Kuncin zuci
by @bintuuu
A hanyarsa na tafiyan yayi dialing numbern Na'ima, har ya gama ringing bata dauka sai ya ajiye wayan a seat din gefensa idonsa na kan titi yana ta tunani, a cikin gari yayi parking gaban wani babban masallaci yayi sallah tukunna, da ya idar da sallahn sai ya jingina da gini a zaunen yayi azhkar dinsa sannan ya miqe, kafin ya qarasa motansa ya sake kiran Na'ima still bata daga ba, da haka ya isa gidan amma sai ya zauna anan cikin motan a parking space, dauko takardun yayi sai ya dago na saman da Mazzy ya bashi last wanda shine dauke da descriptions din kalan alluran da Bilal din ke yiwa Na'ima ada, qura ido yayi a takardan zuciyarsa na karyewa, what if ya cigaba da mata? It could've killed her, sai ya damqe takardan ransa na zafi kawai ya maida duka takardun ma'ajiyansu bai duba ba sauran bal, da ya kulle motan ya nufi side dinsa sai hankalinsa yakai kan motan laila da ke fake at last space cikin jerin motocin dake parking lot din, dauke kai yayi ya wuce part din nasa kawai ya ganta zaune a falon kan kujera ta ta tankwashe kafanta tana danna wayanta, ganinsa yasa tayi murmushi tace "Yaya Ina wuni, ya jikin naka" sai kawai ya gyada kai ya zauna a kan kujeran dake facing dinta yana kallonta, a nutse yace "Waye sa'anki cikin gidan nan da inkin zo bakya shiga ku gaisa" Laila ta sauqe kafanta qasa sai kuma ta danyi stiff bata amsa ba tana kallonsa sai yace "Zan daukeki da mari ina magana kina shiru" da rawan murya tace "Yanzu nazo ai Yaya zan shiga" rai a bace yace "Tashi ki fita daga falon nan, before i loose my temper on you" zatayi magana ya sake cewa "Fita, sannan kada in sake ganin kafarki a side dinnan ever again" ganin kallon da yake mata tayi saurin amsawa da "Toh Yaya, yanzu ma zanje mu gaisa" bai kulata ba ya miqe tareda wucewa upstairs tabisa da kallo ranta na baci, fita tayi daga falon ta nufin gurin motan ta, tasan Husna ce ta kai qararta gurinsa kuma zatayi maganinsu, zasu san ita suka sakawa Ido, gaisuwa ne dai bata ga dama ba kuma baza tayin ba dan Mamma ba sonta take ba tasani kuma alwashi taci duk ranan da burin ta yakai ga gaci sai taso zasuga Ahmad din ma, tana qwafa ta shiga motan taja abarta tabar gidan bata shigan ba, sai da Ahmad yayi wanka ya fito sannan ya sake kiran line din Na'iman ta dauka a sannan, cikin sanyin murya tace "Ina aiki da Mami dazu" yace "I call to tell you zanzo ne" sai tace "Da wuri ai ake zuwa" ahankali yace "Nayi latti kenan Babe" shiru tayi sai ya sake cewa "It's okay, gobe zanzo to" tace "Allah ya kaimu, bari nagama aikin" da haka sukayi sallama ya shirya cikin plain sky blue t-shirt da plain black trouser sannan ya tafi cikin main gidan nasu, part din Mamma ya wuce direct ya sameta nan falonta tareda Ummi last born dinsu suna hira, zama yayi kan kujeran yadan kishingida Ummi ta gaishe ya amsa ahankali sai Mamma ta kallesa anutse tace "Wani abu na damunka ne" sai ya girgiza kai kawai ya gaisheta ta amsa, ta sake cewa "Mahaifinka yadawo dazu yanata kiran layinka baya tafiya" Ahmad da yasan saboda jejin da yaje ne sai yace "Ya dawo garin?" Tace "Dazu sauqarsa kuma kai yafara nema" sai ya gyada kai tareda miqewa zai fita yakusa cin karo da Husna da ta shigo itama sai tayi baya tana gaishesa ya amsa da "Lafiya" ya wuce, shigansa babban falon mahaifin nasa