unguwar, ya tabbatar mata da ga shi nan zuwa, sannan ta sauke wayar, ta mayar masa da wayarsa cikin motar, sannan ta zagayo ta durkusa a gabansa tana kallonsa, har yanzu jikinsa rawa yake, sai ka kalle shi da gaske za ka gane hakan. “Ka dan yi hakuri, wani daga cikin ‘yan uwanka yana hanya zai zo ya daukeka” Ba ta da tabbacin ya ji ko kuma ya fahimci me ta ce, ta dai fada ne dan idan Allah yasa yana jinta hankalinsa ya kwanta din, idan da hali. “Wace ce ke?” Ta ji ya tambaya. “Wata baiwar Allah” Ta amsa masa cikin mamakin kalar tambayar da ya mata, dan a halin da yake ciki ba ta dauka zai iya yi mata irin wannan tambayar ba. “Tafiya za ki yi?” Ya sake tambaya, kamar wanda yake kallonta haka ta girgiza kai. “A’a zan zauna har sai ya zo” “Dan Allah kar ki barni ni kadai a nan” “To” Ta amsa tana masa kallon mamaki. Zama ta gyara tana ta kallonsa, ba wai dan tana iya ganin fuskar tasa ba, sai dan kawai mamaki da kuma tarin tambayoyin da suka cika kanta game da shi, wadda ba ta jin za ta iya furta masa ko da ɗaya ba. sun shafe a kalla minti talatin a wurin daga ita sai shi, ba um bare um-um, lokaci zuwa lokaci take lekawa ta ga ko yana numfashi. Suna nan zaune a wurin mutumin da take tunanin shi ne ta yi magana da shi a waya ya zo, ya dauke shi, sannan ya mata godiya, har ya naimi da ta zo ya rage mata hanya, amma ta ki, ganin shi da yake da mara lafiya ai ba sai ya rage mata hanya ba, da haka suka rabu ita ma ta kama hanyar nasu gidan.

Na san Salmanians ba za ku bani kunya ba.

#SalmaAhmadIsah

#Candy

#Bahadejia

#Madubi

#Hindatu

#Zulaihat

#Tahir

#Fa’ik

#Jabeer

#Sanah

#Nusy

#Lee