sai bai samesa ba yana cikin dakinsa, Anty kadai ya samu zaune tana danna waya ta dago kai suka gaisa sama sama kowa yayi shiru basu sake cewa komai ba, can Anty ta miqe zata fita sai Baba ya fito dan yaji shigowan Ahmad din, cikin ladabi Ahmad ya sauqa qasan carpet ya zauna sai da Baban ya qaraso ya zauna a kujera suka gaisa, ya amsa sama sama wanda Ahmad najin yanayin amsawan yasan da wani abu, sai Baban ya aiki Antyn ta dauko masa wani envelope daya bari a gefen bedside drawer, suna zaunen Mamma ta shigo falon itama sai Anty ta dawo dawo falon tareda miqawa Baba folder din, aikuwa nan ya budesu ya ciro abun ciki ya zubasu nan gaban Ahmad a nutse yace "Kamin bayanin what I'm seeing here Ahmad, wacece ita? me yasa kake alaqa da ita?" daskarewa Ahmad yayi yana kallon hotunan Na'imansa da akayi linking da maza daga ita sai lingeries, ga kuma takardu masu dauke da rubutu, shi kasa dauka ma yayi sai Mamma ce ta dauka tana fadin "innalillahi wa inna ilaihi rajiun, wannan ai Na'ima ce, yarinyar da Mamin su Faruk ke riqo" rai a bace Baba yace "Daga ina take?" Mamma ta amsa da "Yar nijar ce Alhaji, bakasan yarinyar bane?" yace "Abubakar ya fadamin suna riqon yarinya amma bai min bayani akanta ba, meye dinsu ce?" kafin Mamma ta amsa sai sukaji Ahmad yayi magana kamar me rada "Sharri suke mata" duk suka kallesa sai ya dago kansa yana kallon iyayen nasa yace "Sharri sukeson yi mata, this is not her" Baba yace "Then who is it?" Ahmad ya sauqar da kai yace "Edits ne Baba, dagaske wannan ba gaskiya bane" rai adan bace Baba yace "Har takardun kenan? mamanka tace daga Nijar yarinyar take and it says here that 'yar Adamawa ce ta zauna a Kano, fadamin gaskiya" ahankali yace "Yar asalin Adamawa ce, akwai dalilin da yasa su Abba suka fadi hakan" Baba yace "Kun taba jin asalin dalilin da yasa ta gudu daga gidan?" Mamma ta ware ido "Guduwa kuma, Ahmad meya me faruwa ne?" Baba ya kalleta yace "It says here that barin gida tayi sanadin kamata da akayi da wani a gidan aurenta" Mamma was shocked har Anty, Ahmad dake jin ransa na zafi yace "Baba ba haka bane wallahi, Dan Allah ku yarda dani" sai Baba yace "Ai bawai ban yarda bane, ni tambayana anan shine, kun taba bincike acan garin nasu ko kawai iya maganar bakin yarinyar kukaji kuka yarda da komai?" sai Ahmad ya kasa cewa komai, Baba ya sauqe numfashi yace "I'm not saying yarinyar ba ta gari bace tun da ba saninta nayi ba, but mind you zan aika ni aimin nawa binciken har acan Adamawan, and if i find anything related to abunda ke rubuce cikin takardun nan, Ahmad..bazaka auri yarinyar nan ba, and that's final" shiru akayi falon sai can Baba yace "Tashi kaje" miqewa Ahmad yayi asannu ya bar falon ransa na tafasa, tunaninsa waye zeyi masa wannan zagon qasan, yasani ayanda Mahaifinsa yake, ko yace zeyi bayani toh ba fahimtarsa zeyi ba dan mutum ne me yarda da asalin abu bawai jita jita ba, yasani sai ya aika Adamawan yaji komai sannan hankalinsa zai kwanta, fitarsa ya hango Adam a parking space yana tahowa gurinsa sai ya qi kallonsa ma ya wuce side dinsu, dakinsa ya nufa direct yana tunani aransa, tabbas kawunnan Na'ima zasu fadi abunda ke rubuce a takardan yasani dan ba kudi Baba zai aika wanda zaije din yakai ba, ta qarqashin qasa zai sa a jiyo masa komai, He has to change labarin ko ta yaya ne.
A wannan lokacin tunanin Ahmad daya ne, even if labarin Na'iman gaskiya ne, even if tayi hakan, burinsa ya chanja labarin da zai dawo kunnen Baban ko tayaya ne....
Komawa falon yayi sai ya samu Adam a zaune yana cin abinci a plate, zama yayi akujeran dake facing Adam din yace "Man, ka rakani Adamawa gobe please" Adam ya dago kai yana kallonsa yace "Meya faru?" sai ya sauqe numfashi yace "I'll tell you everything on the way" Adam ya dan tsaya kallonsa sai kuma ya gyada kai tareda cewa "Allah yakaimu goben" da haka sukayi shiru sai can Adam yace "Abinci fa" Ahmad ya girgiza kai yanajin komai na fita aransa...A daren ranan Ahmad ya fara duban flight din da zai kaisu Kano dan da mota yakeson suje Adamawan washegarin, aikuwa gari na wayewa da yaje gaishe da iyayen nasa sai bai samu Mamma a falon mahaifin nasa ba, cikin sakin fuska Baba ya amsa masa kamar babu wani abunda ya faru jiyan har yana dan jan sa da hira game da ayyuka, anan falon ya yi breakfast tareda Adam dan anan ya samesa shima, sai da yaje gurin Mamma ne ya fada mata zaije Kano, tana kallonsa tace "Wani abun ya sake faruwa ne" ahankali yace "A'a tareda Adam ma zanje" jin hakan sai takawo aranta ko batun aiki ne, sai tace "Inka dawo zamuyi magana" yace "Toh" ta sake cewa "Allah ya kare" ya amsa da Amin sannan ya fita tana bin bayansa da kallo..
Cikin 40 minutes suka isa Kano bayan sunyi boarding, a gidan Ahmad dake wata shahararriyar unguwa suka dauki wata motan dan shida Adam din suna da nasu gidajen kusa da kusa anan unguwar, sai da suka dauki hanya Ahmad ya fara yiwa Adam din bayanin komai a nutse, a tunanin Ahmad zuwa sannan zai iya shanye komai saidai har sannan in yana maganan yanajin dacin abubuwan a ransa, yana jin zafin wahalan da Na'iman sa ta sha a rayuwa while yana raye acan wata duniyar, Adam was shocked to hear labarin for the first time, da bacin rai yace da Ahmad "Kuma har yanzu baka koya wa dan banzan hankali ba, Ahmad you need to break this guy, meye Mazzy yakeyi har yanzun" sai Ahmad yace "Za'a samesan soon" ya qarasa maganan yana juya kai dan yasan Adam can be tough but he's as soft as cotton sometimes, ba qaramin aikinsa bane in ya fada masa watarana yaje ya samu yasa an sake Bilal din saboda tausayi, and he's not planning that on Bilal..yana kallon titi ya rinqa tunanin wanda zai iya tura saqon nan har gurin mahaifinsa, who is behind it?
Basu suka isa garin su Na'ima ba sai yamma, ahakan sunyi gudu sosai a hanya dan cikin G-wagon din Ahmad mai smooth din gudu suka tafi, da suka isa garin sai da suka tsaya wasu uzurarrukansu sannan suka dauki hanyar gidan Ayuba, Ahmad bai sha wahalan gano gidan ba dan yana da envelope na information dinsu kawu Ayuban da Mazzy ya hado masa daman, a qofar gidan sukayi parking Adam na bin gidan da kallo ganin yara na tuyan awara da qosan yamma a gefen gidan, fita sukayi sai Ahmad yayi hannu a yaro daya daga cikin yaran dake kofar gidan, aisai duka yaran suka yo kansu suna gaishesu, a nutse suka amsa sai Ahmad yace su yi masa magana da babbansu, gidan suka koma can sai ga Umma Jummai ta leqo yafe da dankwali akanta, dan daskarewa tayi tana kallonsu Ahmad din, sai Adam yace "Ina wuni" da sauri ta amsa tana fadin "Kuyi hakuri Dan Allah bari ayi sauri a kirasa yana kasuwa nan kusa" Adam ya sake cewa "Babu komai, abamu ruwa muyi sallah tukunna" Umma ta amsa da sauri ta koma cikin gidan, yaron da aka aika din kuwa bai dade ba yadawo yace gasunan tahowa, aikuwa ko minti goma ba'ayi ba sai ga kawu Ayuba wujiga wujiga cikin sauri shida Nasirun, dan ko hulan sa bai tsaya dauka ba yataho dalilin ce masa da akayi baqin sunzo da babbar mota, duk a tunaninsa Yayan nasu ne ya dan leqosu bayan shekaru, dasuka shigo zauren sai suka dan tsaya suna kallon su Ahmad din dake sallah anshimfida musu tabarma dama da sallayansu a mota ga ruwan pure water a gefensu da Umma ta aika a siyo musu a plate din silver, dan zama sukayi a bakin tabarman suna tunanin wannan balaraben da ga ina kuma, dan bilhaqqi Ahmad din ya musu kama da balaraben saboda yafi Adam din haske nesa ba kusa ba, bayan su Ahmad din sun idar suka juyo gurinsu sai Ahmad ya fara miqa musu hannu kawu Ayuba ya karba sukayi musabaha, gaisuwa suka hau yi sai ya zamo kamar sune manyan basu kawu Ayuban ba dan bilhaqqi suke ranqwafo da kai cikin biyayya Adam na kallonsu da mamaki, sai da aka gama sannan Adam ya fara introducing dinsu yaqara da a Abuja suke da zama, Kawu Nasiru yace "Ma Sha Allah, can birnin tarayya kenan, ahh ma sha Allah" daga nan Ahmad yayi gyaran murya ya fara bayanin yaga yar gurinsu yana so amma kafin azo wannan fagen yanaso ya fada musu abunda ya faru da ita har zuwa haduwarsa da ita, nan suka amsa da toh cikin ladabi, sai Ahmad ya fara basu labarin da Nafisan ta basa Adam na dorawa a wasu fannin, duk son kudin su kawu Ayuba sai da suka girgiza da Ahmad yace "Ku kawun nan tane ba shakka amma rashin sauraronta da kukayi a lokacin da tazo gurin ku shi kadai zai sa in iya kulleku Billahillazi, dan baku mata adalci ba, da yau an wayi gari yaron can ya kashe ta kuma kunada naku kamashon" Kawu Ayuba ya matse kwalla yana fadin "Tabbas..Tabbas wannan hakane, kaicon mu, baiwar Allah Na'iman ashe abubuwan da suka faru kenan" kawu Nasiru yace "Baza muga laifinta dan bata zo garemu ba lokacin da zata tafin, ba muyi riqo da amana ba, Allah ka yafe mana, Allah mun tuba" Ayuba yace "Ayya yarinyar tawa tana ina yanzu, wallahi ni daman tun da akacemin yaron nan yana shaye shaye nafara dana sanin komai da muka aikata" Adam na hararansu yace "Ai da sai ku bibiyi bayan yarinyar taku tun lokacin, shi fa amanan maraya ta wuce duk tunanin mutum, da kuka bada ita ga Yayan naku ai bawai bakuda haqqin bibiyarta bane, har abada Na'ima amana ce a gareku dukanku" suka gyada kai a tare suna fadin "Hakane, wannan hakane" sai Ahmad yace "Maganar wai an kamata da wani a gidan nata ba haka bane, labarin ba haka yake ba" Kawu Ayuba ya gyada kai da sauri yace "Ai ka gama magana kuma, kuskure kam munyiwa yarinya sosai, in sha Allah sai batun gyarawa, kuma da yardar Allah sai Abdullahi ya gamu da bacin ranmu matuqa" Ahmad ya gyada kai tareda jawo wata babbar jaka ya rinqa ciro kudi bunch bunch yana ajiyewa agabansu kawu Ayaban, da mamaki suke kallon tulin kudin da tun da aka haliccesu basu taba ganin me yawan sa ba, saida Ahmad ya gama jera musu kudin sannan anutse yace "Ga wannan kuyi hidima da ita, yaran ku kuma ni zanji da karatun su dan neman ilimi yakamata suyi ba abunnan da sukeyi a kofar gidan ba" atare suka amsa da "Allahu Akhbar, mungode mungode bawan Allah, Allah ne kadai zai biyaka" ya gyada kai ya sake fadin "Gidan nan naku ma zan turo ajida komai in Sha Allah, amma banason batun zuwana gurinku yaje kunnen kowa" Nasiru yace "Daga nan mun binne komai da yardar Allah" yace "Kawun nawa zai maida ita kano, ni kuma zan sanar daku ranan sai kuje can ayi komai daku" Ayuba yace "In sha Allahu damu za'ayi komaii, Abdullahi dai yaji kunya" Ahmad yace "Ni dai burina kar in sake jin sharrin da aka mata yana tashi a garin nan, batayi ba toh kowa ma yasan da batayin ba" da ladabi suka amsa da "In sha Allah" sai Ayuba ya sake cewa "Yanzu 'yar tamu har qasar bature taje, Allahu Akhbar Allah mai yanda yaso, kaima halan baturen na ko" Ahmad yayi murmushi sai Adam na murmushin shima yace "Baba ai dazu na fada muku a Abuja muke da zama, muma Hausa Fulanin ne kamar ku, amma ruwa biyu ne shi wannan din" Ayuba yace "Toh toh nima dai nace, dan tun zuwan naku nake tunanin hakan ganin hasken nasa da nayi" da haka suka miqe zasu fice ashe Umma Jummai na bakin soron ta cikin gida, sai ta leqo tana zuba gaisuwa kawu Ayuban yace "Maza kira Abida tazo su gaisa" ta amsa da toh Malam sannan ta koma cikin gidan, kawu Nasiru yace "Nima da nace ko in yi magana a tawa iyalin tazo ku gaisa tunda yanzu duk anzama daya ai" Ahmad na murmushi yace "Hakane in sha Allah zamu dawo ai, munason zuwa masauqi ne a gobe da safe mu juya" suka amsa da badamuwa, sai da Ahmad ya tabbatar an shigar musu da kayan abincin da ya ciko booth din motan nasa sannan Adam ya tada motan bayan sunyi sallama suka tafi...
A washegarin ranan su Ahmad suka koma Abuja yana jin nutsuwa na shigansa, dayake fitan asuba sukayi sai ya kasance zuwa la'asar ma sun isa gida, sai daya yi wanka ya nutsu sosai sannan ya kira line din Na'iman, a lokacin tana gyaran wardrobe din Mamin sai ta amsa tareda maqala wayan a kafada ta cigaba da linke kayayyakin, a nutse suka gaisa, cikin sanyin murya tace "Ina ka shiga haka, line naka baya tafiya dazu" ya amsa da "Na danyi tafiya ne, dazu na dawo" sai sukayi shiru, can yace "Babe zanzo zancen yau" murmushi tayi tace "Baka manta ba daman", shiru taji yayi sai can ta dago wayan taga be katse ba ta sake maidawa kunnenta tace "Don't even say what's on your mind Ahmad" dariya ya fara yace "Ni me nace kuma?" tace "Uhm uhm nidai, sai kayi shiru haka kake fado magana babba" yana dariya qasa qasa yace "Sharri zakimin Babe" tace "Uhm" sai yace "Toh bari zan bari sai ina kallon ki ido da ido zan fadi maganan" cikin shagwaba tace "Nidai banasoo" nan Ahmad yaji babu abunda yakeson gani kamar ita a wannan lokacin, cikin kwantar da murya yace "Babe sai lallai dare ake zuwa, nifa zanzo da yamman nan" tana murmushi tace "Zan tambayi Nafisa ko ana zuwa da yamman" sai yace "Ki bari Babe zan tambayi Adam inji ya akeyin abun gaba dayansa" shiru sukayi Na'ima bata daina jera kayan ba, can kuma ahankali Ahmad yace "Na'eemah" ta amsa da "Uhm" ahankali, yace "Sau nawa yayi miki alluran nan abaya?" sai ta danyi stiff, cikin sanyinta tace "Bazan iya tunawa ba, amma tana sani bacci sosai da rashin qarfin jiki" ahankali yace "I'm sorry Na'eemah" ta gyada kai kawai batace komai ba, yace "I'm never letting you go, in sha Allah it's you and me on this boat kinji, we'll keep padding it har zuwa inda Allah zai kaimu madakata" hawaye na zuwa idonta tace "And I'll be right there with you Ahmad, I'll be there in sha Allah" .
Bayan sun gama wayan sai Na'ima taje dakin Nafisa ta sameta tana kallon wani series a laptop dinta, zama tayi a bakin gadon tana gani sai Nafisa ta dan dago kai tace "Dazu Netflix suka sake new episodes" Na'ima tace "Ni namanta ma password din Netflix account din naki, ki bani in kalla nima" Nafisa ta harareta tace "Ai na gama yin premium subscription dake Bobo, asarar kudin nakeyi kawai bakya ganin komai" Na'ima na dan dariya tace "I promise zan gani this time, kiyi hakuri Anty Nafisa" ta wani tabe baki tace "No no no...kema ki bude naki account din my dear" dakyar Na'ima ta lallabeta sannan ta sake bata password din, dan in tace zata bude nata account din batasan wane film zatayi searching ba saboda Nafisa nada su dayawa a account dinta, sai da suka nutsu sannan Na'ima tace "Nafisa wai Yaya Ahmad ba..uh.. yace wai zezo gurina yau" sai Nafisa takai hannu tayi pausing kallon sannan ta miqe zaune tana kallon Na'iman tace "Zuwa as in zance kenan kadai" Na'ima ta kauda kai tana murmushi, sai Nafisa ta fashe da dariya tace "Wohoho Na'ima kuna kasheni" har sannan Na'ima bata juyo ba tana murmushi sai Nafisan ta sake cewa "Toh muje ki fadawa Mami, sai mu je muyi girki, wani kaya kike planning sakawa toh" Na'ima ta juyo tana dan dariya tace "lalala abun har babbane haka, ni bawani girki da kaya" Nafisa ta mata hararan wasa tana dariya tace "Kin isa ma, ai in saurayi zai zo zance haka akeyi dalla, taso muje gurin Mami tukunna" Na'ima ta girgiza kai tana fadin "nyi bazan iya fada mata ba Nafee" kawai Nafisa taja hannunta suka tafi gurin Mamin dake can main falon gidan tareda Abu, zama sukayi a kujera kusa da kusa suna facing Mamin, itama tana kallonsu tace "Meye kuke kallona haka" Nafisa ta kalli Abu tace "Ka bamu guri Malam" yana murmushi yace "Ai sai naji komai" Nafisa tace kalli Mami tace "Mami kingansa dai ko, kice ya bamu guri manyansa zasuyi magana" dan murmushi Mamin tayi ta juya gun Abu tace "Toh kaji manya ne zasuyi magana wai" yana dariya ya miqe yace "Yes Mami" sai da ya fice Mami tace "Toh manya i'm all ears" Na'ima tayi murmushi tana duqar da kai sai Nafisa tayi dariya tace "Kaii Mami" tace "Nidai ina sauraronku, meya faru da yaran nawa yau" Nafisa tace "Dama Na'ima ce zatayi baqo anjima da dare, shine mukazo fada miki" sai Mami ta kalli Na'iman tana murmushi sanin waye baqon sannan tace "Ma Sha Allah Habibti, Allah ya kawoshi lafiya" Nafisa na murmushi tace "Mami ina tunanin muyi fried rice ko me kika gani" sai tace "Hakan ma yayi amma sai ku qara da snacks, akwai ganyen zobo jiya lantana ta siyo kaman yana store, ko kuma kunada wani juice din in mind?" Nafisa tace "Eh Mami, zamuyi na pineapple sai mu hada da zobon" tace "Badamuwa, ki bude falon baqin ku gyara" Nafisa ta amsa da toh itadai Na'ima tayi shiru tana murmushi qasa qasa ganin Mami sai fara'a take mata..Aikin abinci suka hauyi harda na gidan gaba daya, basu suka gama ba sai bayan maghrib, bayan sunyi sallah sai Na'iman tayi wanka tana fitowa ta samu Nafisa kwance kan gadon nata tana danna waya, dagowa tayi tace "Bobo an kiraki a waya" ta gyada kai tana gyara zaman towel din jikinta ta dauko wayan, Ahmad ne ya kirata sai tabi bayan kiran, yana dauka suka gaisa yace "In nayi sallahn isha zan iso Babe" tace "Allah ya kaimu" da haka sukayi sallama ta bangaren Ahmad shima bayan yayi sallah tareda Baba da Adam a masjid suka dawo gidan tare, zama Adam yayi a falon tareda debo abinci a dining ya kunna kwallo yana ci sai Ahmad ya wuce sama dan ya shirya bai dade ba ya sauqo yana gyara link din hannun white jamfan jikin sa yanata tashin qamshi, ya karyo hulan nan aka kamar wani sabon ango, Adam ya bishi da kallo yace "Sai ina haka da daren nan" Ahmad ya fara duban car key dinsa anan kan table bai kallesa ba yace "Zanje gurin matar da zan aura" Adam ya hangame baki yana dariya yace "Kut this guy bansan ranar da zaka daina bani mamaki ba" Ahmad yayi murmushi kawai yana gyara zaman hulansa, sai Adam ya sake cewa "Toh ai da aboki ake zuwa, sai ayi introducing dinsa shima" Ahmad na kallonsa anutse yace "Sai mu zauna tare kaima kana kallonta kenan" Adam yayi dariya yace "A'a bayan hakan ni zan tashi in baku guri ne, kaga ma tunda gidanmu ne sai in tafi gurinsu Mami nima" Ahmad ya girgiza kai yana nufan kofa yace "Kayi zamanka bana buqata, zuwa wani lokacin sai kaje ka gaida su Mamin" sai Adam ya bishi da kallo yana dariya, shi abun ma burgesa yayi, finally Abokin nasa yasamu muradin zuciyar tasa..
Da Ahmad ya fita kafin ya qarasa parking space motan Abba ta shigo compound, PA dinsa ya kawosa gurin kiran da Baba ya masa, qarasawa Ahmad yayi gurin su sai Abba ya miqa masa hannu sukayi musabaha Ahmad din na gaishesa cikin ladabi, da haka Abba ya nufi bangaren Baba da kofan falonsa ke nan compound din ba sai an shiga cikin gidan ba, sai da Ahmad ya gaisa da mataimakin Abban sannan ya shiga tasa motan ya bar gidan, da ya isa ma acikin gidan yayi parking sannan ya kira Na'ima tana dauka anutse yace "Babe gani a parking lot" tana tsaye gaban madubin tace "Mami tace mu gyara maka dakin baqi ai" yace "Okay dear" da haka ta kashe wayan tana kallon kanta a madubin, shirin atamfa peach color tayi wanda ya haska fatarta sosai ya fito da kyawunta, sai ta dauko lip balm ta shafa kadan sannan ta dauki mayafi, da ta tashi fitan sai ta leqo kanta corridor tanajin kunyan haduwa da mutan gida kuma, Jiyo tashin muryoyinsu tayi a falon Mami dake gefen dakinta sai ta fita ahankali ta nufi falon baqin dake next to main falon gidan dake qasa, sai da ta isa bakin qofar kuma ta kasa shiga can kuma ta daure tana murmushi ta tura qofan ahankali ta leqo kanta har sannan tana murmushi, idonta ne ya fada cikin nasa yana zaune a kujera hannunsa riqe da waya, ba qaramin kyau taga yayi mata ba cikin fararen kayan, yana murmushi shima sai kallonta yake yace "Babe bazaki shigo ba" tana murmushin ta fara takowa cikin falon kanta a qasa sai kallonta yake zuciyarsa na isa gareta....